Skip to content
Part 25 of 25 in the Series Duniyata by Fatima Dan Borno

Gaba ɗaya sun gama fita hayyacinsu, suka ji bugun ƙofa da ƙarfi. Dole Irfaan ya dakata daga abin da yake shirin yi, ya manneta da ƙirjinsa da yake jin kamar ya tsaga ƙirjin ya cusata a ciki.

Jin bugun ƙofar ya yi yawa yasa Ihsaan ta ɗan ruɗe. Irfaan ya raɗa mata,

“Ki kwantar da hankalinki kinji? Babu wanda zai shigo ki natsu.”

Ahankali natsuwar ta dinga zuwar mata. Shi ya taimaka mata ta mayar da komai nata, sannan ya kaita kujera ya zaunar da ita. Shima ya kintsa kansa sannan ya tafi ya buɗe ƙofar.

Cike da mamaki yake duban Shamsu. Kafin yasan me zai ce har Shamsu ya ratsa shi ya wuce ciki yana cewa,

“File na kawo maka kasa hannu. Tun ɗazu nake kwankwasa ƙofa baka buɗe ba, ko dai gimbiyar ce ta hanaka?”

Ya ƙarashe yana duban Ihsaan da ta rufe idanunta kamar mai barci. Babu komai abakinta saɓanin da suka taho da jan baki abakin. A zuciyarsa ya ce,

‘Maye ya shanye. Zanyi maganinka Irfaan.’

“A’a su Ihsaan barci akeyi ne?”

Da ƙyar ta iya buɗe jajayen idanunta. Akaro na farko ta ji wani irin mugun tsanarsa. Bata ga dalilin da zai dinga yi mata irin wannan shisshigin ba. Ina ruwansa da barci take yi ko idonta biyu? Bata ce masa uffan ba ta mayar da idanun ta rufe. Irfaan ya dinga tausar zuciyarsa, da ƙyar ya iya tanƙwara kansa ya ƙaraso kawai ya karɓi file ɗin.

Ko alama Shamsu baida alaƙa da case ɗin. Hasalima admin ce take da ikon kawo masa file ɗin ba Shamsu ba.

Shi kansa Shamsun awurinta yaje ya karɓe file ɗin ya kawowa Irfaan, saboda tunda suka shiga suka rufe hankalinsa ya gaza kwanciya, har kowa da ke cikin ɗayan Ofis ɗin sun fahimce shi baya cikin natsuwarsa.

“Ɗauki ka je.”

Irfaan ya yi magana cikin ɓacin rai. Har zai sake magana Irfaan ya riga shi,

“Ihsaan tashi mu je gida kada ki yi barci anan.”

Anan ma buɗe idanun kawai ta yi. Ihsaan wata irin macece mai tsananin sanyi idan irin hakan ya haɗata da Irfaan. Takan rasa duk wani ƙwarin jiki. Muddin Irfaan zai taɓata sai ta jima bata dawo daidai ba.

“Ko dai bata da lafiya ne?”

Shamsu ya tambaya yana sake kallon Ihsaan.

Babu wanda ya amsa masa, ya kamo hannun Ihsaan suka fice Shamsu yana biye da su a baya.

Bayan sun tafi ne Salisu ya ƙaraso wurin Shamsu ya ce,

“Shamsu kana wuce gona da iri. Kana yawan yiwa Oga Irfaan shisshigi kafi kowa sanin halinsa, don kuwa sai dai ka baiwa wani labarinsa. Ina kula da abubuwan da kake yi. Don ya shigo da matarsa sai ka hana kanka sakat? Sai kace wanda ke sonta? Kada ka mance fa lokacin da muka je ɗaukota kafi kowa zaƙewa da zaginta. Yanzu shisshigin me kakeyi babu ko kunya?”

Shamsu ya ɓata rai sosai ya ce,

“Ji wata maganar banza. Ina ruwanka da ni? Kuma ni da ace Irfaan ɗin bai kirani ba, babu abin da zanje yi. Allah ya tsareni inso wannan ‘yar ƙauyen. Kada ka sake yi min haka bana so.”

