Skip to content
Part 29 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Sosai Fatima ta samu sauki, kawai dai ba ta koma gidanta ba ne, sai ta yi arba’in.

Ita kanta ta ji dadin hukuncin Mama, saboda gidan ba kowa daga ita sai Ummi, Ummi ma da dare ne kawai suka fi zama tare.

Amma a nan kam ku san kullum gidan cike yake, wannan ya shiga wannan ta fita, hakan yana debe mata kewa, hade da rage mata wasu tunanin, musamman a kan mutuwar Alhaji, da take ganin kamar ita kawai aka yi wa mutuwar.

Dama-dama yanzu Ya Jamil wata irin kulawa yake ba ta ta musamman, da ace tun farko ta samu wannan kulawar ta ba ta ki karbar tayin Mama na auranshi ba.

Idan zai shigo gidan sai goma, sai ya neme ta, ga wata shakuwa ta musamman tsakaninsa da Hana, abun yana mata dadi sosai, Abban take kiranshi, shi ma kuma ta amsa sunan Abban a wurin ta, soyayyar uba da ƴa yake nuna mata. Shi ya sa ku san ko wane lokaci ta manne da shi.

Falon Mama a cike yake da zuriyarta, Aunty Hauwa, Aunty Ayyo, Jamil, sai Aunty Lami da ta zo daga Katsina kan maganar bikin Zainab.

Duk abin da suke tattaunawa Fatima tana jin su, uffan ba ta ce ba, har sai lokacin da Aunty Lami ta ce “wai shi kuma Jamilu ace duk matan da ke Nigeria saboda Allah Mama bai ga matar ba sai a Indiya?”

Ba Fatima ce kawai ta kalle shi ba, kowa a dakin sai da ya kalli inda yake zaune.

“Ummm! Ke ma dai kya fada, wai an yi wa ƴa mugun miji” cewar Aunty Hauwa cikin rashin gamsuwa da abun.

Aunty Ayyo dai ba ta ce komai ba, illa raba ido da take yi tsakanin mutanen da ke cikin dakin.

Nisawa Mama ta yi kafin ta ce “Ni gaba daya ma kaina ya kulle ai.”

“Kun san an ce matar mutum kabarinsa, dalilin da ya sa Ya Jamil zuwa karatu ƙasar indiya kenan” Aunty Ayyo ta fada hade da bin su da kallo.

Aunty Lami ta ce “Ke da Allah can, yanzu haka hwa ma irin yan kauyen nan ne da talauci ya yi masu yawa take neman mahwaka, shi ne ta makale mishi, shi kuma yake ta karaswa wai zai auri Indiya.”

Karon farko da Fatima ta tintsire da dariya mai sauti, ya zuba mata idanunshi da suka sauya launi zuwa bacin rai, dalilin da ya sanyata yin kasa-kasa da dariyar tana kuma sauraron Aunty Hauwa.

“Kamar kina wurin Lami, ko kuma irin tsaffin nan. Ka ga ka rufawa kanka asiri ka dawo cikin dangi ka yi auranka,”

“A toh! Ka hita batun wata ba’indiya can.” cewar Aunty Lami idon ta a kan Jamil.

Shi dai ban tanka ba, kamar ma baya cikin falon.

“Ikon Allah! To wai ku ina ruwan kallo da gajiya? Na ga daga kwance ma ai yi ake yi, ku kyale shi ya yi auranshi, ko ba komai a haifo mana yara kyawawa masu gashi” Aunty Ayyo ta kuma fada cikin salon tsokana.

“Ke wasa kika dauki lamarin.”

“To Aunty Lami tun da yana son a bar shi, kuma ita ma tana so, kodai koren yunwar ne ai na ga ba ruwan mu.”

“To wai tana sallah kuwa?” Mama ta katse maganar Aunty Ayyo.

Duk sai suka mayar da hankalinsu a kan Jamil

“Hala ba ka ji?”

“Amma ai ta ce za ta musulunta” ya amsa Aunty Lami kamar ba ya so.

“Umm! Ni kam bari in tafi gida ma, Allah ya tabbatar da alkairi” Aunty Hauwa ta fada a lokacin da take ta shi tsaye.

Har ta fita babu wanda ya kara cewa komai, Jamil ma sai ya bi bayan ta.

