Skip to content
Part 13 of 25 in the Series Duniyata by Fatima Dan Borno

Ya ɗaga idanunsa yana fatan ganinta fes. Sai dai kuma akasin hakanne ya bayyana. Ihsaan ɗin dai ita ce agabansa bata sauya ba. Gani ya yi ma kamar ta ƙara zama baƙa ce. Yana so kullum ya natsu ya ƙare mata kallo, amma baƙinta yakan hana shi hakan domin shi bai taɓa ganin halitta mai tsananin baƙi irin Ihsaan ba.

“Menene haka? Baki tsaya anyi gyaran ba ko?”

Ya furta mata cikin takaici. Ihsaan ta girgiza kai hawaye cike da idanunta ta ce,

“Ka tambayeta kaji, na tsaya kuma ta yi min.”

‘Tirƙashi!’

Ya furta a zuciyarsa yana sake jijjiga kai. A natse ya ce,

“To me kika zo yi a ɗakina?”

Sosai ta sake sunkuyar da kanta sannan ta ce,

“Na zo ne innuna maka gyaran.”

Shiru ya yi yana nazarin kalamanta masu kama da raini.

“Ok. Jeki.”

Babu musu ta juya. Haka kawai zuciyarsa ta dinga tafarfasa tana yi masa zogi.  Ya rasa wa zai ɗorawa laifin cusa masa Ihsaan a tsakanin Abba da Sulaiman. Ko kuma shi kansa da ya yarda.

Zai ƙara haƙuri har zuwa wani ɗan lokaci ya gani ko baƙin zai ragu.

*****

Ranar Monday ya shirya tsaf cikin kayan ‘yan sanda, ya fito yana sauri. Shi gaba ɗaya tsakanin jiya da yau, ya fara mance Ihsaan a cikin gidan. Tun zuwan Larai ya sami sukuni. Haka zalika Samira mai gyaran jiki tana can tana gyara Ihsaan da dukkan kalolin kayan gyara.

Ita kanta ta jinjina ƙarfin fata irin na Ihsaan. Domin bata taɓa yiwa wani gyara bai yi haske ba, sai akan Ihsaan. Ita abin har tsoro ya fara bata.

Irfaaan ya kutsa kansa cikin falon mahaifiyarsa. Ƙamshin turaren wuta ya dake shi. Sai da ya lumshe idanu sannan ya buɗe su fes akan Zarah da ke sanye da kayan Makaranta. Da sauri ta ƙaraso ta riƙe hannunsa ta ce,

“Yaya ka tashi lafiya?”

Ya amsa da “Lafiya lau ‘yar auta.”

Yadda ya lura tana so ta yi masa magana yasa ya ɗan dakata yana dubanta,

“Yaya don Allah ka yiwa Umma magana ta barni inje gidanka.”

Shi kansa baya so ta je gidan domin yasan ‘yar rahoto zata zama, don haka ya ce,

“Ki bari sai ranar da babu Makaranta sai inɗaukeki da kaina.”

Ba hakan ta so ba, sai dai bata ga fuskar da za ta sake iya furta komai ba.

Ganin iyayensa basu fito ba, yasa ya nufi dinning table ɗin ya fara karin kumallo.

Tunani ne kala-kala a cikin zuciyarsa har Abba ya fito, Umma tana biye da shi riƙe da hular Abban. Da sauri ya tashi tsaye ya gaida Abba sannan ya gaida Umma.

Tare suka zauna domin ƙarasa karyawa.

“Ya Ihsaan tana lafiya ko?”

“Lafiya lau Abba.”

Umma ta ce

“Da fatan dai gyaran jiki yana kyau?”

Irfaan ya kafe Umma da ido, har sai da ta ji a jikinta ita yake kallo, don haka ta ɗago tana dubansa,

“Ina tambayarka ka tsaya tsareni da idanu.”

Irfaan ya yi murmushin takaici ya ce,

“Umma da zaki taimaka ki je ki ɗauko mai gyaran nan da kuɗinki ya huta. Wato Umma yarinyar nan ana yi mata gyara ne jikinta yana ƙara narkewa da baƙi. Andai ci nasarar ta daina warin nan. Umma kuyi ta min addu’a domin kuwa ada can baya ba aljanah na aura ba, yanzu ne dai na auri Aljanar.”

Umma da Abba suka saki dariya sosai, saboda yadda Irfaan ya yi maganar dole ya baka dariya. Irfaan ya ci gaba da duban su Umma yana mamakin yadda babu ruwansu suke cikin nishaɗi abin su.