Ya wuce fuuu kaman zai tashi sama. Salisu ya girgiza kai kawai ya wuce abinsa.

Kai tsaye gidansu Umma suka wuce. Abba ya tara su a falo, ya ce yana so zai aurar da Zarah da Sadiq… Iffan kuma sai nan gaba kaɗan.

Wannan lamari ba ƙaramin farin ciki yasa a zuciyar Irfaan ba.

“Abba angama magana da na wurin Zaran kenan?”

Abba ya jijjiga kai,

“Mun kammala magana. Mun yanke shawaran watanni biyu masu zuwa za ayi bikin.”

Gaba ɗaya suka yi adduar Allah ya kaimu. Zarah da Ihsaan suna komawa gefe Ihsaan ta yi tsalle ta rungumeta suna ta murna.

Bayan sun koma gida ne Ihsaan ta dubi Irfaan ta ce masa,

“Ko dai akwai wani abu da abokinka yake nufi dani ne? Ina jin zafin abin da yake min.”

Irfaan ya dubeta kamar zai yi magana sai kuma ya ce,

“Nan da Sati biyu zaku kammala Makaranta ko? Zaki yi aiki ne ko kuwa zaki bari ingina maki asibitinki?”

Ta fahimci ya kauda maganar ne, don haka ta ɗan yi shiru, daga bisani ta ce,

“Zanyi aiki a asibitin nan da suka matsa min da roƙo, na yanke shawarar zan zauna da su ɗin kafin Allah ya kawo yadda za ayi. Wallahi idan na je asibiti sai naji na ƙara imani. Wato matsalolin mata suna da yawa. Ina so idan ma asibitin za a gina muje karkararmu a gina acan su amfana da karatuna.”

Irfaan ya jinjina kai.

“Wannan ma shawara ce. Ihsaan ba mata ne kaɗai suke cikin wani hali akan laluraba harda mazan. Kawai don dai kun cika son kanku ne da yawa.”

Ihsaan ta yi dariya ta miƙe ta yi kitchen.

*****

Komai ya yi farko zai yi ƙarshe. Ayau Ihsaan ta kammala dogon karatun da ta ɗauko mai tsananin wahala. Su Umma ne suka kewayeta a cikin mutane kowa murna yake yi mata. A yau ɗin aka zaɓe su harda ita aciki aka basu award na girmamawa akan ƙwazonsu.

Ihsaan ta ɗauki award tana farin ciki hawaye na sauka daga idanunta ta ce,

“Na sadaukar da wannan karramawata ga mutane biyu masu mahimmanci a cikin rayuwata. Na sadaukarwa Yaya Sulaiman da Yaya Irfaan.”

Duk da bata ga Irfaan a wurin ba, sai leƙe take yi amma babu shi. Sai jin mutum ta yi abayanta yana tafa mata. Tana juyowa ta dube shi sai ta fashe da kuka. Shi kuwa tsabar farin ciki ya kasa magana sai tafi kawai da yake yi mata. Duk acikinsu Ihsaan ta fi kowacce yarinya ƙwazo.

Da ƙyar ya lallasheta ta daina kukan. Mutuwar Sulaiman ya dawo mata sabo, yasha gaya mata wannan ranar tana tafe, ashe da gaske yake yi. Bata taɓa zaton zata iya kaiwa labari ba, sai gashi ta kai har ta wuce. Ta yi zaton ƙwaƙwalwarta ba zata iya yin abin arziki ba, ashe ita ce ma wacce tafi duk uban ɗaliban.

Kai tsaye gidan Umma suka wuce, anan suka ga abin mamaki. Zarah da Sadiq da Iffan sun haɗa mata ‘yar ƙwarya-ƙwayar walima acikin gidan. Farin ciki ya yi mata yawan da ta kasa rufe bakinta.

