Skip to content
Part 20 of 25 in the Series Duniyata by Fatima Dan Borno

Dukkansu basu sake cewa uffan ba, har suka iso gida. Abba yana zaune a falonsa ya ɗaga kai domin ganin wanda ke masa Sallama. Shiru ya yi ya kafe su da idanunsa, yana nazarin Irfaan. Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce,

“Me ya sa ka ɗaukota?”

Irfaan ya ɗan sosa kai ya ce,

“Abba yanzu ma da naje kuka na sameta tana yi.”

“Cewa na yi me ya sa ka ɗaukota? Amsa kawai na tambayeka ba bayani ba.”

Ya kasa magana sai sunkuyar da kansa da ya yi. Ihsaan ta ƙaraso wurin Abba ta durƙusa ta ce,

“Abba da bai zo ba zuciyata bugawa za ta yi nima in mutu.”

Abba ya ɗan yi murmushi irin nasu na manya ya ce,

“Ihsaan ba za ki mutu adalilin nan ba insha Allahu. Idan ba ki koyi zama da ‘yan uwanki ba sai yaushe za ki yarda da ƙaddararki? Ki yi haƙuri Ihsaan ki daina damuwar nan, wanda ya mutu har abada ya mutu kin ji? Addu’a kawai yake da buƙata.”

Kafin ta yi magana Zarah ta fito, tana ganin Ihsaan ta yi tsalle ta ƙanƙameta tana murna. Irfaan ya harɗe hannayensa ya zuba masu idanu. Shi kaɗai yasan irin tunanin da yake yi.

 Sai dare Irfaan ya ɗauketa ya mayar gidansa.

Tana zaune tana gyara kayansa da ya watsar ko ina, ya shigo idanunsa suna lumshewa.

“Sannu da shigowa.”

“Yauwa Ihsaan.”

Bata dube shi ba ta ci gaba da gyaran da take yi, har ta kammala. Sannan ta dawo kusa da shi tana dubansa,

“Yaya saukanmu ya kusa me za ka yi mana?”

Ware idanun ya yi yana murmushi,

“Iyye Ihsaan ɗina angirma fa. Yanzu gaya min me kuke so.”

Ta ɗaga kanta sama alamun tunani, sannan ta ce,

“Ka siyo mana su Chocolate da yawa tunda wanda kake kawo mana baya isarmu.”

Sosai yake dubanta yana murmushi,

“Yanzu Ihsaan na yi zaton cewa za ki yi inɗaukeku inkaiku ƙasar waje ko Dubai haka, ku yi siyayya ku ga yadda duniyarsa take?”

Tana dariya ta ce,

“DUNIYATA da ta su duk iri ɗaya ce, sai ɗan bambancin da ba za a rasa ba. Amma ni nafi son wannan Duniyar ita kaɗai ta fiye min ƙasar waje.”

Yatsanta yake kallo yadda take nuna shi a matsayin duniyarta. Jikinsa ya ƙarasa mutuwa ya ce,

“Ni ne Duniyarki?”

Ta ɗaga gira,

“Yes! Kaine DUNIYATA.”

Kalma ce guda ɗaya, ta wurga masa, sai dai girmarta ta wuce misali. Kalmar ta zauna masa a rai, zai ajiye wannan kalma a wuri mai matuƙar mahimmanci. Ya lumshe idanunsa yana nanata,

‘DUNIYATA.’

Ya rasa me zai ce mata da ya wuce zuba mata idanu. A hankali kuma ya ji ta yi magana cikin sanyi,

“Umma ta gaya min za ka ƙara aure.”

Dam! Gabansa ya faɗi, amma sai ya danne ya ci gaba da murmushinsa wanda iyakarsa fuska. Ta ci gaba da cewa,

“Idan har sai na amince Umma za ta yarda ka ƙara aure, ni na yarda. Bani da matsala akan ƙarin aurenka. Kuma insha Allahu da ni za ayi dukkan hidimomin bikin. Ka bar mana haɗa lefe ni da Zarah Wallahi za ka sha mamakin irin kayayyakin da zamu haɗa.”

Tunda take magana yake kallonta. Bai yi mamakin iya tsara zancenta ba, don tun tana ƙarama Allah ya halicceta da iya tsara zance kamar marubuciya.

“Ke kuwa baki kishin mijinki ne? Sau tari kina bani mamaki Ihsaan. Ko duk ƙiyayyar da kike yi min ne ya jawo hakan?”

