Skip to content
Part 8 of 25 in the Series Duniyata by Fatima Dan Borno

Duk da Irfaan baya son barin mahaifinsa, amma tafiyar nan tafi komai faranta ransa. Nan da nan ya hau shirye-shirye. Cikin abin da bai wuce sati biyu ba, jirginsu ya daga sai London.

Bayan tafiyar Irfaan ne ciwon da Abba yake ta dannewa ya taso masa gadan-gadan. Hankalin Umma a tashe a lokacin da Abba yake magana da kyar,

“Kiyi hakuri. Ina fama da ciwon koda. Likitana ya gaya min idan ba ayi min dashen koda ba komai yana iya faruwa. A dalilin hakanne na tura su Sadiq karatu a waje domin bana so hankulansu ya tashi har su yi tunanin za su iya sadaukar min da kodansu. Na gaya masa a bincika ko akwai wanda zai iya siyar min da nasa kodan, idan kuwa ba a samu ba, gara a barni har Allah ya yi ikonsa.  Ina so ki rike min wannan alkawarin na ba zaki taba gayawa ‘ya’yana halin da nake ciki ba. Don Allah”

Ya karashe maganarsa a wahalce.

Umma ta yi kuka har ta gode Allah. Tayaya zai yi haka? Me ya sa ba zai bari daya daga cikin ‘ya’yansa su taimaka masa ba?

“Don Allah yallabai ka bari Irfaan ya dawo ya bayar da nasa guda  daya don Allah.”

Murmushi ya yi ya ce, “Kin mance Irfaan ba cikakken lafiya gare shi ba? Shiyasa na nesanta shi da ni, idan ba haka ba zai yi kasada ne ya bayar da nasa, karshe shi kuma mu koma muna fama da shi. Don Allah ki barni ki yi min addua kawai.”

A gigice Umma ta wuce wurin likitansa ya tabbatar mata har yanzu ba asami koda ba. Ta bazama wurin ‘yan uwa da abokan arziki, akan ko akwai mai taimakawa. Amma aka rasa mutum guda da zai bashi. Umma ta dawo tana kuka tana cewa, “Babu wanda zai iya baka koda sai dolenka. Don Allah ka bari ko na Sadiq a cire.”

Abba ya ciji baki ya ce, “Yaran nan dukkansu ba lafiya ce ta ishesu ba. Ba zan iya ba, na fi son rayuwarsu fiye da tawa. Ban kuma ce ki sake zuwa wani wuri dan ki roki a bani koda ba.”

A ranar haka Umma ta wuni ko gyangyadi ta kasa yi. Wasa-wasa sai da Abba ya share wata guda cur a gadon asibiti yana jinya. Gaba daya angama fidda rai da shi. Duk ya lalace ya zama kamar ba Abba ba. Ita kanta Umma mai jinya ta zama abin tausayi. Kullum jikin Irfaan yana gaya masa babu lafiya a cikin gidansu, hakan yasa watarana ya kira video Call suka ki dauka, ya sake kira anan ma suka ki dauka. Don haka ya aikawa mahaifinsa da sakon murya, yana rokonsa idan gida babu lafiya ne su sanar masa zai yarda da kaddara mai kyau ko akasinsa.

Ganin babu amsa dabara ta fado masa ya kira likitan gidansu ya ce masa, “Ya labari ?” Kawai dabarar yin hakanne ya fado masa ba don yasan me ke faruwa ba. Anan Likitan ya kama ce masa,

“Ya kamata ku zo a nemo shawara domin har yanzu yallabai ya kasa samun wanda zai bashi koda, gashi yana shan wahala.”

Gaban Irfaan ya fadi da karfi, ya yi ta maza ya ce, “Zan dawo a cikin satin nan, a fara shirye-shirye ina dawowa za a cire nawa asa masa. Don Allah kada ka sanar da kowa wannan maganar da muka yi.”

Likitan ya amsa da insha Allahu. Nan da nan Irfaan ya fara shiri. Shi kansa baya fahimtar abin da yake yi. Sati guda shirin ya dauke shi, wanda yake jin kamar ya fasa ihu saboda bacin rai. Addu’a kawai yake yi kada mahaifinsa ya rasa rayuwarsa kafin isowarsa.

