Skip to content

Fadime 1 | Babi Na Shida

4.5
(2)

<< Previous

Hannu bisa ƙirji take kallon Mallam tana kallon Salame tun bayan da ta gama jin zancensa. Ba ta taɓa zaton yar Faɗimen nan za ta iya shirya makirci har haka ba. Wai ita za a kaudama tunani cikin sigar rainin hankali daga abinda ta ƙudurta.

Inaaa! Uban Barbushe ma ya yi kaɗan, ballanta yar kiyashin yarinyar nan.

“Kin tsokano tsoliyar Dodo, ido na idonki sai kin gwammace Falmata ba ta haɗa makwanci da Bashari ba an samu cikin ki.” Ta furta tana duban Salame.

Sororo Salame ta yi tana binta da kallo. A karo na farko kenan tun kulla kawancensu sama da shekara Goma Sha Biyar da tsoron Uwale ya ɗarsu a cikin zuciyarta. Bata taɓa ganin zazzafar ƙiyayya irin wannan ba.

A ɗarare ta mike tana mai bin bayanta.

*****

Fes ta fito cikin zani da rigar da Kande ta saka mata bayan ta gama wanke mata duk wani annakiya da gansa kukar fatarta da cikin gashinta.

Ma sha Allah kawai Hajiya ke ambato ganin irin kyawun da ta yi. Idan ba zaman minti goma kayi da ita ba, a haka ba za ka za ci tana da lalurar taɓin hankali ba.

Abinci aka zubo mata inda ta zauna kusa da Hajiya tana ci tana mata surutunta wasu na hankali wasu kuma na akasinsa.

Saukowar Sagir ne ya saka ta tashi da hanzari ita da kwanon nata ta isa gabansa tana kallonsa. Shi ma kallon nata ya tsaya yi kan kuma ya doka mata harara yana furta

“Kauce daga gabana da Allah kin kafe ni da idanuwa kamar mayya.”

“Kanin Uwale zan bi ka inda zaka.”

Banza ya mata ganin ta ma raina masa hankali. Ya kalli Hajiya da ke murmushi. “Ka je da ita mana ko hira ai ta taya ka.

Kasa maganar da ya yi niyyar ya yi, sai kawai ya juya yana mai faɗin.

“Sai na dawo Hajiya “.

Faɗime ma abincin ta aje ta yi sama inda aka nuna mata za ta na kwana. Sai dai maimakon ta buɗe na ta ɗakin, sai ta yi ɗaya ɗakin dake gabda matattakalar benen.

Buɗewa ta fara yi da dukkan ƙarfinta amman ƙofar ta ƙi buɗuwa alamun an saka lock. Haƙura ta yi ta dawo ɗakinta.

Nan ma maimakon ta kwanta bisa tattausan madaidaicin gadon na ta sai ta shige ƙarƙashin gadon ta kwanta. A hankali nannauyan barci ya sace ta.

Da wuri Kande ta shigo ɗakin da zummar tashin Faɗime ayi wankan safe, sai dai wayam babu ita akan gadon, babu alamun ma mutum ya kwana samansa.

Toilet din ɗakin ta buɗe nan ma bata ciki. Fita tayi da hanzari ɗakin Hajiya nan ma bata ganta ba, sai Hajiya dake ninke wasu kaya.
“Lafiya dai Kande, na ganki kamar a firgice ?”.

“Ina fa lafiya hajiya banga ɗiyar nan ba, na ɗauka nan ta zo.”

Nan da nan Hajiya ta miƙe.

“Bangane ba, ai ɗakinta ta kwana dan sai da naga shigarta na tafi. Kin leƙa gurin Ilu ko ta farka ba ta ga kowa ba, ta fita can ?”

“To, to bara na je gun nasa.” Tare da Hajiyar suka fito, Ilu ya ce ko masallaci bai fita ba, balle a ce za ta fita sannan.

Hankalin Hajiya ya fara tashi ba shiri tace ma Kande ta ɗauko mata wayarta a kira Babban Mutum.

Fasa kai wayar kunne tayi ganin Faɗime ta sauko tana mutstsika ido. Kallon Kande ta yi, ta dawo ga kallonta ga Fadime da ta tsaya tana kallonsu.

