Skip to content
Part 3 of 25 in the Series Duniyata by Fatima Dan Borno

A natse ya miƙe yana faɗin yana zuwa. Tunda ya fita bai sake dawowa gidan ba, sai cikin dare. Abin mamaki da al’ajabi, kayan kallon falon a kunne suke, hakan yasa ya fara tunanin ko Zahra ce da Iffaan basu yi barci ba. Sai dai yana shiga ya yi turus, daga irin burin da ya ci akan yi masu faɗa akan abin da ya hanasu yi yau suka karya dokarsa.

Ihsan ce a zaune a ƙasa ta kafe tv da idanu babu ko ƙyaftawa. Kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci tana cikin damuwa. Har zai juya ta ji motsi, don haka ta waiwayo da sauri.

Duk yadda yake sauri ya ɓace daga falon gudun tsautsayi yasa ta yi masa magana, hakan bai yiwu ba. A guje ta taso tasha gabansa idanunta cike da hawaye,

“Don Allah ka taimakeni ka kaini wurin Yaya Sulaiman. Ya tafi ya barni ka kaini.”

Ta ƙasashe cikin zazzaƙar muryarta da Allah ya azurtata  da ita.

Ya rasa irin tunanin da ya kamata ya yi, tsakanin wucewa ya bata wuri da kuma tsayawa nema mata maradinta. Sosai ya ƙosa su rabu don haka ya ce,

“Nima bansan inda zan ganshi ba.”

Har ya juya ya fara taku, kamar ance masa ya waiwayo, ya ganta anan tsayen tana zubar da hawaye.

Cike da takaici da kuma tausayinta ya dawo yana dubanta. Ba zai jurewa kallon irin wannan baƙin ba don haka ya kauda kai yana jinjina irin baƙin yarinyar,

“Zo muje inkaiki wurinsa.”

Fara’a ya wanke fuskarta. Da sauri ta biyo bayan Irfaan, har zuwa ɗakin da Sulaiman yake.

A zaune suka same shi ya yi tagumi. Mamaki yasa Irfaan dubansa. Sai dai kafin ya yi masa magana har Ihsan ta ƙaraso ta kwantar da kai a jikinsa,

“Bazan iya barci babu kai ba. Kayi alƙawarin ba zaka taɓa yin nesa dani ba, shi ne tun yanzu ka iya tafiya ka barni.”

Ta ƙarashe cikin shagwaɓa. Baki buɗe yake kallonsu. Sulaiman ɗin kuwa harda ajiyar zuciya.

“Baki ga nima na kasa barcin ba?”

Bata yi magana ba sai sake kwantar da kanta da ta yi. Ya ɗagota ya ɗibi dambun naman da Umma ta aiko masa, ya ce,

“Buɗe bakin.”

Babu musu ta buɗe ya zuba mata. Tana ci tana murmushi,

“Wannan abu akwai daɗi. Don Allah Yaya Sulaiman mu yi zamanmu anan kada mu koma gurin Innayo kullum tana yi maka faɗa akaina ranka yana ɓaci.”

Ya dubi fuskarta yana girgiza kai,

“Kada kiyi min kuka tunda kinsan bana so.”

Nan da nan ta shanye kukan.

“Innayo tana sonki, rashin fahimta ce kawai. Kada ki damu kinji?”

Nan ma gyaɗa kan ta kuma yi.

Irfaan da ya gaji da ganin abun mamaki ya yi gyaran murya. Duk suka waiwayo suna dubansa. Gaba ɗaya sun mance yana tsaye. Sulaiman ya saki murmushin da yake tsayawa Irfaan arai ya ce,

“Yaya Barka da dare. Ihsan ta dameku ko? Insha Allah gobe zamu tafi.”

Duk jarumta irin ta Irfaan sai da yaji jikinsa ya mutu. Ya rasa dalilin da yasa ‘yan ƙauyen nan suka tsaya masa arai bayan shi bai kasance mai sanya abu arai ba.

“Kada ka damu Sulaiman. Nan gidanku ne ka zauna har sai lokacin da kaso komawa. Idan ma zaka zauna anan  gaba ɗaya duk ɗaya.”

Yana maganar yana tafiya. Sai dai amsar da Sulaiman ya bashi yasa shi waiwayowa yana dubansa,

“Yaya Irfaan ai ban isa inzauna anan ba. Ni bana so insaba da rayuwar jin daɗi domin nasan na ɗan lokaci ne. Kuma ko ba haka ba Innayo ba zata yarda ba. Gani take yi kamar Ihsan ta mallakeni ne sai yadda ta yi da ni.”

