Skip to content

Fadime 1 | Babi Na Daya

2.4
(5)

FAƊIME

Kan uban nan!

Uwale! Uwale!! Uwale!!!

Fito ki gani, fito maza ki ga abinda Faɗime ke yi.

Mtss! Uwalen daga ɗaki ta ja tsaki bayan ta ƙara miƙa kan gadon da ta haɗa shi da tarin  tsummokara.

‘Allah ya yi dare gari ya waye, yanzu za a fara kiran mutum kamar wanda ya gille kan sarkin Mayu.’

Ta faɗa a zuci, sai kuma ta ɗaga muryarta.

“Wai me ya faru ne Hansa’u? Ba fa zan fito daga ɗakin nan ba idan ba kokon nan kika gama damawa…”

“Uwale wallahi fito ki gani Fadime ce ta yi kashi take lakace shi tana haɗiɗiya kamar sakin Ɗan waken Kulu…”

Ai kan ta rufe bakinta ta wuntsulo bisa gadon, zani yana kwancewa tana sake maidawa haka tayi waje tana kudunduma ashariya.

Kai tsaye bakin murhu ta nufa ta sunkuci ruwan da za’a yi mata damun Kokon ta sheƙa ma hargitsattsiyar matsakaiciyar budurwar dake yashe a ƙasa tana damalmala ƙazantarta  haɗe da tanɗe hannun.

Yarinyar ta fasa ihu bayan saukar ruwan a jikinta, kafin kuma ta yi tsit sakamakon marin da aka bi ta da shi.

“Kwashe shi ki zubar masai shegiya mai siffar jakai, kwashe shi na ce dan kan lalataccen ubanki kanki aka fara hauka? Ki kwashe na ce tun kafin na sunkuta ki cikin rijiyar can na rantse da Allah!”

Yarinyar ta zuba mata ido tana sauke ajiyar zuciya kafin kuma ta kwashe mata da dariya, tana kai hannunta dake cike da kashi kusa da bakin Uwalen.

Baya ta ja da sauri tana waige- waige kamar mai neman madoki, sai kuma ta ji tsit yarinyar tabar dariya.

Duƙawa ta yi ta fara tattara ƙazantar, ta haɗa cikin hannunta ta miƙe tana yiwa Uwale murmushi kamar ba ta da wata matsala. Uwalen ma shiru ta yi tana kallonta ganin ta doshi banɗaki tamkar wata mai cikakken hankali. Sai dai kafin ta juya ta yiwa Hansai magana, yarinyar ta daka wata sufa ba ta zame ko’ina ba sai gaban Hansai dake juya kokonta da ta gama damawa. Ca6al, Haka ta watsa kome da ke hannunta bisa damammen zazzafan kokon, ji kake facal! Sai a fuskar Hansai.

Hansai ta zabura jin saukar zazzafan kokon bisa fuskarta, kafin kuma ta rarumi buta ta fara ɗauraye fuskar tana yi tana fidda kwallar azaba.

Baƙin takaici da ya lulluɓe Uwale shi ya hanata kataɓus ta tsaya tsai tana kallon Faɗime ta rasa wane irin hukunci za ta mata. Wannan Kokon burin da ta sha kansa yawa gare shi. Babban takaicinta da Geron da aka dama Kokon ma aronsa tayi a shago. Ita bata sha ba, ita da biyan bashi ke nan? Tuna hakan da ta yi ya sa ta rarumar Faɗime da bugu tare da luƙa-luƙan ashariya. Faɗime na ta kyakyata musu dariya abinta.  Ganin hakan Hansai ma ta taho suka haɗu suna ta jibgarta.  Sai dai fa kamar ƙara mata sautin dariyar suka yi, sai ma sune hannuwansu suka fara zafi. Abin da ya fusata Uwale ke nan ta danƙeta ta watsata ɗakin kajinta haɗe da garƙame kofar tana faɗin. “Wallahi ko Ubanki bai isa ya fidda ke ba idan  ba kuɗin Gerona ya ba ni ba.”

Hansai ta sauke numfashi tana duban Uwar ta ta, kafin kuma takai kallonta kan kokon da ya canja launi. “Uwale yunwa nake ji fa, ai duk ke kika ja mana. Na faɗa miki tunda kin samu cikar burin naki ta haukace ki fidda ta daga garin nan kinƙi. Wallahi watarana kina ji kina ganin abincin da zamu ci zai gagare mu…”

“Yi mini shiru da Allah can sokuwa kawai. Ke kinsan sakamakon da zan samu  duk ranar da na wayi gari bata kwaryar ƙauyen nan? To bari ki ji, ke din da na ci burirrika kanki sai kin zama tsohuwar guzuma mai shekaru Hansin kafin ki auru, a hakan ma kar kiyi zaton abin arziki za ki aura. Kuturu shi ne mijinki, kuturun ma mabaraci me yawo da yagaggen wando. Dan haka idan har kika ga Faɗime ta bar ƙauyen nan to ba na numfashi ne a doron duniyar nan.”

Hansai ta zumɓuri baki cikin ƙunƙune take faɗin. “To Uwale kinsan hakane ki kyale ta da lafiyarta mana, ina dalilin baɗi ba rai? Wannan abin fa da kika aikata daidai yake ace ki danƙi ruwa cikin tafin hannunki ki yi mintuna biyu da shi kacal ba tare da ya tsiyaye ba! Abu ne kinsan da ba zai taɓa yiwuwa ba dawwamarta anan ɗin me ya sa za ki yarda ki yi duk tarin waɗannan sharuɗan ? Haka ni fa ba zan iya zama gida ɗaya da mahaukaciya ba Allah ma ya sani.  Kina gani rannan Takalmin sallata ta ɗauka ta yanka mini kamar ta samu nama. Idan ma ba mugun abu irin naki ba tunda kin samu nasara kan…”

Doke mata baki tayi da hanzari tana kaɗa mata manyan jajayen idanuwanta masu kama da jan goro tsakiyar kindirmo.

