Skip to content
Part 19 of 25 in the Series Duniyata by Fatima Dan Borno

Tun shigarsu garin Saulawa take rarraba idanu, komai yana dawo mata sabo. A hankali ta rage sa baki a hirar da ake yi da su Umma. Sadiq ya fara kula da sauyawarta sakamakon ya fi kowa tsokanarta.

“Anti Ihsaan wancan ma gida ne?”

Sadiq ya sake antayo mata tambaya cike da zolaya. Duk suka zuba mata idanu, ganin tana shirin rushewa da kuka.

“Ihsaan ina fatan ba kuka za ki yi ba? Ki daure kin ji?”

Hawaye ya ziraro, tana zare idanu ta ce,

“Umma Yaya Sulaiman ne.”

Umma ta girgiza kai,

“Idan kina so inyi fushi da ke to ki yi kukan.”

Ihsaan tana girgiza kai tana cewa,

“Umma Yaya Sulaiman… Ya tafi..”

Sai kuma tasa kuka mai tsuma zuciya, tana yi tana ajiyar zuciya. Duk motar akayi shiru. Zarah ma tasa kuka sosai. Duk suna tunawa da ranar da suka zo bikinta.

Da ƙyar aka samu Ihsaan ta yi shiru. Kai tsaye gidan Baba Marka aka fara wucewa. Gidansu yana nan a yadda ta barshi, sai ƙarin lalacewa da ya yi. Komai ya dinga dawo mata sabo. Ta tuna mahaifinta, ta tuna irin rayuwar da suka yi tare.

Jikin Marka babu inda baya kyarma. Yau Ihsaan ce ta zama haka? Ta yi mamaki, a zatonta babu inda Ihsaan za ta kai. Sai gashi tun ba aje ko ina ba, Ihsaan ta fi karfinta.

Umma bata nuna ƙyamarta akan Marka ba ta zauna suka ɗan taɓa hira sannan suka nufi gidan da Ihsaan bata ƙaunar zuwa. Tun daga ƙofar gidan take kallon wurin zamanta da Sulaiman, har zuwa shigarsu ciki.

Wajen wanke-wanke ta kaiwa duba, ta tuna abubuwa masu yawa. Da baya da baya take komawa tana girgiza kai, har sai da Umma ta riƙeta,

“Umma Yaya Sulaiman ya tafi..”

Ta durƙushe bisa guiwowinta ta fasa wani irin kuka mai cin rai. Kuka take yi jikinta yana kyarma. Sai yanzu ta ƙara amincewa Sulaiman ya yi mata nisa. Ga ɗakinsu nan da suka yi rayuwa a rufe.

Babu wanda bai zubda hawaye ba. A ƙasa ta durƙushe tana shessheƙa. Da lallashi da ban baki aka samu Ihsaan ta zauna a ɗakin Marka. Sai dai ta yi alƙawarin ba za ta zauna a cikin gidan ba, ta gwammace ta koma wurin Marka ta zauna fiye da ta zauna a gidan su Sulaiman.

Duk hirar da akeyi babu bakinta a ciki, ita kaɗai tasan yadda zuciyarta ke ciwo.

Innayo ta gabatar masu da abinci sai dai babu wanda ya iya ci, mota suka nufa suka kwaso kayan ciye-ciyensu suka ci.

Haka Umma da su Sadiq suka tafi suka bar Ihsaan a cikin gidan su Sulaiman. Ihsaan tana ganin sun tafi ta jawo ƙafafunta tana cijewa ta nufi hanyar waje. A guje Innayo ta biyota tana zare idanu,

“Ina kuma za ki je?”

Ihsaan ta watsa mata wani irin kallo mai cike da tsana sannan ta ce,

“Gidanmu zanje.”

Innayo ta ɗan yi yaƙe ta ce,

“Anan za ki zauna har lokacin komawarki.”

Hawayen da take ta dannewa suka zubo mata ta girgiza kai,

“A lokacin da naso ki barni da Yaya Sulaiman hakan ya faskara. Kin kasa yi mana uzuri. Da ace zaki mayar da yanzu baya, babu ko shakka da zan zauna ko baki roƙeni ba, muddin dai zaki barni inrayu da Yaya Sulaiman.”

Innayo ta yi zuru-zuru sanna ta kama borin kunya,

“Yanzu ya wuce kuma, sai mu tari gaba. Ki yi haƙuri ki dawo ki zauna.”

Ihsaan ta yi murmushi mai ciwo, sannan ta ci gaba da tafiya. Har ta kai bakin ƙofa, sai kuma ta juyo ta ce,

“Babu amfanin zamana anan. Zan tafi gidanmu.”

Ta wuce kawai, tana tafe tana kuka wiwi kamar wacce akayiwa mutuwa.

