Skip to content
Part 5 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

“To kar dai ki cinye ni, kika kura mun wa’annan manyan idanun naki kamar k’wai.”

Sosai abun ya ba ta dariya, ta kwantar da kanta a kan kujerar kafin ta ce,

“Kodai ka cinye ni, tun da na fito fa kake kallona.”

“Ni kuwa in kalle ki in ji me?” ya fada hade da tabe baki.

“Ka ji dadi mana.

Mu tafi mana ko ba ka gama kallon nawa ba?”

Wannan karon shi ma murmushi ya yi,

“Jira nake ki gama kallon nawa. Bari ki ji in fada miki, ba kina ta rawar kai ba kamar angon kare za ki birni, wallahi kina yi mun shirme zan baro ki a can.”

“To sai me don ka baro ni a Daura? Daura ai kamar in fita daga daki ne zuwa tsakar gidanmu, an fada ma ko Abuja ka bar ni ba zan dawo gida ba ne?”

“Afff! Ni dai fada miki kawai na yi” ya fada daidai lokacin da ya hau hanyar da za ta sada shi da kwanar Sandamu.

“Idan ka bar ni ma sai na zabi wanda nake so ya kawo ni gida.”

“Wannan kuma karyarki.”

“To ka jira mu isa za ka ga yadda zan hada go slow.”

“Fatima a tarihinki fa, babu wanda ya taba cewa yana sonki sai dai a can kauyen Katsayal da kika bi Mama biki, shi ma tun da ya zo sau daya bai sake dawowa ba. Wai me kika fada mishi ne ya ki dawowa?”

Shiru ta yi hade da kau da kai gefe tana kallon yadda suke wuce wasu motocin wasu kuma na wuce su.

Ya fahimci ya yi mata kwaf daya, don haka ya tuntsire da dariya me sauti kafin ya kara da.

“Don Allah ba ni labarin yadda kuka yi.”

“Sai ka kawo kudi.” Ta fada ba tare da ta kalleshi ba.

Ya kuma tuntsirewa da dariya hade da buga sitiyarin motar.

“Wai ba za ki ban labari ba.”

“Ka san Allah kana kara yi mun maganar nan, sai na bari an kusa zuwa checking point din can in zunduma ma ihu in ce sato ni ka yi.”

Da yanayin gargadi a kan fuskarta take maganar. Ya kuma fashewa da dariya ba tare da ya ce komai ba.

Har suka isa Daurar basu kara wata magana me tsawo ba.

A can tsallaken shagon ya yi parking. “To fita”

“In fita kuma? Mu fita dai.”

“Babu inda zan je, kin manta irin rainin wayon da kike mun, kuma ni ne zan taya ki sayen kaya, har in dakko miki ko? Allah ya kyauta, idan kin fasa siyayyar in juya mu koma gida, ko ba komai dai kin sha dadin mota.”

Mustafa kayan haushi gare shi, idan ta biye mishi bata mata lokaci kawai zai yi da kuma rai.

Cikin katon shagon ta shiga, sun iya tarar customer don tana shiga suka mika mata gurin zama hade da tambayar me za a ba ta.

List din ta ta fitar cikin karamar posser ta fara lissafa masu.
Cikin mintuna talatin suka hada mata koma, tare da daya daga cikin hadiman shagon ya rakota da kayan har gurin da Mustafa ya yi parking.

A lokacin kuwa  ya kwantar da kanshi ne a jikin kujera yana sauraran Radio.

Kwankwasa kofar motar ta yi da hannunta.

Ya dago kai yana kallonta.

Ba ta yi magana ba, shi ma bai yi ba, amma ya fahimci me take son ya yi.

Ya fito hade da bude boot din suka zuba kayan.

Bayan ta daidaita a mazaunin gaban motar ne yaron ya leko hade da mika mata wata jutter da biro, “Dama Ogana ne ya ce ki ba shi No wayarki.”

Ta waiga hade da kallon Mustafa wanda shi ma ita yake kallo.

A zuciyarta kuwa fadi take “Ubanwa zai ba ta waya a wannan lokacin, waya sai wane da wane, duk gidansu daga Yaya Jamil, Baba, Kabir, sai Yaya Bashir ne kawai ke da ita. Ita idan ban da amsa kira ma ba ta iya komai a waya ba, duk karambaninta ba ta taba waya.”

Duk wannan maganar zucin da take yi idonta na a kan Mustafa, shi din ma ita yake kallo.

Abun mamaki sai ya ga ta karbi jutter hade da biro ta rubuta No wayar ta ba shi.

Bayan sun hau kan hanyar dawowa ne Mustafa ya kalleta” No wa kika bayar? Na ga dai ba ki da waya.”

“Ta Baba na bayar.”

Ido ya zaro.

“No Baba, lallai tun da ake cewa ba ki da hankali ban yarda ba sai yau. Me ya sa za ki bayar da No Baba?”