Hatta Baba Sani sai da ya bayyana acikinsu. Ihsaan ta yi kuka har ta ji babu daɗi.

Agajiye suka dawo gida, kowannensu ya nufi ɓangarensa. Ihsaan ta yi wanka ta shafe jikinta da humra kamar yadda ta saba, ta nufo ɗakinsa hannunta ɗauke da kofin shayi. Yana kwance akan gado kamar mai barci.

“Ka gaji ko? Ga tea.”

A natse ya tashi ya karɓa yana kurɓa ahankali.

Bayan sun natsa ne ya jawota jikinsa sosai ya ce,

“Congratulation Dear. Na sauke wani nauyi mai girman gaske, wanda na ɗauka shekaru masu yawa, sai yau Allah ya bani ikon saukewa. A yanzu nima zan iya yin komai tunda na cika alƙawarina.”

Ta kasa magana sai ajiyar zuciya. Ana zagin maza, ita kuwa ta yi dacen mijin aure, mijinta ɗan aljannah ne.

A natse yake sarrafata cikin wata siga mai wahalar fasaltawa. Jin su suke yi awata duniya. Ya dinga bin ko ina ajikinta. Hakan yasa ta ƙara narke masa. A wannan lokacin ta ji wani irin azaba irin wanda bata taɓa ji ba, girgiza kai kawai take yi. Ta ci alwashin ko mutuwa zatayi ba zata taɓa yi masa raki ba. A irin wannan rana mai matuƙar mahimmanci Irfaan ya karɓe ajiyarsa, a irin ranar shi da kansa ya zama cikakken mutum, a irin lokacin nan ya fanshe duk wata gajiya da ya kwaso.

Bayan ya samu natsuwa barci ya kwasheshi ba tare da ya iya dubata ba, itama ta kasa motsa koda ɗan yatsanta hakan yasa ta kwanta ahaka. Cikin dare yana farkawa ya dasa daga inda ya tsaya. Tana jinsa, tana jin zafin har cikin ranta amma ta kasa nuna masa wata alama da zata nuna masa ba zata iya ba.

Sai da ya kula kamar da gawa yake kwance kafin ya ankare da irin mummunar ta’asar da yayi. Ya dinga girgizata shiru. Babu shiri ya ɗauketa ya yi waje da ita.

Farfaɗowa ta yi ta ga anayi mata ƙarin ruwa. Umma tana gefenta tana yi mata sannu. Umma ta jima tana mamakin abin da suka ji daga wurin likita. Wato tun tsawon shekarun nan Irfaan bai taɓa karɓan hakkinsa agun matarsa ba sai yanzu. Shi kuwa wani irin mutum ne?

“Umma zansha ruwa.”

Ta katsewa Umma tunanin da take yi, da sauri ta bata ruwan tasha. Umma ta ci gaba da jinyarta har ta ji sauƙi, don haka ta ɗauketa ta dawo da ita gidanta akan sai ta sake warkewa.

Umma ta dage tana baiwa Ihsaan abubuwa na gyara, da su farfesun ‘yan shila yaji alawasshi. Irfaan duk ya ƙosa adawo masa da matarsa don haka yaje ya sami Abba ya yi ta kame-kame har Abba ya fahimce shi, yasa Umma taje tace mata ta fito su wuce gida.

Tun da ta dawo taga yadda yake rawan jiki da ita tasan akwai magana. Sai dai ko a fuska bai ga tsoronsa ba, sai ma kulawa da yake samu.

Duk yadda taso ta daure cikin dare sai da jikinta ya dinga kyarma. Cikin wata murya yake mata magana adaidai saitin kunnenta,

“Kiyi haƙuri ranar na fita hayyacina ne, kinsan yadda kike kuwa? Kin gigitani, kinsa na fita hayyacina, kina da… “

Da sauri ta juyo ta rufe bakinta da nasa, saboda batason kalaman da yake yi mata. Anan suka sake tsunduma wata duniyar. Wannan karon bata ji irin zafin da ta ji a ranar farko ba.

