Skip to content
Part 23 of 25 in the Series Duniyata by Fatima Dan Borno

Duk suka fice suka bar mata ɗakin. Hakan ya sake bata ƙwarin guiwar rungumar filo tsam a jikinta tana jin ƙamshin turaren Irfaan tamkar ita ce ta fesa turaren.

Acan ɓangaren Amira kuwa, bayan ankaita gida ta kasa zaune ta kasa tsaye. Damuwa ce fal a cikin zuciyarta. Da yake ance so hana ganin laifi, sai ta tsinci kanta da dumu dumu da yiwa Irfaan uzuri. Hasalima ta fi tsanar Ihsaan, a ganinta itace silar komai. Wayarta ta zaro ta kirawo lambar Shamsu, ta zayyane masa komai. Shamsu ya furzar da wani irin huci ya ce ta jira shi gayi nan zuwa gidansu yanzu.

“Shamsu na tsani Ihsaan, zan iya kasheta akan Irfaan. Shamsu ka fahimceni Irfaan shi ne rayuwata.”

Shamsu ya ƙwalalo idanu ya ce,

“Ke Amira. Mene ne laifinta? Shi ya kamata ki yi fushi da shi ba ita ba. Yanzu dai ina bayanki nima kuma, zan tsaya maki dan ganin Irfaan ya rabu da Ihsaan. Irfaan ai da ke ya dace ba Ihsaan ba.”

Amira ta saki baki tana dubansa cike da mamaki,

“Ka ce Irfaan ya rabu da Ihsaan? Tabɗijan. Don Allah ka yi maganar da hankali zai ɗauka.”

Dariya ya yi irin ta mugunta sannan ya ce,

“Ki yarda da ni mana.”

Ta girgiza kanta da ƙarfi ta ce,

“A’a ka faɗa mini abin da zai sa inyarda da kai ɗin. Kasan kuwa yadda ya tara min jama’a akan kawai na ambaci Ihsaan? Ko wanene bokan yarinyar nan wallahi ba ƙaramin hatsabibi bane. Indai kana bayana da gaske kaje zuwa kwana biyu ka nema min mafita.”

Shamsu ya jinjina kai ba tare da ya iya furta komai ba.

*****

Kwana biyu Irfaan ya zama cikin ayyuka waɗanda suke neman su sha masa kai. Sau tari ma baya kwana a gidansa. Abin da Ihsaan ta kula shi ne ya sauya mata, ya daina bata duk wani kulawa. Kullum yana cikin aiki. Hakan yasa itama ta tattara shi ta watsar, ta ci gaba da karatunta babu ji babu gani. Sadiq ke taimaka mata daga gefe.

Yau asabar, tun safe suke aikace-aikace ita da Larai. Sunsha wahala sosai kasancewar sun fitar da komai na gidan sun wanke. Bayan sun kammala ne ta je ta watsa ruwa. Kasancewar garin zafi akeyi don haka tasa ƙananun kaya ta haye gadonta taja bargo.

Shigowarsa kenan, ya dinga duban ko ina yana jin sassanyar ƙamshin yana ratsa shi. Yana kewar Ihsaan ɗinsa sosai, yana jin tarin damuwa a zuciyarsa. Kai tsaye ya nufi ɗakinta tare da tura kansa ciki. Baya iya hango fuskarta don haka ya haye saman gadon ya buɗe bargon ya shige.

Taso ta daure ta yi kamar batasan yana ciki ba, sai dai abubuwan da yake mata ya hanata hakan. Ta dage ta fizge kanta, sai kuma ta fasa kuka.

Ya sani ya yi laifi, sai dai yana so Ihsaan ta sami daman yin karatunta ba tare da ya matsa mata ba, muddin ya ci gaba da shige mata tana haɗa soyayya da karatu za a iya samun matsala. Babban damuwarsa ita ce yau yaga Ihsaan ta zama cikakkiyar likitan mata, idan hakan ya faru shikenan burinsa ya gama cika. Ganin aski ya zo gaban goshi shiyasa ya sarara mata.

Yadda take kuka yasa tausayinta ya kama shi. Sosai ya jawota jikinsa ya sa bakinsa a kunnenta yana magana,

“Yaya Irfaan ya yi laifi. Na zo ne ki hukunta kinji?”

Aikuwa ta ware hannunta tana dukansa a ƙirji. Hannun ya riƙe yana kallonta.

“Tsaya kada ki ji wa kanki ciwo bari insamo maki madoki.”

Dakatawa ta yi da dukan tana dubansa. Shi kansa ya rame.

“Ka mance da amanar Yaya Sulaiman ko? Me ya sa?”

Yana murmushi ya cusa hannunsa akan mararta yana magana ƙasa-ƙasa,

“Ban isa in mance wannan amanar ba. So nake ki kammala karatu in ajiye takwaran Sulaiman a wannan wurin.”