“Wai Mama amincewa za ki yi”

Cewar Aunty Ayyo hankalinta a kan kofa.

Tabe baki Mama ta yi hade da fadin “Kamar dai a garin gaba-gaba Maryam, ace duk matan da ke garin nan sai Jamilu ya tsallaka Indiya, ni ko Sandamu bana fatan ya tsallake a neman matar aure.”

“A toh!” Aunty Ayyo ta yi maganar hade da karyar da wuya gefe.

“Munahika” Aunty Lami ta fada hade da aika mata da harara.

“Me na yi na mufunci kuma?”

“A gabanshi ai cewa kika yi matar mutum kabarinshi ko?”

“Ku ji Aunty Lami, to ni na fara fadin matar mutum kabari sa? Kawai share masu fili zamu yi, su yi ta yi Laaadhifattta… “

Maganar Mama ce ta hana Aunty Lami fadin abin da ta yi niyya “Duk ga wadda ta ja min wannan watsiyar nan gayyar sauro”

Fatima ta waro ido a kan Mama ganin yadda take ta aika mata da harara “Ni kuma me na yi?”

“Da tun farko kin yarda da auran Jamilun me zai hada mu da wannan galudayar tallar tsintsiya ba dauri.”

“Kuma dai” Cewar Aunty Lami cikin mamaki.

“Wai ni Mama ma ba takaba kike yi ba?” Fatima ta yi maganar hannunta a kan haba

“an hana magana ne” Mama ta tambaya ita ma idonta a kan Fatima.

“Amma dai ai babu kyau tuna abin da ya wuce, na gani.”

Tsoki Mama ta ja hade da jan carbin da yake hannunta, wanda ita kanta ba ta san me take fada ba.

Aunty Ayyo ta kwashe da dariya “Gidanmu gidan shagali, wannan shi ake cewa maganar Kano jikar kanwa, kanwa jikar magana.”

Tare da Aunty Lami suka kuma yin wata dariyar, Fatima kam fita ta yi zuwa dakinta, dama Ummi ta kwaso masu kayan da ta wanke, kuma ba ta ninke ba, ta tafi islamiya ita da Hana.

*******

Da yake yau Juma’a ce, tun da Mustapha ya fita misalin 12pm bai dawo gidan ba, sai yanzu karfe 8pm daidai.

Kamar kullum garin akwai yanayin sanyi kadan-kadan, kofar dakin Blessing ta faro kallo da yake a kulle, sannan ya karasa ta shi kofar.

Ya san ko 10mns bai yi za ta shigo, musamman yau da ta yi dauriyar rashin kiran shi tun da ya tafi, abun mamaki har ya share mintuna talatin bai ji alamun ta ba.

Ya san kuma tabbas ba ta isa yin bacci ba, ganin har kusan 40mns babu ita sai ya kira lambarta, shigar ke da wuya kuwa ta daga murya kasa-kasa.

“Are you alright?”

“No. I’m not” ta amsa shi a hankali.

“Kina ina?”

“I’m in my room”

“OK.” ta amsa hade da mikewa ya nufi dakin nata.

Shiru tsakar gidan, idan ka dauke sautin karar TV, da yan kide-kide, wanda a lodge din ba bakon abu ba ne, sai dai idan ba wuta.

Kofar a bude take, shi ya sa ya shiga kai tsaye.

Kwance take lullube da bargo mara nauyi, shigowarsa ya sanya ta bude fuskar ta.

“Good evening” ta fada cikin karfin.

Bai amsa ba ya ce “What’s wrong with you?”

“Cikina ke ciwo, sai kuma headaches kadan-kadan.”

“Kin je clinic ne?”

“Ban iya zuwa.”

“Shi ne ba za ki nemi taimakon wani ba, let assume ba na nan, za ki gaba da kwanciya a nan har ki mutu” cikin fada ya yi maganar.

Ta yi shiru kamar za ta sake mishi kuka ta ce “Sorry”

“Sorry for yourself I beg”

Duk suka yi shiru, yana kallon yadda take ta murkususu a cikin bargon, kamar bayan mintuna biyar ta yaye bargon, a dudduke ta shiga toilet, daga inda yake tsaye yana jin yadda take ta kwarara amai.

