Skip to content
Part 4 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Dayan bayan daya take bin su da kallo, kamar yadda su ma suke kallon ta, har zuwa lokacin da kowa ya dauke ganinsa a kanta.

“Tashi ki je ki gyarawa Jamilu dakinsa.” cewar Mama lokaci daya kuma ta shige dakinta.

Bayan shigewar Mama sauran ma fita suka yi daga gidan.

Dalilin da ya sa kenan ta mayar da hankali akan aikin. Cikin awa daya ta canja fasalin dakin, sosai ya yi kyau, ta sake net din da ta daura a kan katuwar katifar da ke kasan hade da cuccusa shi kasan katifar, sosai ya yi kyau ta yadda kowa zai yi sha’awar shiga ya kwanta.

Sauran tarkacen ta fito dasu tsakar gida, tana son ware masu amfani dana zubarwa, a daidai lokacin Mama ta shigo da sallama.

“Ya jikin Yaya Bashir din?” Fati ta yi saurin tambaya bayan amsa sallama Mama.

“Da sauki sosai ma.”

“Na ga kin dade.” Cewar Fatima.

“Ke idan kika fita naki yawon da wuri kike dawowa?”

Sallamar Mustafa ce ta hana Fati bayar da amsa.

Akan dutsen dake kasan bishiyar dalbejiyar ya zauna bayan ya gaishe da Mama

“Lafiya kuwa? Sai yau na ganka.”

“Ba sosai ba, wallahi jiyan nan zazzabi ne ya rufe ni shi ya sa ban samu na zo ba.”

“Assha! Allah ya sawake, ai tun da naga ban ganka ba na ce kodai ba ka nan, ko ba ka ji abin da ya faru ba.”

“Na ji, lokacin sosai bana jin dadi.”

“To Allah ya kyauta, ya ba ka lafiya.”

“Amin” ya amsa yana kallon Fatima da ke zaune ta juya mishi baya.

“Ke dai kin ki komawa Islamiya ko? Sai tonon fada.”

“Ka ji, kamar ba kai ne ka kore ni ba.”

“Da na kore ki, Zainab ba ta koma ba.”

“To kuma yaushe za ka hada Zainab da ni, ita daban ni daban.”

“Ke ya kike?”

“Kai ma ai ka sani” Har yanzu ba ta waigo ba, take amsa mishi.

Jin ya yi shiru ne ya sa ta waiga tana kallonshi.

“Zan koma idan na dawo hutu.”

Ya tabe baki. “Ke dai kika sani.”

Ta dan yi dariya me sauti kafin ta ce,

“Ka rika zuwa gida kana koya mun.”

Sosai ranshi ya baci da maganar tata.

 “Saboda ni za ki yi wa karatun?”

“Ka sani ko ka dauke ni ina ma yaranka extra lesson.”

“Mtswww!” Ya ja dogon tsaki hade da mikewa yana kakkabe jallabiyarshi.

“Malam wallahi ranar can ina da gaskiya ka kore ni fa, wallahi irin wannan rigar ce…”

Saukar takalmin da ta ji a gadon bayanta ne ya hana ta karasa maganar.

Ta yi saurin gantsare bayanta hade da fadin,

“Wayyo Allah Mama an karya mun baya.”

Duk abun da ke faruwa mama na ji da kuma hangesu ta gefen labule, ba ta yi magana ba haka ba ta fito ba.

“Miko mun takalmina.” Ya fada daga inda yake tsaye fuska a daure.

Shiru ta yi tana murza idanunta.

“Ba za ki miko ba?”

“Zan miko.” Cikin kunkunai ta yi maganar tare da turo baki, lokaci daya kuma ta mike hade da daukar takalmin ta nufi inda yake tsaye.

“A tsaye za ki ba ni?”

Aje gwiwowinta kasa ta yi, hade da mika mishi.

Caraf! Ya rike kunnenta hade da murza shi da karfe. Ta saki ihu hade da kiran Mama. Wannan karon kam dole sai da Mama ta fito.