Mamaki ya ci gaba da bayyana ƙarara abisa fuskarsa. Wai yarinyar da yake yiwa kallon aljana ita ce waninsa ke sonta kamar ya mutu. Yarinyar da idan ya ganta yake jin azaban tashin hankali, wai ita ce wani yake samun natsuwa a dubanta. Yana son sanin tarihin irin wannan soyayyar. Sulaiman yana da kyau, irin wanda yafi ƙarfin Ihsan ɗin nesa ba kusa ba. Ko dai da gaske asiri iyayenta suka yi dan su samu ta shiga?

“Astagfirullah!”

Ya furta yana danasanin munanawa ‘yar uwarsa musulma zato.

Bakinsa ya yi nauyin da ba zai iya furta komai ba. Ciwon kai yake ji mai tsanani. Dole ya fice da wasu tunane-tunane.

Washegari tun asuba Abba da Irfaan suka fita, kasancewar suna da Meeting ɗin gaggawa.

A ranar ne kuma Sulaiman ya yi Sallama da mahaifinsa domin komawa ƙauyensu. Ihsan harda kukanta wai bataso ta tafi. Umma ta haɗa masu sha tara na arziƙi da kuɗi. Sulaiman da mahaifinsa suka yi godiya.

Suna tafe ahanya suna hirarsu. Mutane da yawa da suka ci karo da su, suka yi ta kallonsu da mamaki. Ita kuwa Ihsan ko a jikinta.

Sun zo tsallaka titi wani mai mashin ya kwashe Ihsan, domin kuwa ta raba hannunta da hannun Sulaiman a lokacin da suke ƙoƙarin tsallaka titi.

Sulaiman ya ƙara so a gigice yana ƙwalawa Ihsan kira. Mai mashin ɗin sai ya rufe su da masifa akan wai wani irin ganganci ne. Zuciya ta dinga cin Sulaiman bai san lokacin da ya bar kan Ihsan ba, ya damƙi wuyan mutumin nan.

Duk yadda akayi dan ya sake shi abin yaci tura. Cewa yake sai ya kashe shi kamar yadda ya kashe masa Ihsan.

Abba da Irfaan ne a bisa shimfiɗaɗɗen titin da zai kai mutum kai tsaye Kawo. Dukkansu a matuƙar gajiye suke. Irfaan ke tuƙi cike da natsuwa Abba kuma yana zaune a gefe hankalinsa yana kan wayarsa yaji alamun mota ta tsaya. Hakan yasa ya waiwayo yana duban Irfaan,

“Yadai? Me ya sa ka tsaya anan?”

Ya jero masa tambayoyi masu kama da juna a lokaci guda.

“Abba ka zauna anan naga cinkoson mutane ne, zan je induba ko lafiya.”

Abban ya girgiza kai,

“Ya za ayi ka tafi kai kaɗai? Muje mu gani.”

Sai da Irfaan ya zagaya ya buɗewa mahaifinsa mota sannan suka jero cikin kakin ‘yan sanda. Dole duk wanda ya gansu su burge shi. Akwai kamala da sanin makaman aiki a tattare da su. Kalaman da suka ji wani a wurin yana furtawa ne yasa suka ƙara ɗaga ƙafa,

“Jama’a kuyi taimako za ayi kisa.”

Da isarsu sai duk mamaki ya kama su. Irfaan ya yi sauri ya ƙarasa gaban Sulaiman yasa hannunsa ya riƙe na Sulaiman. Babu shiri Sulaiman ya juyo da sauri yana duban wanda ya riƙe hannun,

“Sakar masa wuyan riga.”

Irfaan ya furta cikin damuwa. Sulaiman ya waiwayo ya dubi Abba da yake kallon ikon Allah. Abban ma gyaɗa masa kai ya yi alamun ya yi abin da Irfaan ya ce masa. Jiki asanyaye ya sakar masa wuyan riga. Yana fara magana hawaye suka goce masa,

“Yaya ya kashe min Ihsan.”

Irfaan ya ware idanunsa. Ganin haka yasa mai mashin arcewa aguje… Sai dai bai kai ko ina ba Irfaan ya bishi da gudu yasa masa ƙafa. Sai gashi tim! A ƙasa. Ya ɗago shi yana dubansa,

“Da zaka gudu ina zaka je? Iyye!”

Ya daka masa tsawa. Sannan ya tasa ƙyeyarsa suka dawo. Abba suka samu a wurin Ihsan da take riƙe da ƙafarta tana wayyo wayyo.