*****

Yana ta shiri tana kallonsa,

“Ina zaka je?”

“Za ki rakani ne?”

“Ina?”

“Taɗi zanje.”

Ta maƙale kafaɗa,

“Nidai bazan je ba. Kayan akwatinta ma ka tarkata ka kaiwa su Umma, tunda bikin su Zarah ya matso sai kawai ahaɗa da naka.”

Ya dubeta ido cikin ido ya ɗaga mata gira,

“Ok sauraniyata. Duk yadda kika ce haka za ayi. Amma yanzu ki zo ki rakani idan muna dawowa zan siya maki kayan kwaɗayi.”

Da sauri ta tashi ta nufi ciki ta zaro gyalenta ta fito.

“Muje to.”

A tare suka fita kaman sabbin ango da amarya.

Kai tsaye gidansu Amira suka nufa. Tun daga nesa suka hangosu ita da Shamsu suna kwasar dariya. Yana murmushi Ihsaan ta waiwayo tana dubansa,

“Wai Shamsu ko dai Amira yake so ne kuma? Kai baka da kishi ne?”

Hannunsa yakai kan nata yana murzawa ahankali,

“Ina da kishi mana. Amma akan matata. Ke baki da kishi ne kike raka mijinki taɗi?”

Itama murmushin ta yi ta ce,

“Idan naga zaka kauce hanya zanyi kishi mana. Amma hanyar da ka biyo dole inbiyota indai inasonka da gaske. Kuma ni bana son ƙarya kai kuma kana gaya min gaskiya. Daga ranar da na tayar da hankalina akan gaskiyar da kake gaya min, daga wannan ranar ƙarya zata ci gaba da shiga tsakaninmu, shikenan sai rashin zaman lafiya.”

Ya jinjina kai yana jinjina irin kaifin tunaninta.

Gaba ɗaya sun sha jinin jikinsu ganin Irfaan a lokacin da basu taɓa zata ba. Duk suka ƙaraso wurinsa suna rawar baki. Ya dubi hannunta yaga tana ɗaure da agogon nan, ya ce.

“Amira nazo induba lafiyarki ne, zan dawo anjima da yamma.”

 Bai jira cewarta ba, ya ɗaga glas ɗin motar suka bar wurin.

Ihsaan dai bata ce komai ba. Kai tsaye gidan Umma suka wuce yabar Ihsaan ɗin agidan shi ya fice. Suna ta shirya kayan akwatinan Sadiq da za akai. Ihsaan ta dubi Umma ta ce,

“Shi kuma Yaya Irfaan yaushe za akai nasa kayan? Umma na ƙosa ayi auren kowa ya huta.”

Umma ta harareta ta ce,

“Ke wacce iriyar sokuwar yarinya ce? Namiji ki ke yiwa tayin aure?”

Zarah ta ja tsaki ta ɗauke akwati ɗaya ta rufe tana cewa,

“Umma ki barta kawai. Wannan Amirar yadda take da buɗewan idanu idan ta shigo ai kin kaɗe.”

Ihsaan ta yi dariya ta ce,

“Allah Umma ba ta yin aure nake yi masa ba. Kawai da soyayyar waje gara ta cikin gida.”

Umma ta miƙe ta ce,

“Sai kuma ki yi. Ku ƙarasa shirya kayan bari inje induba Abbanku ko ya tashi.”

Umma tana fita Zarah ta dirar mata tana ta masifa, Ihsaan dai sai kallonta take yi.

Bayan Magrib Irfaan ya dawo gidansu Amira kamar yadda ya yi alƙawari, sai dai yana zuwa ya ce ta bashi agogon nan. Babu musu ta ɗauka ta bashi.

“Ko kina so inbaki kyauta ne?”

Ya tambayeta, ta amsa da kai. Ya ce

“Ok zan dawo maki da shi insha Allahu.”

Bayan ya ɗauko Ihsaan suna zaune a falo tana kwance a jikinsa shi kuma yana zaune yana duba cikin agogon ta ce,

“Kamar wani abu yana damunka.”

