Skip to content
Part 18 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Biki bidiri birede yau ake gobe sai labari, yau dai ga Fatima ta kwana a gidan Mustafa, kamar almara. Ta kwana a matsayin matarsa, shi kuma a matsayin mijinta.

Abin da ko mafarkin shi bai taba ba shi ba.

Duk lokacin da ya kalli tsaunin dukiyar da aka dankawa Fatima, sai jikin shi ya mutu, ya ji kamar ba shi da abin da zai iya ciyar da mai wannan dukiyar.

Amma yana addu’a Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da ke kansa.

Yau gidansu Mustafa kin yankewa ya yi da mutane, har aka yi magriba, kawayen Fatima da yan’uwanta na nesa suna ta zuwa yi mata sallama. Ga kuma mutanen gari yan ba a basu labari na zuwa ganin daki.

Ita kanta Fatiman ba ta samu kanta ba sai karfe takwas na dare, zaune take gefen gado bayan ta idar da sallah.

Jakarta ta janyo hade da dakko envelope din da Aunty Hauwa ta ba ta.

Sakon Ya Jamil ne da Zainab ta ba ta ranar da suka dawo daga kano. Ita kuma ta aje a kasan filon Aunty Hauwa, a can ta manta, sai jiya Auntyn ta ba ta.

Kwantawa ta yi sosai saman gadon, a lokacin da ta bude wasikar, lokaci daya kuma ta fara karantawa kamar haka…

“Assalamu Alaikum. Ina fatan kina cike da koshin lafiya, saboda lafiyarki tana daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci a gare ni, da kuma sanya ni farin ciki.
Ina mai yi miki fatan alkairi a rayuwar auranki, sannan don Allah ki rika sanya ni a cikin addu’arki, Allah ya yaye min abin da nake ji a yanzu.
Kar ki manta na fada miki idan kina da matsala ki tuntube ni.”

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, tare da zubawa ceiling din dakin ido, sakon na shi a cukurkude amma hakan bai hana ya sanyaya mata jiki ba.

Sai yanzu take jin wani abu da ba ta san ko menene ba a kan Jamil din.

Sai take jin ina ma shi ne yau a matsayin Mustafa, ta rasa dalilinsa na kin bayyana mata soyayyarshi, da ace yana gida tabbas da ta samu lokaci ta je sun yi magana, kila hakan zai taimaka wajen magance abin da yake ji din. Duk da ba ta san ko menene ba.

Jin alamun za a shigo ne ya sanya ta dukunkune takardar tare da jefata bayan gado.

Mustafa ne ya shigo hannunsa rike da leda baka, ta amsa sallamarshi, hade da mikewa ta bi bayanshi zuwa falon.

Kan kujera ta same shi zaune, ledar da ya shigo da ita tana gaban shi.

Kujerar da ke fuskantar shi ta zauna,, lokaci daya kuma tana gaishe shi cike da mutuwar jiki.

Idanuwansa akanta yake amsa gaisuwar ya dire da tambayarta “Me ya faru? na ji kin yi sanyi, ko har yanzu ciwon kan ne?”

Kai ta girgiza alamar, a’a.

“To menene?” ya kuma tambaya.

“Ba komai.” ta fada a hankali hade da share hawayen ta.

“Fatima!” ya kira sunanta a sanyaye, har ga Allah baya son wannan yawan kukan nata, tsawon daren jiya da kuka ta kare shi, haka wunin yau ma.

“Don Allah ki fada min idan akwai matsala, ke din amana ce a wurina.”

Kai ta girgiza alamar a’a.

“Zo nan” ya yafitota da hannun shi.

A sannu ta yunkura zuwa inda yake, kafin ta karasa ya janyota ta fada jikinsa.

A sannu ya rungumeta, yayin da sautin kukanta ya karu, bai ce mata komai ba, har zuwa lokacin da sautin kukan nata ya ragu.

“Ki yi hakuri don Allah, ban san me kike yi wa kukan ba, amma dai ki yi hakuri, fatana Allah ya ba ni ikon sauke nauyin da aka dora min. Rokona a gare ki shi ne, da zarar kin ga na kauce daga yadda kika sanni ki tunatar da ni zan gyara.” a hankali yake maganar, dalilin da ya sa jikin Fatima mutuwa likis.

Ajiyar zuciya ya sauke, ” Je ki kitchen ki samo wuri sai ki debarwa Inna abin da ke cikin ledar nan.”

Kamar dama jiranshi take yi, ta mike hade da daukar ledar ta yi waje.

Dakin Inna ta yiwa tsinke, a lokacin Inna kwance take saman gadonta mai rumfa har ta fara bacci, yayin da Ummi ke kwance a karamin tana karatun hausa novel.

Ummi ce ta amsa sallamar Fatima hade da mikewa zaune tana kiran “Inna! Inna!!”

Cikin magagin bacci Inna ta amsa kiran tana fadin “Me ye wai?”

“Dama Aunty Fati ce ta shigo.”