Yana son ture abincin da yake ci, yana tunanin idan ya ture za su fahimci ransa yana mugun ɓace ne, don haka ya ci gaba da tsakura kawai ba tare da ya sake cewa uffan ba.

Umma ta ce,

“Anjima zanje gidan indubata. Yanzu ya maganar Makaranta? Dole za asanyata ba tare da la’akari da wani abu ba, domin shi ilmi babu ruwansa da kyau ko akasinsa.”

Abba ya jinjina kai,

“Hakane. Yanzu kai Irfaan menene tunaninka akan karatun Ihsaan?”

Irfaan ya dinga jujjuya abin da zai fito daga bakinsa. Daga bisani ya yi ƙarfin hali ya ce,

“Ina tunanin inkaita Makarantar kwana kawai Abba. Za ta fi mayar da hankali ga karatunta.”

Umma ta dubi Abba duk suka yi murmushi. Abba ya girgiza kai,

“Malam Irfaan babu inda Ihsaan za ta je. Idan munje Office ka gama abubuwan da zaka yi ka wuce Makarantar su Zarah ka yi mata rijista. Ko kuma ka koma ka ɗauki Ihsaan ɗin, tunda su suke bayar da uniform da komai. Kada kuma ka kuskurewa abin da na gaya maka.”

Irfaan ya dinga kaɗa kai alamun zai yi yadda Abban ya ce. Baya so ko alama ya buɗe baki da nufin yin wata magana, bare har ya yi wa iyayensa magana da muryar da bata dace ba.

Umma ta yi masu rakiya har wurin mota. Irfaan ya buɗewa mahaifinsa mota bayan ya shiga ya sara masa sannan ya rufe shi ya zagaya ya ja motar suka nufi Ofis.

Bayan sun fito suna takowa Abba yana riƙe da hannun Irfaan ɗin, wanda gaba ɗaya hankalinsa ba a kwance yake ba. Tun daga nesa ya fara shan kallo. Yadda yake tunanin zai ji ɓacin rai, sai Allah ya taimake shi bai ji ɗin ba. Abba kuwa bai ma san da wata matsala ba ya wuce Ofis ɗinsa.

Irfaan ya kama hanyar shiga nasa Ofis ɗin ya ji su Ramatu suna cewa,

“Idan kika ga yarinyar kamar aljana. Gaskiya na kwana da mamaki Wallahi. Shiyasa akace masu shegen iyayin nan da ƙaryar tsafta ƙarshen matan da suke aure abin ayi ta ihu ne.”

Irfaan ya yi ta danne zuciyarsa har ya samu ya wuce ba tare da ya nuna ya ji ɗin ba.

Yana daf da shiga Ofis ya ji Talatu ɗaya daga cikin yaran Ofis ɗin, tana zungurar ɗayar tana cewa,

“Zo mu je mu yi masa Allah ya sanya alkhairi mu ji ko zai amsa.”

Sai anan Irfaan ya ɗan waiwayo sai kuma ya saki malalacin murmushi. Shi kaɗai ya barwa kansa sanin abin da zai yi masu. Yanzu ne za su yi asalin gane kalarsa.

Da sauri ya buɗe Ofis ɗin ya shiga ya zauna tare da rintse idonsa. Allah-Allah yake su shigo ɗin, don haka ya miƙe kawai yana kai komo a tsakiyar Ofishin.

Har sun sa hannu za su buɗe mariƙin ƙofar Shamsu ya yi saurin dakatar da su,

“Ina zaku je? Kun fara hauka ne? Duk abubuwan da kuke cewa ina can ina kallonku. Kuma Irfaan duk ya ji maganganunku. Na hango irin murmushin da yake yi idan zai yi wata mugunta. Ina baku shawarar ku nisanci Irfaan don Wallahi zai iya baku kashi a wurin nan, ba sai na tuna maku halinsa ba.”

Duk sai jikinsu ya yi sanyi. Dole suka fasa shiga suka koma. Shamsu yana buɗe ƙofar ya ji anfinciko shi. Ya rintse ido yana cewa,

“Irfaan ni ne fa. Menene haka wai?”

Sai a lokacin ya sassauta riƙon da ya yi masa yana huci. Daga bisani yaja tsaki ya koma ya zauna yana jijjiga ƙafa.

“Gaskiya ka rage zuciyar nan. Haba mana. Yanzu da ka ji min ciwo fa? Bamu muka kashe zomon nan ba.”

Irfaan ya miƙe ya nuna masa hanya ya ce,

“Fita. Nace ka fita!!”

