Skip to content
Part 19 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Kamar ko wace ranar Juma’a idan Alhaji ya zo gidan yake kasancewa a cike, da yaya da kuma jikoki, wannan lokacin ma hakan yake a cike.

Shigowar Fatima yasa gidan ya barke da hayaniyar ganinta, ita kam wangale baki kawai take yi, yayin da Mustafa tuni ya shige wajen Alhaji.

Su Aunty Aisha sai tsokanarta suke, ita kanta Mama bakinta ya kasa rufuwa, sai murmushi take yi, cike da jin dadin ganin yadda Fatiman ta canja a cikin sati hudu kacal.

Ta murje ta yi haske, jikinta ya kara mulmulewa gwanin sha’awa. Lokacin da ta shiga bangaren Alhajin Mustafa yana fitowa, hannunta ya kamo ya yi kissing wa bayan hannun sannan ya wuce, murmushi ta yi kawai hade da sallama a falon Alhajin.

Ya fadada murmushin sa, “Fatima.”

Kanta a kasa wata irin matsananciyar kunyar Alhajin take ji, kai a kasa ta gaishe shi, ya amsa cike da kulawa.

Sannan shiru ya biyo baya, kafin ya katse shirun da fadin,

“Mun yi magana gami da karatunki, amma mijinki ya roki alfarmar don Allah a dan jira ko nan da shekara daya ne, saboda shi ma ya yi applying zuwa degree, kuma ya samu Admission, shi ya sa yake son ki yi hakuri zuwa next year sha Allah sai ke ma a nemar miki.”

Kai ta daga alamar gamsuwa.

“Akwai wata matsalar ne?”

Kai ta girgiza alamar babu.

“Fatima!” Ya kira sunanta a hankali.

Kai ta dago suka hada ido kafin ta yi kasa da kan.

“Ki zauna da mijinki lafiya kin ji, ki toshe kunnenki daga jin duk wasu maganganu. Ki zama mai rike sirrin mijinki Fatima, kar ki sake ki zama mace mai bude sirrikan mijinta. Ki rufa mishi asiri a lokacin da yake da shi ko babu. Ki taimake shi a lokacin da kika fahimci yana da bukatar taimakonki.”

Da ƙyar ta ce, “In sha Allah.”

“Sannan idan kina da matsala, kai tsaye ki zo wajena, ki fada min, ban ce ki je wurin kowa ba.”

Nan ma kan ta daga.

“Idan akwai wani abu ki fada, idan kuma babu ta shi ki je Allah ya yi miki albarka.”

“Amin na gode.” A hankali ta furta hakan, lokaci daya kuma ta mike hade da ajiye mishi basket din da ke hannunta.

“Allah ya yi miki albarka, na gode sosai.”

A zuciyarta ta amsa da amin.

Daga nan wurin Mama ta yi burki, suka gaisa cike da walwala, da alama Maman ta sauka, don kuwa sun dade suna hira.

Sannan ta koma tsakar gidan, inda sauran yan’uwanta suke, bayan ta dauki zanen Mama guda daya.

A tsakar gidan ta cire kaf kayan jikinta ta sagala a kan igiya har da breastwear.

Aunty Aisha da ke ta dariya ta ce “Abar hali a ci me? Dama an ce idan ka rabu da ganin mutum kar ka tambaye shi hali, tambayar shi ya yi dukiya, don hali dai yana nan ba canji.”

“To! Ai ke tuni na san irin zaman da nake yi da ke, A’i. Dama kuma ke ba ki taba ganin dan karuwa a gado, bakinki, ya yi shiru, sai kin tambayi ina uban shi.”

“To idan ba mugun damu ba me ya kai fura zane?”

“To mugun damun ne.” Fatima ta ba ta amsa lokacin da take zama a tsakiyarsu.

Mama da ta fito ta rike haba tare da fadin “Oh ni Hajara, anya Fatima kanki daya kuwa?”

