Skip to content

Fadime 1 | Babi Na Hudu

1
(1)

<< Previous

A hankali take buga ƙofar tana yi tana waiwaye. sai da tayi bugu kusan biyar tukunna aka buɗe a fusace. 

“Ke billahillazi kika ƙara buga mini ƙofa, idan na fara tamaula dake sai mun dangana da Rafin garin nan na jefaki cikinsa, kinji ma na rantse. Za ki ɓace mini ko kuwa ? 

Kakkauran Mutumin ya furta ma hargitsattsiyar yarinyar dake tsaye gabansa.

“Ni fa bazan tafi ba sai ka ba ni kuɗi.” 

“Da ke ubanki ya ba ni ajiya ko?”

Ya furta yana harararta. 

Gadan-gadan tayi kansa za ta shige cikin gidan ta gefansa yayi saurin tare ƙofar da hannuwansa yana mamakin ƙarfin hali irin nata.

“Ka bar ni na shiga ina yin kashi zan tafi, Allah.”  Ta furta tana nuna masa sama. 

Dafe kansa ya yi, a hankali ya furta.

“Na shiga uku ni Manu” 

“Ko kusa da biyu baka kai ba Manu. Gwarama ka bi zancena kabarta ta kwana nan. Idan yaso gobe da sassafe sai ka kaita tasha kasa ta duk motar daka fara tararwa. Wallahi in ba haka ba kajamana bau ke nan, kai ba da haihuwarta ba, kai da ciyarwa, dan babu alamar ko dukan mutuwa za ka mata za ta iya barinka.”

Siririyar matar mai zubin taɓarya ta faɗi daga bayansa. 

“Amman dai tun ɗazu na faɗa miki ba ni da ko sisin da zamu sha Koko gobe ko ?” 

“Kasan da hakan tun fari me ya kai ka kula ta? Harda sammata ruwa wai kai kaga kyakkyawar budurwa ko?” 

“Bansan tana da taɓin hankali ba ai.” 

“Yanzu ai gashi ka sani, kana kuma girbar sanin.” 

“Dadinta dai bance miki ina nadama  ba.” 

“Oh shi ya sa fa naga ka babbake ƙofa kana ƙoƙarin gwada kwanji da ita.” 

“Manu kashi fa nake ji.” 

“Sakarshi anan!” Ya furta a fusace yana mai ba ta hanya ta wuce. 

*****

“To Alaƙaƙai sai ki yi ki gama mu tafi tun kan mu rasa motar safen.

” Ina ma kika ce za ki ?” 

” Kaduna, kawo, gidansu Malam mai Salati.” 

“Bance ki mini kwatance ba ni, ni ko na zuwa bakin kasuwar ƙauyen nan ba ni da balle na gari guda. Kin ma san yadda za ki yi, abu ɗaya na sani wanda kinji na rantse ko zaki mutu baki sake kwana gidan nan, kai Allah wadaran taimako ma irin naki.” 

“Wai Manu lafiya kake taɗi da mahaukaci ? Ita ina tasan ba ka da ko sisin? Barta ta ci tuwanta, inda ragowa ma a ƙulla mata a leda ta yi guzuri, na samo mafita ni kam.”  

“wace irin mafita.” 

Ya furta da sauri yana mai ƙarasawa gurinta.” 

“Yo bani kunnanka mana, haka zan Faɗima ka mini ganɗanɗan gabana.”

A hankali ta raɗa masa, aiko ya kwashe da dariya.

“Shi ya sa fa nake miki son da ba nawa kowa nan duniyar.”

Cike da jin daɗi ta ce, har Iya, Manu ?”  “Ban ce ba.” 

Ya yi saurin tare ta yana watsa hannuwa.

A Cikin Tasha

“Wai motar sai yaushe za ta zo ?” “Yauwa ga wata mota can jeki tambayeta.” Ya furta yana nuna mata motar da baki.

“To ni ƙishi nake ji Manu.”

“To na ɗaure ki ne ? Ga famfo can jeki tara kai kisha.” 

“Sai dai ka ɗebo mini a leda.”

kallonta ya yi yana mamakin yadda take ba shi umarni haka tamkar uwarsa, sai kuma ya saki murmushi.