Da sauri Shamsu ya miƙe yana faɗin, “Allah ya baka haƙuri.”

Yana fita ya wuce wurin su Talatu yana gaya masu yadda Irfaan ya yi masa yana zaton su ne. Anan kuma sai kowa ya kiyaye masa. Masu gulmar ma suka daina.

Suna kallonsa ya fice daga Station ɗin gaba ɗaya. Kai tsaye ya wuce gidansa ya sami Ihsaan tana zaune kuka kawai take yi. Shi kuwa kukanta sake harzuƙashi yake yi. A ganinsa idan kukan ne ma shi ya fi dacewa ya yi ba ita ba.

“Ki ɗauko hijabinki daga cikin sabbin kayanki, ki fesa turare ki zo nan.”

Jikinta babu ƙwari ta miƙe ta yi yadda ya ce mata. Larai mai aiki ta ƙaraso ta ce,

“Yallabai dama ina so ingaya maka Ihsaan bata cin abinci sai kuka kawai. Ko cikin dare na tashi sai na ganta tana kuka, tana kiran sunan Yayanta Sulaiman.”

Shiru ya yi kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya furzar da wani huci mai zafi ya ce,

“To na gode. Umma zata zo anjima bana so ki gaya mata hakan. Ni zan ɗauki mataki.”

Ta amsa cike da girmamawa sannan ta koma ciki.

A gaban motar ta zauna tasa ƙafafunta abisa kujerar ta maƙale jikinta sosai. Yana satan kallonta bai ce komai ba har suka isa makarantar.

Yana kallon yadda kowa ke kallonta cike da mamaki. Wasu kuma gulmanta kawai suke yi. Bayan ya gama yi mata komai ne ya ɗauketa ya dawo da ita gidan.

Bai yi mata magana akan cin abinci ba, bai kuma ce ta ci ɗin ba,  ya wuce abinsa.

Ya fita babu jimawa Umma ta shigo. Tana ganin Umma ta rugo da gudunta ta rungumeta tare da sa kuka.

“Umma don Allah ku kaini wurin Yaya Sulaiman shi kaɗai yake sona.”

Umma ta shafi kanta cike da tausayawa,

“Kada ki damu kinji Ihsaan? Yayanki Irfaan ma yana sonki.”

Bata ce komai ba, hakan yaba Umma daman kiran Samira da aka ajiyeta a wani ɗakin daban. Ta yi wa Umma bayanin babu ci gaba akan Ihsaan. Umma ta ce,

“Babu komai. Kinyi ƙoƙari ma. Tunda ta yi kyan gani. Me ya sa ba a gyara mata kanta ba?”

Umma ta tambaya bayan ta zame ɗankwalin Ihsaan ta ga kan a cukurkuɗe.

“Eh naso insa mata mai amma ta ƙi yarda. Sai dai a wanke hakannan ayi mata kitson.”

Umma ta jinjina kai,

“Ko hakan akayi mata za ta ji daɗi ai akan. Sannan a koya mata yadda zata gyara haƙoran nan naga har yanzu sai ahankali.”

Anan ma Samira ta sake yiwa Umma bayani,

“Walh Hajiya na nuna mata komai har yadda zata wanke haƙoran. Ahaka ma ai sunyi kyau kenan. Da alama dai haƙoran ba za su fita ba, sun riga sun dafe.”

Umma ta yi shiru tana tausayawa ɗanta. Ta yi alƙawarin duk ranar da ya ce zai ƙara aure ba zata taɓa hana shi ba, domin wannan kam ba aure bane.

Dole ta sallami Samira. Bata kula da Ihsaan bata ci abincin ba, gashi kuma Irfaan ya hana Larai ta sanarwa Umma. Haka Umma ta koma gida.

Da Magrib Ihsaan da Larai suna falo, ita Ihsaan tana kwance a ƙasa yunwa ta riga ta ci jikinta.

Irfaan ya sakko daga mota a matuƙar gajiye. Sulaiman ma ya fito tare da karɓan kayan hannunsa. Tun safe ya roƙi Sulaiman akan ya zo. Bai sami isowa ba, sai wajen la’asar, shi ne ya jira Irfaan suka taho tare.

Shi kansa yana murnar yau zai ga Ihsaan ɗinsa. Gaba ɗaya kewarta ke hana shi barci.

Irfaan ya nuna masa hanya ya ce,

“Ka fara shiga.”

Babu musu ya shiga da Sallama. Idanunta kawai ta ɗaga ta dube shi. Bata da ƙarfin da za ta iya tashi, sai hawaye da ke zuba.

