Skip to content
Part 20 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Kwana biyun Mustafa, Ummi da Inna ne ke ta jigila da Fatiman.

Ta ce wannan take so, idan an yi kuma da ta ci kadan sai ta ce ta koshi, wani kuma ko cin ma ba ta yi, a bangare daya kuma ba ta iya shan ruwa.

Da zarar ta sha sai amai, sai dai a zuba july juice a ciki, ko a siyo mata dangin minerals.

Har zuwa lokacin kuwa Fatima ba ta san ciki ne da ita, don babu wanda ya fada mata, har kuwa Mustafan.

Tsawon sati Mustafa na a gida, ciwon Fatima ba sauki, daga wannan sai wannan, ita kanta ta gaji, wani lokaci sai ta fashewa su Inna da kuka ta ce kila dai mutuwa za ta yi a yafe mata, kamar yanzu ma da take kwance kan tabarma a tsakar dakin Inna.

Awara Ummi ta siyo mata, tun da ta ci awarar take kwarara amai, har karfinta ya kare, Mustafa kuwa tamkar zai bugi Ummi haka yay ta masifa, wai me ya sa za ta ba Fatima awara.

Duk kuwa da yadda Ummi ke kare kanta, ta hanyar fada mishi, Fatiman ce ta ce a sawo mata awarar tana so. Amma sam ya ki saurara.

Inna dai Uffan ba ta ce ba, sai sannu da takewa Fatima.

“Inna don Allah a kai ni gida wurin Mama.” cewar Fatima cikin murya mai ban tausayi.

“Ki yi hak’uri Fati, ciwon na dan lokaci ne, zai wuce kin ji.”

“Ni dai a kai ni in ganta Inna, in roke ta ta yafe min. Kullum cewa kike zan ji sauki kuma har yanzu.”

Inna ta dan murmusa kadan sannan ta ce “Ki kara hak’uri kin ji.”

Ta mayar da kallon ta kan Mustafa “Ya Mustafa ka kai ni wurin Mama don Allah.”

Tausayin Fatima ya kama shi, ji yake kamar a cire cikin nan, idan dai haka, ciki yake to kuwa daga wannan Fatin za ta jima ba ta kara yin ciki ba.

Ya kalli Inna tare da marairaicewa “Inna a kai ta mana”

“Kai! Fita ka je ka yi harkarka. Ke Ummi sanya mata ruwa ta yi wanka, sai ta dan ji dadin jikin.”

Haka Mustafa ya fice jiki a mace, daga nan kuwa gidan Mama ya zarce.

A lokacin Mama kokarin dora girkin rana take, saboda karfe sha daya na safe.

Ganin Mustafan ne ya dakatar da ita, daga hada busasshen rogon da take yi a cikin dawa.

A jikin bishiyar bedi ya duka, kansa a kasa suka gaisa da Maman. Shiru ya biyo baya, ita ce ta fara katse shirun da tambayar

“Lafiya dai ko? Ko jikin Fatin ne?”

Ya dan yi shiru sannan ya daga kai alamar eh.

“To me ya faru yanzu, aman ne bai tsaya ba har yanzu?”

Kai ya kuma dagawa alamar Eh.

Shiru ya ratsa, kafin Mama ta ce “To yanzu ya aka yi?”

Ya dan sosa kai “Dama zuwa za ku yi.”

Ido Mama ta fitar “In je kuma? Ina zan je?”

Marairaicewa ya yi kamar zai fasawa Mama kuka “Mama Fatima na jin jiki sosai, ta damu tana son ganin ki. Don Allah ki yi hak’uri ki je Mama.”

“Ni Hajara!” abin da Mama ta fada kenan hannunta a kan haba.

“Don Allah Mama ki yi hak’uri ki je.”

“Amma da kaina, ba ga yan’uwanta nan ba, sai ni ce za kwashi kafa rabe-rabe in tafi gidanta fisabillilahi.”

“Mama don Allah!” kamar zai yi kuka haka ya yi maganar.

“Kai kar fa ka biyewa Fatima, ita fa haka take ba ta da dauriyar ciwo, ciwo kadan sai ka dauka an jima za ta mutu. Ka fita harkarta, ni babu inda zan je. Tashi ka fita ka ba ni wuri. Kuma ko me kake yi, wallahi Mustafa kar ka wuce gobe ba ka koma makaranta ba. Wane irin sakarci ne wannan?”

Duk irin magiyar da ya yi wa Mama cewa ta yi ita fa ba za ta je ba, ya fita ya ba ta wuri.

Haka ya hakura ya fice gidan, Maman na kara jaddada mishi lallai gobe ya koma makaranta.

Daga nan gidan Aunty Hauwa ya shiga, sai da suka gaisa da Aunty A’i da ke ta hidimar ta a tsakar gida, ta tambaye shi mai jiki sannan ya wuce falon Aunty Hauwa.

Kwance take bacci yana son daukarta.

Ganin Mustafa ya sanyata tashi zaune, tana tambayar shi lafiya dai ko.

Kamar yadda ya fadawa Mama haka ya fada mata.

Aunty Hauwa kam jikinta mutuwa ya yi, da sauri ta shirya suka nufi gidan.

