Skip to content
Part 15 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Safiyar Lahadi Fatima da wani irin ciwon kai mai zafi ta tashi, duk shirye-shiryen da su Aunty Hauwa suke, domin rakiyar Jamil Kano, inda jirginsu zai tashi gobe Monday, Fatima na kwance a bedroom din Aunty Hauwa tana jin su.

Duk yadda Aunty Hauwa ta so Fatima ta je rakiyar kiyawa ta yi. Har albishir ta yi mata na Zainab ma zasu je ita da Aunty Lami, amma Fatima ta ki amincewa da tafiyar. Dalilin da ya sa Aunty Hauwa ta kyale ta.

Lokacin da ta sha paracetamol sai ta dan ji sauki, shi ya sa ma ta fito babban falo, tana kallon masu shiga da kuma masu fita. Misalin uku da rabi duk yan rakiyar Jamil sun shirya.

Aunyty Hauwa, Aunty Ayyo, Ya Bashir da kuma Aunty Aisha. Fatima ji take yi kamar ta sanya hijabinta ta je gidan Mama. Ba ta son Jamil ya tafi ba tare da ta kara ganin shi ba.

Tana son kara ganin fuskarsa tare da muryar shi. Wani irin yanayi take ji, mai kama da ka tafka wata katuwar asara, ko kuma asarar na shirin samun ta.

Ana idar sallahr la’asar Aunty Hauwa ta fice zuwa gidan Mama, fitar da ta yi ta tamkar da duk wani ragowar kuzari na Fatima.

Wani mulmulallan Abu da ya danne mata zuciya tun dazu, ya fara fashewa a hankali, dalilin da ya ba hawayenta damar gangarowa.

Tun tana yin kukan mara sauti, har ta warware muryar ta, ta shiga rera kukan kamar wacce aka ce an fasa auranta da masoyinta.

Yi take iya karfinta, kuma da za a tambaye ta kukan na menene, ba ta san amsar bayarwaba, saboda ita ma ba ta san na menene din ba.

Da kanta ta gamsu lallai ta yi kuka, kuma ta koshi da shi. Toilet ta shiga hade da wanko fuskarta, ta fito wajen barandar Aunty Hauwa ta zauna shiru.

Aunty A’i (kishiyar Aunty Hauwa) da ke ta zirga-zirgar ta a tsakar gida ta kalli Fatima cike da kulawa. “Har yanzu jikin ne Fati?”

“A’a da sauki, kaina ne dai kawai ke dan ciwo.”

“To kodai mu je asibitin ne?” cewar Aunty A’i cike da kulawa.

“Ba sai mun je ba Aunty.” fatima ma ta ba ta amsa.

Tana zaune a wurin har aka kira sallahr magriba, ta mike zuwa daki hade da yin alwala ta yi sallah.

Tana kan sallaya ta ji sallamar Mustafa, dama jikinta yana ba ta zai zo, tun da ya san Aunty Hauwa ba ta nan.

Mikewa ta yi zuwa karamin falon Aunty Hauwa, tana kokarin zama ya shigo.

Suka zauna a tare lokaci daya kuma tana gaishe shi.

“Har yanzu ba ki koma Fatimanki ta baya ba.”

Guntun murmushi ta yi sannan ta ce “Kaina ne ke ciwo.”

Rufe bakinta ya yi daidai da mikewar shi, zuwa inda take zaune, lokaci daya kuma ya kai hannunsa saman goshinta.

“Fatima wannan ai zazzabi ne ba ciwon kai kawai ba.”

Karo na farko da namiji ya taba ta, ta ji wani irin abu ya ja ta, tare da ratsa magudanar jininta. Cike da mutuwar jiki ta ce “Eh har da zazzabin ma.”

“Kin ci abinci ne?”

Kai ta girgiza alamar, a’a.

“Ya kamata ki ci wani abu sai mu je asibiti. Me kike son ci in samo miki? Ko tuwon Mama kika missing?”