*****

Dukkan ayyukansa ya zama gagararre saboda rashin mutum ɗaya da ke cikin rayuwarsa. Ya kasa zaune ya kasa tsaye. Tunanin Ihsaan kaɗai yake yi.

Bai tashi sanin amfaninta ba, sai da dare ya yi ya dawo gidan. Tsit!  Kamar babu kowa a ciki. Babu shiri ya tattara ya koma gidansu.

Umma suna ba Abba labarin abin da ya faru da suka isa Saulawa, a lokacin ya shigo gidan. Sai da ya gama saurare sannan ya shigo jiki asanyaye.

“Umma kuma me ya sa kuka barota?”

Abba ya yi murmushi ya yi masa alama da ya ƙaraso wurinsa. Bai ce komai ba ya ƙaraso ya zauna a ƙasa,

“Irfaan ina alfahari da kai. Nasan kana da biyayya, amma ban taɓa tunanin za ka yi min irin wannan biyayyar ba. Na ji tsoro matuƙa kada Sulaiman ya yi kuka da irin riƙon da za ka yi wa Ihsaan. A yanzu kuma na saki jikina, domin na gane Irfaan ɗina ba zai iya rayuwa babu Ihsaan ba.”

Irfaan ya ɗan yi shiru daga bisani ya yi magana cikin sanyi,

“Abba duk abin da nake yi ina yi ne saboda kai da Sulaiman. Abba na jima ina so ingaya maka zan ƙara aure amma tausayin Ihsaan yana hanani hakan. Abba kuyi min izini inƙara aure, na yi maku alƙawarin ba zan taɓa cutar da ita ba.”

Gaba ɗaya ɗakin kowa ya ɗauke wuta. Har yanzu fuskarsa tana ɗauke da soyayyar Ihsaan wanda shi kansa baisan abin har ya yi girman da ake iya karanta a fuskarsa ba.

“Me ya sa za ka ƙara aure?”

“Abba na yi wa wata alƙawarin aure da jimawa. Na ƙi gabatar da ita ne har sai Ihsaan ta kammala karatunta. A lokacin na kammala cika dukkan alƙawarin da na ɗaukarwa Sulaiman.”

Abba ya girgiza kai,

“Duk abin da za ka yi a yanzu ba zan hanaka ba, muddin ba zaka auro wacce za ta cusgunawa Ihsaan ba.”

Umma za ta yi magana Abba ya ɗaga mata hannu,

“A’a ya yi mana biyayya a yanzu lokacinsa ne. Ta shi ka je.”

Irfaan ya girgiza kai,

“Anan zan kwana gidan ya yi min girma da yawa.”

Duk suka yi murmushi amma banda Umma.

Hirar kawai suke yi hankalinsa baya gurinsu. Duk sun fahimci hakan, har Abba ya sallami kowa suka kama gabansu. Irfaan ya shiga ɗakinsa ya kwanta shiru.

Shigowar Umma yasa ya tashi zaune yana kallonta da mamaki.

“Umma lafiya?”

Bata bashi amsa ba, har sai da ta nemi wuri ta zauna a bisa gadon, sannan ta dube shi sosai,

“Irfaan ka nemi yardar Ihsaan akan ƙarin aurenka idan ta yarda mu ma zamu yarda.”

Irfaan ya yi murmushi ya ce,

“Ihsaan tasan komai akan yarinyar. Ta santa. Wataran ma bana son zuwa gareta amma Ihsaan ke matsa min.”

Umma ta saki baki galala tana kallonsa,

“Amma dai anyi sakaran yarinya. Namiji za ta yiwa irin wannan saken? Zata dawo ta sameni.”

Irfaan ya yi murmushi ya jawo hannun Umma ya ɗora akansa ya ce,

“Umma ba dai cewa surukarki za ki yi ta dinga wahal maki da yaro akan kishi ba?”

Umma ta zabga masa harara tare da cire hannunta, \

“Da kyau! Ita kuma ba ‘ya ba ce ko? Kasan Allah? Haka kawai na ji hankalina bai kwanta da auren da za ka ƙara ba. Ka yi wa Allah ka ƙarawa Ihsaan lokaci Wallahi za ta fi haka insha Allahu.”

Sosai yake duban mahaifiyarsa. Sannan ya yi magana,

“Umma… Idan Ihsaan za ta dawwama ahaka na yi maki alƙawarin zan zauna da ita da zuciya ɗaya. Ba zan taɓa muzguna mata saboda muni ko wani abu nata ba. Bazan kuma bari wani ya cutar da ita koda da kalaman baki ne ba. Ki yarda da ni. Zan ƙara aure ne saboda wasu dalilai.”