“Me kuma na yi?”

“Au tambaya ma ki ke yi don Allah. Haka kika ga sauran yan’uwanki na yi. Yanzun fa ba da ba ne. Sai kawai ki cire kaya ki zauna haka a tsakar gida.” Cewar Mama har zuwa lokacin hannunta na kan habarta.

Fatima da ta saki baki tana kallon ta, ta janye idonta, tare da rike habarta” Na shiga ukuna. Gidan ubana ne fa, ni da gidan ubana. To Mama don na yi aure shi ne me? Nan fa gidanmu ne, kuma har yanzu hakan bai canja.”

“To mai gidan uba,, barkanmu da ba a golanci aka kawo mu gidan nan ba, da Wallai Fatima ce za ta kore mu. Tun da gidan ubanki ne ai sai ki yi tsirara ma, mutum da gidan uban shi.” cewar Aunty Ayyo.

“Kin dai san ai zan iya wallahi.”

“To gwada.” cewar Aunty Sadiya.

“Wai da ma kuka dame ni, don Allah yaushe Aunty Hauwa ta daina fitowa gidanta da zane a kirji ne? Ke ma Aunty Ayyo kwanan ne fa kika daina haura katanga idan kin yi dare.”

“Yaushe na tsallako mutane da zane a kirjin?” Aunty Hauwa ta cafe a lokacin da take shigowa.

Dukkansu suka kwashe da dariya har da Fatima.

“Aunty Hauwa mu fadi gaskiya, ba kya baro gidan Hakimi zuwa nan gidan da zane a kirji?”

“Amma ke kin san lokacin ne? Kin san lokacin da aka yi hakan?”

“Afff! Ashe dai an yi.” cewar Fatima tana gyara zamanta

Aunty Hauwa ta wuce bangaren Alhaji tana fadin, “Ni shi ya sa ba komai nake son a ba Fatima labari ba, shegen baki ne da ita uwa reza. Lokacin fa tun ina amarya ne, kuma fa ko cikinta babu, amma kin ji kamar a gaban ta aka yi.”

“Ba ma gara ke ba, ni yaushe na haura katanga kamar wata barauniya.” cewar Aunty Ayyo cikin tabe baki.

“Ni fa kaf dinku ina da tarihinku a nan dina.” Ta yi maganar a lokacin da take buga tafin hannunta.

“Ban da nawa kam.” Cewar Aunty A’isha.

“Wallahi na ki ma ya fi yawa, ke da zan daure ma idan na zama alkali ko kin dauka na manta ne? Ba dole in samu detail na ki ba, saboda kafa hujja.”

Dukkansu suka yi dariya.

Haka suka wuni cikin raha, a yi fada a shirya.

Sai isha’i Mustafa ya zo suka tafi, bayan ya gaishe da Mama.

*****

Dakin Inna suka yada zango Mustafa ya ci abinci, don Fatima a koshe take, suka kara taba hira, sannan suka wuce sashensu.

Zaune take a tsakiyar gadon bayan ta yi wanka hade da shirin bacci.

Mustafa kuma yana kan side drower, sako yake turawa da wayarsa kirar Samsung.

“Fatima.” ya kira sunanta bayan ya tabbatar da tafiyar sakon da ya tura.

“Na san kin ji labarin tafiyata makaranta ko, dama can ina ta processing, Allah bai amince ba sai yanzu, hakan baya nufin rashin ci gaban naki karatun, shi ya sa ma na fara tunkarar Alhaji da maganar kafin ke, na san za ki fahimta sosai ta bakin shi. Kar ki ji kamar burinki ba zai cika ba don Allah.”

Sauke numfashi ta yi sannan ta ce” Ba komai Ya Mustafa, daga ni har kai Allah ya cika mana burikanmu na alkairi. Na yarda da kai, bana jin za ka yi wani abu da zai zama muzgunawa ne a wajena.”