Tare suka yi guntun murmushi a lokacin da ya kai karshen maganar shi.

Sai ta samu kanta da daga mishi kai alamar eh.

“To tashi mu je ki ciwo.”

Make kafada ta yi “Sai dai ka amso min.”

Sosai yake son hanyar sasanta Fatima da Mama, ba zai so ta sanadiyyar shi Mama ta ci gaba da fushi da ita ba.

Burin shi kawai ya ga Fatima cikin farin ciki da walwala a ko wane lokaci.

Ya daukar ma kansa in sha Allah hawayenta ba za su zuba ba ta dalilin shi. Zai tsayar da zubarsu ma ta dalilin wani.

Da wannan tunanin ya nufi gidan Mama.

Zaune take kofar daki ta shimfida tabarma, radionta na ta ɓaɓatu, ka rantse da Allah sauraro take yi, amma ko daya ba ta san abin ake fada ba.

Hankalinta ba ya gidan, ta raba shi kashi-kashi, wani kano, wani gidan Aunty Hauwa, wani Indiya, wani kan Fatima, yayin da wani yake a kan Mustafa da ya rangada mata sallama kamar daga sama.

Firgigit ta dawo hayyacinta, lokaci daya kuma ta amsa mishi sallamar fuska a sake.

Ba ta taba canjawa Mustafa ba ko sau daya duk wannan abun da yake faruwa.

Wuri ya samu nesa da ita kadan ya zauna, lokaci daya kuma yana gaishe ta.

Ta amsa cike da kulawa kafin ya ce “Mama kun fara kewa ne?”

Kamar jira take yi ta amshe “Ka bari kawai Mustafa, wallahi gidan duk ya yi min fadi. Ni na rasa me ya sa ma na amincewa Jamilu wannan tafiya.”

Murmushi Mustafa ya yi, “Ai kamar gobe za ki ga ya gama ya dawo. Zaman kadaicin kuwa a hankali za ki saba.”

“Kayya! Shekara biyar akwai tsawo Mustafa ina raye ba na raye ban sani ba.”

“Mutuwa kuma Mama ai a kan kowa ne. Fatanmu dai Allah ya sa mu cika da imani.”

“Amin.” ta amsa a sanyaye.

Shiru ya dan ratsa wurin kafin ya ce “Uhhh… Dama Mama tuwo mu ka zo a sammana.”

“Gidan bakonka ne Mustafa? Ga shi can a dakin girki, tun da na kwashe ma ban bi ta kanshi ba.”

“Dama a kwano za a sanya min, zan kaiwa Fatima ne, ba ta da lafiya.” ta cikin duhun magribar yake laluben reaction din Mama.

Duk yadda kuwa ta so boye damuwarta hakan ya ci tura.

Ji ta yi wani irin dam gabanta ya fadi, tana son Fatima sosai ko a cikin yaranta, ba ta damuwa da wautarta, ita kanta wautar Fatima wani lokaci nishadi take sanya ta.

Ta zabi ta auri Jamil ne, saboda tana ganin Jamil shi ne ya santa, ya san halinta, saboda haka zai yi hakuri da duk wata wautatta.

Kuma ta san sha Allah Fatima ba za ta wulakanta ba a hannun shi. Amma ta watsa mata kasa a ido.

Ta kai karshen tunaninta da ajiyar zuciya, kafin ta yunkura ta mike zuwa kitchen din.

Langa tuwo da miya mai fulawa ta dauka, ta sake daurayewa, sannan ta juye tuwon a babbar langar, karamar kuma ta zuba miya.

Ya karbi tuwon yana fadin “Mun gode. Ina jin ma dai asibiti za mu je yanzu.”

“Ciwon ya yi zafi ne?”
Jiki a mace ta yi tambayar.

“Eh tun jiya ne ba ta da lafiyar.”

“To Allah ya sawake, ya ba ta lafiya sai ku je asibitin ai.”