“Wallahi duk inda kika ganni daga yau, ki rika dinke bakinki har sai na bar gurin.  Kin ji ni?”

Daga kai take alamar, Eh.

Mama da ke tsaye tana murmushi, “Yi hakuri sakar mata kunnenta.”

“Da shi ne ba ta jin magana ai Mama.” Ya fada a lokacin da yake sakin kunnen.

“Ko dai mutuwa ai na jin kunyar idon mahaifi, amma ni a gidan ubana a gaban uwata za ka ci zalina.” take fada lokacin da take ja da baya.

“Ba kin ji ta ba, bakinta baya mutuwa.” Cewar Mustafa yana kallon Mama.

“Kuma ita zan ba ka ta yi ma zaman daki.”

“Ni Allah ya kyauta, bana gayyar ta.”

“Yo ni sai an gayyace ni nake zuwa, sai ko idan ban yi niyya ba.”

“Tun da gidanki ne ai sai ki je. Ni na tafi Mama kar yarinyarki ta tayar mun da zazzabi.” in ji Mustafa da yake niyyar fita.

Bayan fitarshi ne ta ce, “Allah ya saka mun da tsawo kamar rakumin dawa. Wai Mama shi ma dan’uwanmu ne?”

Dariya mama take sosai kafin ta ce,

“A zaman gari ba, kawai dai shi  hadimin hakimi ne, sannan yaro ne me hankali da girmama manya. Shi ya sa ya zama kamar dan gida.”

Tabe baki Fati ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Yau dai yininta a dakin ya Jamil ne, yayin da Mama ta shiga kitchen.

Da misalin 1:30pm Jamil ya shigo gidan, dakinshi ya fara shiga daga bisani ya shigo bangaren Mama, a lokacin kuwa zaune Mama take tana cin dambun shinkafar da ya ji zogale da kayan miya, Fatima kuwa kwance take a 3seater sosai ta gaji.

Bayan amsa gaisuwarshi da mama ta yi, “Ina ka je tun dazu?” ta tambaya, idonta a kanshi.

Ya dan shafa kai a hankali hade da Jigina bayan shi a kujera.

“Na dan mike kafa ne, kin san ban saba zama guri daya ba. Ina abincina?”

“Kawo mishi abincin shi Fati.”

Mika ta yi a hankali kafin ta ce, “Wallahi na gaji Mama.”

“To in je in dakko kenan.” Jamil ya fada yana kallonta.

Ta waro ido hade da mikewa zaune, “Ni na isa, ko don ciwon nan naka ai na dakko maka.”

“Kin dai ga dama.” Cewar Mama a daidai lokacin da Fati ke fita.

“Ya jikin naka?”

“Akwai sauki sosai, kaina ne kawai yake dan ciwo.”

“To sannu Allah ya sawake, ga ka likita kuma ba ka son shan magani.”

Shiru ya yi bai amsa ba, har lokacin da Fati ta shigo mishi da abincin.

“Wai ke zamanki kenan ba kya son sanya kaya, kullum zane a kirji.”

Ta bude baki daidai lokacin da take dagowa,

“Ka ji, to ni da gidan ubana, gidanmu ne fa. Kai Allah ya kyauta, ni fa ko da gyale ma bana iya fita waje, don Allah ku bar ni in yi ƙiba, kullum dai ni na yi abu ba daidai ba.”

Mama da ta rike haba ta ce,

“To sannu me gidan uba, wanda ba shi da gidan uba ya yi kuka, don Allah ki tafi ma tsirara tun da gidan ubanki ne.”

Zumbura baki ta yi kasa-kasa kuma tana fadin, “An taba kwallin idonki ai.”

“Ki fadi duk abin da kike son fada, mara kunya tun da ke ba wanda ya tsira a gurinki.”

“Wai ya Jamil ba ka ga na gyara ma dakin ba ne?” Ta canja hirar tasu,

“Na gani.” Ya amsa da kyar kamar baya so.

“Hala bai yi kyau ba, na ji ba ka ce komai ba.”