“To ranki shi daɗe.”

Da hanzari ya bar gurin yana mai godewa Allah cikin zuciyarsa, tsayawa ya yi jikin famfon yana kallon Faɗime. Can dai da Allah ya sa hankalinta ya yi wani gun, sai ya yi wuf yasha kwana shi ma. Da gudu-gudu ya fice daga tashar. Sai da ya tsallaka titi ya sauke ajiyar zuciya yana mai fatan kar Allah ya ƙara haɗa shi da ita. 

Ta daɗe tana zazzaga tashar har sai da gajiya ta saukar mata tukun ta dawo jikin famfon ta kafa kai tasha ta ƙoshi. Ka na ta miƙe tana bin motocin da ido har zuwa sanda ta isa gaban wata A Kori Kura dake cike da Rake. Mutane na ta sabgoginsu dan haka ba wanda kula da sanda ta ɗane Motar. Can ƙarshen motar taje ta kame nan fa ta hau facaka da duk wanda hakorinta ya iya ɓantara. Jin tashin motar bai sa ta motsa ba, sai ma kwanciya da tayi a hankali barci ya silaleta. 

 Azahar ta nausa, sa’ilin da hasken zazzafar ranar ya cika doron duniya. Wannan shi ya hana Faɗime sukuni ta kama kuka tana matse ƙafafuwanta jikinta, alamun zafin ƙarfen yana mugun taɓata. Ba ƙaramar galabaita ta yi ba kafin motar ta kai inda za ta tsaya. Ba ɓata lokaci Faɗime ta rarrafo ta dire daga motar. 

A hankali ta ƙarasa gindin bishiyar da ta hanga nesa kaɗan da ita. Zama ta yi ƙasanta tana ta sauke numfashin wahala. Kallo ɗaya za ka mata kasan  ƙishi ke damunta, dan ko laɓɓanta sunyi fari fat, sai hadiyar yawun da ke neman ƙafewa take yi. 

Kamar ance juya damarki, ta hange shi nesa da ita kaɗan ya ɗaga babbar robar (SWAN) Yana kwankwaɗa cikin kwanciyar hankali. Shi dai kam bai san sanda ta iso ba, sai ji ayi an warce robar  da ƙarfi har ana buge masa baki. Dafe bakin yayi yana runtse ido sakamakon zafin da ya ratsa shi.

“Me haka kuma Yaya, kafa ji mini ciwon walla…” 

Wacce ya haɗa ido da ita ne ya saka shi daka tsalle gefe gudu zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri. 

A duniya inda abinda ya ƙi jini to MAHAUKACI ne, harga Allah ba ƙaramar tsorata ya yi ba. Dan haka ya juya da sauri zai bar gurin, sai dai kan ya kai da ɗaga ƙafa ya ci karo da Yayansa. 

“Ina kuma za ka salon ka ɓace mini sarkin gajen hakuri ?”  Shiru ya yi yana mai nunawa Yayan bayansa ba tare da ya juya ba. 

“Me kake nuna mini Sagir, banga komai ba, ji fa yadda kake ta gumi, me ya faru?” 

Ya furta yana mai shafa fuskarsa”. 

Da hanzari Sagir ɗin ya juya jin ance masa ba a ga abinda ya gani ba. Sai dai ga mamakinsa ba ta gurin, ba ta kuma ilahirin gurin duka. 

Riko hannun Yayan ya yi da hanzari yana ja. “Ka zo mu wuce. Yanzu wata mahaukaciya ta fisgen ruwa ina cikin sha, ba ƙaramar tsorata na yi ba, yanzun nan fa bai kai ace ta tafi ba.”

Ya furta cike da shakku yana sharce gumin fuskarsa.

Yayan ya dafa shi yana ɗan murmushi.

“Lalle kam sai dai mahaukacin, dan shi kadai zai taɓa ka na ga tsoro cikin idanuwanka. (Don’t worry my beloved Bro) Mu ƙarasa mu ci abincin sai mu tafi, ko ba kai kace kana jin yunwa yanzun nan ba ?” 