Yana isowa Nigeria kai tsaye ya dauke shatar mota sai asibitin. A guje ya karasa fitowa yana ware idanu. Mahaifinsa ya hango ana gungura shi akan gadon asibiti. Da gudu ya karaso ya rike keken. Umma tana biye da su ta yi kuka har ta gode Allah.

“Ina zaku kai shi?” Ya tsinci bakinsa da tambaya.

“Zamu kai shi ayi masa dashen koda ne. Ansami wani bawan Allah ya bashi kodansa.”

Mamaki sosai ya kama shi. Wanene wannan? Ba shi bane mai  mahimmanci a yanzu ba, aje ayiwa mahaifinsa aiki shi yafi mahimmanci.

Umma tana ganinsa ta karaso da sauri ta rungume shi tana kukan farin ciki.

“Ana shirye-shiryen shiga da mahahaifinka dakin tiyata sunanka yake fadi yana cewa yadda kayi masa biyayya Allah ya baka ‘ya’yan da suma za su yi maka. Naji dadin zuwanka Irfaan na ji dadi.”

Jikinsa ya karasa mutuwa ya rasa da kalman da zai yi amfani da ita wajen lallashin mahaifiyarsa. A wannan gabar shima yana bukatan mai lallashinsa ne don haka duk suka yi shiru.

Andauki lokaci mai tsawo sannan likitan ya fito yana gumi. Da sauri suka tunkare shi sai dai sun kasa cewa komai.

“Ku kwantar da hankalinku anyi aiki cikin nasara. Allah ya baiwa yallabai lafiya ya tashi kafadunsa. Irfaan ka biyoni Office.”

Dukkansu farin ciki ya bayyana a fuskokinsu. Anan ya bar Umma tana godewa Allah ya bi bayan likitan.

“Dokto waye yaba mahaifina koda? Zan sadaukar masa da rabin dukiyata, zan yi masa duk wani abu da yake so ko da kuwa abun yafi karfina.”

Dokton ya yi murmushi ya ce, “Nima bansan shi ba, ya ce kuma ya bayar ne saboda Allah. Ya rokeni kada ingayawa kowa ko shi waye. yanzu haka yana nan a asibitin nan amma bani da ikon nuna maka shi. Kai dai kawai ka gode Allah. Na tambaye shi nawa yake bukata ya ce baya son ko sisi ya yi hakanne saboda Allah da kuma kai kanka.”

Shiru Irfaan ya yi yana son dole sai ya san waye wannan. Zai bar abin aransa amma tabbas sai ya yi amfani da aikinsa wajen binciken wannan bawan Allan da ya taimaki mahaifinsa.

“Wato Irfaan da ace bawan Allan nan bai zo a lokacin  ba da ka rasa mahaifinka. Saboda lokacin da kazo tuni lokaci ya kure maka da har zamu kwantar da kai muyi abubuwan da ya kamata har a cire asanya masa. Mu kara gode Allah.”

Kalaman Dokto suka katse masa tunaninsa.

Kansa ya kara wani irin girma. Soyayyar wannan bawan Allah da baisan ko waye ba ta darsu a zuciyarsa. Yana son mahaifinsa fiye da komai, akansa zai iya yin komai. Zai iya sadaukar da komai nasa indai mahaifinsa zai rayu. Ya yarda ya zama talaka likis muddin zai rayu da iyayensa.

Daga nan suka ci gaba da tattaunawa da Dokto amma hankalinsa gaba daya yana kan wannan wanda ya taimaki mahaifinsa.

Sati biyu tsakani jikin Abba ya yi kyau sosai. Dukkansu iyalan da ka gansu zaka gane suna cikin farin ciki da annashuwa. Daga nan kuma Irfaan ya fara shirye-shiryen komawa.

*****

Kitso yake kwance mata suna hirarsu kamar basu da wata matsala. A lokacin ya hango wani shati a bayanta kamar na duka. Don haka ya yi saurin daga rigar.

