Skip to content
Part 2 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

Daliban Kirki

01. 

Ɗalibai ‘yan kirki waƙe za mu fara, 

Kome za mu fara sai mu ce Bismillah, 

Bayan mun farka sai mu je mu yi Sallah, 

Sannan mu je mu gaida iyayenmu. 

 02. 

Daga nan kuma sai mu je mu yi wanka, 

Bayan mun yi wanka sannan sai mu shirya, 

Daga nan kuma sai mu je mu karya, 

Sannan mu tafi zuwa makarantarmu.

 03. 

Ba ma yin wasa in har mun hau hanya, 

Kowa yasan tabbas ai muna da kunya, 

Kuma an sanmu sam-sam ba ma jayayya, 

Alhamdullah mun zamo masu tarbiyya.

 04. 

A kodayaushe muna son junanmu, 

Kuma sam-sam ba ma raina iyayenmu, 

Muna yin ladabi gare su malamanmu, 

Neman aƙidar mu. 

 05. 

Mun ci sa’a mu dai ba ma shashanci,

Mun zamo ɗiyan kirki masu sada zumunci,

Kuma kowa yasan ba mu da lalaci, 

Mun ɗau aniyar yin faɗa da jahilci.

 06. 

Ya Allah muna roƙonKa Ka shirye mu,

Sannan mun roƙeKa Ka kare iyayenmu,

Daga su har ma da dukka malamanmu,

Albarkacin Muhammadu Manzonmu. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tambaya 1Tambaya 3 >>

1 thought on “Tambaya 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.