“To don kin gyara mun daki sai na yi ta kwakwazo ya yi kyau.” ya fada bayan ya yi kicin-kicin da fuskarshi.

“Kwantas!” cewar Fati lokacin da take fita dakin.

“Mama na ba ku guri ke da gold dinki, Allah ya kawo Babana, shi ya sa nake tafiyata gidan Aunty Hauwa ai.”

“Don Allah yanzu ma ki tafi, idan kin tafi ma kar ki dawo, kuma Baban naki ai gobe zai zo idan ya tashi komawa sai ku tafi tare.”

“Abu da ma makaranta zan koma, kuma ina tafiya, wallah na san sai kun yi kewata.”

Da alama Mama ta gaji, don shiru ta yi ba ta ce komai ba.

*****

Ranar jumu’a kuwa Alhaji Musa ya iso gida, daga Daura inda yake aiki a ma’aikatar gona.

Abincin gidan ma na ranar ya fi na kullum yawa, saboda baki, Alhaji Musa kuwa bai samu kanshi ba sai bayan sallahr isha’i bayan ya je gidansu Danliti da kanshi ya bi ba’asin sabaninsu Danlitin da Fati.

Fati ce zaune a falon na shi tana lissafa mishi abin da take son tafiya da shi makaranta.

Duk abin da ta lissafa baya musawa sai ya ce, “To haka ya ishe ki ko?” ko ya ce, “Sai me kuma?”

Mama da ke zaune gefensu tana saurarensu ta kasa hakuri.

“Ke tashi ki fita tun da ba ki da hankali, ke ko tausayi ma ba ki da shi, a kanki ne aka fara makarantar kwana?”

“Ina ruwanki? Idan ban siya mata ba wa zai siya mata?” cewar Alhaji Musa cikin muryarshi mai laushi.

“A toh! Kuma idan ba ka nan ba ta kula ni sai gold din ta, yanzu da shi ne shiru za ta yi.”

“Ta shi ki je ki rubuta duk abin da kike so don kar ki manta. Gobe sai Mustafa ya dauke ki a motata ku je Daura ku sa yi komai.”

Ranta fari kal ta fita dakin tana godiya.

“Wallahi Alhaji ka daina shagwaba yarinyar nan, ba fa ita kadai ba ce ‘yarka, kuma gidan wani za ta.”

“Amma yanzu ita kadai ce ai.”

“Shi ya sa kullum rashin kunyarta karuwa take yi.”

“Kuma ba kwa son yi mata addu,’a?”

Shiru Mama ta yi, ita akwai abin da take hange game da Fatima wanda ta kasa fassarashi har yanzu, sannan ba ta san ya za ta fada mashi ba.

Shi ba mazauni ba ne, ballantana ya rika kallon shirgin da Fatin ke yi. Duk da aljanu basu taba bigeta ba, amma ba a rasa su a kanta.

Ita kawai ce ke kokarin tsawatar mata, amma shi a komai goyon bayanta yake.

Sauran yaranshi zasu kawo bukatarsu me muhimmancin, amma bukatar Fatima sai ta hana a biya tasu a kan lokaci.

Sam! Fatima ba ta san babu ba, muddin za ta furta tana son abu to Alhaji Musa sai ya yi mata shi.

“Bari mu ba su Mama guri.”

Ranar asabar da misalin karfe tara na safe Mustafa ya iso, tun da ya iso kuwa kafsawa suke da Fatima.

Har zuwa lokacin da ta shirya cikin blue lace me jefin farar fulawa, ko mai ba ta shafa ba, turaren humra kawai ta shafa saboda yadda Mustafa ya matsa su tafi.

A  cikin zaure ta saka dogon farin hijabinta.

Ta bude marfin motar hade da zama.

“Mu je” Ta fada hade da kallonshi.

Dama ita yake kallo,  hakan ya ba kwayar idonsu damar haduwa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 3Daga Karshe 5 >>

2 thoughts on “Daga Karshe 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×