“Akul Hansai! Akul na ji zuciyata ta kwasheki kin furta wannan rufaffen sirrin. Zan ɓata miki rayuwa bar ganin ni na tsuganna na haifeki. Akan jinin Bashari zan iya ɓata rayuwar kowa idan na ce kowa ina nufin ko waye!”

Ta sauke zazzafan numfashi kafin ta ci gaba.

“Watsar da kokon bayan gida, ki tafi gidan Maimuna kice mata ta sam mini koko idan ta dama.”

Hansai ta zumɓuri baki kafin ta tafi aiwatar da abinda ta ce mata.

Ita kuma ta zauna tana tunano shuɗaɗɗun abubuwan da suka shuɗe.

A haka Maigidan ya zo ya tardata “Lafiya naga kinyi shiru kina numfarfarshi?” Kafin ba shi amsa ya ɗora.

“Ina Faɗime ne ? Ban ji ƙusur-ƙusur ɗin ta ba.”

Kukan da aka fasa daga ɗakin kaji ya sa shi kallon Uwale dake doka masa harara a tsorace.

“Ba dai itace a wancan mummunan ɗakin ba ? Haba Uwale me ya sa hakane?”

Sai kuma ya juya da hanzari ya doshi ɗakin. Ƙakkarfan rikon da yaji an yi masa ta ƙeya ne yas a shi waigowa da hanzari yana tunanin wasu ƙartine suka hauro masa gida.

Sai dai ga mamakinsa Uwale ya gani ta cukune fuska tana tururi bakinta na fidda kumfa, abinda bata taɓa yi masa yau takai hannunta jikinsa.

“Ba ni Ɗari Da Hamsin(150) kafin ka fiddo ta.”

Ta furta tana miƙa masa hannu. Ya bi hannun da kallo  a tsorace cike da ɗumbin mamaki. Sai kuma ya shanye mamakin ya ce. “Sakar mini wuyan na samu sararin numfashi sai muyi maganar. “

“Bazan saki ba fa Malam sai  ka ba ni. nasan shegen wayonka yanzu sai  ka kalallame mutum da ban hakuri, hakan kuma bazai hana anjima waccar tunkiyar ‘yar taka ta sake ɓata mini rai ba. Wallahi ka ji dai na rantse, ko ka bani ko na mata dukan da za kai kuɗin asibiti a gabanka. Zan iya ɗaukar asarar kome amman ban da ta cikina ka fi kowa sanin hakan. Koko na ta kwa6’bawa kashi fa Malam!”

“Kashi fa kikace Uwale…? Ya faɗi da sigar mamaki. “To yanzu ki mata uzuri mana kinsan halin da take ciki. Duk mai cikakken hankali ai ba zai aikata haka ba, kuma… “

Kallon da ta watsa masa mai cike da ma’anoni ya sa shi yin shiru ba shiri. Sai kuma ya ɗaura cikin sanyin murya.

“Allah Uwale ban da Naira Ashirin  ba abinda nake magani duk cikar kauyen nan, ke kinfi kowa sanin haka. Ki fito da ita ta ci abinci na miki alƙawari kafin rana ta faɗi  ko bara ne zanyi na kawo miki (150) ɗaya, dan ALLAH.”

Ta cika shi jikinta a ɗan sanyaye.

“Ban yafe ba ka yi bara Malam. Salon ka ɓata mini suna gurinsu Maimuna, kamar ni a dinga zunɗen mijina ma sai ya yi bara yake ciyarmu, to ba da ni ba wannan ƙarantar. Na ji zan buɗe ta amman ka ji na rantse sai dosuwar azahar. sannan anyi na farko anyi na ƙarshe. Duk ranar da Faɗime ta sake saka ni asara ko za ka sai da kayan jikin ka sai ka biya ni.”

Ta furta tana watsa masa hannu alamun gargaɗi. Ya lanƙwashe kai yana kallonta, sai kuma ya zauna ɗin kamar yadda ta ce. Sai yanzu ya ke ƙissima ƙarfi irin na Uwale sa’ilin da ya ji inda ta danƙar masa na masa zafi.

A daidai nan Hansai ta shigo jikinta caɓa-caɓa da kwata da jirwayen koko. Idanuwan Uwale da Malam basu sauka ko’ina ba sai kan fasasshen robar dake hannunta.

“Ba dai Kokon kika ɓarar a kwata ba ?” Suka haɗa baki gurin tambayar.

“Idan ma ɓararwa na yi ai da sauki Baba! kwatar gabaɗaya na faɗa a gaban mazan unguwa. ” Ta basu tana mai rushewa da kuka kuka.

Daga ɗakin Kaji suka ji an kwashe da dariya yi ake ba kakkautawa.

“Ai idan har baku buɗe ni ba, kuma ba za ku ci abinci ba.”

Zazzakar sassanyar muryar mahaukaciyar ta furta daga ɗakin.

Uwale ta mike a fusace tayi ɗakin tana ɗura mata ashariya.

“Dan kan…”

Abinda ta ci karo da shi ne ya saka ta cin burki tana haɗiɗiyar yawu ba ƙaƙƙautawa…

Ku danna tauraron da ke kasan rubutun nan dan nuna godiyarku gare ni.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×