“Ina kika shiga ne ana ta nemanki ?”

“Barci nake inda kika kai ni jiya.”

“Kande kika ce ba ta ɗakin nata?”

“Kwarai kam Hajiya har bayan gida na duba.”

“La ba ki kwankwasa mini gadon ba ai da na fito, bansan kina nemana ba.”

“Wai ƙarƙashin gadon kika shiga kika kwanta Faɗime ?” Shiru tama Hajiyar tana kallon Dining Table.

“Karki sake barci ƙasan gado, in ba ki son gadon za a shimfida miki bargo ki kwanta ƙasa, kin ji ko ?”

“Ku ba ni Abinci na. “

Da hanzari Kande ta riƙo hannunta “Mu je ki ɗauraye jikinki da baki sai kizo ki ci. Haka nan suka tafi tana ta waiwayen kulolin da aka jera bisa Dining ɗin.

Awa guda cur suka kwashe sai ga Faɗime ta sauko harta fi jiya kyawun gani. Lokacin Hajiya da Alhaji har Sagir sun fara cin nasu. Tsayawa ta yi tana kallon Alhajin. ganin haka Hajiya ta yafi to ta. Ta kuwa tafi ita ma ta ja kujera ta zauna kusa da Sagir.

“Hajiya shi ne Baban Babban Mutum ko ?” “Mun sameku lafiya Baba?”

Da Murmushi yake kallonta kasancewar Hajiyar ta bashi labarin komai daren jiya.

“Lafiya kalau yar Baba ya jikin na…”

“Lah har ka tuna mini Babana, shi ma idan na masa abin dadi yar Baba yake ce mini. Amman fa yanzu Tauraruwa sunana.”

“To tauraruwa yi shiru aci Abinci ” Alhajin ya fada fuskarsa fal murmushi.

Shi kam daga gare shi ba shida wata matsala dan dama marmarin ɗiya mace yake yi. ‘Yayansa ke nan biyu Abdallah (Babban Mutum) sai Auta Sagir. To wa ya ƙi daɗin Iyali, shi danta shi ne ma abar masa ita nan har abada ta zama ɗiyar cikinsa.”

Sagir kuwa da sauri ya aje fork ɗin hannunsa yana mata kallon mamaki. In bai yi da gaske ba yarinyar ba ƙaramin rainashi za ta yi ba. Ga Hajiya can gefe tana facing Alhaji ba za ta zauna kusa da ita ba sai shi?

“Ke! Tashi ki koma kusa da Hajiya tunkan na saɓa miki. Ni sa’an wasanki ne wai?”

Ko kallonsa bata yi ba hankalinta na kan Hajiya da ke zuba mata Abincin.

“Stupid, magana nake miki fa, za ki tashi ko sai na ɓarar dake ke da abincin” Ya furta yana dukan Teburin.

Hakan ne ya razanata ta ɗago tana kallonsa, sai kuma ta washe baki.

“La ƙanin Uwale yaushe ka dawo?”

Takaici ya saka shi komawa dabass yana kallon Alhaji dake masa dariya.

“Ka barta ta zauna mana tunda ba kanka take zaune ba. Ka ga ita bata ma kula kana gurin ba.”

Fork ɗinsa ya ɗauka yana jujjuya shi cikin abincin. Faɗime ko ana turo mata ta zare tarkacen cokulan ta aza hannunta. Sai da taci tayi nak. Hankalinta ya dawo kan Sagir da har yanzu caccakar abincin yake yi yana latsa phone kamar ba ya so. Fakar idonsa tayi ta kwashe ƙashin da ta tsotse ta taune shi ya zama diddiga a hankali ta watsa cikin abincinsa, ba idon Hajiya bare na Alhaji kasancewar suna ‘yar hirarsu.

Akan idonta ya ɗebo harda ɗan murmushi yana kallon wayarsa ya kai abincin baki. Sai da ta tabbatar ya haɗiye, tukunna ta yi shewa tana ƙyaƙyata dariya harda riƙe ciki tana nuna Sagir da hannunta. Dukansu ido suka zuba mata basu san abinda ta gani take dariya haka ba

“Walahi Hajiya ƙanin Uwale ya ci Abincin bakina.”

“What!!!”

