Skip to content
Part 22 of 25 in the Series Duniyata by Fatima Dan Borno

Cikin natsuwa yake murza sitiyarin motar, zuciyarsa cike da tunani kala-kala. Duk yadda yaso ya yakice Ihsaan da ke yi masa gizo abin ya faskara. Duk yadda ya rintse ido ya buɗe, sai ya hangota cikin shigarta mai tsananin fizgar hankalin mutane.

Ita kuwa Amira duk irin abubuwan da Ihsaan ta yi mata na karramawa hakan bai sa ta janye daga irin muguwar tsanar da ta yi mata ba. Ji take yi tamkar zuciyarta zata yi bindiga tsabar tsanar Ihsaan. Ta yi rantsuwa ko da bala’i sai ta shiga cikin gidan Irfaan.

Tsaki ta ja a cikin zuciyarta wanda batasan a zahiri ta yi ba. Irfaan da ya tsani tsaki ya ware idanu yana dubanta,

“Tsaki? A cikin motata? Akan me?”

Ya yi tambayar cikin jin zafinta. Amira ta kafe shi da idanunta tana hango tsabar tsanarta a cikinsu.

“Me ya sa zaka fusata haka don kawai na ja tsaki? Kuma tsakin da na ja ba da kai nake ba, bansan lokacin da ya fito fili ba. Saboda baka sona ne shiyasa kake irin wannan fusatar? Haba Irfaan ka tausayawa zuciyata mana.”

Bai ce uffan ba ya ci gaba da tuƙinsa. Sai da ya yi kamar ba zai yi magana ba, sannan ya ce,

“Bana son tsaki. Yanzu kuskure kika yi, maimaita hakan kuma ganganci ne. Babu dalilin don kinyi abu na yi maki magana ki sauya mini manufata.”

Zuciyar Amira ya sake ɓaci, tsautsayi yasa ta ce,

“Na tabbata da ace Ihsaan ce ta ja tsakin nan ko motsi ba zaka yi ba, bare kayi mata faɗa. Saboda ta riga ta shanye…”

Bata kai ga ƙarasa maganarta ba, yaja dogon burki, wanda ya tashi hankalinta. Saura ƙiris ya haddasa hatsari akan babban titin na unguwan Sarki. Yana huci ya zagaya ya buɗe murfin motar ya fincikota a tsakiyan titi. Bai damu da yadda motoci suke ta horn ba, bai damu da irin surutan da jama’a suke ta yi ba. Bai kula a wannan hanya akwai Abba da Umma da su Ihsaan da suke saurin su isa gida ba, ya jawo hannunta har zuwa gefen titin yana jin kamar ya rufeta da duka.

“Kinyi na ƙarshe! Ba tun yau nake gaya maki ba, ki fita sabgar gidana, ki daina magana kina sa iyalina. Kin kasa bambance matsayi da girman budurwa da matar aure, kin kasa bambance matsayin Ihsaan da na kowacce ‘ya mace awurina.”

Ya ɗan sassauta murya,

“Zan iya yi maki wulakancin da ya fi wannan muddin kika sake taɓa darajar matata. Idan ita ce ba za ta taɓa yi min tsaki ba, ko da kuwa a cikin kuskure.”

Abba ya dubi Umma, yana mamakin yaushe Irfaan ya zama mara tausayi da zai tarawa yarinya ƙarama jama’a a tsakiyan titi. Ihsaan tasa hannu ta toshe bakinta tana jin ƙarin son mijinta. Ya daɗe yana kare mutuncinta. Tun ranar da aka ɗaura masu aure yasa katangar ƙarfe a tsakaninta da masu yi mata wulakanci.

Kafin Abba ya sami ƙwarin guiwar isowa Ihsaan ta ƙarasa ta ƙanƙame Irfaan. Hawaye kawai ke zuba daga idanunta. A lokacin idanun Amira ya raina fata, ta gane zata sha wahala matuƙa wajen ganin ta raba ma’auratan nan, idan ma ta ci galaban shiga cikin gidan zaman baƙin ciki kawai za ta yi. Ƙila agabanta Irfaan zai dinga kissing matarsa. Ta haɗiyi wani dunƙulelen abu da ya tsaya mata a tsakanin zuciya da maƙogoro.