“A’a ai kuma na ƙoshi indai cikin nan zamu ci. Mu tafi kawai, na ci ana gaba inda su Alhaji ke yawan tsawan nan. “

” Murmushi ya yi gami da ɗaga kafaɗa “As ur wish”. 

 “Ka dai rufe boot din da kyau sanda ka mai da sallayar ko, na san halinka da yawan barin boot a buɗe?”

Ya furta sanda suka iso jikin motarsu.

Jin shiru ya saka shi yin murmushi.

‘Ashe fa yau sagir ba magana ya ga Dodansa’ Ya furta a zuciyarsa yana mai buɗe ƙofar motar. 

 Tafiya kaɗan suka yi suka isa ɗan madaidaicin Gidan Abincin (Restaurant). Kai tsaye suka shige cikinsa gami da jan kujeru su zauna. Aljihunsa ya shafa sai kuma ya miƙe da hanzari yana faɗin; “Zaɓar mana abinda zamu ci bara na ɗauko phone ɗina.” 

Kaɗa masa kai kawai ya yi cikin ƙosawa ganin waiter din bai iso ba ga yunwa na nuƙurƙusarsa, dan haka ya fara kwala masa kira. “Waiterr” Kafin ya gama sauke numfashinsa Faɗime ta bayyana gabansa tana mai washe masa baki. 

“YES SIR” 

Ta furta cikin zazzakar muryarta tana mai ɗora hannu bisa kugunta. 

*****

Duk wata kwalla dake bisa kwabar ɗakin sai da ta sauke ta bincikata, babu. Haka duk wani tufafi na Malam sai da ta zazzage nan ma babu. Kanta fa ya ɗau zafi, zafin da bata fatan zarginta ya zama na gaske. 

“To ki duba kayan Faɗime mana ko zaki dace, kai abin da mamaki gasu ba wani girma gare su ba balle ace za su fito da wuri.”

Cewar Salame cikin jimami. 

“Babu fa! Na ce miki tun safiyar yau da aka tabbatar mini ta fice daga gidan nake nemansu bangansu ba.” 

“Anya Uwale baki ganin Malamin nan ya yaudaremu ? Idan ba haka ba me ya ce game da yarinyar nan…” 

Shiru ta yi tana tunani; 

“Idan har na turara mata maganin zai kafeta kafewar da sai na umarce ta za ta iya fita ko da nan da wajen gidan nan ne!” 

Haka ya ce, na tuna Salame, amman ba na jin Iliya zai yaudare ni. Almajirin Mai Salatine fa, ba kuma irin sirri na da bai sani ba. Inda da karya a lamirin da haukan bai sameta ba ai. Tunda dai maganin ɗaya ne. Ni yanzu babbar damuwata da banga Wurin nan ba. Shi kaɗai ya isa ya dawo da yarinyar nan duk inda ta shiga.”

“Ni fa akwai wacce na ke zargi kan wannan lamarin…” 

“kamar ya?” Tayi saurin tare ta.

“Indo mana, ba itace wacce kuka kafa dashin mako-mako kika cinye mata kuɗin ba ?…”

Ba ta jira amsarta ba ta d’ora; “To ki tabbatar za ta iya kome dan ta ɓata miki rai, musamman da wannan shegen bakin naki ba ya iya ɓoye ƙiyayyar da kike ma yarinyar nan. ” 

“Aiko idan har ya zamana ita ce silar  ta da mini da hankali haka, wallahi kinji na rantse yadda Hansai ba za ta auru ba sai bayan wasu ƙididdigaggun lokuta haka itama zan tsinke alaƙar da ke tsakaninta da Malam Musan!”

“Hmm! Zai fi miki idan kika bar batun nan muka tunkari abinda ke gabanmu. Kuskure ne an riga da anyi, sai dai mu tafi inda za a duba mana makomarsa tunda ke baki ga naki layun ba.”

Cikin ƙunar rai ta jawo gyalenta ba ta damu da canja tuttturnan zanin da ya kwashi mako guda jikinta ba suka fice.