Ya furta da ƙarfi yana miƙewa tsaye, sai yanzu ya kalli plate din nasa. Tabbas ga ɓurɓushin taunannan ƙashi a ciki.

Ji ya yi cikinsa ya wani yamutsa da gudu ya yi toilet ɗin falon yana kakarin Amai. Sai da ya amayar da duk abinda ya ci, tukunna ya fito ido jajur yana huci.

“Ba zan iya ba. Zan iya rugurguza mata ƙashi idan har ba za a daina haɗa mazaunina da na mahaukaciyar nan ba. Zan bar muku gidan gabadaya a nemi a rasa na rantse da Allah. Me aka ɗauke ni? Ance sai ta zauna damu na haƙura bance kome ba, to akan wane dalili kuma za a haɗa gurin cin abinci da ita . Ina mahaukaci ina dining table. Kuma ku duba ku gani ni kaɗai take gwadawa haukanta, ina jinta har gaishe da Alhaji ta yi. Ni na ɗora mata da za ta dinga sauke mini shi, a kuma hanani ɗaukar mataki a kanta, wannan ba abar tausayi ba ce, ina faɗa muku za ku yi nadamar riƙe ta, za ku yi nadama lokacin da ba ta da amfani. Amma shi ke nan.

“Ta sauke makan marar kunyar banza marar kunyar wofi, su Alhajin za ka sa gaba da masifa kamar kai ka haife su ? Wanene sila ? Ina ce ba kai ne ka jawo aka taho da ita nan ɗin ba. Na faɗa na ƙara faɗi, Sagir ko za ka mutu Fatima yanzu ta fara zaman gidan nan.  Idan baka son ganinta kullum safiya ka dinga liƙe idanuwan naka. Nadama kuma sai dai kai ka ganta, babu ta yadda za a yi ka yi taimako domin Allah ya zama tsiya, sai dai ƙaddara. Ke kuma ‘Yar tauraruwa kin kyauta mini sosai, nan gaba ma a baki zai baki da hannunsa. Amma dai karki sake zuba masa abincin baki.”

Babban Mutum ya furta. Shigowarsa ke nan ya tarda zancen.

“A’a Sagir fa da gaskiyarta. Idan ma ta ƙara haka sai na zane mata hannuwa. A kan me ya ci daɗin ‘Yar ɗiya ba zai yi faɗa ba ? Ya ka Auta kayi haƙuri da kaina zan ɗau matakin lamarin nan. Babba, maza kira likitan naka muyi abinda zai fisshemu, ko Auta ya samu lafiya. “

Ɗan murmushi Sagir ɗin ya yi jin abinda Alhajin ya faɗa. Gaishe da Yayan ya yi cikin ladabi, kana ya tashi ya bar wurin.

Shi ma dai Babban zama ya yi yana mai gaida su. Nan fa ya sanar da su Dr Misbahun ba yanzu zai komo daga tafiyar ba sai bayan Sati BIYU. Allah ya nuna mana kawai Hajiya ta iya cewa, suka shiga tattaunawa kan lamuran da suka shafe su.

Haka nan dai Faɗime ta ci gaba da zama da su da dadi ba dadi har ta samu wata uku cur gidan. Cikin wata ukun nan Sagir mutuwa ne kawai bai yi ba. Akwai ranar da ya kawo abokansa gidan ba ƙaramin ɓacin rai ta saka ranar ba. Kawai suna tsaka da hirarsu sai gata ta fado falon tana tattare zaninta har saman santala santalan cinyoyinta. Duka suka zuba mata ido kasancewar ranar suka fara ganinta. Kafin ya yi magana ta riga shi.

“Ƙanin Uwale Hajiya ta ce ka zo ka mini tsarkin kashi.”

“What!?”

Abokan Su kai exclaiming a kusan tare suna kallonsa. Bai san sa’adda ya mulmulo ashar ya narka mata ba.

“Dan ubanki tashi ki ɓace daga nan, ina kika taɓa ganin gandamemiyar Budurwa kamarki an mata tsarki ? Ko yau haukan naki haka ya rawaito miki ? Sorry friends mahaukaciya ce karku ji shirmenta da Allah. “

Lahhh Walahi ƙarya yake yi dan ya ganku ne, kun ganni fa , Ta tashi tana juyawa gabansu , ina haukan anan ? Kawai bai so ya mini ne don karku masa dariya. Amman kullum shi yake mini ko a wando na yi shi yake wanke mini.”