Sai a lokacin hankalin Irfaan ya dawo jikinsa. Abba ya ƙaraso yana duban Irfaan,

“Irfaan zan ɓata maka rai.”

Abin da Abba ya iya furtawa kenan saboda ɓacin rai. Wasu ‘yan sanda suka ƙaraso suna masifa akan an ajiye mota a tsakiyan titi, mutane sai raɓawa suke yi suna wucewa.

Suna isowa suka haska idanun Irfaan suna tambayarsa dalilin ajiye mota a tsakiyan titi. Ganin Irfaan yasa duk suka sara masa suna cewa “Sorry sir.”

Ko kallonsu bai yi ba ya jawo Ihsaan da ke jikinsa tana kuka ya kaita har cikin motarsa ya zagaya ya tada ya wuce abinsa. Zarah ta dubi Sadiq da Iffan suka taɓe baki sannan suka wuce kusa da Abba suna ji yana bada umarnin ‘yan sandan su kai Amira gida. Sai da suka tabbatar Abba da Umma sun shiga mota, sannan suma suka shiga. Zarah ta jinjina kai ta ce,

“Yaya Sadiq wai baka kula da wani kallo da Yaya Irfaan yake yi mana ba? Nifa tsoronsa nake ji. Kai Yaya Iffan ka huta babu sunanka a ciki.”

Sadiq ya taɓe baki ya ce,

“Daga taimako? Ni sai inbashi haƙuri.”

Iffan ya tuntsure da dariya ya ce,

“Allah shi ƙara. Shi Yaya Irfaan kwara-kwata ba a iya masa. Shiyasa na yi ta godewa Allah da kuka ɓoye min komai.”

Haka suka yi ta tattaunawa har suka iso gida.

Shi kuwa Irfaan tafiya kawai yake yi yana jin sautin kukan Ihsaan har cikin zuciyarsa. A hankali ya jawota jikinsa ba tare da ya ce komai ba.

Bai ja burki a ko ina ba, sai a cikin gidan iyayensa. Ya yi tunanin gara ya je Abba yayi masa faɗan da zai yi kawai. Har ya kashe motar bata daina kukan ba. Yasa hannu ya ɗago haɓarta yana magana a tsakiyar fuskarta,

“Ihsaaan.. Me ya sa kike zubar da hawayenki?”

Tana son ɗauke kanta tana ƙoƙari cusa fuskarta a cikin ƙirjinsa sakamakon wani abu dake zagaye dukkan ruhinta. Amma sai ya hana hakan. Alamu sun nuna mata yana ci gaba da kawo fuskarsa daidai bakinta, hakan yasa ta rintse ido, jikinta yana kyarma.

“Ihsaaan… Ki yi min magana mana.”

Abin da yake so ya yi bata so, haka zalika bata da ƙwarin guiwar hana faruwarsa. Ahankali ya haɗa bakinsu wuri guda yana aika mata da rikitaccen saƙo. Tunda Ihsaan take a duniya bata taɓa tsintar kanta acikin irin yanayin da ta tsinci kanta ayanzu ba. Wannan rana ce mai matuƙar mahimmanci wanda ba zata taɓa manceta ba.

Shi kansa Irfaan zai iya rintsuwa bai taɓa shiga irin halin da yake ciki a yanzu ba. Hannunsa yakai ƙirjinta, mamaki ya kama shi a lokacin da cikar halitta ya bayyana ajikinta har haka. Gaba ɗaya ya kasa sarrafa kansa. Jikinsu babu inda baya kyarma. Aka haskesu da hasken mota. Jiki babu ƙwari ya saki Ihsaan da hawaye kawai ke zuba a idanunta babu baki.

Sadiq ya yi saurin kashe hasken motar yana cewa,

“Kamar fa Yaya Irfaan yana cikin motarsa. Na shiga uku yau.”

Duk suka yi zuru-zuru. Irfaan ya ɗan gyara rigarsa ya fito daga cikin motar zuciyarsa tana tafarfasa.