Shiru ya yi yana kallonsu bayan da suka gama kora masa jawabin. A hankali kuma sai ya sadda kai yana bin jibgegen carbinsa mai ‘ya’ya dubu da kallo. Ya jashi sosai, jan da in ka kafa ido kana lissafi zai ta sarma dari biyar, kana ya dago ido jajur yana dubansu; “Yaya Uwale wai kin tabbatar ta shaki hayaƙin nan yadda ya kamata kuwa ? Na kasa gane abinda nake gani.” 

A fusace take harararsa. 

“Wai ni sau nawa zan faɗa ma na turareta, ko ni sai da hayaƙin ya dama balle ita. Me kuka maida ni ne Malam Iliya. Da fa ƙarfina da kuma kwarina bari ganin kamar ba ta YAU ba ce ni ɗin ? Ta ya ya dan wannnan abin zai gagare ni ? Ni kawai ka duba mini jihar da tayi a dawo mini da ita yau ɗin nan. Shi ne kawai abinda ya kawo ni ba wai tambayar na yi ko ban yi ba kuma…”

“Haba Uwale yi hakuri mana, kika gama da Bashari ma, balle wata Kiyashi Faɗime, ki saurare shi mana ya gama aikinsa ” Ta faɗa tana kallon Malam da kansa ke ƙasa yana jan carbinsa.

“Shi ke nan bari naga yadda za a yi.”

Ya faɗa yana aje carbin gami da jawo wani FAI-FAI dake cike da yashi. Sai dai Ja guda ya yi da ɗan yatsansa manuni bisa Faifan ya ɗago hankali tashe yana kallonsu.

*****

Yau kwana uku ke nan yana zarya gabar rafin bai ganta ba. A saninsa Faɗime ba ta kwana biyu duk rintsen da take ciki ba ta zo gurin ba domin kawai ta ganshi. Amman inya lissafa daidai yau kwanansa 12 ke nan rabon da ya ganta, tun rabuwar da suka yi kan mummunan zancen da baya fatan ya sake jin makamancinsa, wanda har takai ya faɗa mata abinda duk sanda ya tuno yake jin tashin hankali da matsanancin tsoro na shigarsa. Tsoro ne ya kama shi da ya tuna yadda suka rabu da Ummansa yau. Tana kuka take sanar masa kar ya dawo mata gida idan har ba da Fadime zai dawo ba. 

“Ina kike baiwar Allah.” 

Ya furta yana kewaye wata bishiyar Dirimi kamar mai tunanin tana bisansa. Murmushi ya saki sanda ya ga yar ƙofar bukkar dake gabansa ta buɗe wani farin dattijo ya fito. Cikin sassarfa ya ƙarasa gurinsa, shi ma Dattijon ya tsaya yana kallonsa, fatansa zatonsa ya zamana gaskiya, dan idan bai manta ba ya sha cema Faɗime ko tazo baya nan ta dinga bar masa sallahu gurin tsohon nan, cikin kwarin gwiwar tuna hakan ya isa gami da mika masa hannu.

“Ikon Allah! wannna shi ne saɓani” Dattijon ya fad’a da alamun damuwa.

“Jiyan nan ƙanwarka ta zo gurin nan cikin wani mayuwacin hali da na kwana dashi raina. ” cikin zakuwa ya ce; “Me ta zo yi Baba, yau kwana uku nake zuwa nan ban sameka ba, itama ba ta zo ba, ina take yanzu ? “

“Yo ina zan sani ? Ka ga dutsen can ? To bisansa ta zauna tana kuka tun ina bata baki har na hakura ganin kamar bata ma cikin hankalinta…” 

“Bangane ba me ya faru da ita ne ?” Ya faɗa a kagauce.

“Gaskiya ina kwautata zaton ta samu taɓin hankali, dan ko furar da na saba bata bata karɓa ba, da na mata magana sai kuka, har sanda wani mutum yazo nan Rafin tsinkar kainuwa, na ga tana masa magana, sai kuma na ga sun nausa yamma tare.

Bai jira ya ida sa ba, ya juya da hanzari ya yi yammar da ya nuna masa, da karfi yake faɗin; “Zan dawo Baba” Shi ko ba haka suka yi da Faɗime ba. Me ke faruwa ne ?