Ba shi da wani zabi illa ya bi ta zuwa ciki, koda ya shiga ma, sai ya rasa me zai yi mata, don haka ya ci gaba da tsayuwa har ta gama aman, ta dauraye bakinta, ya dan kauce mata, ta wuce. Yaraf! Ta fada kan katifar hade da mayar da numfashi.

Shiru ya yi a kofar toilet din yana tunani, bai kamata ya bar ta haka har zuwa wayewar gari ba, bai san abin da zai faru cikin dare ba.

Amma kuma fita yanzu ma waje goma sauran nan akwai damuwa, kasancewar a cikin lungu suke.

Ga shi ba shi da kudi isassu a hannunsa.

Amma kam zuwa asibiti shi ne mafitarshi.

Da wannan tunanin ya fito dakin zuwa bakin hanya, sai da ya bata kusan 20mns sannan ya samu napep.

Lukman da shigo dakin juye-juye kawai take yi a tsakiyar dakin hade da dafe cikinta da hannu biyu.

Sorry kawai yake aika mata, har zuwa lokacin da yi shiru a kwance, alamun cikin ya lafa.

“Za ki iya tashi ne mu je hospital, napep na jiranmu”

Ba ta amsa ba, amma ta shiga kokarin tashin kamar yadda ya bukata.

Doguwar riga ce baka, irin mai walkiyar nan a jikinta, wanda hannayenta suka tsaya a kan shouldernta.

Hular net ta lalubo hade da riga top mara nauyi ta dora.

“Let’s go.” ta yi maganar hade da mika mishi possernta.

Duk yadda bai so taba jikinta ba, dole sai da ya rike ta, saboda ya fahimci ko wane lokaci za ta iya faduwa.

A cikin keken ma da ciwon cikin ya kuma tasowa, kan jikinsa ya janyota, saboda zamewa ta yi zuwa ba tare da ta sani ba.

Private hospital suka je ma fi kusa, ba jimawa aka basu gado.

Daga karshe dai Ulcer ce da typhoid ke damunta.

Mustapha shi ya yi komai na asibitin, sannan shi ya kwana da ita.

Da safe ya dawo gida don nema mata abin da za ta karya.

Misalin karfe tara ya kuma komawa asibitin, tare da wasu daga cikin ƴan lodge din nasu.

Fate ce ta hada mata tea, bayan ta yi mata brush, ita ce kuma ta ba ta tea, yayin da sauran ke ta yi mata sannu.

Basu bar asibitin ba sai 10am. Sai a lokacin ne take fadawa Mustapha Mamanta da sisternta suna kan hanyar zuwa.

Cike da mamaki ya ce “Kin fada masu ne?”

Kai ta daga alama eh.

“Kina da matsala, taya za ki taso mutane daga Maiduguri fisabilillahi, bayan ma kin ji sauki”

“Tun jiya ne fa na fada masu, and I want see them, almost 2months ban gansu ba.”

Bai amsata ba, illa ciro wayarshi da take ringing a gaban aljihu.

Ganin Fatima, sai ya yanke kiran, tun dazu ya kirata, ba ta, daga ba, kila ba ta kusa sai yanzu ta ga kiran.

“Barka da safiya” Ya fada bayan ta daga kiran.

Ita ma ta amsa hade da gaishe shi, ya tambayi su Hana da Ziyad da kuma sauran mutanen gidan.
Daga suka shiga tattauna komawar da za ta yi nan da sati biyu masu zuwa.

Inda yake tabbatar mata, sha Allah zai zo ya rage saura kwana uku ta dawo din.

Duk hirar da suke yi Blessing na kallon sa, hade da sauraro.

Ya sauke wayar zuwa cikin aljihun da ya dakko ta.

“Mom Hana ko?”

Kai ya daga kawai alamar eh.

“Hey! love birds, you love this women well-well wo!”

“She deserved more” Ya amsa ta, hade da kallon wayarta da ke kara.

“My Mom is arrived, please help me take her in” ta yi maganar bayan ta sauke wayar daga kunnenta

“Ta iso har asibitin?” ya tambaya cike da mamaki, daga Maiduguri zuwa Enugu ai ba karamar tafiya ba ce, amma ace har sun iso, kamar wasu aljanu.

“Eh. Na basu address din tun dazu, suna kofar asibiti ma.”

“OK.” ya fada hade da boye mamakinsa

Haka ya gama zagaye kofar asibitin, bai ga wata mata da ta yi kama da Maman Blessing ba.