Jikin Umma ya yi sanyi. Ta ce,

“Shikenan. Allah ya yi maka albarka.”

Ya amsa da,

“Ameen tare da ‘yan ƙannena.”

Har suka yi sallama ta tafi bai daina kallon ƙofar ba. Ji yake kamar Ihsaan za ta shigo masa da baƙin shayi.

Kiran da ake masa a waya yasa ya zaro ya ɗaga kawai tare da buɗe muryar wayar.

“Me ya sa nake kiranka baka ɗagawa?”

“Ina wurin iyayena ne.”

Ya bata amsa a takaice.

“Ya maganarmu?”

Ta tambaye shi cike da ƙosawa,

“Na shigar da maganarmu wurin iyayena. Don haka ba zamu yi aure ba, sai nan da shekaru uku lokacin Ihsaan ta sami daman ƙarasa karatunta.”

Ta tsani suna magana yasa sunan Ihsaan. A yanzu kuma sai ta fi jin tsanar Ihsaan ɗin fiye da kowane lokaci.

“Menene fa’idarka na yin hakan?”

“Ki yi haƙuri alƙawari na ɗauka nake son saukewa.”

“Alƙawarin me?”

“Bai shafeki ba.”

Duk suka yi shiru.

“Na yi kewarka sosai.”

Ta katse shirun.

Sai da ya shafi kansa sannan ya ce,

“Na gode.”

‘Jan ajinsa ya yi yawa.’

Ta faɗa a zuciyarta. Dole ta yi masa sallama ba tare da ta so hakan ba.

Washegari da sassafe Irfaan ya ɗauki motarsa ya kama hanyar Saulawa.

Tana zaune a tsakar gidan bakinta duk ya bushe, saboda tunanin Sulaiman. Ɗaya ɓangaren kuma na zuciyarta tana cike da kewar Irfaan wanda ta ɗauki hakan a matsayin shaƙuwa musamman saboda kyautatawarsa gareta.

Baba Marka ta fito tana dubanta,

“Ke kuwa lafiyarki ƙalau? Har ruwan kokon ya sha iska amma baki kai komai bakinki ba.”

Bata ce mata komai ba, sai sunkuyar da kai da ta yi.

“Assalamu alaikum.”

Suka ji sallamarsa. Yana tsaye cikin fararen kaya sunyi masa kyau. A jikin aikin da akayi a rigar akwai ratsin baƙi.

Da sauri ta tashi tsaye tana kallonsa,

“Lahhh Yaya Irfaan.”

Zuba mata idanu kawai ya yi yana kallon yadda duk ta fita hayyacinta. Da sauri ta ƙaraso ta kama hannayensa. Farin ciki ya gaza barinta ta furta komai.

Ya ɗan shafi fuskarta ya ce,

“Kinga yadda kika rame? Kin ci abinci?”

Baba Marka da ta gama zaginsu a zuciyarta da ‘yan iska ta yi carab ta ce,

“Yauwa gara da kazo. Ta ƙi ci ta ƙi sha. Wai saboda Sulaiman.”

Murmushi ya ɗan yi, sannan ya jawo hannunta suka zauna a tabarma.

“Kin ga dalilin da yasa bana so ki yi nesa da ni ko? Babu mai iya kula min da ke a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Ki tashi mu tafi gida.”

Baba Marka ta yi maza ta ƙaraso ta zube tana gaida shi. A natse ya amsa yana ƙare mata kallo.

Ihsaan babu kunya ta tattaro yanata yanata ta fito wurin mota ta barsu suna sallama.

“Mu je gidansu Sulaiman ko?”

Da sauri ta girgiza kai ta kamo hannunsa tana so ta yi kuka,

“Shi kenan kada ki yi kukan mun fasa zuwa.”

Duk yadda ta so ta haɗiye hawayen hakan ya faskara sai da suka zubo. Bai ce mata komai ba duk suka shiga mota suka ɗauki hanyar Kaduna.

Sai da suka yi nisa sannan ya jawota ta kwanta a gefen kafaɗansa. Sai kuma a lokacin ya tuna da Abba. Tsoro da fargaban abin da zai gaya masa suka shige shi.

A gefen wani restaurant ya tsaya ya siya mata abinci da abin sha, sannan ya shigo ya miƙa mata suka ci gaba da tafiya.

Kasancewar babu yadda zai yi ya iya ci, ita ke gutsuran kazar tana sa masa abaki. Sai ya ce ta ci sau uku tasa masa sau ɗaya.

Sai a lokacin wata natsuwa ta ziyarcesu. Dukkansu sun yi kewar juna.

“Gaya min jiya kinyi tunanina?”

Ta ɗago asanyaye sannan ta ce,

“Eh na yi.”

‘Yar mutan Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Duniyata 18Duniyata 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×