Kunya ta rufeta, ta yi saurin mayar da kanta ƙirjinta ta ƙanƙame shi. Irfaan ya yi murmushi sannan ya ɗago fuskarta.

“Kin yi kewata?”

Kanta kawai ta ɗaga.

“To me ya sa banga kina nemana ba?”

“Na barka ne kasha iska.”

Bai ce komai ba ya dawo bakin gadon ya zauna kawai.

“Yauwa Yaya akwatunan nan mun cika su da kaya.”

Ya juyo yana dubanta da rashin fahimta.

“Akwatun wa?”

Ta shagwaɓe ta ce,

“Akwatunan Amira da ka bamu mu haɗa. Allah baka ga kayayyakin da muka sa a ciki ba, sai sun burgeka.”

Sai yanzu ya tuna. Yana mamakin yarinyar da ita ko ajikinta. Zuciyarsa tana gaya masa bata sonsa ne kawai. Har yanzu soyayyarta tana gurin marigayi. Miƙewa ya yi yana duban ƙwayar idanunta,

“Kinyi ƙoƙari gaskiya. To ki ajiye min zan sanar da Umma. Tunda bikin bai wuce sati biyu nake so asa ba.”

Ga mamakinsa ko ajikinta. Ya juya kawai yana cewa,

“Ki kawo min kofin tea.”

Yana ficewa hawayen da take dannewa suka zubo. Ta yi saurin gogewa ta miƙe dan zuwa yi masa abin da ya buƙata.

Da Sallama ta shigo yana amsa waya, bai kalleta ba amma kuma ya amsa Sallamarta. Kalaman da yake yi ya hanata ajiye tea ɗin, ta yi tsaye tana saurarensa. Da ace bata jin muryar wacce yake waya da ita da babu ko tantama zata ƙaryata shi.

“Ke da kika kusa shigowa gida na mene ne naki na ƙosawa da zuwana?”

“A’a nidai gaskiya ka zo yanzu. Wallahi akwai wani abu da nake so ka gani ne.”

Kofin hannunta ya suɓuce ya faɗi ƙasa, ta yi tsalle ta koma gefe saboda kada ruwan zafin ya sameta. Irfaan ya bita da kallo, a lokaci guda ya kashe wayar yana Salati. Da sauri ya ƙaraso kusa da ita yana mata sannu.

Gaba ɗaya Ihsaan ta rasa me ke yi mata daɗi. Shi kuwa duk yadda yaso ya karanci wani abu a fuskarta abin ya faskara. Don haka ya miƙe yana cewa,

“Ki bar tea ɗin, yanzu zan je gidansu Amira indawo.”

Ta amsa da “To idan kaje ka gaida min ita.”

Ya amsa yana cewa,

“Babu rakiya?”

Da ƙarsashinta ta miƙa masa hannu ya ɗagata suka yi hanyar waje. Har mota ta rakashi tana yi masa fatan dawowa lafiya.

Bayan tafiyarsa ta yi tagumi tana jin tarin damuwa. Shi kuwa kai tsaye gidansu Amira ya nufa. Suka ɗan taɓa hira ya ce mata kansa yana ciwo zai koma gida. Ba haka taso ba, ta so ace ya zauna ya kai sha biyun dare suna tare. Ta karɓi wayarsa akan zata tura saƙo. Kai tsaye kan lambar Ihsaan ta tafi, ta rubuta mata saƙo kamar haka,

‘Ina wurin Amira kada ki ji ni shiru.’

Tana turawa ta goge. Ihsaan tana zaune tana kurɓar ruwan zafi, ta ji shigowan saƙo. Sai da ta kammala sannan ta jawo wayar tana tunanin ko ‘yar makarantarsu ce. Ta karanta saƙon yakai tashi uku. Daga bisani ta yi murmushi. Tasan ba Irfaan ya tura saƙon ba, amma mamakin da take yi ta yaya har wayar Irfaan ya tafi hannun Ihsaan?

Bai dawo da wurin ba, saboda ya wuce wani wuri. A zaune ya sameta, tana ganinsa ta kama murna. Ya miƙa mata tsarabanta hakan ya ƙara sanya farin ciki a fuskarta. Bata nuna masa taga saƙo ba, ta ci gaba da hidima da shi har barci ɓarawo ya saceta anan falon. Shi ya ɗauketa yakaita ɗakinsa ya jawo masu bargo suka kwanta.

Cikin dare ya jiyo muryarta tana addu’a cikin sanyi, don haka yasa kunne sosai yana jin irin addu’ar da take yi. Bayan ta yiwa Sulaiman addu’a kamar kullum sai ta koma kansa,

“Ya Allah, idan har wannan aure da mijina zai yi alkhairi ne Allah ka tabbatar mana da shi, idan kuma babu alkhairi kuma yana sonta Allah ka mayar da shi alkhairi. Allah kada ka jarabci mijina da sharri irin na wasu matan.”