Tafukan hannunta tasa ta rufe fuskarta, sannan ta buɗe tana dariya,

“Yaya idan na yi kishin ma ba fasawa za ka yi ba, idan na yi kukan na yi tunanin sai dai incutar da kaina. Ina jin mata da yawa suna cewa duk irin tashin hankalin da mace za ta yi akan ta hana mijinta ƙarin aure sai ya ƙara, ko da kuwa tana kwance ne a gadon asibiti. Idan da gaske ne to me zai sa intada hankalina? Kuma nima ina son ka auri wacce kake so, indai na kasance mai adalci.”

“Wacce nake so? Kina nufin ke ba sonki nake ba? Ihsaan idan baki amince akan inƙara auren nan ba, ni kuma zan fasa. Sai innuna maki abin da wasu matan suke faɗa ƙarya suke yi, halin mazajensu kawai suka sani basu san naki ba.”

Ta ɗan dube shi ta kama hannayensa wanda har ta saba, da wahala su yi magana har su gama bata kama hannayensa ba, ko kuma shi bai kama nata ba..

“Yaya Wallahi na amince ka ƙara aure. Amma da sharaɗi.”

Da sauri ya ce,

“Sharaɗin mene?”

Yadda ya matse mata hannu yasa ta ɗan yi ƙara. Sai asannan ya fahimci zafi ta ji, don haka ya sassauta riƙon yana dubanta.

“Yauwa sharaɗina shi ne idan dai mu zamu haɗo lefe to na yarda ka auri Amira.”

Takaici ya rufe shi. Tsantsar yarinta yake gani a idanunta. Kawai sai ya saki hannun ya koma ya kwanta,

“Shikenan zan baku kuɗi ku je ku haɗo kayan lefen.”

Farin ciki ya tsirga mata ta ce,

“To ai bamu san size ɗinta ba.”

Gaba ɗaya hirar ta gundure shi, don haka ya bata amsa ido a rufe,

“Duk abin da za ki siyo ki siya daidai jikinki. Domin naga har ƙafarku iri ɗaya ne.”

Ihsaan ta ɗanyi shiru tana so ta tuna da girman Amira, sai dai da yake a fusace suka je ba za ta iya tuna komai ba. Dole ta rufe babin ta zaro wayarsa a cikin aljihunsa ta danna lambar Zarah. Tana ɗauka ta ce,

“Zarah albishirinki?”

Zarah ta amsa da,

“Goro.”

“To Yaya dai ya bar mana haɗa lefen bikinsa.”

Zarah ta ɗan yi Shiru tana tunanin me ya hau kan Ihsaan ne? Kawai ta ja tsaki ta kashe wayar. Irfaan yana kallonta yaga yadda ta bi wayar da kallo, sai kuma ta basar.

*****

Rayuwar tana daɗa miƙawa. Ihsaan antsunduma a karatun likita babu ji babu gani. A irin lokacin kuma Allah ya amshi addu’ar Irfaan ya sami muƙamin da yake nema ido rufe.

A irin lokacinne kuma Abba ya yi ritaya.

Gagarumin biki za ayi na ban mamaki wanda Abba da kansa ya shirya hakan. Biki biyu za ayi, da bikin ɗaura masa muƙaminsa. IG da kansa zai ɗaura masa muƙamin a can Abuja, duk da wannan ba wani taro bane, sosai.

Amma wanda Abba da Umma suka haɗa masa gagarumin taro ne na ban mamaki.

A babban ɗakin taro na Arewa House za gabatar. Kowa ka gani kansa ya ɗau zafi, musamman Zarah da Ihsaan.

Ihsaan ta kwaso wasu kaya za ta kai ɗakin Umma ta ji tattaunawan da ya ɗaga hankalinta,

“Yanzu Irfaan kasan dole da matarka za ka tafi gaban IG a ɗaura maka ƙarin girmanka duniya suna gani suna ɗauka. Ta yaya zaka je da Ihsaan? Ko dai zaka tafi da Amira ne? Tunda ita zaka aura. Ko me ka gani?”

Irfaan ya dubi mahaifiyarsa ya ce,

“Umma anya ke ce kuwa? Babu inda bazan shiga da Ihsaan ba. Wallahi Umma zan nunata a idon duniya ba tare da na ji ko da ɗar ba. Amira kuma bata isa ta taka wannan matsayin ba, ko da kuwa ace na aureta ne. Umma don Allah mu bar maganar nan anan.”

Umma ta jinjina kai,

“Mun barta. Allah ya yi maku albarka. Wallahi yadda naga jama’a ana ta hirar wannan abu sai ya tuna min da takaicin bikinka da bamu samu mun yi hakan ba.”