A lokacin Fatima zaune take cikin dakin Inna, ta hada bayanta da bango suna hirarsu.

Tun da ta yi wankan sai ta dan ji karfin jikin sosai, musamman da ta ci dambun masara da ya ji zogole. Ummi ce ta kuma sawo mata.

Duk suka mayar da hankalinsu kan Mustafa da Aunty Hauwa da suke shigowa.

Fatima ta bi Aunty Hauwa da kallo, kamar ranar ta fara ganinta, saboda ko hijabinta a baibai ta, sanya shi, kuma a karkace.

Sai da suka gama gaisawa da Inna hade da tambayar mai jiki sannan, suka gaisa da Fatin.

“Daga ina kike Aunty Hauwa?” Fatima ta tambaya a lokacin da Aunty Hauwa ke amsa gaisuwar Ummi.

“Daga gida mana?”

“Kin kalli yadda kika sanya hijabinki kuwa?”

Sai a lokacin Aunty Hauwan ta duba

Dukkansu suka kama dariya har da Mustafa da ke tsaye bakin kofa.

“Ina fa na lura, ga wanda ya je ya rudani nan, wai Fatima ba lafiya ta ce in zo.”

“Cikin dariya Inna ta ce ke da kin riga kin san irin wannan ciwon kuma. Daga fa cin awara ne ta kama amai.”

“Ai a rude ya je min ne.”

Suka kuma saka dariya, sannan Aunty Hauwa ta juya kan Mustafa

“Wallahi kar kuma zuwa gidana a kan wannan batun, idan ka matsu ka dakko Fatiman ka kawo ta gudana.”

Haka Aunty Hauwa tai ta masifa suna mata dariya, ta fice ko bangaren Fatima ba ta shiga ba.

*******

Kan dole Mustafa ya koma makaranta, amma ba don ya so ba.

Kafin ya tafi kuwa, sai da ya kama katon ragonshi ya siyar, ya siyawa Fatima waya kirar Motorola da layin Celtel.

Minti-minti zai kira ya ji ya jikinta.

Ita ma haka take damun shi da flashing, ba shi kadai ba, duk dangin Fatima sai da suka san ta yi waya. Musamman Zainab, har free call suke yi.

Lambar waya kuwa, ko a jikin kwalin ashana ta gani sai ta gwada kira ta ji ko za ta shiga.

Ciwo kuwa kullum da in da salon da yake zo mata da shi, yau ta ji tana son wannan, gobe wancan, yanzun wannan an jima wancan.

Wani lokaci gidan Mama take tafiya, ta je can tai ta rigima, ta hana kowa zaman ƙalau, ba sau daya ko biyu ba Alhaji ke baro wurin aikinshi zuwa gida, saboda rikicin Fatima, tun Mama na biye mata, har ta fara korarta, tana yin sallama Mama za ta dora fadin “Koma inda kika fito wallahi, ni dai nan ba zan iya wannan fadi tashin ba. Ko kuma ki samu wurin zuwa.”

Wani lokaci ta shafawa idonta toka, ta shige dakin Maman ta yi kwanciyarta, tana sauraron fadan Mama, wani lokaci kuma ta tafi gidan Aunty Hauwa.

A can ma haka Aunty Hauwa za tai ta jaraba, har ta gaji ta yi shiru. Ita kuwa sai ta yi niyyar tafiya.

Mustafa kuwa sai da Mama ta yi zagir-zagir sannan yake iya yin sati ba tare da ya zo ba.

Amma da kwana biyu uku ya zo.

Har zuwa lokacin babu wanda ya fadawa Fatima tana da ciki, ita da kanta ta fahimci hakan, saboda rashin yin period nata.

Ita ma sai ta share, ba ta taba nunawa kowa ta san ciki ne da ita ba, har Mustafa, yadda ya share ita ma haka ta share shi.

Wannan shi ne halin kunya irin na mutane wannan zamanin, iyaye bassa hirar da ta shafi irin haka da yaransu, ita kanta mace kunya ta ke ji, ace tana da juna biyu, bare ta fadama wani, saboda Fatima ko Zainab ba ta fadamawa ba, kamar yadda Zainab din ba ta taba yiwa Fatima maganar ba.

*****

Cikin Fatima wata bakwai ba kowa ne ya san da shi ba, bai yi irin girman nan ba, yanzu kam ta samu lafiya, komai ci take yi, shi ya sa take zuba wata irin kiba, ga haske ta kara ta yi fes.

Kasancewar yau juma’ar karshen wata, Alhaji zai zo gida, sannan kuma yau Mustafa ya gama exam din shi ta first semister, yau zai zo gida, sai aikin ya yi mata yawa, don ma akwai Ummi.

Shinkafa da miya ta yi, kajin Mustafa biyu Inna ta sanya aka yanka hade da gyarawa.

Misalin karfe biyu suka kammala komai, Fatima ta debi wacce za ta kai gida, sannan ta debarwa Mustafa.

Ba ta bar gidan ba sai uku saura, hannunta rike da basket din abincin da za ta kai.

