Skip to content

Daga Karshe | Babi Na Shida

  • by
4
(2)

<< Previous

Zainaib da ta san shiriritar Fatima a gida, tana mamakin natsuwarta a makaranta, sosai take mayar da hankalinta gurin karatu.

Kamar wannan lokacin ma da tattara komai ta watsar ta fuskanci karatunta, tana son samun result me kyau da zai taimaka mata zuwa makaranta gaba da secondary.

Tana son zama malamar jinya ko ta makaranta, so take ta ji alert na shigar mata duk wata tana kashe matsalolin gabanta ba tare da ta jira miji ba, kamar dai yadda yan’uwanta mata kan yi.

Hankalinsu kwance su sanya sutturar da suke so takalmin da suke so, turarurruka, da sauran kayan kyale-kyale na mata.

Ba sa jiran miji, tana son ta ganta a irin wancan matakin. Kuma ta san karatun ne kawai zai kai ta, don haka take mayar da hankalinta sosai.

A can gida kuwa Kabir ya zo, in aka je tambayar mishi auran Asma’u. Mama ta yi kokarin cika alkawarin Fatima, don kuwa an sanya bikin ne bayan Fatin ta dawo da sati daya.

Daya alkawarin ne ba ta samu damar cikawa ba, don Kabir ya kawo uzurin da ba zai iya ziyartar Fatin a makaranta ba, amma ya dauki alkawarin duk lokacin da za aje mata visiting zai aiko da kudin da za a siya mata abu a kai mata.

A can makaranta kuwa Fatima mayar da hankali ta yi sosai a kan karatunta

Duk da lokuta da dama maganar Mustafa na ba ta da aji yana damunta sosai, tana son tattauna maganar da wani, dalilin da ya sa kenan ta kalli Zainab da take gefenta tana zana hoton Amoeba a cikin littafin practical nata na Biology ta ce,

“Kin san me Ya Mustafa ya fada mun kuwa? Wai cewa ya yi bana da aji ban iya kwalliya ba, kullum ina zaune da zane kirji.”

Zainab ta dakata da rubutun tana kallon Fatima daga bisani kuma tuntsirewa da dariya ta yi kafin ta ce,

“Wallahi ya gama da ke.” har yanzu dariyar take yi

“Mtsww!” Fatima ta ja dogon tsaki

“Amma gaskiya ne?”

“Gaskiya ne mana Goggon Fati, mace ai yar kwalliya ce, idan ba dai Goggon kike son zama.” Zainab ta ba ta amsa

“To ya zan yi in gyara? So nake in ba shi mamaki.”

“Ki rika kwalliya kila yana son shiga ne.” Cewa Zainaib a lokacin da ta mayar da hankalinta kan zanenta.

“Ina zai shiga?” Fatima ta tambaya hade da kallon Zainab.

“Zuciyarki mana.”

“Uwar ma zuciyata, zan lafta miki ashar, an fada miki aure ko soyayya na gaba ne yanzu.”

Mikewa ta yi hade da dakko kayan sport na makarantar ta sanya, don a lokacin karfe biyar na yamma kuma kwararriyar yar volleyball ce. Bayan ta gama shirin ne ta fice ba tare da ta cewa Zainab komai ba.

*****

A can gida kuwa hankalinsu ya karkata ne kan hidimar auran Kabiru, kamar yau ma da dakin Mama yake cike da yaran ta da jikoki.

Aunty Sadiya dake aure Katsina ta zo dauke da gudunmuwa ta Aunty Asma’u ma da take aure a Kano ta iso su Aunty Aisha, Hauwa da Aunty Maryam duk suna hallara a gida, ana ta hirar zumunci hade da tattauna yadda biki zai gudana

Anko kala uku aka fitar shadda material da atamfa. Aunty Hauwa ita ta yi wa Zainab da Fatima duka ankon. Yayin da Mama ta zabawa Fatima lace green da jefin fulawa fara me kyau, kowa ya ga lace din ya kan yaba kamar yanzu ma da yake hannu Aisha yaba kyan lace din take

“Mama ki fansar mun da lace din nan, ko kin dinkawa Fatima ba wani sanyawa za ta rika yi ba, a haka zai lalace.”