Ihsaan ɗinsa kenan, duk yadda yaso ya ɓoye damuwarsa muddin suka haɗa idanu sai ta gane.

“Eh. Ina so ki yi haƙuri intafi ofis yanzu.”

Ta girgiza kai,

“Aa ban yarda ba.”

“Ok tashi ki ɗauko min laptop ɗina.”

Nan ma ta maƙale kafaɗa. Dole ya ƙyaleta. Cikin hukuncin Allah barci ya kwasheta. Ya yi ajiyar zuciya ya ɗaga waya ya kira ofis ɗinsu ya ce yana so a kama masa Shamsu, a ɗauke shi ya nuna gidansu Amira itama a kamo masa ita.

Cikin abin da bai wuce awa ɗaya ba, har ankammala ayyukan da yasa ayi.

Bai sami shigowa ofis ɗin ba, sai da safe ya ce Ihsaan ta shirya su je. Abun da ya ƙara ɗaurewa Ihsaan kai ganin Abba da Umma a cikin ofis ɗin. Ga wasu mutane da bata sansu ba, sai daga baya ta fahimci ashe iyayen Shamsu ne.

Bayan sun natsa yasa a fito da Shamsu da Amira. Dukkansu ido ya raina fata, Shamsu ya yi magana cikin fushi,

“Me na yi maka kake wulakantani? Yaran aikina kake sawa suna kamani kamar wani ɓarawo. Zan nemi transfer inbar maka wurin ka cinye idan zaka iya.”

Irfaan ya murɗe fuska ya ce,

“Inspector ka ladabtar min da shi.”

Inspector ya fara dukan Shamsu. Abba ya ce,

“Kada ka sake dukansa Sani.”

Irfaan ya dakatar da shi. A lokacin aka shigo da iyayen Amira wanda Irfaan da kansa ya nuna masu wurin zama. Sama-sama suka gaisa idanunsu akan Amira.

Abba ya dubi Irfaan ya ce,

“Me ke faruwa ne?”

Shamsu ya yi carab ya ce,

“Wai dan ya ganni tare da wannan budurwar tasa Amira, shikenan yasa aka kamo mu, aganinsa ko cin amanarsa zan yi. Wallahi Abba ba soyayya nake yi da ita ba.”

Mahaifin Shamsu ya dubi Irfaan rai a ɓace ya ce,

“Ka bani mamaki Irfaan. Wannan shi ne karo na biyu da kake sawa a wulakanta ɗan uwanka da kuka taso tun yarinta. Akan me? Saboda kawai ɗaukaka ta zo maka? Ko don ka ga iyayenka suna goyon bayanka? Nima ayanzu ina goyon bayan ɗana.”

Amira dai sai kuka kawai take yi, da sun haɗa idanu da Ihsaan sai ta watsa mata harara. Abba ya sake jinjina kai ya ce,

“Alhaji Saleh banga abin tada hankali ba, tunda ga Irfaan ga Shamsu agabanmu. Duk dalilin da zai sa Irfaan ya ce mu zo nan ba ƙaramin dalili bane. Irfaan me ke faruwa?”

Irfaan ya yi shiru daga bisani ya ɗago kai ya dubi Amira ya dubi iyayenta sannan ya buɗa baki ya ce,

“Da farko naso in aureki saboda irin soyayyar da kike nuna min. Duk a cikin zuciyata babu sha’awar ajiye mata biyu. Ina jin daɗin zama da Ihsaan don haka nayi alƙawarin ko zan aureki ɗin sai idan zaki mutunta matata ta gida. Tashin farko saboda naje wurin taro da Ihsaan an haskamu a tv, kika kirani kina zagar min mata, kina kushe halittarta, kina yi min magana da isa. Wawan namiji ne kaɗai a lokacin zai iya amincewa ya aureki, domin tun ba aje ko ina ba kin nuna min ba zaki mutunta matata ba, idan kika shigo zaki dinga kushe min halittarta ne kawai kina haɗa min husuma. Tun a lokacin na janye maganar aurenki.