Da sauri Inna ta mike zaune “Ina Fatin take.”

Fatima da ta kasa tsaida hawayenta, da kyar ta yi kokarin saita muryarta ta ce “Gani nan.”

“Lafiya ko? Ko Mustafan bai dawo ba ne har yanzu?”

“Ya dawo.” ta ba ta amsa

“Wai kuka kika yi ne?”

Dama jira take, sai ko ta kara rushewa da kukan.

A rude Inna ta ce “Ke Ummi, kira min yayan naki.”

Lokacin da ta shiga bangaren nasu, Mustafa na kan sallaya zai yi shafa’i da wutri, shigowarta ya sanya shi dakatawa.

“Dama Inna ce ta ce ka zo.” ta fada bayan ta gaishe shi.

Tare suka juya zuwa dakin Innan, Fatima rakube tana kuka ka rantse da Allah koro ta ya yi, ya ce ba za ta kwana a wajen shi ba.

“Ke Ummi ku tafi can bangaren zan yi magana da yayanku.”

Tare suka kuma juyawa da Fatima, ya rage daga Mustafa sai Inna.

“Me yarinyar nan take wa kuka ne?”

“Wallahi Inna ban sani ba” ya ba ta amsa da iya gaskiyarshi.

“Ba ka yi mata komai ba?” ta kuma tambaya

“To Inna me zan yi mata? jiya fa aka kawo ta gidan nan, ni yaushe ma na zauna a gidan bare in yi mata wani abu?”

Nisawa Inna ta dan yi sannan ta ce “Mustafa, Fatima har yanzun yarinya ce, don Allah kada ka yi mata gaggawa, ka bi ta a hankali ka ji, har ta, saki jikinka da kai, yanzun tsoronka take ji, dalilin da ya sa kenan take ta wannan kukan.”

Sai a lokacin Mustafa ya fahimci zancen Inna, da sauri ya yi kasa da kanshi, wata irin masifaffiyar kunya ta lullubeshi, ji yake kamar ya cewa kasa ta yi mishi alfarmar tsagewa ya shige ciki.

Dalilin da ya sa Inna ta kuma cewa” Ita wannan ledar ka dauka ka kai mata, duk abin da ka sawo mata ba sai ta kawo min nan ba, idan ta yi niyya ta debo kawai ta kawo min, ni dai fatana kawai shi ne ku zauna lafiya. Mustafa ka rike amanar yarinyar nan don Allah. Ko mafarkinka bai taba ba ka za ka hada jini da zuriyar Alhaji Musa ba. To don Allah kada ka kwance mana zane a kasuwa.”

Tun dazu bakin Mustafa ya mutu, saboda haka bai iya cewa komai ba.

Illa bin umarnin Mama na mikewa hade da daukar ledar ya fice jiki a mace.

A can kuwa Fatima har ta warware suna ta labarin novel ita da Ummi.

Yanzu ma Ummin ce ke ba ta labarin novel din da take karantawa mai suna Banan.

Shigowar Mustafa ya sanya ta yin shiru, yayin da Fatima ke dariyar abin da Ummi ke fada, wai jarumar labarin ce ta dorawa kowa busasshen danwake a kan abinci, sun yi tunanin soyayyan nama ne, kowa kuma ya tauna sai ya yi shiru ya jira dan’uwanshi ya tauna, don mugunta.

“Je ki samu Plate a kitchen ki debarwa Inna, ki ba Ummi ta kai mata.”

Yana gama fadin haka ya wuce bedroom.

A can kitchen kuwa Ummi kin karɓar kazar ta yi, ta ce tsiren kawai za ta karba, kaza kam ta Fatiman ce, za dai ta zo da safe idan Fatin ta rage ta sqn mata.

” Kuma wallai ba zan fadawa Inna akwai kaza ba, don haka kar ma ki kawo. Ki aje min kawai idan kin rage.”

Ta yi maganar a lokacin da take ficewa daga part din gabadaya.
*****

Kamar yadda Inna ta bukata haka Mustafa ya ci gaba da lallaba Fatima, step by step yake koya mata yadda za ta yi rayuwa da shi, idan ya fahimci ta haddace wannan ya zame mata jiki, sai ya kuma bullo da wani, a haka har zuwa lokacin da ya mallake ta gabadaya a matsayin matarshi.

Ita din ma ta yi kokari, ta danne hade da jurewa ta yadda Inna da Ummi basu fahimta ba.

Dama Inna ba ruwan ta da sabgarsu, ko tsakar gida ba ta zama, duk da part din su Fatiman daban.

Ummi ma sai ta wuni ta kwana ba ta leka part din su Fatima ba, sai idan Fatiman ce ta matsa ko kuma abu mai muhimmanci ya kai ta.

Maganar abinci ma da kyar Fatima ta shawo kan Inna ta bar masu ita da Ummi.

Don haka aikin gidan Ummi da Fatima ne ke yi, idan ma weekend ne ba sch ti Ummi ke yin komai, iyakacin Fatima yanka albasa, bare maggi da sauran kananun abubuwa.