“Oh Allah Ni kam na shiga uku.

Ya furta yana dafe kansa.  Dagowa ya yi da nufin fincikarta ya ga wurin wayam har sun watse. Da sauri ya bisu suna shirin ta da motansu. Haka nan ya babbasu haƙuri, suka ce ba kome sun fahimci lamarin. A ranar ya so ya mata dukan da zai kwantarta amman Hajiya ta shiga tsakani. Haka nan suke rayuwa  bai da wata power a kanta, koyaushe ita ke cin nasarar ɓata masa rai.

Yau da farin ciki fal Babban Mutum ya shigo gidan yana mai kwalama tauraruwa kira. Sai ko gata gabansa “Ɗauko hijabinki maza mu tafi asibiti Dr musbahu na can yana jiranmu.” Dariya ta kama yi tana tafi sai kuma ta je ta ɗauko. Sallama su kai ma Hajiya suna shirin fita Sagir ya sawo kai. Har sun wuce shi, sai kuma Babban mutum ya tsaya da ɗan murmushi.

“Sagir zo mana” Ya faɗa yana yafito shi.

“Yauwa ɗauko motarka ka kai Fatima gurin Misbahu yana asibiti yanzu haka, na masa bayanin komi kawai shiga zaku yi. Ni ma zan taho ina gama abinda ke gabana.”

“Ni Yaya?”

“To da waye Sagir in ba kai ba?”

“Gaskiya ya ya mota ta babu mai.”

“Buɗe boot din tawa motar akwai mai ka dauka ka zuba.”

Shiru ya yi cikin ƙunci yana kallon Hajiya da ke hangensu, suna haɗa ido ta mai da kallonta wani gurin daban.

“Yaya lokaci za…”

“Sagir ka wuce ku tafi tunkan na ɓatama bansan jin kome.” Ya kai kallonsa ga Faɗime.

“Wuce ki bi shi ni ma inan nan biyo ku.” Da murnarta ta fita har ta riga mai motar isa motar.

“Sagir!!” Ya ƙara kwala masa kira.

“Wanda ya ma wani mugunta shi ma dai za a masa, dan haka aji tsoron Allah. Ka yi da jiki kuma kaga hadiri ne garin.”

Kaɗa masa kai kawai ya yi. Bai san magana sam dan ji yake da ya buɗe baki kukun baƙin ciki ne zai ƙwace masa.

Tukin yake yi ammam shi kansa baya jin dadinsa kasancewar yadda ransa ke matukar ɓace. Ni san dake tsakaninsu da asibitin ya sa har sai da ruwan ya fara sauka. A hankali zuciyarsa ta fara sanyi kaɗan-kaɗan sakamakon wani tunani da ya tsirga masa. Da karfi ya taka burki yana mai faka motaŕ gefe. Titin ya yi tsit kasancewar ruwan ba na wasa ake yi ba, sai yan ɗaikakkun motoci dake wucewa. Fito wa ya yi duk da ruwan dake dukansa ya buɗe bangaren Faɗime.

“Fito mini daga mota.”

Tsayawa ta yi tana kallonsa tana kallon ruwan daka ganta kasan a tsoroce take. Ganin haka ya sa ya riƙo ta tana dagewa hannunta bisa handle ɗin motar haka fincikota game da jefata cikin sassanyar ruwan saman. A razane ta kwaɗa ihu sai kuma tayi tsit tana sauke nannauyan nishi. Komawa ya yi cikin motarsa da sauri ya rufe yana kallonta ta ciki. A hankali ta rarrafo tana buga motar tana maganar da baya iya ji kasan cewar yasa ear piece, sai ya ma kauda kansa can ɗaya 6arin game da ɗago wayarsa ya kama chatting.