Irfaan ya kai kallonsa ga Mutumin da ya bugeta ya ce,

“Tafi.”

Sulaiman ya ware idanu zai yi magana, ya girgiza masa kai. Dole ya haɗiye maganar da ke bakinsa. Ya rasa dalilin da yasa yake kallon Irfaan a wani babban matsayi a cikin zuciyarsa.

Abba ya kama hannunta tana dingishi suka nufi mota dukkansu.

Basu sami komawa gida ba sai bayan da suka kaita asibiti, aka dubata sannan suka samo shatar mota wacce zata kaisu har gida.

Ihsan ta dubi Irfaan cikin damuwa da sanyin murya ta ce,

“Mun gode Yaya Irfaan.”

Wani abu mai tsananin zafi ya daki zuciyarsa. Ko alama baya so ta yi masa magana. Ya jima yana jujjuya maganarta, ya kuma ƙi amsawa har suka barosu. Kamar ance ya juya yaga ta kafe shi da idanunta. Gabansa ya faɗi da ƙarfi. Dole ya janye nasa idanun domin babu alamun zata janye nata. Bayan sun fara tafiya a mota, ya juya ya ɗan dubi gefensa. Abin mamaki Ihsan ce tasa kanta a window ɗin motar ta kafe Irfaan da idanunta kamar mai nazarin ta yadda zata cinye shi muddin ta sami sa’ar kama kuruwarsa.

“Abba…”

Irfaan ya kira sunan mahaifinsa a wahale. Abban ya ɗago yana dubansa ba tare da ya amsa ba. Hakan yaba Irfaan ƙwarin guiwar ci gaba da magana,

“Abba, Wallahi Ihsan ɗinnan cinyeni zata yi. Aljanah ce ba mutum ba.”

Abba ya tuntsure da dariya har yana sheƙewa. Hakan yasa ran Irfaan ya ƙara baƙinkirin. Ya kirne sosai ya ci gaba da cewa,

“Abba da gaske nake yi maka Ihsan Aljana ce ba mutum ba. Ko ka taɓa ganin ‘ya mace mai muni irin nata? Gashi dai babu kwafato a ƙafafunta, amma hakan ba zai sa ingazgata cewa ba Aljana ba ce. Idan kuma baka yarda ba, ka dubi hagunka zaka amince da ni.”

Abba yana dariya ya dubi hagunsa. Ihsan ce ta yi zuru da idanu tana kallon motarsu Abba. Abba ya ɗaga mata hannu bayan ya tabbatar da ya zuge gilashin motar. Da sauri itama ta zaro nata hannun daga cikin na Sulaiman ta dinga ɗaga masa hannu, tana dariya da jajayen haƙoranta da suka dafe Saboda datti.

Irfaan ya ci gaba da tuƙinsa kawai yana jin tarin damuwa, har hanya ta raba su da motar su Ihsan.

*****

Cikin zazzafan hawaye ta ɗago tana duban Innayo,

“Kiyi haƙuri Innayo ba zan iya yin aikin nan ba, ƙafafuna zafi suke yi min.”

Innayo ya fizgota tana janta kamar Akuya har sai da ta sadata da wurin wanke-wanken sannan ta dankwafar da ita. Tsananin azaba yasa Ihsan sakin ƙara,

“Idan baki yi wanke-wanken nan ba sai na ƙarasa ƙafafun nan. Ai ni mai mashin ɗin nan bai burgeni ba, da bai kashe min ke kowa ya huta ba.”

Sulaiman dake tsaye a bakin ƙofa ya kafe mahaifiyarsa da idanunsa da suka kaɗa suka yi jaa saboda ɓacin rai,

“Idan mai mashin ya kashe Ihsan shi ne gawa na biyu, ni kuma na uku. Kinga kenan kema zaki yi kuka kamar yadda iyayen Ihsan za su yi, harma sai kin fi su tunda zaki rasa ɗanki.”

Innayo ta saki baki tana kallonsa. Sai da ya koma ɗaki ya sako ƙananan kaya, sannan ya ƙara so wurin wanke-wanken ya kama Ihsan ya dawo da ita gefe ya zaunar a kujera.

“Kiyi haƙuri kin ji? Watarana sai labari. Sai Innayo ta ci arziƙinki, sai kin zama wata mace ta alfarma. Waɗanda suka tsaneki za su koma masoyanki, za kuma su yi danasani. Zauna anan zanyi wanke-wanken.”