Irfaan ya yi murmushi ya ce,

“Kin ga yanzu sai ki fanshe kawai, kafin lokacin bikina da Amira. Ko kuma bikin Abubakar ko na Zarah. Ke Umma ai baki da takaici tunda ga aurarrakin ‘ya’yanki nan a gabanki.”

Da sauri Ihsaan ta koma da kayan suka yi kiciɓus da Abba. Ya lura idanunta hawaye ne kwance don haka ya dubeta,

“Kuka kike yi ne Ihsaan? Wani abu akayi maki?”

Kalaman da suka sa Umma da Irfaam fitowa kenan suna kallonta. Jikinsu duk ya yi sanyi suna tsoron kada dai ace ta ji hirarsu.

“A’a Abba ba kuka nake yi ba.”

Duk sai suka yi ajiyar zuciya. Ta wuce kawai da kayan maganganunsu suna yi mata amsa kuuwa.

*****

Yau saura kwanaki biyu. Yana zaune a falo yana tattara wasu takardu,  Amira ta kira shi a waya. Bayan ya kammala kintsa su, ya ɗan duba ya tabbatar Ihsaan ta shiga kitchen  sannan ya bi kiran..

“Yanzu da Ihsaan zaka je wurin nan? Tayaya zaka jawowa kanka abin zagi? Don Allah ka rufa mana asiri ka bari inzo mu je, ita sai ta zauna a gida. Kada ka manta duk duniya za su ga wannan abu, so kake ayi ta maka dariya?”

“Malama don Allah dakata. Kada ki sake kirana da irin wannan maganar na gaya maki.”

Ya katse wayar kawai ransa yana ƙara jagulewa. Kiran Shamsu ya sake shigowa. Shima dai akan Ihsaan yake magana. Dukka abokansa babu waɗanda basu yi masa magana akan Ihsaan ba, amaimakon ya fahimcesu sai ya akasin hakan. Domin kuwa ji yake da suna kusa da shi ne babu abin da zai hana shi bai yi masu wulakanci ba.

Duk Ihsaan ta ji tattaunawarsu a haka ta ƙaraso ta zauna kusa da shi, ta ɗauki hannunta da ta gama amfani da ruwa ta manna masa a fuska. Sassanyar ajiyar zuciya ya saki sannan ya dubeta,

“Ya akayi ne? Kun amso ɗinkunanku?”

Ta dube shi yadda yake son kauda damuwar fuskarsa ta ce,

“Ni tsoron idon jama’a nake yi. Ko za ka sa Amira amadadina?”

Sai da ya jawota ta kwanta a ƙirjinsa ya ce,

“Ihsaan… Har abada baki da madadi. Allah ya riga ya baki wannan girman da matsayin kin ji? Bani amsata kun amso ɗinkunanku?”

Idanunta sun kawo hawaye, ta yi ƙoƙarin shanyesu ta ce,

“Bamu amso ba, ya ce sai zuwa anjima zamu koma. Yanzu Hijabi zansa ko gyale? Kasan ban taɓa sa gyale ba, kada insa Hijabi ayi ta min dariya.”

“Kisa duk abin da ya yi maki inga mai maki dariya.”

Ta ɗan yi murmushi kawai.

Bayan sun kammala shirye-shiryensu suka bi jirgi zuwa Abuja. Acan za ayi masa ƙarin girman. Duk wani masoyin Irfaan ya sami isa can. Hatta su Ramatu sun tafi, musamman don su sake samun daman yin dariya sosai. Kai tsaye a gidansu na cikin Abuja suka sauka. Shi kuwa Irfaan tunda ya tafi basu sake ganinsu ba, ya ce kawai su haɗu acan.

Umma da Abba da kuma Iffan suka tafi a mota ɗaya, Sadiq da Zarah da Ihsaan za su taho a tasu motar.

Wuri ya yi wuri. Manyan masu muƙamai ne a wurin da gogaggun matansu. Sun yi kyau har sun gaji.

A lokacin da aka kira Irfaan cikin kakin ‘yan sanda, sai ya shiga raba idanu domin har zuwa lokacin bai ga idanun Ihsaan ba. Dole ya tashi ya iso gaban manyan ‘yan sandan ya sara masu.

A lokacin aka ambaci sunan matar Irfaan wato Ihsaan don ta bayyana a wurin.

Wurin ya yi tsit! Sai yanzu gaban Irfaan yake faɗiwa.

Ƙwas-ƙwas-ƙwas takun tafiyarta yasa duk aka jiyo yana kallonta.

Shi kansa Irfaan ɗin idanu ya zuba mata.