“Kin ci gaba da damuna da kiran waya da text. Ina amsa maki ne saboda bana son matata itama ta yi maki gori wataran, dan bansan me Allah ya ɓoye ba. Daga baya nayi tunanin yaudara ce abin da nake yi don haka na sameki ni da ke na gaya maki kiyi haƙuri ki nemi wani mijin ni bazan ƙara aure ba. Kika yi kuka daga baya kika roƙeni indinga kulaki ko gaisawa ce muna yi, har zuwa ki yi aure. Kika roƙeni indinga baki shawarwari akan lamuranki duk na yarda.

“A lokacin da na fahimci kamar matata bata kishina na haɗa baki da ke domin ina so dole sai naga kishin Ihsaan. A karo na farko da naga kishinta kenan ranar da ta ji muna waya muna musayar kalamai, har ta fasa kofi. Naji daɗin hakan, amma cikin ƙanƙanin lokaci ta kauda kishin nan ban sake gani ba har yau ɗinnan.

“Tun da naga Shamsu yana bibiyan Amira, yana kuma zuwa gidana sai na kasa samun natsuwa hakan yasa na ajiye agogona da gangar wanda ba agogo ne da aka sani ba. Abba agogon da aka kawo maka ɗinnan ne kai kuma ka bani. Abin da basu sani ba, agogon yana naɗar min duk wata magana da suka yi.

“Abin tashin hankalin da naji, shi ne Shamsu yana ɗaukar Amira suna fita hotel-hotel, Shamsu yana son matata Ihsaan kamar ya haukace.”

Dukka wurin suka sa Salati. Shamsu ya duƙar da kansa ƙasa, Amira ma ta sunkuyar da kai. Ihsaan ta kalle shi tana tuna abubuwan da suka faru. Irfaan ya ci gaba da cewa,

“Ko da yake maganar son matata da yake yi, na daɗe da sani tun ranar da halittarta ta bayyana Shamsu ya kasa ɓoye halin da yake ciki, har na yi masa gargaɗi. Ranar da na tabbatar kuwa shi ne adalilin agogon nan. Shamsu ya sami Amira ya nuna mata yana so da ƙarfi da yaji tasan yadda zatayi ta rabani da Ihsaan shi kuma zai san yadda zai yi yaga ta mallakeni. Daga baya Amira ta nuna masa ita so take a kashe Ihsaan ya ce shi sam bai yarda ba sai dai a kasheni. Itama ta nuna bata yarda ba, da haka suka yafi gidan boka, wanda Shamsu ne ya kai Amira. Bayan Shamsu ya fita ya barta ta nunawa bokan nan ita so take akashe mata Ihsaan. Boka ya bata magani, a lokacin Amira ta fita ta bar jakarta wanda nake ganin agogon yana ciki domin kuwa naji bayanan Shamsu yana roƙon bokan nan kada yayi mata abin da tace, amma shi yana so abashi maganin da zai kasheni ba tare da kowa yasan hakan ba.

“Ina ganin sunyi ta yin maganin babu nasara ne. Bansani ba sai ga yaron aikina ya zo mini yana gaya min Shamsu yasa a tare ni ahanya a kasheni saboda kawai ya mallaki matata Ihsaan. Ya sake roƙona indaina fita babu ‘yan sanda hakan hatsari ne ga rayuwata.

“Abun mamaki sai ga ƙawar Amira itama ta zo ta sameni tana roƙona insa matakan tsaro sosai akan Ihsaan domin zuciyar Amira ya bushe akan sai ta ga bayanta saboda kawai tana so ta mallakeni.