Sulaiman ya haɗa kan kayan wanke-wanken ya wankesu tas! Sannan ya ɗora ruwan kunun karyawa. Jiki babu ƙwari Innayo ta koma ciki, tana tunanin bokan da ya kamata ta kaiwa aikin Ihsan.

Bayan ya kammala ya kamo Ihsan ya kaita banɗaki ya gasa mata ƙafafunta yana yi yana lallaɓata. Ɗaki ya maidata yasa kwaɗo ya rufeta ta waje ya yi wucewarsa.

Yana fita Innayo ta yi wuf ta tashi ta kama hanyar ɗakin Ihsan. Ganin kwaɗo yasa ta yi turus tana tunanin ko sun fice ne. Hakan yasa ta zama ƙaramar mahaukaciya tana ta surutai ita kaɗai.

Sadiya ƙawarta ce ta yi sallama hakan yasa Innayo sakin ajiyar zuciya sanin cewar Sadiya ta fita tsanar Ihsan.

“Gara da kika zo.”

Ta tarbi Sadiya da guntun kalamanta masu nuni da cewa tana da buƙatar ganinta. Hakan yasa duk suka zauna a ƙofar ɗakin Ihsan. Jin mugayen kalamansu da kuma yadda suka tsara za su sami kishiyar mahaifiyar Ihsan ayi komai da ita ya ƙara tada hankalinta. Da ƙyar ta ɗingisa ta taka kujera tasa kanta a windo tana kallonsu.

“Haukata shegiyar ya kamata ayi.”

Cewar Sadiya. Innayo ta antayo ashar ta ci gaba da cewa,

“A haukatata ɗana ya yi ta wahalar nemo magani ko? Kasheta ya kamata mu yi. Wallahi gani nake yi Marka bata iya izaya ba, tunda har ta barta a raye. Ni kasheta zanyi.”

Sadiya ta riƙe haɓa tana duban Innayo, ta ce,

“Haba! Ai abin da Marka ta aikatawa Ihsan gara ace kasheta ɗin ta yi. Kinga ko banza zata huta domin Aljannah zata tafi. Don haka kada ki sake haɗa muguntarki da ta Marka ta wuce yadda kike zato.”

Muryar Ihsan suka ji tana magana,

“Yanzu don Allah me na yi maku kuke son kasheni? Innayo don Allah kada ki kasheni, ki bari ina so inga ranar da Yaya Sulaiman yake yawan gaya min zata zo, ranar da duniya zata yi alfahari dani kamar yadda yake cewa. Ranar da zaku zama masoyana. Ni nasan babu wannan ranar. Amma don Allah kada ku kasheni don Allah.”

Innayo ta waiwayo a firgice tana duban baƙin fuskar Ihsan. Batasan lokacin da ta rarumo bokiti ba, ta bugi windon da ƙarfinta saboda tsananin takaici. Tuni Ihsan ta yi ƙasa da kanta tana jin gabanta yana faɗuwa.

Lallai ba zata yarda Innayo ta illatata kamar yadda Baba Marka ta yi mata ba. Tana so taga ranar da Sulaiman yake gaya mata zata zo.

Muryar Sulaiman ta ji hakan yasa ta sake zuro kanta tana kallon komai,

“Innayo…”

Yaja sunanta cikin tsananin takaici,

“Wallahi Innayo kika korar min Ihsan sai na shiga duniya. Wallahi Wallahi Innayo kika kashe Ihsan sai na kashe ‘ya’yanki dukka sannan inkashe kaina. Kinga kin rasa mu kenan. A zatona godiya zaki yi wa Ihsan da ta taimaka ɗanki ya dawo hanya? Ina son Ihsan irin son da bana jin boka ko malam zai iya cire min. Ki yarda Allah ne ya haɗa ni da ita.”

Daga haka ya wuce kawai ya buɗe ƙofar ya shiga. Ihsan tana ganin ya shigo ta maƙalƙale shi jikinta yana rawa,

“Kada su yi min irin abin da Baba Marka ta yi min. Wayyo yanzu ya zanyi?”

Ya yi murmushi wanda bai kai zuci ba ya ce,

“Kada ki damu duk idan zan fita tare zamu dinga fita. Kiyi min alƙawarin dagewa kiyi karatu. Zan sadaukar da komai nawa dan ganin na faranta maki.”

Ta gyaɗa kai kawai ba tare da ta iya furta komai ba.

Muje zuwa.

‘Yar mutan Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Duniyata 2Duniyata 4 >>

1 thought on “Duniyata 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×