Gadon ya hau sosai tare da janyota jikinsa” Na gode ma Allah Fatima da ya ba ni ke a matsayin mata, in sha Allah ba zan ci amanarki ba, zan yi miki hallaci ma fi kyawon halicci, zan ci gaba da sonki gami da kaunarki har zuwa numfashina na karshe. Ki rike wannan.”

Tuni Mustafa ya kashe ta da kalamansa masu dadi, wanda suke kara mata son shi, da ninka yardarta a kanshi.

In sha Allah za ta ba kowa mamaki, Mustafa zai yi alfahari da ita sosai a matsayin matarsa.

*****

Ba ta san ta shaku da Mustafa ba, sai ranar da zai tafi Kano don ci gaba da karatun shi a fanni na’ura mai kwakwalwa.

Tun tana daurewa, har dai ta sake kukan ta mai sauti, a lokacin da ta ga ya dauki jakarsa ya rataya.

Jikinsa ya mutu lakwas, da kyar ya sauke jakar zuwa kasa, lokaci daya kuma ya janyota jikinsa a hankali yana bubbuga bayan ta alamun lallashin.

Sautin kukun nata ya fara yin kasa, duk kuwa da tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi.

Ya ja ta zuwa kan kujera, ya dorata a kan cinyoyinsa, yayin da kanta ke kwance a kan kirjinsa.

“Fatima ba kya so in tafi ne?”

Kai ta girgiza alamar a’a

“To menene?”

Shiru ta mishi sai wani sabon kukan da ta fara.

“Fatima da kwarin gwiwarki zan tafi, idan kuma ba kya so wallahi zan fasa tafiya. Burina kawai shi ne ki yi farin ciki.

Na fi ki jin zafin tafiyar nan, duka fa watanmu uku da aure, ba ni da hali ne, amma da na tafi da ke na kama mana gida a can. Please fada min me kike so?”

Kamar ba za ta yi magana ba, sai kuma ta ce” Ina jin tsoro ne Ya Mustafa, kar ka je wata ta dauke maka hankali, ka manta da ni.”

Murmushi mai sauti ya yi tare da dago fuskarta” Kishi Fati, dama kina da kishi wai? Oh my God “

Duk da idonta yana cike da hawaye sai da ta dalla mishi harara.

Shi kuma ya ja habarta tare da cewa.

“Ba wannan ne yake damunki ba, ni na san me ke damunki, damuwarki shi ne zan yi nesa da ke. Ki dauka a kan dole ne zan yi hakan, saboda ni na ma fi ki damuwa Fatima. A bangare daya kuma ina son tabbatar miki da cewa ban taba kallon wata mace ba sai ke, ba ni da lokacin batawa na saurarar wata mace, yanzu lokaci ne na gina mana rayuwa. Ki rika yi min addu’a Allah ya cika min burina.”

Hannu ta kai hade da dauke hawayen da ke bin fuskarta.” In sha Allah zan yi. Ina yi maka fatan alkairi, Allah ya tsare ka daga dukkan sharri amin. “

Ba don sun so ba suka rabu, Fatima kuwa wunin ranar da ciwon kai ta wuni. Ga babu wayar da za ta kira ta ji ya isa.

Ummi da Inna ne ke ta kokarin debe mata kewa.

Saboda Ummi littafai ta yo renting ta ce Fatima ta kwanta, ita kuma ta karanta mata.

*****

Tun da Mustafa ya tafi Fatima ke fama da ciwon kai, da kuma zazzabin dare, daurewa kawai take yi, don ma ba wani aiki take yi ba.

Duk bayan kwana daya Mustafa ke kiran wayar abokinshi, abokin ya bayar a kawo ma Fatima su yi magana. Wannan na kara rage mata kewar shi, har ma abun ya zama jikinta.

Yau Sunday, ya kama satin Mustafa biyu da ta fiya, yau din kuma ta tashi da wani irin zazzabi mai zafin gaske.