“Kunji abin da ya faru. Amira kina murna ina gaya maki kalamai agaban matata ko? To Ihsaan ta fi kowa fahimtata abin da yasa baki isheta kallo ba, ta riga ta karanci abin da ke cikin zuciyata da fuskata. Ta gane ba abin da ke zuciyata nake fitar maki ba. Kuma agogo na kawo maki ne saboda insami abubuwan da nake da buƙata kuma na samu. Zan ladabtar da ku daga ke har abokin shashancin naki, daga ƙarshe inmakaku kotu. Ko na yafe maku, hukuma ba zata yafe maku ba.”

Wuri ya rikice da Salati da koke-koke. Alhaji Saleh ya dubi ɗansa cike da ɓacin rai ya ce,

“Amma kaji kunya Shamsu. Duk abin da Irfaan ya yi maka bazan ce don me ba. Allah ya shiryeka idan mai shiryuwa ne.”

Abba ya ɗago duk ya jiƙe saboda tashin hankali. Duk yadda yaso ya furta wani abu ya kasa. Sai ma iyayen Amira da suke yi mata Allah ya isa da yarensu.

Abba ya tashi ya dubi Umma ya ce,

“Tashi mu je.”

Duk suka watse. Ihsaan ta dubesu sosai ta ce,

“Kai idan banda ƙaramin ƙwaƙwalwa gareka tayaya zaka iya mallakata? Wallahi da ka ci nasarar kashe Irfaan da da hannun nan nawa zan kashe dukka zuri’arku. Ke kuma kina zaton ni shashasha ce ko? Dama irin wannan ranar nake zuwa. Ihsaan da Irfaan su kaɗai suka dace da juna babu na ukunsu. Kina ‘ya mace mai tarin daraja kika zaɓi hanyar banza.”

Irfaan ya dawo ya jawota sosai jikinsa ya manna mata sumba sannan ya ce a tafi da su ɗakin amsa tambaya dan yana da buƙatar su maimaita irin laifukan da suka yi da bakinsu. Shamsu ya girgiza kai,

“A’a Irfaan ba sai ka kaini wannan ɗakin ba, zan faɗa komai.”

Irfaan ya yi murmushi yasa aka fice da su, ya jawo matarsa suka wuce gida.

*****

Cikin hukuncin Allah akasha bikin Sadiq da Hafsat, ita kuma Zarah da angonta Ahmad. Ansha biki na girma. Ihsaan ta zama tauraruwa awurin.

Ihsaan ta ci gaba da zuwa aikinta cikin nasara. Albashinta na farko ta je ta yi wa Abba da Umma da Irfaan siyayya, albashi na biyu ta yi wa Sadiq da Iffan da Zarah siyayya. Sun yi matuƙar jin daɗi sunsa mata albarka.

Haka ta ci gaba da ayyukanta tana taimakon mata, a ɓangare guda kuma tana kula da mijinta fiye da da. Su Shamsu kuwa tuni anyanke masu hukunci mai tsauri a gidan yari wanda fitowarsu sai Allah.

Yau suka zaɓa a matsayin ranar da za su kaiwa garin Saulawa ziyara da kuma duba filin da Baba Sani ya gayawa Irfaan akan idan yana so sai ya siya ɗin suyi asibitin.

Suna isowa akayi masu caaa. Innayo duk ta zama abar tausayi, sun je sun sami bata da lafiya, don haka Ihsaan ta dubata ta aika aka siyo mata wasu magunguna ta ce ta fara amfani da su nan da kwana biyu zata aika a ɗaukota akaita asibitinsu. Innayo ta yi kuka ta yi kuka, ta kama ƙafafun Ihsaan tana roƙonta gafara. Ihsaan da ta ji hawaye ya cika mata idanu, ta kama Innayo da dukkan dattin jikinta ta rungumeta tana hawaye,

“Baki yi min komai ba, idan ma kinyi min na yafe maki Innayo. Allah ya jiƙan Yaya Sulaiman.”

Irfaan ya girgiza kai ya amsa da, “Ameen.”

Kayan abinci Irfaan ya siya masu sosai.

Daga nan suka wuce gidan Marka. Ita lalacewar da ta yi ma abin ba a magana. Gidan ya ƙarashe rushewa a wani ɗan lungu take kwana.