Sulaiman ya ƙaraso ya durƙusa a gabanta yana duban yadda ta sake zabgewa. Amma kuma akwai canji a jikinta tun daga kayan jikinta zuwa ƙmashin turare da take yi.

Irfaan ya ciro tissue daga aljihunsa ya miƙawa Sulaiman. Hakan yasa Sulaiman kallonsa, ya gyaɗa masa kai.

A hankali yasa hannu ya karɓa ya goge mata hawayen.

Sai a lokacin Irfaan ya nemi wurin zama ya zauna yana faɗin,

“Alhamdulillah.”

Idanunsa a rintse ya ce,

“Sulaiman wannan ƙanwar taka zan dinga zaneta ne. Abincin ma ta ƙi ci sai kiran sunanka take yi. Yanzu dai Larai ki kawo abinci nasan za ta ci tunda kana kusa.”

Larai ta nufi kitchen shi kuma Irfaan ya miƙe yana cewa,

“Bari inɗan watsa ruwa.”

Sulaiman ya zauna a ƙasan hakan yasa Ihsaan tashi zaune jikinta babu ƙarfi. Abinci ta ci sosai, sai ga bakinta ya buɗe. Sulaiman yana bata labaran ban dariya tana ta ƙyaƙyatawa.

A haka Irfaan ya fito ya same su. Gaba ɗaya sai suka bashi tausayi.

“Me zai sa Sulaiman ya rabu da matarsa?”

Sai yanzu zuciyarsa take son sanin dalili, sai yanzu ya gane dalilan da Sulaiman ya bashi akan sakin Ihsaan sun yi ƙanƙanta da yawa. Waɗannan dalilan basu isa su sa Sulaiman barin abin da yake so ba. Idan da gaske ne, kuɗi zai nema agunsa ya tafi wata duniyar ya ci soyayyarsa da tsinke.

“Sulaiman ka gaya min gaskiya me ya sa ka saki Ihsaan?”

Suka ji tambayar a tsakiyar kansu. Shi kansa baisan lokacin da ya yi masa tambayar ba, kasancewar ya hango tarin farin ciki a zuciyoyinsu, ya gane Ihsaan ba za ta taɓa zama inuwa ɗaya da kowa ba idan ba Sulaiman ba.

Ya hango tarin soyayya mai tsanani wanda raba su tamkar raba ɗaya daga doron duniya ne.

“Sulaiman ka gaya min gaskiya me ya sa ka saki Ihsaan? Ka faɗa min idan zan iya taimakonka na yi maka alƙawarin zan yi komai da iya ƙarfina.”

Sulaiman bai damu da tambayoyin da Irfaan yake yi masa ba, ko ba komai ya fara hango canjin da yake yiwa Ihsaan kwaɗayi.

“Zan gaya maka dalili a duk ranar da na dawo domin ka bani Ihsaan. Bana tunanin Ihsaan za ta wuce shekaru biyar a wurinka ban karɓi ajiyata ba.”

Ya sake jefa Irfaan a cikin ruɗani.

“Kiwonta ka bani kenan.”

Ya faɗa cikin raha. Shima murmushin ya yi ya ce,

“Abin da na baka kayi kenan Yaya Irfaan.”

Ihsaan tana jin su bata ce komai ba. Irfaan ya miƙe ya ce,

“Ta shi mu je mu yi Sallah. Anan gidan zaka kwana zuwa gobe sai ka koma tunda yamma ta yi.”

Sulaiman ya jinjina kai. Sun tashi da nufin fita Ihsaan ta miƙe za ta bi su.

Irfaan ya watsa mata wani irin kallo sa yasa ta ja ta tsaya tana zazzare idanu kamar za ta yi kuka. Sulaiman ya ɗan yi murmushi ya ce,

“Kyautatawata.. Yi haƙuri ki je ki yi Sallah kafin mu dawo inbaki wani labari.”

Nan da nan ta saki fuskar tana dariya. Gaba ɗaya Irfaan ya kasa sabawa da abubuwan Ihsaan da Sulaiman. Kullum sukan zame masa abin kallo da mamaki.

Ita kuwa murna take yi yau za ta kwana tare da Yaya Sulaiman. Ita kanta Larai ta yi mamakin yadda taga Ihsaan tana dariya. Abin da bata taɓa gani ba kenan.

“Ihsaan Yaya ya zo yau babu kuka ko?”

Ihsaan ta ce,

“Ina sonshi sosai.”

Larai ta yi dariya kawai ta shige banɗaki.

‘Yar mutan Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Duniyata 12Duniyata 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×