“Ya Salam.” Ya furta tare da rintse idanunsa.

“Ihsaan gaya min gaskiya waye ya yi maki haka?”

Ta dan yi shiru daga bisani hawaye suka dinga gudu a fuskarta kamar dama jira take. Ko da yake daman azaba ya isheta tana jin zafi a wurin sosai, tsoron faruwan wata matsala ya hanata gaya masa.

“Dama da baka nan ne su Baba Marka da Innayo suka kamani suka yi min duka akan rabon gadon Baba. Wai dan Malam Liman ya ce kason gadon Baba mafi yawa nawa ne, shi ne suka dakeni wai idan suka sake ganin kafafuna a wurin rabon gado sai sun cire min su. Bari ka ga ciwukan da suka ji min.”

Jikin Sulaiman har yana kyarma ya mike da nufin ficewa. Ihsaan ta rike kafafunsa, ya waigo yana dubanta,

“Kayi hakuri watarana sai labari.”

Yana huci ya ce, “Idan baki sakeni ba zan rabu da ke infita sabgarki inkyaleki da su. Ki sakar min kafa.”

Furucinsa sun yi wa Ihsaan wani iri kasancewar bata taba ganin ya furta irin hakan agareta ba. Don haka tasa kuka. “Kina ganin wasa nake yi maki ko? To shikenan ki tafi na sakeki, saki uku!”

Da Ihsaan ta kula sosai da ta hango yadda jikinsa yake kyarma, da ta kula sosai da ta hango hawaye kwance a kwayar idanunsa, da ta kula sosai da ta fahimci kwanakin nan Sulaiman yana cikin matsananciyar damuwa. Sai dai bata yi hankalin da zata iya fahimtar wadannan abubuwan ba, haka zalika ta hanyar da ya biyo mata ba lallai ta fahimta ba.

Innayo ta hankada labulen ta fada dakin tana Salati. Ita kanta sakon da Sulaiman ya furta a yanzu ya yi matukar gigitata. Ya yi abin da ake kira babu zato babu tsammani. Har yanzu Ihsaan bata saki Sulaiman ba, sai ma kara kankame shi da ta yi tana jin kalman sakinta a tsakiyar kwakwalwarta. Ta sani sarai, tasan menene saki a aure domin kuwa a Islamiyya ana yi masu. Shi kansa auren ta fahimci menene shi. Ba zata mance ba, malaminsu ya gaya masu idan aka saki mace saki uku babu aure a tsakaninta da mijinta muddin ba wani auren ta yi ta fito ba. Don hakane ta yi baya zata fadi, ya yi saurin tarota yana jijjigata.

Sulaiman kuka kawai yake yi da iya karfinsa yana jijjigata tare da kiran sunanta yana gaya mata wasa yake yi. Innayo ta kawo ruwa aka shafa mata. Idanunta jajir take kallon Sulaiman,

“Yaya Sulaiman da gaske ka sakeni? Kai ka gaya min Allah ne gatana kaine gatana. Me na yi maka? Shi kenan babu aure a tsakaninmu? Waye zai iya aurena? Waye zai iya zama dani kamar yadda kayi? Ni mummuna ce Yaya, wari nake yi, kowa toshe hanci yake idan ina kusa da mutum, amma kai baka taba yin hakan ba. Kai kadai ka taba gaya min ina da kyau. Waye zai iya yi min kwatankwacin abin da kake yi min? Shi kenan na rasa komai na rasa kowa.”

Sulaiman yana kuka yana girgiza kai,

“A’a Ihsaan ban rabu da ke ba, wasa nake yi maki, ba zan iya rabuwa da ke ba har abada.”

Gaba daya sun gigice sai sumbatu suke.

Innayo ta ce, “A’a Sulaiman ba a wasa da saki. Ihsaan kam ta saku. Ka ganni nan? Babu ruwana Wallahi kaje kasan abin da zaka gayawa mahaifinka.”

