Skip to content

Fadime 1 | Babi Na Sha Uku

5
(1)

Karanta Babi Na Sha Biyu.

“Jabiru mu ɗauke ta kawai mun samu ganimar da za mu ƙarawa Iman.”

Gyaɗa masa kai  wanda aka kira da Jabirun ya yi yana mai rataya zungureriyar bindigarsa a kafadarsa.

Ita kuwa tunda ta samu kanta ta hau jijjiga Abbati tana kiran sunansa, amman Ina! Shiru kake ji yaron babu wani alamun motsi a tattare dashi.

Rashin abinyi ya saka ta ɗago kai ido jajur tana kallon dan ta’addan da ya rufe rabin fuskarsa da wani koren ƙyalle. To shi ɗinma ita ya ke kallo, kafin kuma ya ce, “ba abinda aka masa, tsora ta ya yi sa’ilin da ake kashe wancan, ruwa za ki shafa masa.” 

Ai da gudu ta saki Abbati ta koma kan gawar Malam da yake nuna mata. Idanuwansa a kafe suna kallon sama, fuskarsa ɗauke da kyakkyawan murmushi, kamar ka ce Malam ya amsa maka, haka ta hau girgiza shi cikin gunjin kuka tana kiran sunansa haɗe da sambatu, amman Inaa! Rai ya riga ya koma ga mai shi. Sai dai fatan cikawa da imani mu ma idan ta mu ta zo.

Jin ƙarar mota yasa Ɗan Ta’addan fincikarta yana mai saɓa Abbati a kafaɗarsa, haka  ya dinga janta tana kuka tana kiran Liman, ya jefa ta cikin ‘yan matan da suka kakkama game da dangwarar mata da Abbati saman cinyarta, shi kuma ya koma cikin motar ya shilla, suka nausa gabas da Maiduguri da gudun bala’i.

Sun daɗe suna keta titi da kwazazzabai cikin baƙar zungureriyar motar tasu kafin sukai wani ɗan jeji dake tsakanin ƙauyen Tikuwa da Gamborin Gala. Nan fa suka sassauka suka tasa ƙeyar ‘yan matan cikin babbar fadar Imam din nasu. 

Cikin jinjina yake kallon manyan kwamandodin nasa (Commanders) wato Jabiru da Mamuda, kafin  kuma ya kai kallonsa ga ganimar da suka kawo masa. Wani abin mamaki yana haɗa idanuwansa da ƴan matan kafataninsu suka duƙar da kansu ƙasa cikin girmamawa, in ka ɗauke  Faɗime da ke ruƙunƙume da Abbati tana ta sauke ajiyar zuciya akai-akai. 

Tsai! Ya yi kanta yana ƙare mata kallon abinda ya hanata russuna gabansa duk kuwa da haɗa idanuwan da ya yi da ita. A hankali kuma sai ya kai kallonsa ga Mamuda. Suna haɗa ido ya tashi ya shiga cikin gidan, sai gashi ya fito hannunsa riƙe da wani ƙoƙo cike da wani baƙin ruwa. Kai tsaye ya doshi wurinta ya sa hannu zai riƙota da nufin ya bata, ta yi saurin ƙanƙame jikinta tana kallonsa.

“Karka taɓa ni! Ba ni zansha da kaina”.

Ta furta da ƙeƙashasshiyar zuciyarta da ta gama bushewa. Ba ta ɗin kuwa ya yi, ba ɓata lokaci ta da ɗaya ta kwankwaɗe tas! Ta miƙa masa ƙoƙansa, gami da mai da kanta ga Abbati tana shafa fuskarsa a hankali.

“Allahu Akbar!”

Kafatanin ƴan ta’addan dake kewaye da Imam din suka ɗau kabbara suna jinjina yadda ta yi. Nan fa aka jera ƴammatan gaba ɗaya bisa gwiwowinsu ya fara musu wa’azi.

“Ku kwantar da hankalinku, babu abin da zai same ku anan. Ku kuma manta kuna da wasu iyayen bayanmu. Naku  iyayen arna ne su, sun zaɓi rayuwar arnanci a cikin gari. Duk kuwa wanda bai yarda iyayensa ba arna ba ne to shi ma ya kafirta. Za mu muku aure cikin mutunci ba irin auren zina da iyayenku ke muku ba, ba zaku sa mu matsalar ci balle sha ba, zaku ci zaku sha daga dangogin abincin da ko kuna gaban iyayenku ba lalle ku samu irinsa ba. Rashin karɓar da’awata kisa ne! Haka zina ga matar da take da aure jifa ne, ga marar aure kuma bulala ɗari, banda sata, shi ma akwai hukuncin datse ma duk wanda ya yi hannu. Ban da kuma ƙoƙarin gudu, ga duk wanda aka kama da hakan shi ma kisa ne. Akwai mai abin cewa ga da’awata?”

Kafatanin ƴan matan suka girgiza kai, alamun Babu. Nan da nan gurin ya sake ɗaukar kabbara.

Da ɗan Murmushi Imam din ya kallo Mamuda. “Kai a cikin waɗannan ɗinma har yanzu ba ka ga wacce zaka aura ba?” 

Kaɗa kansa ya yi yana kallo ɓarin da Faɗime take. A hankali ya ce; “Na samu Imam, in da hali a ɗaura mini waccar mai yaron.” 

Da sauri Jabiru ya kalle shi ya kallo Imam. 

“A’ah sam wallahi! Ni za a bawa ita, dan kuwa na riga shi a zuciyata, kawai ya yi saurin furtawa ne. “

A zuciye Mamuda ya taso masa, dama saboda irin kallon da ya ga yana mata ya zaɓe ta. Banda haka shi bai da ra’ayin mace, a wani ɓari ma na zuciyarsa, mamaki yake yadda farat ɗaya ta dame shi.

“To ai sai ka aura na gani, kai duk…” 

“Ya isa!”

Imam ɗin ya katse su sanin yanzu zasu fara halin.

“Kai Jabiru ka yi hakuri a bawa Mamuda tunda kai mata biyu gareka, shi kuwa wanann ce ta farko da ya taɓa nunawa, sai ka duba cikin sauran ka zaɓa, ba ɗaya, ba biyu ba, idan ma kwarkwara kake so ni ban hana ka ba. Amman banda wanann.” 

Sunkwi da kansa kawai ya yi ransa na ƙuna sanin tunda Imam ya furta haka, babu wani abu da zai ta da zancensa.

Nan da nan sauran yan ta’addan suka dinga zaɓen matan ana ɗaura musu aure, wasu su biya Sadakin da kansu, wasu kuma Imam ya biya musu. Ba a tashi daga fadar ba sai da kafatanin yan matan aka sanyasu ɗakunan mazajensu cikin gine-ginen ƙasar da da alama yan ta’addan ne suka gine gurin har ya zama wata ƴar ƙaramar Alƙarya cikin dokar dajin.

Babi Na Sha Hudu

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×