***** 

Miƙewar da ya yi a tsorace yana nuna ta da yatsa, ya saka shi ƙumewa da teburin bayansa, kafin yagama tantance zafin da ya ji, ya ƙara cin tuntuɓe da kujera ji kake TIMM! Ya zube bisanta.

Yayan da shigowarsa ke nan yaga wannan lamarin ya yi kansa da sauri yana salallami ba tare da kula da Yarinyar dake gefensa tana tiƙar dariya harda riƙe ciki ba. 

“Sannu Sagir, tashi ko baka dai ji ciwo ba ko ? Ina zaka ne ba za ka zauna a kawo ma abincin ba, tashi mu gani…”

Shiru ya yi ganin yana nuna masa bayansa da yatsansa, da hanzari ya waiga shi ma idanuwansa suka sauka kanta sai ya wara ido cike da murmushi yana kallonta tana dariya. Fuska ya yi ganin Sagir ya yi sakota yana masa kallon mamaki, hannuwansa ya sa ya ta do dashi tsaye.

“Kar dai ka ce mini wannan ƙaramar yarinyar ta tsorata ka ɗazu ?” 

Cikin rawar jiki yake kallon Yayan.

“Haba Yaya, ba za ka tambayi yadda tazo nan ba, ko yadda ta ɓace mini ɗazu, sai tsoron da naji shi ne abin tambaya. Wannan yarinyar idan ba Aljana ba to fatalwar wata ce. Wallahi munyi gamo, ai dama Alhaji ya ce nan guraren cike yake da…”

“Yo ba a motarku muka taho tare ba. Ni ba Aljana ba ce sai da kai.” 

“Ka gani ko, ka gani ko ƙila ma jikina ta shiga muka taho.”

Ya furta yana mai nufar ƙofar fita daga wurin. 

Tsirarrrun mutanen da ke zaune a gurin cin abincin suka kwashe da dariya.

“Kai mahaukaciya ce ba abinda kake zato ba.” 

Suka furta kusan a tare. 

Ko juyowa bai yi ba, ballantana su saka ran zai tsaya. Shi kaɗai ya ganta ɗazun shi ya sa ba zasu taɓa ganewa ba. Ba abinda ya fi mishi yanzu irin ya shige mota ya rufe kansa ko ya samu natsuwa.

Matsawa ya yi kusa da ita yana ƙare mata kallo. Shi curarran gashin da ta dunƙule ta cure tsakiya ya yi butu-butu da ƙasa ya fi ba shi dariya. To ita ɗinma tsayawa ta yi tana kallonsa, tana kallon masu abinci. Zai yi magana tayi saurin riga shi.

“Ni fa dan ku ba ni abinci na biyo ku.” “To me ya sa kika fisge masa ruwa yana cikin sha.”

“ƙishi nake ji, na ce ya ba ni ya watsa mini a fuska, ni kuma sai na sa ƙarfina na kwata.”

Ta furta tana mai tattaro kwanjinta na hannu. 

“Lalle kam ki na da karfi da kika iya kwatar ruwa gurinsa. To me ya sa baki zo mun tafi ba kika ɓoye ?”

Shiru tayi tana kallon wani wajen guda.

Ganin haka ya sa aka kawo mata abinci, tana karɓa ta fita kofar gurin ta zauna tana ɗiba hannu ba ka hannu a kwarya, kan ka ce mene wannan ta cinye. Shi dai yana shirin karɓar nasa da yasa a masu shi “Take Away” ya ji an warce ledar a hannun wanda ke miko masa.

“Ban ƙoshi ba.” 

Ta furta tana son ɓarka ledar.

“Ah’ah karki vata bari a ƙaro miki.”

Sai dai Ina, harta fara farka ɗan soson da aka zuba abincin wani ya zube ƙasa wani bisa jikinta, haka tabi tana tattarewa tana ci. Shi da mutumin suka bita da kallon tausayi.

“Yanzu haka ba da haukan aka haifeta, samunsa tayi a sama.” 

Mutumin ya furta yana kallonsa. 

