Skip to content
Part 12 of 25 in the Series Duniyata by Fatima Dan Borno

“Umma da kun yi haƙuri tukuna.”

Ya ce da ita yaba nazarin fuskarta. Kafin ta yi magana ya jiyo muryar Abba yana magana cike da walwala,

“A’a Irfaan. Nasa ankammala yi maku duj wani gyara a gidanku. Don haka zaka ɗauki matarka ku tafi. Ko yau na faɗi na mutu burina ya cika, naga auren Irfaan. Ina jin daɗi araina Irfaan ya zama cikakken mutum.”

Mamaki da takaici suka haɗu suka lulluɓe shi, sai dai ko alama bai nuna komai a fuskarsa ba.

Ya tashi yana cewa ya yi baƙo. Kai tsaye wurin Sulaiman ya nufa wanda ya amsa kiran Irfaan ɗin.

“Sulaiman ka zo mu je Ihsaan ta ganka.”

Idanunsa a ƙasa ya girgiza kai,

“Kayi haƙuri bazan iya zuwa ta ganni yanzu ba.”

“Kada kayi min gardama kazo mu je. Na yi mata alƙawarin kawoka.”

Shiru ya ziyarci wurin. Daga bisani ya biyo shi suka shigo har falo. Ihsaan ta ɗago da wani irin farin ciki wanda yaso yaba kowa mamaki.

Jikinta har yana kyarma ta nufi Sulaiman. Fahimtar abin da take shirin yi yasa ya yi saurin durƙusawa yana gaida Umma. Duk da haka sai da ta ƙaraso tana dariya mai haɗe da hawaye.

Umma da Abba suka fice daga falon. Sulaiman ya nemi wuri ya zauna.

“Ihsaaan bana hanaki kuka ba?”

Tuni sabbin hawaye suka shiga zarya a idanunta.

“Ka tafi ka barni.”

Ta bashi amsa cikin kuka. Ya yi murmushin ƙarfin hali sannan ya dubeta sosai.

“Yaya Irfaan yana da kirki. Kinga a ƙauye baki gane karatu, yanzu ne zaki yi karatu zaki goge sannan ki koma ƙauye zaki sha mamakin yadda za a soki. Idan kina kukan nan kina ɗaga min hankali. Don Allah ki daina kinji?”

Ta goge hawayenta ta ce, “Zaka dinga zuwa? Ina jin tsoro bazan iya barci babu kai ba.”

Zuciyarsa ta yi rauni. Yana jin inbanda dalili babu abin da zai sa ya iya rabuwa da farin cikinsa. Yana yiwa Ihsaan mugun so irin wanda baya jin akwai wanda zai iya kwatanta yi mata irinsa. Soyayyar Ihsaan tafe yake da kowane bugun zuciyarsa.

A hankali ya ɗaga kai ya dubi Irfaan,

“Yaya ka taimakeni ka riƙe min amanar Ihsaan. A lokacin da zan dawo inbuƙaceta nasan zaka iya hanani, domin a irin lokacin kaima ka riga kayi nisa a cikin sonta. Amma ina ji a zuciyata za ka iya sadaukar min da komai.”

Irfaan ya ce a zuciyarsa,

‘Lallai yaron nan bai da hankali. Ni ne zan so Ihsaan?’

A fili kuma sai ya ɗan yi murmushi ya ce, “Sulaiman kenan. Allah ya kaimu lokacin.”

***

Umma da kanta ta ɗauki Ihsaan zuwa ɗakin mijinta. Ta ɗau burin gyarata har ta zama abar kwatance.

Da ƙyar ta lallaɓa Ihsaan akan zata kawo mata tsohuwa ta zauna da ita, sannan ta yarda ta zauna. Kuka kuwa tasha shi babu adadi. Hatta muryarta sai da ta dashe da kiran sunan Sulaiman.

Acan cikin zuciyarta ta tsinewa Marka da Innayo yafi a ƙirga. A ganinta sune  silar shigarta cikin matsala.

Har dare babu Irfaan babu dalilinsa. Ita kuwa tana nan zaune ta kasa motsawa saboda tsoro.

Can ta jiyo ana buɗe ƙofa ta sake maƙale jikinta. Sosai yake dubanta cike da tausayi. Tun bayan da aka kawota gidansa baya garin, ya tafi Zariya aiwatar da wani aiki. Duk abubuwan da yake yi hankalinsa yana kanta.

“Ihsaan kinyi barci ne?”

Ta yi saurin buɗe gyalen da aka rufota ta dube shi ido cikin ido ta ce,

“Shi ne zaka tafi ka barni ni kaɗai? Don Allah ka mayar da ni gurin Yaya Sulaiman don Allah.”

Muryarta tana da zaƙi ya yin furta magana. Sannan tana da shagwaɓar da ita kanta batasan tana da ita ba. Da hannu ya yafitota.

“Ki yi haƙuri kinji? Zo ki zauna ki ci kaza nasan yunwa kike ji.”