Tana sanye da jan Lace. A takaice dai shigar jajaye ta yi. Gashin kanta yasha gyara ta zubo shi baya ta yi ɗauri wanda ya bayyana gashin. Fara ce tas! Tasa ɗankunnen Gold har zuwa zabban da ke hannunta na Gold ne. Ta yafa wani gyale shima ja, mai adon duwatsu masu ɗaukan idanu.

Duk wanda yasan Ihsaan idan ya ganta a yanzu zai ganeta ne kawai a fuskarta da babu abin da ya sauya daga kamanninta. Sai wannan farin da ya bayyana. Ta yi jan ƙunshi ahannu da ƙafa sai suka ƙara ƙawata fatarta.

Shamsu da Yusuf kuwa garin kallo har suna miƙewa tsaye basu sani ba. Abba da Umma suka kalli juna. Sai kuma suka dubi Zarah da Sadiq yadda suke ta fara’a.

A lokacin Ihsaan ta dubi jama’a ta buɗe bakinta alamun dariya, fararen haƙoran nan suka bayyana. Wani irin haƙorin makka mai tsanani sheƙi ya haska daga cikin bakinta.

Irfaan ya ci gaba da kallonta kawai. A ‘yan watannin baya ya yi ta zargin akwai wani abu da take ɓoye masa, sai dai ya kasa gano ko menene sai yanzu.

Yadda ƙugunta da ƙirjinta suke cike tam! Yasa zuciyar Irfaan ya ɗan sosu. Akusa da mijinta ta tsaya, a lokacin ya shaƙi wani sihirtaccen ƙamshi irin wanda bai taɓa jinsa a jikinta ba.

Bayan anmanna masa ƙarin girmansa, ya sarawa IG ya juya kawai ya sarawa Ihsaan. Ƙoƙari take yi ta hana hawayen idanunta zuba, don haka ta rungume shi tsam tana jin wani abu yana yawo a jikinta.

“Kada ki yi min kuka.”

Ya raɗa mata bayan shima ya rungumeta. Masu ɗaukar hoto kuwa sai ɗauka suke yi. Ya miƙa mata hularsa ya ɗan rankwafo ta ɗora masa akansa, sannan itama ta sara masa.

Yadda ta yi ko maƙiyinta ne ya gani dole ya ji ta burge shi. Bayan ankammala ne tana riƙe da hannun Irfaan suna bin mahalarta taron suna gode masu. Dukkan maganar da take yi da turanci take yinsa, dan ta ƙi yarda ko da wasa ta furta wata kalma ta Hausa.

Da haka har suka ƙaraso wurinsu Shamsu da su Ramatu. Ihsaan ta miƙawa Ramatu Hannu suka gaisa. Tana kallon tsabar mamaki a cikin idanunsu.

Har gaban Amira suka ƙarasa. Kallon kallo kawai suka dinga aunawa juna. Sannan Ihsaan ta saki murmushi ta ce,

“Da fatan za ki koma gida lafiya.”

Ta jawo hannunsa suka wuce wurin Umma da Abba. Anan kuma sai dauriyarta ta gaza. Ta saki hannunsa ta faɗa jikin Umma tana kuka mai sosa zuciya.

Tunda take jin mutane masu kirki da karamci bata taɓa ji ko ganin kamar su Umma da Irfaan ba.

Ita kuwa Zarah juyawa ta yi ta miƙawa Sadiq hannu suka tafa. Karaf!  Akan idanun Irfaan ya kafe su d ido. Hakan yasa duk suka waske.

A gajiye sosai suka koma gida, sai dai fa sun tafi sun bar mutane da yawa a cikin waswasi. Wasu ma saboda ana basu labarin munin matar Irfaan yasa suka halarci wurin. Sai dai kuma ganin akasin hakan ya basu mamaki. Gashi kuma tabbas Ihsaan ɗin ce dan ga sunanta, amma ba wacce suke tunanin gani ba.

Shi kansa Shamsu da mutanansa sun tabbatar ita ɗin ce, amma yadda akayi ta sauya daga jiya zuwa yau abin mamaki ne. Shi kansa Shamsu ya ganta gani sosai, dan shi ya kaisu filin jirgi.

Duk yadda Irfaan yaso ya haɗu da Ihsaaan dan ta amsa masa wasu tambayoyi abin ya faskara. Domin ta yi ta kaucewa hakan. Haka Zarah da Sadiq. Har suka tattara suka koma gida. Sai kuma aka hau gagarumin shirin walima.

Ihsaan ta ɓoye kanta aka ci gaba da yi mata dilka irin na asalin Maiduguri.

Gashin nan ya ƙara shan gyara sai sheƙi yake yi. Wannan karon adon blue suka yi kalan sararin samaniya. Shima irin shigar da ya yi kenan. Shi kaɗai yasan me ke cikin zuciyarsa, sai ya ba Ihsaan mamaki.