A can gidan kuwa Aunty Lami ce da su Aunty Bilki matar Yaya Bashir zaune kasan bishiyar dalbejiyar tsakar gidan suna hira.

Mama kuwa zaune take a kofar daki, kan dutse da take alwala, tana sauraron hirarsu, wani lokaci ta yi dariya, wani lokacin kuma ta sanya baki.

Yanzu ma Aunty Ayyo ce ta ce “su Fati bam-bam ko an yi nauyi ne, an kasa zuwa yau?”

“Ita wannan har wani nauyi ta sani” cewar Aunty Sadiya.

“Ai barkanmu dai wannan ciki na Fatima ya girma, amma ai mun ci wuya. Ni ban taba ganin ciki irin na Fatima ba.” cewar Mama daga inda take zaune.

“To dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka.” cewar Aunty Aisha tana dariya.

Aunty Hauwa da ta shigo lokacin ta dora “Me ake yi wa dariya ne?”

“Zancen Fatima ake yi mai ciki, Mama ta ce wai suke da bar ka da ya girma.”

Dariya Aunty Hauwa ta fara hade da fadin “Wallahi fa. Kai na ga jaraba, tun da aka samu cikin nan bamu huta ba, Fatima ba dauriyar ciwo, za ki rantse ba za ta kai an jima ba Lami. Ke ranar mijin da ya zo ce min ya yi shi dai a cire cikin bai so”

Su Aunty Ayyo da suke kwance suka mike zaune a tare cike da mamaki, Mama kuma ta ce “Ke don Allah!”

“Wallahi haka ya ce min Mama.”

“Yarinta.” cewar Aunty Lami.

Sannan ta dora da fadin “Yanzu ba ga shi ya wuce ba. Kodayake da sauran kuka, wai an daka gumba an cinye ba a ba, maye ba. Tun da haihuwa na baya.”

“A ranar za a yi abun, wai mai karyar ciki ta haihu” Aunty Aisha ta fada cikin dariya, suma duk sai suka fashe da dariyar.

A daidai lokacin ne kuma Fatima ta yi sallama.

Duk suka bi ta da kallo ba tare da sun amsa sallamar ba.

“Hala gulma ta ake yi, ke dai Aunty Sadiya na san ba’a gulma da ke, me suke cewa?”

“To mu kuwa mu yi gulmarki Fatima mu ce me, me ye abun gulma a jikinki?” cewar Aunty Aisha

“Yo ke idan dai kina wuri Aunty A’i ba za a taba fadin alkairi a kaina ba. Ni fa tuni na san zaman da nake yi da ke. Ke Bilki har da ke ko? Ke da ba ma yan’uwarmu ba, bamu hada komai da ke ba fa. Kawai yayanmun kike aure.”

Aunty Bilki da ba ranar ta fara jin wannan gorin ba ta ce” Kuma ba ki da ruwan wanke ni ba, tun da na haifa miki yaro, ga kuma wani a ciki. “

” Yo ke kika haife shi? Tiyata fa aka yi miki. Wannan yaron ko tsine mishi kika yi ba ta bin shi.”

“Ke wai har yanzu ba ki yi hankali ba? Dadi ne ke sanyawa a yi wa mace aiki?” cewar Aunty Lami.

“Kai ki yi shirunki Aunty, ai ba yau ta fara ba.” cewar Aunty Bilki

“Atoh! Gara dai ki fada mata ta wajena, ni da ke kar ta san kar ne, ba a shiga tsakaninmu.”

Aunty Ayyo ta tuntsire da dariya “Aunty Lami ba ki ga mun yi shiru ba, ai basa batawa kuma bassa shiryawa. Da kin bar su.”

“Aunty Lami barayin ne suka kara shigo maku?”

“Ban sani ba, ki hita idona, ki je ki yi abin da ya kawo ki.”

“Na ga ba zuwa gida kike ba sai dalili”

Aunty Bilki da Aunty Ayyo ne kawai suka yi dariya.

Aunty Lami dai Uffan ba ta ce ba.

Aunty Hauwa kuwa tuni ta shige bangaren Alhaji don gaishe shi.

Ita ma Fatima bangaren Alhajin ta wuce, yayin da take kunshe dariyarta.

Tana yin sallahr magriba ta wuce gida, saboda tuni Mustafa ya shaida mata dawowar shi.

Bai shigo gidan ba sai da aka yi isha’i, kyakkyawar tarba ya samu daga Fatima, tarbar da ke nuna ta yi kewar shi ba kadan ba.

Hutun satin biyun da ya yi, sosai Fatima ta samu kulawa, ga karatun addini da yake dora mata, ji ta yi kamar kar ya tafi, ko don karatun ma, sai yanzu ne take jin dadin karatu, ta ji ina ma, tuntuni suka fara hakan.

Shi kansa ba don ya so ba, ya koma makaranta, a lokacin da hutunsu ya kare.

Sai dai ya tafi ne kirjinsa cike da kaunar Fatima, da ace yana da halin kama masu gida tabbas da ya mayar da ita Kano.

Amma kila zuwa gaba ya yi hakan.

“To Allah ya sa” In ji ni

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 19Daga Karshe 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×