Daga nan ta fice. Kafin wani lokaci har Innayo ta sanarwa jama’a lallai Sulaiman ya saki matarsa har saki uku cikin subutan baki. Daga Ihsaaan har Sulaiman a ranar a daki suka wuni sukuku. Dare yana yi Innayo ta kama jan Ihsaan a dole sai ta fito daga dakin. Ihsaan tana kuka tana fadin babu wanda zai rabata da Sulaiman dinta. Dole Sulaiman ya fita daga dakin ya zauna a kofar ya yi tagumi.

Cikin dare ta daidaici Innayo ta yi barci ta fito ta zurawa Sulaiman idanu da ke zaune ya yi tagumi. A hankali ta karaso kusa da shi ta zauna tare da zura kanta a kafadarsa. A tare suka saki ajiyar zuciya mai karfi. Babu wanda ya iya furta uffan har barci ya kwasheta.  Ya dauketa ya kai ciki tare da jawo mata zanin rufan da suke rufuwa da shi.

A kwana daya rak! Gaba daya sun rame sun lalace. Baba Sani ya zo babu shiri. Sakamakon kiransa da Innayo ta yi a wayar makocinsu.

Sosai ya girgiza da lamarjn nan, A ranar ya yi fada kamar zai doki Sulaiman. Ya ci gaba da yi masa fada akan yadda ya yi saurin furta saki wanda wannan ba dabi’a ce ta musulmin kwarai ba.

Ihsaan dai tana gefen Sulaiman babu um bare um-um. So take taga wanda ya isa ya rabata da Sulaiman dinta. Batasan menene farin ciki ba sai da ta hadu da shi. Bata san menene shakuwa ba sai da ta hadu da shi. Idanunta sun kode saboda azaban kuka.

Baba Sani ya ce Ihsaan ta ci-gaba da zama a dakinta zai koma bakin aikinsa idan anyi kwana biyu zai dawo.

Bayan tafiyan Baba Sani, Sulaiman ya faki idanun Innayo ya jawo hannun Ihsaan suka fice daga gidan. Can nesa da gidaje suka je suka zauna shiru. “Ihsaan kinsan me ya sa na kawo ki nan?”

Bai jira cewarta ba, ya dora da cewa, “Na yi magana da wani abokina zai aureki auren kisan wuta. Bai wuce kiyi sati daya a hannunsa ba, sai ya sakoki ni kuma indawo da ke dakinki.”

Ihsaan ta dube shi sosai sannan ta noke kafada, “A’a ni ba zan iya zama da kowa har na tsawon sati ba. Ni bazan yi nesa da kai ba, bazan yarda inzauna da kowa ba sai kai.”

Ta fasa kuka. Ya jawota ya kwantar da ita a jikinsa yana bubbuga bayanta. Shi kadai yasan me yake ji a zuciyarsa. Bai ankara ba ya fara jin jifa da duwatsu. Ba kowa bane ya jagoranci wannan cin mutuncin face Marka. Ihu take tana cewa kwarto ya saki mata yana binta a cikin jeji. Wannan lamari ya yi matukar tayar da hankalin Sulaiman lamarin da ya jawo masa sarkewa da tari mai karfi. Kokari yake ya kare Ihsaan amma hakan ya gagara sai ma kifewa da ya yi a wurin jini yana bin bakinsa.

Ihsaan ta fasa kara tana girgiza shi. Hakan yasa duk masu harbin suka yi ta kansu. A lokacin Innayo ta karaso da kururuwa tana fadin shikenan ankashe mata da. Tana karasowa ta fizgo Ihsaan ta yi cilli da ita, ta buga kanta da wani dutse. Tuni jini ya wanke mata fuska. Sai dai ba wannan ne a gabanta ba, damuwarta Sulaiman dinta da ke kwance babu ko numfashi.

Da kyar suka samu wasu mutane suka taimaketa suka dauke shi sai asibiti. Ihsaan ta samu ta bi bayansu ta boye a bayan asibitin jikinta babu inda baya kyarma. Saman goshinta kuwa ya kumbura ya yi suntum. Sai kusan yamma sosai ta sami daman shiga dakin da yake, bayan ta tabbatar Innayo ta bar asibitin.