Jikinsa ya ƙara mutuwa. Ita kuwa Ihsaan wacce iriyar mace ce? Sulaiman ya sha sanar da shi irin kyawawan halayya irin na Ihsaan yanzu ya sake tabbatar da hakan.

Ya rufe idanunsa yana jin wani abu yana damunsa sai dai ba zai iya cewa ga asalin abin da yafi damunsa ba.

Tun hawansa kujera yake gamuwa da masifu kala-kala, sharri da jifa babu irin wanda ba ayi masa. Addu’ar iyaye gaskiya ce, domin kuwa ita take riƙe da shi. Hatta su Shamsu sun canza masa, musamman yadda ya dage yana aiki babu sani babu sabo.

Yau kamar kullum yana zaune a Ofis zuciyarsa tana tafarfasa. Tayaya Shamsu zai amshi cin hanci a wurin mutanen da suke yaƙi da su?

Shamsu yana shigowa ya rufe shi da ruwan bala’i

“Kai dai shashasha ne wallahi. Kuma ina tabbatar maka muddin bincike ya tabbatar da gaskiyar magana zaka yi sanadin kakinka. Fice min a ofis pls.”

Shamsu ya dube shi sosai ya ce,

“Irfaan? Saboda ka taka wani matsayi shi ne har zaka mance da matsayina na babban amininka? Shi ne yau har kake neman hanyar da zaka yi sanadin cin abincina? To baka isa ba Irfaan.”

Idanun Irfaan sun kaɗa sunyi jazir. Da za ace masa waye yafi tsana zai iya cewa Shamsu.

Ya dubi wani ɗan sanda ya ce,

“Ku rufe min shi har sai na gama bincikena.”

Shamsu ya zaro idanu. Irfaan ya taso yazo gabansa yana kallonsa ido cikin ido,

“Ina so ka gane bambanci babba da yaro a wuri. Tunda ka yarda na sami matsayin dole ka bi doka. Babu wanda ya isa ya ci mutuncin kujerar nan ko da kuwa babu kowa akai inƙyale shi. Ku tafi da shi na ce.”

Shamsu yana ji yana ganin aka cacumeshi kaman wanda ya yi sata aka sauke masa hula aka cire belt ɗinsa suka wuce da shi. Irfaan ya koma ya zauna ya dafe goshinsa. Sosai yake jin tsanar kujerarsa, bai san akan masifa yake ba, sai da ya hau kan kujerar da yake a yanzu.

Maganar rufe Shamsu ya bi ko ina. Iyayen Shamsu suka je gurin Abba suka gaya masa, tare da mamakin wai Irfaan ne zai yi hakan. A lokacin Abba ya aika Irfaan ya zo. A falon Abban ya sami iyayen Shamsu da shi kansa Abban suna zaman jiransa. Har ƙasa ya durƙusa ya gaida su. Abba ya dube shi ya ce,

“Irfaan me ke faruwa a tsakaninka da aminin naka?”

Ji yake kamar ya fasa ihu, baya so ko alama yana magana akan matsalar Shamsu dole ya daure ya ce,

“Abba laifin cin hanci ake tuhumarsa da shi. Da aka kira shi babu ladabin magana a tare da shi, sai yake nema ya wulakanta ogansa agaban yara.”

Abba ya fahimci abin da Irfaan yake nufi. Don haka ya ce,

“Tashi ka tafi.”

Mahaifin Shamsu ya yi saurin cewa,

“A’a yallaɓai na yi zaton zaka bashi umarnin ya sako shi ne? Ko ma menene sai ya biyo baya.”

Abba ya girgiza kai,

“Bana shiga sha’anin aikin Irfaan. Abin da yasa na kirawo shi nan ina so ku ji dalilin ne. Nasan da wahala Irfaan ya rufe Shamsu haka kawai ba tare da dalili mai ƙarfi ba. Ku tafi kawai gaskiyarsa zata fito da shi.”

Jiki babu ƙwari suka bar gidan.

Acan ɓangaren Amira kuwa ta yi ta kiran Shamsu akan maganar gidan malaman da za su koma ita da shi, amma wayarsa a kashe. Dabaran kiran Salisu ya zo mata, bayan sun gaisa ne take tambayarsa ina Shamsu, anan ya kwashe komai ya gaya mata. Ji ta yi zufa yana keto mata. Babu shiri ta kira Irfaan wai ita adole zata iya sawa a sake shi. Tana fara maganar ya kashe wayarsa gaba ɗaya.

‘Yar mutan Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Duniyata 22Duniyata 24                 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×