Inna ce a kanta da Ummi tamkar su dauke ciwon zuwa jikinsu.

Da kyar Inna ta lallabata ta sha kokon gero da ya sha kayan kamshi.

Dire kofinta ke da wuya, ta yi waje da gudu, amai take shekawa tamkar za ta amayar da kayan cikinta.

Abu kamar wasa, daga safe zuwa azahar Fatima ta galabaita, ko ruwa ta sha sai ta yi aman shi.

Ba shiri Inna ta yafa zanenta, ta fice zuwa wurin abokin Mustafa.

Mustafan a ka kira mata, ta shaida mishi abin da ke faruwa.

Ko mintuna goma Mustafa bai kara ba a cikin Makarantar ya dakko hanyar gida, bayan ya fadawa abokin na shi, ya ba Inna kudi a kai Fatima asibiti kafin ya iso.

Misalin karfe uku na yamma kwance take, hannunta manne da allurar karin ruwa, Aunty Hauwa, Ummi, Inna da su Aunty Aisha duk suna kan tabarma a kofar daki.

Suna hirarrakinsu, saboda jikin Fatiman akwai sauki sosai, musamman yadda suka san me ke damunta a lokacin, ciki ne da ita, da bai wuce sati shidda ba.

Sai magariba aka cire mata ledar ruwa ta biyu, a kuma daidai lokacin ne kuma Mustafa ya dira asibitin, ba tare da ko gida ya je ba.

Kunyar su Aunty Hauwa ce ta hana shi shiga cikin dakin, sai ya tsaya daga kofa, yana kallon Fatiman da ke zaune a gefen gado, suna shirin tafiya gida. Saboda an sallame su. Bai ce komai ba, illa kallon ta kawai da yake yi daga bisani ya juya zuwa ofishin likita.

Aka yi masa bayanin komai, lokacin da ya fito su Fatima ma har sun fice daga asibitin.

Sai da su Aunty Hauwa suka kai ta har gida, sannan suka wuce gidan Mama.

Mustafa kuwa sai da ya yi sallahr isha’i sannan ya shigo gidan, dakin Inna ya fara shiga suka gaisa, tare da tattaunawa a kan ciwon Fatima, sannan ya wuce bangarensu.

A lokacin Fatima kwance take a kan kujera, jikin nan fayau, haka ba tare me ba, kamar ba ita ce ta sha ruwa ba.

Kanta ya daga ya zauna, sannan ya mayar da kan a kan cinyarsa hade da shafa sumarta

“I’m sorry Fati, sorry, sannu kin ji, Allah ya ba ki lafiya, ina jin kamar in karbe ciwon nan daga jikinki. Na rasa kalmar da zan yi amfani wajen yi miki sannu.”

“Me ya sa ka dawo?” ta yi tambayar a hankali cikin murya irin ta mara lafiyan da ya sha jiki.

“Ta ya ba zan dawo ba, a tunaninki zan iya bacci ba tare da na ganki ba? Hankalina sam ba zai kwanta ba ai.”

Murmushi ta yi, hade da yunkurawa alamun za ta ta shi.

Ya yi saurin mayar da ita, “No kwanta kawai, kina bukatar wani abu ne?”

“A’a zan zauna ne da kawai.” Ta ba shi amsa bayan ta tashi zaunen.

Suka zubawa juna ido, kafin ta dauke nata hade siririn murmushi.

Shi kuwa cigaba da kallon ta ya yi, cike da so da kuma kauna, gami da wani irin shauki, tamkar ya bude kirjinsa ya saka ta ciki.

Fatima dauke da cikin shi, wane irin abu ne wannan mai kama da mafarki.

Da ace bai yi applying ba, aka ce Fatima na da ciki, tabbas da fasawa ya yi, ya zauna yana kallon ta hade da tarairayarta har zuwa lokacin da Allah zai nufe ta da sauke abin da ke cikin ta.