Ba tare suka iso wurin taron ba, amma kuma tare suka shigo. Ya sha mamakin ganin dandazon mutane.

Bayan sun zauna ya sake juyowa yana kallonta. Ta yi kyau har ta gaji. Jikinta har wani yalo-yalo yake yi tsabar gyara.

Amira ta sami isowa sai dai jikinta asanyaye yake. Ta tabbata lokacin rabuwanta da Irfaan ne ya zo, tunda har yana tare da Ihsaan a matsayin mata. Sai dai har yanzu bata daina mamakin yadda akayi wannan baƙin ya ƙanƙare ba. Ko ɗigon baƙi babu a jikinta.

Su Umma da Abba sun ƙaraso. Da isa Umma take nuna Ihsaan a matsayin matar Irfaan. Akaf cikinsu Irfaan ne kawai fuskarsa babu yabo babu fallasa. Sannan irin kallon da yake yi wa Ihsaan ita kanta ta fahimci kallo ne da yake sanar da ita girman laifinta a wurinsa.

Bayan anbuɗe wurin taron da addu’a mai gabatarwa ya juya yana kallon Ihsaan ya fara bayani kamar haka.

“Amarya kuma uwargida agurin Mai girma CP wato Hajiya Ihsaan za ta yi wa jama’a barka da zuwa, daga nan za ta gaya mana wanene mijinta, domin kuwa kowa yasan babu wanda ya kai mace sanin waye mijinta.”

Ihsaan ta ɗan waiwayo ta dubi Irfaan da ya ƙara wani kyau da kwarjini. Ta ga yadda ya ɗan haɗa rai, ta yi murmushi ta tashi ta fito. Duk yadda zan fasalta irin kyan da ta yi ba lallai alƙalamina ya iya fasaltata ba. Amma dai na baku gari.

Sassanyar muryarta ta fara kwararo bayani bayan ta kore shaiɗanu. Ta yi godiya sannan ta waiwayo ta dubi mijinta duba na tsanake. Kafin ta mayar da bakinta daidai saitin abin maganar da ke hannunta,

“Allah ya ka sakawa mijina.”

Tana furta hakan hawaye suka sakko daga idanunta. Jikinsa ya yi sanyi da jin furucinta. Wuri ya hargitse da hayaniya kowa na faɗin,

“Ameen mai kyau.”

Sunan da suka laƙaba mata kenan. Zarah ta ƙaraso tasa tissue ta ɗauke mata hawayen ta koma gefe. A lokacin wurin ya sake yin shiru. Ihsaan ta sake ɗagowa ta dubi mutanen wurin ta ɗora idanunta akan Amira, ta sauke ɗauke kai ta kalli su Shamsu tana tuna kalamansu akanta. Sannan ta ce,

“Duk ‘ya macen da ta sami Irfaan a matsayin mijin aure ta gode Allah. Domin kuwa ta sami namijin da zai ɗagawa matarsa ƙafafu ta shiga Aljannah ba tare da hassada ko mugunta ba. Mijina ɗan aljannah ne insha Allahu. Sunan mijina, Mijin marainiya. Ina so a yanzu zan gaya maku wanene mijina, da irin ƙoƙarin da ya yi wanda samun kamarsa sai anyi da ƙyar. Tunda ga waɗanda basu kai shi komai ba, sun gaya masa ba za su iya rayuwa da ni ba.”

Wuri ya sake ɗaukan shiru. Kowa ya fahimci akwai magana mai girma a zuciyar Ihsaan wanda ta zaɓi wannan ranar a matsayin ranar da za ta fitar da abin da ke ranta.

Ihsaan ta ɗan yi shiru. Tana so yau ta gayawa duniya irin ƙoƙarin da Irfaan ya yi akanta. Tana so Irfaan yasan abin da ta ɓoye masa agaban jama’a. Tana so yau su Shamsu susan wacce suke wulakanta halittarta. Tana so ta gayawa duniya har yanzu akwai maza masu son zuciyar mace ba wai kyawun fuskarta ba. Yau take so kowa ya fita daga cikin duhu. Waɗanda suka kwana suna tambayar yadda akayi Ihsaan ta canza zuwa fara a lokaci guda suma su sami amsar da zai fitar da su daga duhu…

Ta ji daɗi yadda ko ina ake haska abubuwan da ke faruwa, ƙila labarinta ya ƙarawa munana ƙarfin guiwa, ko basu yi kyau ba, su dai gane akwai waɗanda za su so su ahakan ba tare da duban wannan munin ba.

‘Yar mutan Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Duniyata 19Duniyata 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×