Da ƙyar ta gane Ihsaan. Ga kyau da ta yi, ga cika ga shigar manya, sannan ita kanta Markan tana fama da matsalar ido ba sosai take gani ba. Ihsaan ta dubi mijinta ta ce,

“Zansa a ɗaukota itama Sadiq zai duba idanunta sai mu ga abin da zamu iya yi.”

Irfaan ya ce,

“Duk yadda kika ce haka za ayi.”

Bayan sun koma gida da kwana biyu Ihsaan tasa aka kwaso su Innayo da Marka, aka wuce da su asibiti. Ita take kula da Innayo, Sadiq kuma yake kula da Marka.

Yau suna zaune Irfaan yana duba wasu takardu ya dubeta tana sanye da riga da wando basu kama jikinta ba, amma sun fiddo yarintarta ya ce,

“Nasa aginawa Baba Marka gida mai kyau sosai na zamani, a cikin gidanku da ya rushe bai kamata abar wurin haka ba. Sai kuma gidan Baba Sani nan ma nasa abuge gidan ayi na zamani. Zan buɗewa Baba Sani gidan gona nasa na kansa tunda kin ga yanzu baya aikin gadin ya koma kulawa Abba gidan gonarsa ta can. Amma me kike gani?”

Ihsaan ta dawo kusa da shi tayi tagumi,

“Sannu da ƙoƙari, sai dai kasan albashina da duk irin kuɗin da kake bani suna nan shaƙe a account ɗina. Ka bar min gina gidansu Sulaiman don Allah sai kayi sauran.”

Bai yi mata musu ba don ya fahimci dalilinta nason yin hakan. Ya ce mata, “Kayan akwatunan nan naga baki taɓa amfani da su ba, bayan na gaya maki na baki kyautarsu.”

“Allah zan taɓa inaso insami lokaci ne inɗibi wasu inkai ɗinki.

Ya dubeta sosai yadda ta yi wani irin haske ya ce, “Zo ki ji.”

Ta matso ya shafi cikinta,

“Wata nawa yanzu?”

Tasa tafukan hannunta ta rufe fuskar tana dariya.

“Kin yi zaton zaki yi min wayo ne? Duk wani motsinki ina kula da shi. Gaya min watannin ko yanzu inyi maganinki.”

Sai da ta ɗan turo baki sannan ta ce, “Wata uku ne fa.”

Farin ciki ya tsirga masa.

“Zan baki tukuici mai girma kuwa.”

Ya dinga sumbatarta tun tana kaucewa tana dariya har ta sakar masa jikin ya yi yadda yake so da ita. Cak ya ɗauketa ya yi cikin ɗaki.

Abubuwansu gwanin ban sha’awa kullum Ihsaan sake shiga zuciyar mijinta take yi har Allah ya sauketa lafiya. Ɗa namiji ta samu kai tsaye akasa masa suna Sulaiman.

Ihsaan ta yi kuka ranar ta sake yiwa Sulaiman addua. Ta hana a ɓoye sunan kai tsaye ake kiransa da Sulaiman, ita kuma takan ce masa Yaya Sulaiman.

*****

Tuni ankammala gina gidajen wanda suka fita daban a cikin garin na Saulawa. Innayo ta warke ras!  Rayuwarsu ta sauya, haka Baba Marka. Kullum taga Ihsaan sai ta sake roƙonta afuwa, takance babu komai.

Bayan wasu shekaru rayuwar ta sake bunƙasa arziƙinsu ya ninku. Sulaiman ya yi wayo, ga surutu. Zarah ma ta haifi ɗa namiji, Sadiq ma haka. Rayuwarsu da ta ‘ya’yansu abin sai son barka.

Alhamdulillahi… 

NA SADAUKAR DA LABARIN NAN A GAREKI

AISHA ƊAN BORNO

DAGA TAKU MAI ƘAUNARKU

FATIMA ƊAN BORNO

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Duniyata 24                

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×