Hannu ya kai hade da shafa cikin nata

Da sauri ta ce “Menene?”

“Ba komai, na san kina jin yunwa ne?”

“Amma ba na son cin komai.” Cewarta kamar za ta yi kuka.

“Ki tuna da kyau, me kike son ci?”

Shiru ta yi na wasu dakiku kafin ta ce “Ban tuna komai ba, dama-dama dumamen tuwo da miyar kubewa busassa, mara manja.”

Shiru ya yi kafin ya ce “Akwai dai tuwon ai, wace irin miya kuka yi?”

“Kuka.” ta ba shi amsa

“To ya za a yi kenan yanzun?”

“Ban sani ba, amma ni shi kawai nake jin zan iya ci.”

Shiru ya yi kafin ya mike tsaye “Ina zuwa?”

Komawa ta yi ta kwanta bayan fitar shi.

Kamar 20mns kuwa ya dawo, bai shigo dakin ba, amma daga inda take tana jiyo ɓuruntun shi a kitchen.

Har ta gaji ta mike zuwa kitchen din a hankali jiri na dibarta

“Me kake yi ne?” ta, yi tambayar bayan ta zauna saman dankalincda ke kofar kitchen din.

“Kina son a sanya miki daddawa ne, ita nake nema.”

Sai da ta murmusa kafin ta ce “Me za ka yi?”

“Miyar kubewar mana.” har zuwa lokacin bai juyo inda take ba, hankalinsa na kan bubbude samirun da ke kitchen din.

Wannan karon dariya mai sauti ta yi “Ya Mustafa wai miyar kubewar za ka yi da daren nan, karfe tara fa.”

“Ba dai kina so ba.”

“Ina so kam, ka bar shi kawai.”

“Allah tun da kina so sai an yi, ina dai daddawar?”

“Tana wurin Inna fa.”

Bai ce komai ba, ya tsallake ta.

Inna da ke bacci ta rika jin bari a cikin dakin ta

“Kai waye nan?”

“Ni ne Inna.”

“Mustafa ne?”

“Eh.”

“Jikin Fatin ne?”

“A’ah Inna.”

“To me ya faru kake ta ɓuruntu kamar bera?”

“Inna daddawa nake nema?”

Ta yi saurin ta shi zaune daga kwancen da take

“Daddawa kuma? Me za ka yi da dadddawa a tsakiyar daren nan?”

“Inna yanzu fa ko goma ma ba ta yi ba.”

“To me za ka yi da daddawar?”

Shiru kamar ba zai amsa ba, sai kuma ya ce ” Miya zan yi.”

Ummi da ke kwance kan karamin gado, dariya ta kwace mata. Don dama ba bacci take yi ba, jin alamun shigowarshi ne ya sanyata, kife littafin da take karantawa kasan filo, sannan ta rufe idonta kamar mai bacci.

“Wace kuma irin miya ce za ka yi da daren nan Ni Maimuna”

“Me ye abun dariya, tashi ki nemo min daddai, ki je ki daka ki yi miyar.”

Ummi ta sakko sumi-sumi, ta dauki dadddawar ta bi bayan shi, don tuni ya fice daga dakin.

Inna kam komawa ta yi ta kwanta, ta ci ba da baccin ta.

Zainab dai ba ta bar sashen nasu ba, sai da ta gama miya, ta kuma dumama tuwon. Mustafa ne ya sako ma Fatiman, amma ko lafiyayyun loma biyar ba ta yi ba, ta ce ta koshi.

Duk yadda ya so kara ba ta kara ba, saboda ta ce mishi amai za ta yi.

Dole ya hakura suka kwanta, sai dai kuma cikin dare ta tashi fiye da sau biyar tana cin tuwon, wani lokaci su tashi tare da Mustafa, wani lokaci kuma ita kadai, kuma ba wani da yawa take ci ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.8 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 18Daga Karshe 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×