Dalilin da ya sanya kiranta ya shaida mata bai gansu ba.

Lokacin da ya bi kwatancen da ta ba shi, zuwa inda suke, sosai kansa ya daure.

Kyakkyawar mace fara tas mai cikar kamala, jikinta nade da lafaya mai laushi.

Gefenta ma wata farar matashiyar budurwa ce, kallo daya za ka yi mata ka hango kamannin Blessing, sai dai kawai ta fi Blessing hasken fata da yarinta.

Ita ma nade take cikin farar lafaya wacce aka ci bakinta da golden din wani kalar yadi da ya kara fito da kyan lafaya.

Bai gama shan mamaki ba, sai da yaga tabon sallah a goshin matar da Blessing ta kira da mahaifiyarta.

Da mamaki tab hade da tambayoyi a bakinsa, ya yi masu jagora zuwa dakin da Blessing take kwance.

Bayan isarsu dakin ne, Blessing ke shaida mishi likita na son ganin shi.

Bai bata lokaci ba, ya nufi wurin likitan.

Lokacin da ya dawo masu da takardar sallamar zaune suke suna hira, da yaren da yake tsammanin kanuri ne.

Lokacin da suka isa gida, dakinsa ya wuce ko ya huce gajiyar da ya diba, don Blessing yau ba ta taruwa, shagwaba take ta zubawa son ranta, shi kunya ce ma take kama shi, bai saba ganin haka ba.

Bacci ya yi sosai, don sai karfe uku daidai ya tashi, a, gaggauce ya yi wanka, ya zira jallabiyar sallahr shi, ya yi sallahr azhar gami da la’asar.

Yana kan yi azkhar din shi na yamma ne, aka kwankwasa kofar shi.

Husaina ce kanwar Blessing tsaye a kofar dakin, hannunta rike da maidaidacin tiren da Blessing ke kawo masa abinci.

“Ina wuni?” ta gaishe shi hade da risinawa.

Ya amsa lokaci daya kuma yana karɓar tiren.

“Na gode” ya fada lokacin da yake komawa ciki.

Sai da ya kammala komai, sannan ya nufi tiren, Rice and stew ce, dafaffen wake wanda ya dahu luguf a bowl daban, sai hadin salad, daya bowl din Kuma pepesoup din kaza ne, wanda ya dagwargwaje don dahuwa.

“Ikon Allah! Wasu dai suna jin dadinsu” ya fada a zahiri. Ba tun yanzu ya san cewa Blessing yar gata ba ce, ko wane lokaci tana cin abin da take so ne, a kuma lokacin da take so.

Zuwa yanzu kuma, ya kara fahimtar ita din ƴar babban gida ce, kawai dai irin ita ba ta nunawa ne, sai dai kuma kowa zai iya fahimtar ita din yar gata ce gaba da baya.

Ba wannan ne kawai abun mamaki a tattare da ita, har da yadda mahaifiyarta ta kasance musulma, to ko ya abun yake
“Oho” ya amsa a zahiri, lokaci daya kuma yana tura spoon a bakinshi.

Sosai ya bude ciki ya ci abinci, bai kwari kansa ba.

Yana tsaka da duba wani littafi da ya shafi shari’a, aka kwankwasa kofar.

Wannan karon mai Husaina ce “I’m sorry for disturbing you. Dama Momyna ce ta ce ka zo”

Haka nan yarinyar ke burge shi, tana da kalar hankali hade da girmama manya, tana da nutsuwa sosai, kallo daya za ka yi mata ka shaida hakan.

“OK.” Ya amsa ta, hade da bin bayanta da kallo, a nutse take jefa hade da daga ko wace kafa tata.

Sai da ya jira umarninsu, sannan ya shiga dakin, a, kofa ya tsugunna kai a kasa yana gaishe da Momy.

Cike da fara’a take amsa mishi, lokaci daya kuma ta shiga yi mishi godiyar irin abubuwan da Blessing ta ce ya yi mata.

Murmushi kawai yake yi kasa-kasa, wani lokacin kuma sai ya saci kallon Blessing wacce take ta murmushi, farin ciki ya gama bayyana a kan fuskarta.

Da kyar ya samu ya sabe, zuwa dakinsa, don zaman shi a can din duk jin sa yake yi a takure.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 28Daga Karshe 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×