Jikinta asanyaye ta zauna a gabansa ya tasa mata ledar da ya shigo da shi. Yadda take cin kazar kaɗai zai tabbatar da irin yunwar da take ji. Ya yi mamakin yadda Umma za ta barta babu abinci.

Ya tashi ya nufi dinning table ɗin anan ya sami abinci ko buɗewa ba ayi ba. Ya girgiza kai kawai. Zamansa ya yi ya ci abin da zai iya ci sannan ya miƙe yana cewa

“Idan baki ƙoshi ba, ki zo ga abinci. Ni zan shiga ciki.”

Da sauri ta miƙe,

“Ka tsaya ingama ci sai mu tafi tsoro nake ji.”

Yarinyar ta fara zame masa damuwa. Takaici ya hana shi magana. Dole ya koma ya zauna har ta gama. Ya rakata banɗaki ta wanko hannu sannan suka dawo ɗakinsa.

“Ke a ina zaki kwanta? Ki koma ɗakinki mana.”

Ta girgiza kai,

“Zan shimfiɗa gyalena a ƙasa a ɗakinka sai mu dinga kwanciya yadda muke yi da Yaya Sulaiman.”

Da sauri ya juyo yana kallonta, sai kuma ya kauda kai kawai ya wuce. Gaba ɗaya Ihsaan ta lalace wajen kallon ɗakinsa yadda ya tsaru. Har ya shiga banɗaki bata sani ba. Wani irin sanyin AC ya haɗe da ƙamshi mai daɗi yana ratsa ko ina.

Har ya fito tana nan zaune ta kafe ɗakin da idanu. Bai dubeta ba ya gama kintsawa ya haye gadonsa tare da janyo tattausan bargonsa ya rufe har kai.

Shi kaɗai yake kintsa abubuwa daban daban a cikin zuciyarsa. Ya rasa dalilin da tun kawo Ihsaan gabansa ke faɗiwa musamman ma idan ya kalleta. Haka kawai yake ji a zuciyarsa tamkar ba za su yi zama mai tsawo ba.

Jin shirun ya yi yawa yasa ya buɗe bargon yana leƙenta. Tana nan zaune a kujeran ɗakin barci ya yi awon gaba da ita. Baya jin zai iya taɓa jikinta bare har ya gyara mata yadda zata kwanta. Don haka ya mayar da kansa yana tunani. Har baya son ya tuna cewa zai je Ofis ranar litinin.

Can cikin dare sanyi yasa ta tashi babu shiri, ta kwanta a ƙasa tare da rufe jikinta da gyale.

Kamar ance ya tashi, ya ganta tana ta rawar sanyi bakinta yana karkarwa. Ta ƙudundune. A natse ya sakko ya ɗauko wani bargo ya zo ya rufa mata. Da zai iya ɗaukanta da babu abin da zai hana shi mayar da ita ɗakinta da baya jin ko leƙawa ta yi.

Washegari sai wajen sha ɗaya na safe ta farka, da kuka sosai. Irfaan yana daga falo yana karyawa da kayan karin da Umma ta aiko, yana jin kukanta amma ko alama bai ji aransa zai iya zuwa yaji dalilin kukan ba.

Allah-Allah yake ya gama ya fice tun kafin ta sa masa wata damuwar.

Da kuka ta fito falon kai tsaye wurinsa ta nufa tana kuka,

“Ka kira min Yaya Sulaiman don Allah. Ni bazan iya zama a gidan nan ba, bana sonka na fi son Yaya Sulaiman.”

Ya dubeta kamar ya kifa mata mari ya ce, “Ni ɗin ce maki akayi ina sonki? Kinsan Allah? Idan kika ci gaba da matsa min kina damuna da kukan nan sai na farfasa maki baki. Zaki wuce ki bani wuri ko sai na tattakaki?”

A ɗan tsorace ta kama hanyar ɗakinsa tana jin wani kukan yana tahowa. Da sauri ya ce, “Ke! Kada ki shigar min ɗaki.”

Cak! Ta ja ta tsaya tana yayyanka idanu. Kai tsaye ya tashi ya nuna mata ɗakinta ya ƙara da cewa,

“Idan kika gama kukan sai ki zo nan ki ɗibi abincinki. Anjima mai aiki zata zo kinga shi kenan sai ki dinga kwana tare da ita.”

Babu musu ta nufi ɗakin da ya nuna mata. Ta ƙudundune kanta ta yi kuka kamar ranta zai fita. Ta kasa sabawa da rashin Sulaiman. Ta shaƙu da shi fiye da kowa. Ta gwammace kowa ya gujeta indai Sulaiman yana kusa.

Abincin da bata iya ci ba kenan har kusan la’asar. Shi kuwa tuni ya fice daga gidan ma gaba ɗaya.

A lokacin ta ji alamun ana ƙwanƙwasa ƙofar. Tana jin jiri ta dinga dafa bango har ta samu ta leƙo. Mai gadin gidan ne ya miƙa mata wani jakan leda ta ce,

“Yayanki Sulaiman ya ce abaki.”