Wata irin shakuwa da soyayya ce ke ta kara samun wurin zama tsakanin Fatima da Mustafa, sai take jin ina ma ace tuni ta yi aure ba yanzu ba.

Wani irin rayuwa take mai cike da yanci, Mustafa burinshi kawai shi ne ya faranta mata, iyakar kyautatawa da kulawa tana samu.

Ummi ta cire mata kewar Zainab, wacce take can makarantar Alkalam tana cin biro

Sai dai kusan kullum sai sun yi waya ta wayar Mustafa, da yake Zainab din na da waya.

Dama Fatima kurman jiki ne da ita, yanzun kuma sai ta kara mulmulewa ta murje ta kara haske a sati hudu da auran nata.

Da misalin karfe tara da rabi na safiyar juma’a kwance take a karamin gadon Inna. Yayin da Inna ke zaune a kan tabarmar kaba tana nika farin kwallin da take amfani da shi.

Hira suke yi sosai, sallamar Mustafa ce ta katse su.

“Ta shi ki je ga mijinki can ya dawo.”

Cike da mamaki Fatima ta mike, saboda bai faye dawowa idan an yi break ba.

A falo ta same shi yana amsa waya, zuwa can kuma ya mika mata, yana fadin “Zainab ce.”

Fatima ta amshi wayar, gabadaya hirar tasu dai tsokana ce Zainab din ke yi, yayin da Fatima ta ki yi mata respond yadda ya kamata, saboda yadda Mustafa ya tsare ta da ido.

A lokacin da take mika mishi wayar bai amsa ba sai dai ya janyota zuwa jikinsa, hade da tura fuskarshi kasan wuyanta yana shakar kamshinta.

Sai da ya gamsu da abin da yake yi sannan ya zauna kan kujera, yana fadin “zabbi ne guds biyu gasu can, an riga an gyara, sai ki sarrafasu yadda kike so, kin san yau Alhaji yana gida, ki je ki gaishe shi.”

Tuni Fatima ta wartsake ta shiga murna hade da godiya, uffan bai kuma cewa ba ya zame ya kwanta a kan kujerar.

Duk hidimar da take yi, yana jin ta, kawai dai ya kasa tashi ne.

A haka bacci ya dauke shi, ko makarantar bai samu damar komawa ba.

Misalin karfe sha biyu na rana, Fatima ta kammala dambun naman, da kuma pepe meat, ta zubawa Alhaji da Mustafa nasu, sauran kuma ta yi dakin Inna da shi, a can suka ci, lokaci daya kuma suna aikin abincin rana ita da Ummi.

Misalin karfe biyu ta fito shirye cikin yellown lace mai digon bluen fulawa, riga da siket ne dinkin ya zauna das a jikinta.

Zaune take kan kujera ta ajiye blue mayafi da karamar possernta a gefe.

Mustafa take jira ya dawo masallaci, su tafi, ta kosa ji take kamar ta shekara ba ta je gidan ba.

Ita ma dai yau za ta je gidan a matsayin daga gidan mijinta take, ranar da kullum take ganin kamar ba za ta zo ba ga shi yau ta zo.

A kan 1sittern da take zaune ya zauna a lokacin da ya shigo.

“Ka matse ni Ya Mustafa.”

“Kodai kin matse ni.”

“Ni din.”

“Eh” ya ba ta amsa, lokaci daya kuma yana kwantawa a jikinta.

Hannu ta sanya hade da shafa kwantattar sumarsa

“Kin yi kiba fa sosai.”

“Dama da abu ta.”

“Amma ba ta kai yanzu ba, idan kin je gida kuma za a ba ki labari.” daidai yana zame sosai a kan cinyarta ya yi maganar.

“Kin yi kyau fa.”

“Na gode, kai ma ai ka yi kyan.”

“Amma ai ba ki fada ba”

Murmushi ta yi “Ka san mu din matan ustazai ne”

Shi ma murmushin ya yi hade da tura hannunsa daya cikin rigarta.

Ganin yana neman bata mata kwalliya ya sanya mikewa bayan ta ture shi.

Ya yi saurin cafkota, ta yi tsalle gefe tana dariya.

Yana daga kwance yake kallon yadda take yafa mayafinta hade da daukar karamar jakarta.

“To zo mu je.”

Make kafada ya yi alamar a’a.

Ta dan langabe kai kamar za ta yi kuka.

Ya zuba mata ido yana kallon ta, murmushi ya yi kafin ya ce mu je.

Shi ne ya dauki basket din suka shiga wurin Inna.

Ummi da ta ce za ta yi wa Fatin rakiya ganin ta da Mustafa sai ta fasa, ta ce su je za ta zo daga baya.

Inna ta bi bayansu da kallon sha’awa, fatan ta Allah ya zaunar dasu lafiya ya kuma basu zuri’a dayyiba.

To Amin in ji ni.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.1 / 5. Rating: 10

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 17Daga Karshe 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×