“Zan fada wa Baba idan an kira shi ya ji alamar ana neman mace to ya ba ni. Bana son in rasa wannan damar ne. Mutum din ya hadu sosai.”

Baki Mustafa ya saki yana kallonta, Saboda iya gaskiyarta kenan take fada

“Hmmm! Wallahi har na hangoni a wata duniya sabuwa, da gaske idan ya ce yana sona amincewa zan yi, duk da na san yana da mata, amma ba ruwana da matarshi, ni fa ra’ayina ma na fi son me mata.”

Ya gangara gefen hanya, hade rai ya yi sosai kafin ya ce,

“Fita ki koma wajenshi, sakarya, ke ko dan jan ajin nan ma na mata ba ki da shi. Daga ganin mutum duk kin wani rude. Wai ke yanzu a shekarunki ma har wani so kika sani?”

Bude baki ta yi daga bisani kuma ta ce,

“Tabbb! Idan ma dai ban san shi ba yau na san shi, kai ya fa hadu.”

“Na ce ki fita ko.”

Marairaicewa ta yi, “To ina zan je?”

“Gurin me kyau din mana.”

Shiru ya ratsa gurin kafin ta ce “To yi hakuri.”

“Ke haka za ki yi naki ‘yan matancin ba jan aji ba komai sokuwa kawai. Ni duk kin bata mun raina ma, akwai bukatar a baki darasin ‘yan matanci.”

“Ki rasa No da za ki bayar ma sai ta Baba tsabar shirme. Gaskiya dai Fatima ina jin kanki ba daya ba.”

“To so kake ajina ya zube?”

“Dama ke har wani aji ne da ke?”

“Ba ni da shi?”

“Kina da shi mana, amma science Sandamu.”

“Me kake nufi?”

Ya mayar da hankalinshi akan tukin kafin ya ce,

“Haba kullum ke kenan zane a kirji, ba kya kwalliya, sai ki yi sati ba tare da kin shafa hodo ba, ba kya abu a natse kullum sai shirme to ina ajin naki yake?”

Ta yi murmushi me sauti wanda yake nuna abubuwa da yawa kafin ta ce,

“To ni ina ruwana, yadda na ga dama haka zan yi abubuwa, ina ruwana da wani aji can.”

“Ni gaskiya na fada miki, amma ko ba za ki daina komai ba ki daina daura zane a kirji.”

“Gaba na ba shi ba baya ba ma.”

“Daura zanen a kirjin?”

“Eh” ta fada hade da murguda baki

“Na fahimci ke ba ki san arziki ba, kuma ba’a yi miki abu a hankali, kin san Allah idan kika dawo gida hutu kullum sai na shigo gidanku, kuma duk ranar da na ganki da zane a kirji sai kin zagaye gidanku kaf da tsallen kwado.”

Ido ta fitar hade da kallonshi ba tare da ta ce komai ba.

“Yes! Haka nake nufi kuma kin san dai zan iya.”

Kwakwalwarta ta dakko mata wani abu da ya faru shekaru uku baya, lokacin tana 14years inda Mustafan ya cafkosu a wani lambun mangwaro suna diba, ganinshi ya sa duk suka watse a guje. Amma ita har gida ya biyo ya ja ta zuwa farfajiyar da suke kiwon dabbobi ya sanyata tsallen kwado, wuyar da ta sha har zazzabi ta yi.

Shi yana da sakin fuska a yi hira da shi har ma ta tsokaneshi, sabanin ya Jamil da babu wannan fuskar.

Amma kuma Mustafa ya fi Ya Jamil iya hukunci, don duk ranar da ta shiga hannunshi to a ranar gwammacewa take kida da karatu.

Ta sauke ajiyar zuciya me sauti lokacin da ya gangara hanyar da za ta sada shi da gida.

Har ya yi parking a kofar gida ba ta kuma cewa komai ba.

Ruwa kawai ta sha, ta wuce gidan kitso da kunshi, don gobe ne za ta koma makaranta.

A gidan kitso maganganun Ya Mustafa ne ke mata yawo wai ba ta da aji, ba ta kwalliya ba ta abu a natse.

Ba ta kwalliya kam amma hakan ba ya nufin ita kazama ce.

Tana da hadin sabulun wankanta me kyau da gyara jiki, don kowa ya kalli jikinta ya san ta mori sabulun wanka, tana da turarurruka da humra masu kamshi da take debowa wajen yayyunta mata duk lokacin da ta je.

Haka manta ma me kyau ne hadin Niger a can ake hadowa ma mama manshafawa

Za ta iya yin sati ko fiye da ba tare da ta zauna ta tsara kwalliya ba. Ita asali ma dai za ta iya cewa ba ta kwalliya. Za dai ta yi wanka ta shafa humra hade da sanya kayanta. Ranar da za ta fita ne kawai take murza farar hoda da man lebe. Shi kenan kawai iya kwalliyarta, amma ba ta zama da kazanta, maganar daure zane a kirji za ta kiyaye ko don tsallen kwadon da ya ce zai sanyata.