Sadiq da Zarah da Iffan duk suka tsaya a tsaye suna sauraren isowarsa da irin hukuncin da zai yi masu. Shi kuwa tsabar borin kunya ce, gani yake yi sun ga abin da suke aikatawa, wanda su sam basu kula ba.

Ihsaan ta lumshe idanunta tana jin ƙarin natsuwa yana shigarta. Sai yanzu ta farga da abin da Irfaan yake shirin aikatawa. Jiki babu ƙwari ta fito ta rasa ta yadda za ta ƙwaci su Zarah. Don haka ta zauna a ƙasa ta ɗan saki ƙara. Agigice ya waiwayo sai kuma ya dawo wurinta yana mata sannu. A lokacin duk suka samu suka wuce ciki da sauri.

Kunyarsa take ji sosai, don haka ta duƙar da kai ta ce,

“Babu komai jiri ne ya ɗan kwasheni.”

Duk yadda yaso ya taimaka mata, ta hana faruwar hakan. Da ƙafafunta ta shiga falon yana biye da ita a baya. Abba yana tsaye cikin ɓacin rai ya ce,

“Me ya sa ka wulakanta ‘yar jama’a? Saboda kawai tana sonka shi ne ta cancanci hakan? Ko kuwa saboda kyawun matarka ya bayyana? Yaushe akayi maka ƙarin girma da har kake karya doka da hannayenka? Saboda kai hukuma ne shiyasa kayi rashin hankalin da kayi yau? Ka bani amsa!”

Ya daka masa tsawa, wanda ya razana dukka ‘yan ɗakin. Ya nuna shi da yatsa,

“To bari ka ji, sai ka auri yarinyar nan tunda kai ka amince da aurenta tun farko.”

Ihsaan ta girgiza kai cikin sanyin murya ta ce,

“Abba kayi hakuri, amma ba saboda kyawuna Yaya Irfaan ya yi hakan ba. A lokacin baya sunyi irin hakan da ita yafi a ƙirga tun Yaya Irfaan baisan waceceni ba. Na amince ya yi laifi, amma tabbas ya yi hakanne saboda yana kare girma da martabar matar aure.”

Sannu a hankali Ihsaan ta warware masu cin mutuncinta da Amiran ta dinga ƙoƙarin yi Irfaan yana taka mata burki. Duk sai jikinsu ya yi sanyi. Abba ya kasa ci gaba da faɗan sai ma ya sallame su ya shige ɗakinsa.

Irfaan yaja jiki ya wuce nasa ɗakin. Kwata-kwata faɗan Abba bai tsaya masa arai ba. Tunanin yanayin da ya tsinci kansa aciki shi da Ihsaan ya shafe masa duk wani ɓacin rai. Bai taɓa tunanin zai iya haɗa bakinsa da na Ihsaan ba. Bai taɓa tunanin haka Ihsaan take ba, sai da ya kasance kusa da ita a cikin yanayi mai wahalar fassara. Ya ji takaicin shigowan Sadiq, shi ya katse komai.

Ya sake yin wani irin juyi, yana tuna lallausan jikinta.

Zai so ya sake samun wannan jikin a kusa da shi ko zai samu ya yi barci cikin nishaɗi.

Ita kuwa Ihsaan tana can cikinsu Sadiq ana hira. Amma ita ta kasa furta komai. Daga um sai um-um. Sai lasan laɓɓanta take yi da ya yi laushi. Zarah ta kafeta da idanu tana kula da duk yadda ta sauya.

“Lafiyarki ƙalau kuwa?”

Ta tambayeta cike da tsarguwa. Ihsaan ta dubeta idanu a lumshe ta ce,

“Na gaji ne sosai.”

Zarah ta jinjina kai,

“Sai ki je ki yi wanka ki yi Sallah ki kwanta.”

Bata iya motsa ko yatsunta ba, sai hasko kanta take yi a jikin Irfaan asanda abubuwan suke faruwa. Wani murmushi ya suɓuce mata. Sadiq ya dubi Zarah itama ta dube shi.

Taku har kullum, ‘Yar mutan Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Duniyata 21Duniyata 23              >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×