Ya ji dadin addu’ar tata sosai.

Ya amsa da “amin”

Jiki a mace Mama ta koma mazauninta, yanzu kam kaf hankalinta a kan Fatima ne.

Ba ko wane ciwo ne take kwantamawa ba, ace sai an kaita asibiti, kila kuma don akwai Jamil ne, shi ya sa ba ta ganin zafin ciwon ta.

Ji take yi kamar ta sabi hijabinta zuwa gidan Aunty Hauwa, yayin da wata zuciyar ke hanata.

Haka dai ta ci gaba da zama cikin wasi-wasi.


*****

Yadda ya bar ta, haka ya same ta, ganin shi ya sa ta tashi zaune.

Ya aje mata kwanon abinci a gaban ta.

Sosai ta yi mamaki, ba ta yi zaton Mama za ta bayar da abincin ba.

“Ki ci don Allah, zan je masallaci, an kira sallah, idan na dawo sai, mu je asibitin.”

Kai ta jinjina alamar gamsuwa.

Shi ma sai ya fice zuwa masallacin.

Kitchen din Aunty Hauwa ta shiga, ta samo plate.

A kasa ta zauna hade da ballar tukakken tuwon farar masara ƙal, ta aje a kan plate din.

Miyar kubewa busassa da ta ji manja hade da kayan miya ga nama a ciki kamar dai naman duk cikin miyar ne a ka kwaso mata.

Murmushi ta yi a hankali, kafin ta shiga ballar tuwon tana ci, duk da ba ta jin dadin bakinta, amma sosai take jin dadin tuwon.

Tana tsaka da ci ne Aunty A’i (kishiyar Aunty Hauwa) ta shigo

“Ina aka samu wannan tuwon kuma?”

Murmushi kadan Fatima ta yi “Ya Mustafa ne ya shigo da shi zai ci, sai ya ji kuma an kira sallah shi ne ya ajiye sai ya dawo masallaci.” ta shirga karya, saboda ba ta son Aunty A’i ta ji ba dadi.

“Towooo! Dama maganar abincin ce ta kawo ni.”

“Ai ki bar shi kawai tun da ga wani nan.”

“To ai kuma kin yiwa Mustafan rani.”

Murmushi Fatima ta yi, “Aunty idan bai koshi ba sai in karbo mishi na nan din ai.”

Ita ma murmushin ta yi. “To ya jikin naki? Kodai mu je asibitin ne?”

“Ya Mustafa ya ce wai idan ya dawo sallah za mu je.”

“Sannu yar gidan Ya Mustafa, komai Ya Mustafa” Aunty A’i ta fada hade da dariya daidai tana fita.

Ba ta jima da fita ba, Mustafa ya shigo, a lokacin kuwa Fatima sallah take yi.

Zama ya yi hade da cinye ragowar tuwon da ta rage.

“Ta so mu tafi.” Ya yi maganar daga wajen baranda inda ya wanke hannun shi.

Mikewa ta yi sanye da dogon hijabin Aunty Hauwa ta bi bayan shi.

Sai da suka fita waje ne, suka jera tare shi ne ya fara cewa “Wai me ke damunki ne?”

“Ciwon kai.” ta amsa shi a hankali.

“Kin sa damuwa da yawa a ranki Fatima, ba tun yau ba nake fada miki, mu janye maganar nan, saboda ni dai ba zan jure ganinki cikin wannan yanayin ba. Ga fushin da Mama ke yi kuma.”

Shiru ta yi kamar ba za ta amsa shi ba, daga bisani kuma ta ce, “Amma dai ka san na fada ma ba wannan zancen ko?”

Kai ya daga alamar eh.

“To ka bar wannan maganar ka yi ta addu’a kawai.”

“Ina yi.” ya fada a hankali.

A daidai lokacin kuma suka shiga katon chemist din.

Sun yi sa a ba kowa, kila don ba a dade da idar da sallahr isha’i ba.