Sai karfe biyar ta baro gidan kitso da kunshi zuwa gida, yunwa har ta ci ta cinyeta.

Lokacin da ta iso gida Mama ta kintsa mata komai na tafiyarta gobe, don haka ta zuba abinci tana ci in da Mama ke ta yaba kunshin da kitson da aka rangada mata.

Bata da yalwar gashi duka gashin bai fi kamu daya ba, amma kuma yana samun gyara yadda yadda ya kamata.

Fatima na daya daga cikin kyawawan gida, fara ce tas, irin fari me fari ba mai ja ba, fuskarta akwai irin kananan tabban kuraje jefi-jefi. Haka jikinta ko ina a cike yake wuyanta cike ba alamun kashi, tana da yalwar kirji da baya, doguwa ce amma ba zakaka ba, sai dai kallo daya za kai mata ka tabbatar da doguwa ce. Ma sha Allah ko ta ina Fati na da kyau daidai gwargwado.

Da misalin karfe takwas na dare tana kwance a kasan bishiya kasancewar ba wuta kuma ana zafi-zafi. Kirjinta ne ke ciwo kadan-kadan alamun ulcer kuma ta san yunwar dazu ce ke son tayar mata da ulcern.

Mama zaune a kofar dakin ita ma a kan tabarma da yar karamar radio tana jin shirin iya ruwa na gidan radion Kano.

Ya Jamil zaune a kan kujera yar tsugunno ya na cin abincin dawowarshi kenan daga kara ma wata mata ruwa.

“Fati” Mama ta kira sunanta.

“Na’am.” Ta amsa daga inda take kwance.

“Au! Ba bacci kike ba, na ji ki shiru lafiya ko?”

Siririn tsaki ta ja.

“Kirjina ne ke ciwo kadan.”

“Ulcer ce ko, ba kin iya cin yaji an ce ki daina kuma kin ki.”  cewar Jamil da ya mike yana wanke hannu.

“Ni fa ban ci yaji ba, kuma idan ban ci yaji ba to me zan ci? Ai shi ne naman talaka, ai mu yaji gaba muka ba shi ba baya, ko a aljanna sai mun neme shi musamman wanda ya ji tafarnuwa.”

Bai yi magana ba, illa wucewa dakinshi da ya yi.

“Zainab ta zo dazu ba kyanan, dama wai tana son jin yaushe zaku tafi.”

In ji Mama.

“Misalin biyar na yamma sha Allah, Baba sai ya tafi damu, tun da shi ma gobe zai wuce Daura.”

“Shi da zai tafi da safe, ke kuma kin ce yamma.”

“Sai in hakura sai ya man.” Cewar Baba da ya shigo yanzu.

“Sannu da zuwa Baba.” cewar Fatima da ta yi saurin tashi zaune don girmamawa.

“Yauwa, kun dawo ko?”

“Eh tun dazu.”

“To akwai wani abu da kike bukata ne?”

“A’a babu komai, na gode Allah ya saka da alkairi ya kara budi.”

“Amin Fatima Allah yay miki albarka.”

“Amin.” ita ma ta fada har yanzu tana tsugunne kanta a kasa.

Mama da ke kallonsu ta tabe baki hade da fadin,

“Mage me kwanciyar daukar rai.”

Murmushi Baba kawai ya yi, lokacin da yake wucewa dakinshi.

Washegari

Misalin karfe biyar sanye take da riga da wando masu ruwan toka hade da farin hijabi da suka sha guga, sanyi me kamshi na fita a jikinta, hannun ta matse da kudi da suka tasarawa 5k. A shekara ta 2006 kudi 5k ba karamin kudi ba ne.

Ya Jamil ne ya ba ta 2k, Mustafa 1k mama 2k. Sosai take jin dadi da farin cikin samun kudin.

Zainab ta shigo ita ma sanye da irin kayan Fatima, a daidai lokacin ne kuma Baba ya fito sanye da manyan kaya farare tas, kanshi nade da farin rawani, Mama na biye da shi a baya.

Idon Fatima ya ciko da kwalla a lokacin da take kokarin shiga motar.

Mama sai jikinta ya mutu ta karasa kusa da ita hade da dafa kafadarta.

“Sai yaushe za ki daina kuka idan za ki koma makaranta? Yanzu ai kin girma da kuka, daga wannan hutun fa sai na shiga aji shidda, kin ga shekara kawai ta rage miki. Bukatata ki mayar da hankali kamar dai ko yaushe. Kuma na yi miki alkawarin ba za a yi aura Kabiru ba kya nan ba.

Sannan yana zuwa zan sa shi ya je ya gano ki tun da kun dade baku hadu ba.”

Da haka Mama ta yi ta lallashi Fatima har zuwa lokacin da motarsu ta bar kofar gidan zuwa bakin hanya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 4Daga Karshe 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×