Ta karɓa kawai tana kallonsa. Tana son tambayar ina yake? Amma bakinta ya yi nauyi. Sosai take jin jiri. Tana kallo ya wuce abinsa. Haka ta ƙanƙame ledan tana shessheƙan kuka. Bata iya buɗe ledan ba ta wuce ciki tana jin ɗaci abisa harshenta.

Wurin Shamsu Irfaan ya nufa yana so su tattauna akan maganar ƙarin girman da zai samu.

Shamsu yana ganinsa ya fara toshe baki. Irfaan ya yi shiru bai ce uffan ba,

“Angon ‘yar baƙa kasha ƙamshi.”

“Don Allah kana da lokaci na ko intafi?” Irfaan ya maido masa martani yana jin takaici yana sake lulluɓe shi.

“Tuba nake. Kasan me ke faruwa a Ofis kuwa? Su Ramatu sun gama yaɗaka ka auro ‘yar ƙauye mai kama da aljana.”

Irfaan ya yi murmushi ya ce, “Ko me akayi min ai da sa hannunku. Tayaya su Ramatu za su ce za su biyo ku ɗauko amarya ku yarda? Duk abin da za su faɗa ba zai dameni ba, domin na tabbata babu wacce za ta iya zuwa gabana ta faɗa.”

Shamsu ya sake tuntsurewa da dariya ya ce, “Idan suka zo gabanka me za ka yi masu?”

Ya yi mamakin tambayar don haka ya ɗan kauda kansa ya ce, “Wata ta zo gabana ta zagar min mata? Ashe daga ranar ba za su sake yin wata rashin kunya ba. Har abada macen da ta raɓu da ni a matsayin mata tafi ƙarfin wani ya wulakanta min ita. Kai dai hankalinka ya kwanta sauranka ka rabawa ma’aikatan jarida hotunan da ka ɗauka.”

Shamsu ya zaro idanu ya ce, “Maye! Wato har ka ganni. Wallahi na ɗauka ne saboda in ajiye maku na tarihi.”

Irfaan ya jinjina kai yana jin ransa yana ƙara ɓaci.

“Idan ana neman munafukaina aka rasaku a farko a nemeku acan ƙasan wuta.”

Ya juya kawai ya shiga mota. Kiran duniyar nan da magiya Shamsu ya yi masa amma ko kallonsa bai yi ba, ya figi motarsa aguje yabar wurin.

Umma ta dubi yadda Irfaan ke kwance a dogon kujerarta ta ce, “Wai ita ɗaya ka bari a cikin gidan?”

Ya ɗan musƙuta ya ce, “Umma wacece kika ce zata yi wa Ihsaan wankan dilka saboda baƙin nan ya ragu? So nake a yau ba sai gobeba a fara yi mata gyaran jiki. Saboda idan na sanyata a Makaranta yanzu akwai matsala. Yara za su yi ta tsokanarta ne. Gara ta ɗan goge ta koyi tsafta.”

Umma ta yi ajiyar zuciya, ta dawo ta zauna tana dubansa, “Tun ɗazu ta ce zata zo shiru. Nima na goyi bayan hakan. Amma kuma Irfaan kai da kace min kafi son baƙar mace ka tsani kyakkyawa menene kuma haɗinka da baƙinta? Na yi zaton tsaftar kawai za a koya mata shiyasa zan tura Larai ta zauna da ita.”

Irfaaan ya ɗan shafi sajensa ya ce, “Umma har yanzu ina nan da ra’ayina. Sai dai kuma baƙin Ihsaan ya wuce tunanin mai hankali ne. Ni ko baƙin ma bai goge ba, ya zamana tana da tsaftarta.”

Umma ta jinjina kai. Sai wajen Magrib mai gyaran jikin tazo akan zata tare a gidan Irfaan har sai ya gamsu da gyaran. Tare da Larai ya ɗauke su suka wuce gidansa.

A falo ya barsu ya nufi cikin ɗakin. Tana kwance shiru idanun nan sun kumbura saboda kuka. “Ihsaan kin ci abinci?”

Ta girgiza kai. Da sauri ya fice sai gashi ya dawo da ruwan tea. A hankali ta dinga sha sai kuma ta kama gumi. Ya sake fita ya dibo mata abinci. Ta ɗan ci kaɗan sannan ya gabatar da mai gyaran jikin da kuma Larai mai aiki.

A ranar ya yi wa Samira mai gyaran jiki izinin ta fara. Shi kuma ya koma ɗakinsa ya ci gaba da sangoginsa.

Larai ta shiga kitchen ta nema masu abincin da za su ci, ta gyara falon da ko ina na cikin gidan, amma banda ɓangaren Irfaan.

Ya yi nisa a cikin shigar da wani aiki a laptop dinsa ya ji  siririyar muryar Ihsaan ta yi masa Sallama. A zuciyarsa ya rintse ido yana jin muryar yarinyar yana yi masa tasiri a jiki. Bai iya amsa Sallamar ba, har ta gaji ta cusa kanta.

Mu je zuwa…

‘Yar mutan Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Duniyata 11Duniyata 13 >>

1 thought on “Duniyata 12”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×