Boda wanda ya wayi Fatima sosai saboda yadda take yawan ciwo a lokacin da take yarinya.

Kuma su kan sha rikici idan an kawo ta chemist, duk da ba ta jin tsoron allura sam, ko goma zai yi mata ba ta tsorata.

“Ulcern ce yau ma?” Boda ya tambaya cikin salon tsokana.

“Wannan fa kar yadauka gidan ubana ba abinci, da kullum ya ganni ya ce ulcer ce.” A hankali ta yi maganar, Mustafa ne kawai ya ji, dalilin da ya sanya shi murmusawa daidai suna neman wurin zama.

A zahiri kuma Fatima cewa ta yi “Ni kaina ne ke ciwo ba ulcer ba.”

Ya murmusa kadan hade da amsa gaisuwar da Mustafa ke yi mishi a lokacin da yake zama kusa da Fatima.

Jininta ya ja, ya mata test, ya hada da amsoshin da take ba shi. Ya fahimci abin da ke damunta.

Typhoid kadan malaria ma kadan, sai kuma ya ce ta rage yawan damuwa.

Tabe baki kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.

“Ko ita ma gaban kuka ba ta, ba baya ba?” Boda ya tambaya cike da tsokana.

Karon farko da Fatima ta yi dariya. lokaci daya kuma ta tuno ranar da ta fadi hakan.

Wani lokaci ne ulcernta ya tashi sosai, sai Jamil ya rakota chemist, a lokacin da Bodan ke kafa mata dokoki shiru ta yi tana saurare, sai da ya ce “Ban da shan yaji.”

A lokacin juyawa inda Jamil yake zaune yana sauraronsu ta ce “Uhhhhh!” kafin daga bisani ta mayar da kallon nata a kan Boda. Shi kuma ya katse ta da fadin “Da alama ba za ki daina shan yajin ba kenan.”

Murmushi ta yi hade da fadin “Gaskiya. Mu yaji ai gaba mu ka ba shi ba baya. Talaka bai sha yaji ba a wannan zamanin to me zai sha? Abun ai sai yay yawa, ba ka ci nama ba, dan yajin ma a hana ka sha. Maganar gaskiya ba zan iya ba.”

A lokacin Bodan cewa ya yi “Ashe kuwa ba za ki rabu da ulcer ba.”

Ita ma a lokacin mikewa tsaye ta yi hade da daukar ledan magungunanta tana fadin “Yo dama har wani warkewa ake yi daga cutar ulcer.”

Ta kai karshen tunaninta a lokacin da take sauka daga kan step din shagon.

“Ba kya kwana cikin net ne?” Mustafa ya tambaya a lokacin da suka kama hanyar gida.

Tabe baki ta yi kamar yana kallon ta “To kuma Ya Mustafa typhoid da Malaria ai ciwon dan Nigeria ne. Waye bai da su?”

Dariya mai sauti Mustafa ya yi “ki dai rika kwana cikin net”

“Zan jaraba, ni ka san da shi da nikab, ji nake yi suna hanamin yin numfashi cikin salama.”

Ya kuma murmusawa “Kuma fa ni kin san idan kika aure ni, idan za ki fita, dole sai kin sanya shi.”

Haka nan ta ji gabanta ya yi wata irin faduwa, har sai da kafafuwanta suka amsa, ta hanyar yin wani irin sanyi. Da kyar ta rika dagasu tana jefawa, kamar mai koyon tafiya.

“Ba ki ce komai ba?

“Zan sanya.” ta amsa a hankali.

Ya yi murmushi kadan, “Fatima kin canja lokaci daya, duk kin yi sanyi”

Ba ta ce komai ba illa murmushi da ta yi.

Sai da ya kaita har gida, ya kuma tsaya tasha maganinta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.9 / 5. Rating: 9

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 14Daga Karshe 16 >>

1 thought on “Daga Karshe 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×