Yana kwance ana yi masa Karin ruwa idanunsa a bude suke tarr.. A hankali take bin bango idanunta jazir, ga wani irin jiri da ke dibanta. Idanu ya daga yana binta da kallo. Ganin zata fadi yasa ya cizge Karin ruwan ya yi saurin nufota yana cewa,

“Ihsaan daina tafiyar hakannan.”

Har kan gadonsa ya kawota ya ajiye yana dubanta da lumsassun idanunsa. Kankame shi ta yi sosai tana shessheka, “Don Allah kada ka rabu dani, don Allah Yaya Sulaiman kada kayi nesa da ni, za su kasheni muddin baka akusa. Me na yi maka ka sakeni? Me ya sa ka sakeni bayan kana sane da zan iya mutuwa.”

Ta hada kalmomin a wahalce. Kura mata idanu ya yi bayan yasa hannu ya tallabo habarta. “Waye ya gaya maki zan iya tafiya inbarki? Ki daina kuka bari insa likita ya duba min ke. Kaddarar kowane dan adam tana tare da shi bai isa ya guje mata ba. Ina so ki sa aranki irin tamu kaddarar kenan.”

Daga haka ya mike ya dauko auduga ya toshe wurin Karin ruwan da ya fizge jini na zuba. Kai tsaye ya fice har zuwa wurin likitocin yana rike da hannun Ihsaan.

*****

Baba Sani ne durkushe agaban Abba. Wanda yake zaune a farfajiyan gidansa yana dan shan iska, kasancewar har yanzu bai koma bakin aikinsa ba. Irfaan yana zaune kusa da shi suna tattaunawa akan wani Case. Tunda ya sake dawowa bai koma ba, kasancewar kwanakin da ya diba zai yi basu cika ba.

“Rankashidade kaji yaron nan Sulaiman ya saki matarsa har saki uku.”

“What?”

Abba ya furta cike da firgici. Irfaan kuwa sarkewa ya yi sosai daga lemun da yakai bakinsa yana kwankwada.

“Kana nufin Sulaiman ya rabu da yarinyar nan? Akan me?”

Abba ya sake jefo masa tambayar cike da damuwa. Irfaan ya kafe Baba Sani da idanu yana son jin karin bayani. Lamarin ya gigita shi yasa tunaninsa tsayawa cak! Ya rasa me zai furta da ya wuce kafe su da idanu.

“Wallahi Rankashidade har yanzu banji wani dalili mai karfi ba. Ka dai san Sulaiman da zuciya. Mahaifiyarsa ce ta kama Ihsaan din suka yi ta duka kamar an aiko masu da jaka. Shi kuma Sulaiman zai je ya yi masifa ita kuma ta rike shi, shi kenan ya antaya mata saki.”

Abba ya yi shiru yana nazarin kalaman Baba Sani, daga bisani ya ce, “A’a Sani ku sake bincikawa sosai. Ba dalilin ba kenan. Akwai wani boyayyen lamari a tsakanin Sulaiman da Ihsaan. Yaran suna da abubuwan ban mamaki. Allah shi kyauta.”

Irfaan ya rasa irin tunanin da zai yi, don haka ya mike kawai ya bar wurin. Can cikin shuke-shuken gidansu ya nutse yana nazarin rayuwar Sulaiman da Ihsaan. A karo na farko ya ji yana so ya taimaka masu. Ya dade yana jin Sulaiman a zuciyarsa kamar kaninsa Sadiq. Zai so ya inganta rayuwarsu gaba daya. Sai dai mutuwar aurensu ya dame shi, zai so ya ga Sulaiman domin jin yadda lamarin ya kaya. Ya jima a cikin wurin ya saka wancan ya kulla wannan.

Da daddare yana jin Ummansa suna hirar sakin. Umma ta nuna tsananin damuwarta, ta kuma koka da cewa akwai yarinta a cikin lamarin. Abba ya musa mata akan babu yarinta, akwai dai wani lamarin ne, domin kuwa Sulaiman kananun shekarun kawai gareshi amma yasan abin da yake.

‘Yar mutan Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Duniyata 7Duniyata 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×