Shi ɗinma tunaninsa ke nan dan haka kawai ya kaɗa masa kai gami da faɗin; “Sake yi mana wani roba biyu”.

Har ya buɗe ƙofar motar yana shirin zura jikinsa, yaji an ruƙoshi an cukwikwiye shi.

“Yo ina kuma za ka tafi kabar ni? ” Agogan hannunsa ya kalla, sai kuma ya kalleta , kome ya tuna ? Sai kuma  saka hannunsa a aljihu ya danƙo kuɗi da yawa ya miƙa mata.

“Karɓi ki koma gida, mu ba anan garin muke ba, garinmu za mu tafi, maza koma gida kar Babanki ya zo nemanki.

“Babana ya mutuuu, yau shekara haka.”

Ta furta tana nuna masa yatsunta takwas. 

Sagir da ya dawo cikin nutsuwarsa haushi ya kume shi, shi sai yanzu ma ya ƙare mata kallo, bai za ci irin sakarkarun mahaukatan yaran nan ba ne dake bin tasha suna kwace. Amman ? Sai kuma ya yi kwafa gami da buɗe motar da ƙarfi ya fito waje.

“Wuce ki tafi, tunkan na yi ƙasa-ƙasa dake a nan gurin.”

Shiru tayi tana ƙarewa bakinsa kallo.

Nufarta ya yi Yayan yayi saurin tare shi.

“Haba Sagir me zaka wa mahaukaciya kuma marainiya, baka ji me ta ce ba ? Ka bari mu lallaɓata harta tafi, in abin ya ƙi yiwuwa dole mu wuce da ita ko gidan mai…”

“Wallahi Yaya ba dai a motar nan ba. Taɓdijam, wannan ƙazantar ? To wai ma me haɗinmu da ita da za ta hana mu tafiya ?”

“Yo ba kun bani abinci ba ?” Ai ƙafata ƙafarka ko za ka mini abin da Uwale ke mini, kuma ko…” 

Tsawar da ya watsa mata ya sakata ƙamewa a gigice tana fasa ihun kuka kamar wacce aka rufe da duka, jikinta har rawa yake ta sunkuya ta danƙo ƙasa bai aune ba ta watsa masa ita a kyakkyawan tufafinsa.

“Tau!” Ji ka ke shi ma ya shimfiɗa mata mari, kafin ta gama dawowa daga hayyacinta ya ƙara buga mata tsawar. Nan ta miƙe a gigice ta kama tafiya

Tsantsan ɓacin ran da ya gani idon Yayansa ya saka shi sadda kai jikinsa na tsuma.

“Ka dake ta, Saboda ba ka da imani da tausayi ? Saboda ba kai aka jarraba da irin ta ta ƙaddarar ba ? Ba kuma za a jarrabeka da hakan ba tunda ka gama tsara taka kyakkyawar rayuwar. Ka wulaƙanta ta da abu mafi ƙaskanci mari ? Marin ma ga ƊIYA MACE me rauni ? Ba tare da kasan ko wane irin mustaƙbal (Future) take dashi ba..?

“Yaya ba ka ga abinda…” 

“Kamin shiru sagir tunkan na rama mata!” 

“Hmm!” Ya sauke numfashi yana mai  bin Faɗime da kallo dake tafiya cikin gigita tana haɗa hanya.

“Idan har na duba ba tada kowa anan gurin. Ko da za ka mutu ka dawo saboda ƙiyayya sai na tafi da ita gida. Ba kuma gida na ba, gidanku, gidan da kake rayuwarka, to tare zaku zauna. A cikin gidan ma ɗakin dake kallon naka. Wannan hannun da ya sauke mata girmanta, shi zai karantarta, motar da kake ikirarin ba za ta shiga ba, sai ka zama Direbanta cikinta . Kai wallahi ka ji na rantse har abinci ma sai ka bata da hannunka. Daga yau kasan wane irin girma ƊAN ADAM ke da shi! ” 

Da gaggawa ya shiga kwala mata kira.

“Ke! Ke!! “

Next >>

How many stars will you give this story?

Click to rate it!

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Share the story on social media.

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.