“Duk kun gama fitinarku ku bar ni da lace din nan idan ta zo ta baki da kanta ba zan hana ba, amma yanzu dai ba wanda zan ba.”

“Ana yi wa Fatima gwaninta ne mama, za ta iya kwance miki zane a kasuwa.” Cewar Maryam da ke zaune tana shayar da karamin danta.

“Wallahi kadan daga aikinta, nan na siya masu Pakistan ita da Zainab yarinyar nan sai cewa ta yi wai ita ba za ta iya yafa gyalen Pakistan ta fita ba, wai ya ma zama uniform kowa shi yake yayi ita ba ta so.” Aunty Hauwa ta fada

Duk suka tuntsire da dariya. Hirar tasu da yawanta a kan Fatima ne.

Da yamma lis suka koma gidajensu

A makaranta kuwa su Fatima suna zana jarabawar karshen zango ne, wanda daga ita zasu shiga aji shidda.

Fatima zuciyarta tab, da yadda za ta shayar da Mustafa mamaki ta iso gida, don kuwa ta yi alkawarin sai ta nuna wa Mustafa ita mace ce me aji ba kamar yadda yake tunani ba.

Tun ta iso gidan ba ta zauna ba ita da Zainab shirye-shirye n biki kawai suke, misalin kai dinkuna amsawo da kuma wanke kai.

Kamar yau ma da ta shigo gidan a gajiye, tun a farfajiyar gidan ta tube hijabin jikinta lokaci daya kuma ta zauna akan dutsen da ke tsakar gida.

Mama da ke daki tana shara ta fito hannunta rike da tsintsiya tana fadin “Har kin dawo daga wanke kan?”

Zame dankwalin da ke kanta ta yi, matsakaicin gashinta ya bayyana bakikkirin

“Ma sha Allah!” Mama ta fada, ta kara da “Ban taba ganin kin yi shiri a biki kamar wannan ba, tun yanzu har kin yi kyau.”

Shigowar Jamil ne ya hana ta bayar da amsa tare suka amsa sallamarshi ita da Mama

Ya jefa kwayar idonshi akan bakin gashin Fatima da ya sha gyara, wanda hakan ya kara fito mata da round face nata, fuskar ta dashe hade da yin fayau idan ka dauke dark spot jefi-jefi a kan fuskar nata, wanda ya zama kamar kwalliya.

Haka nan ya ji jikinshi ya yi wani iri, bakon yanayi ya ziyarce shi.

“Sannu da dawowa.”

Fatima ta fada a lokacin da ta kai hannu tana sosa tsakiyar kan nata a hankali ba don yana mata kaikaiyi ba. Labbanshi ne kawai ya motsa alamar amsawa a lokacin da ya duka yana gaishe da Mama.

Bayan amsa gaisuwar ne ya wuce sashensu, don dawowarshi daga gurin aiki kenan

“Dazu sakona na Kano ya iso, na zaba miki gyale kore me kyau da zai yi daidai da leshenki.” cewar Mama tana kallon Fatima

Fatima da daman Maman take kallo ta ce “Haba Mama, kin daukan mun Koren leshe, kin siya mun sarka Koriya, duk na yi shiru ban ce komai ba, yanzu kuma sai ki siya mun koren mayafi, hala so kike ran bikin akuya ta yi ta bi na, ta yi tsammanin ciyawa ce?”

Jamil da yake niyyar fitowa duk yadda ya so kin daurawa sai da ya yi murmushi me sauti.

Mama kuwa daure fuska ta yi, kafin daga bisani ta daga tsintsiyar da ke hannunta ta jefawa Fatima.

Cikin hanzari Fatima ta mike gami da kaucewa tana dariya.

Jifan Mama bai fadi a banza ba, don kuwa ya samu ƙwaurin Mustafa da yake shigowa.

Dalilin da ya sa Fatima kara tuntsirewa da dariya kenan tana kallonshi…

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×