Duk mai imanin da ya kalli Faɗime a wannan lokacin sai ya yi tur da wannan zaluncin. Tun tana bugawa da dukkan ƙarfinta har ta daina. Da sauri da sauri take fidda numfashi jikinta yana karkarwa. Minti goma sha biyar ya kwashe tukunna ya buɗe motar yana kallonta. Zuwa yanzu ta sa kanta bisa ciinyoyinta yana iya jiyo yadda take kokawa da numfashinta. Dagowa tayi tana kallonsa, kallon da ya faɗar masa da gaba a karo na farko a rayuwarsa tun saninsa da ita. Da sanyin jiki ya isa gareta tana ƙanƙame jikinta haka nan ya jawo ta ya jefata motar da sandararrum kayan jikinta. Shi ma ya koma game da ta da motar yaci gaba da tuƙinsa cikin kwanciyar hankali. A hankali ya saki kiɗa, yana jin yadda wani nishadi ke shigarsa. Ba ƙara bi takan Faɗime ba dake lafe a ba ya ido wuri-wuri har suka isa asibitin. Parking motar ya yi kana ya fito ya buɗe ɓangaren Faɗime yana faɗin.

“Ai sai ki fito an iso kuma wallahi inji kin faɗawa Yaya wannan abun, sai na miki wanda ya fi shi mu…”
Kasa ƙarasawa ya yi ganin yadda ta sandare jini yana fita a hancinta babu wani alamun numfashi a tattare da ita “Fatimaa!!” Ya furta da karfi a kuma karo na farko tun haɗuwarsa da ita. Da gaggawa ya zaro sandararen jikinta cikin fitar hayyaci ya shiga kwaɗawa Nurses kira. Da gaggawa suka karɓeta suka shiga da ita wani ɗakin, shi kuma ya tsaya safa da marwa. Babban tashin hankalinsa Yaya.

Dr Musbahu zaune cikin office ɗinsa yana ɗan bubbuga biron hannnunsa bisa table din gabansa. Sai Babban mutum da zuwansa ke nan ya tadda Faɗime bisa gado ba yadda take. Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba. Sai dai bai saurari Sagir da ke son masa magana ba ya biyo Dr zuwa office ɗinsa.

Doctorn ya nisa yana kallonsa.
“Gaskiya yadda binciken mu ya nuna ta shafe sama da watanni uku cikin wanann yanayi, wanda jinkiri da rashin samun taimako a lokacin da ya dace ya jawo mata illoli da dama. Na farko dai a duk sanda akai irin wananan Allurar ba a so ko Yaya kana mu amala da ruwa indai ba ruwan zafi ba ne. Rashin kiyaye hakan ba ƙaramin effecting din wanda akai ma yake ba, dan kuwa idan ana sa ran in aka masa wacce zata dawo dashi cikin cikakken hankalinsa, to indai yana mu’amala da ruwan sanyi zai iya zama ƙila wa ƙala. Duk ma ba wanann ba gaskiya yanzu lokacin da za a kashe waccar ɗinma ya wuce, babu abinda zamu iya irin mu zubawa sarautar Allah ido. Idan Allah ya kawo sauƙi a kowanne lokaci za ta iya dawowa cikin tunaninta. Idan kuma aka sami akasin haka kuwa zata iya zaucewa ma gabaɗaya ko kuma tayi mantuwar abinda ya gabata a baya (loosing Memory). Zan dai ɗora ta kan wasu magunguna ko za a dace. Sai dai da Allah gaba a kiyaye da barinta ta ammali da ruwan sanyi dan kuwa ba ƙaramin illah yake mata.”

“Lahaula walla kuwwata illah billah.” Ya Allah ka fitar da yarinyar nan daga wanann tsananin da take ciki. Dr ni na kasa gane wata allura kake nufin anyi mata, nufinka allura ce ta sata cikin wanann halin ?”
“Kwarai kuwa Abdallah. Ni kaina tambayar da zan maka ke nan, ya akai aka mata wannan muguwar Allurar, Allurar da ba a fiya yiwa yaran da basu kai shekara ashirin ba.”

“Ina zan sani Dr?”

Haka nan muka same ta mu ma fa, sai dai idan ta farka in gwada tambayarta dan wani zubin zaka ga tana faɗin abubuwan da suka faru da ita. Kai Allah wadaran azzalumin da ya shirya wannan abin. Yanzu zamu iya ganinta kenan ?”

“Sosai kuwa ta daɗe da farkawa ai, fatana dan Allah a kula a gaba.”

“Insha Allah Dr nagode sosai”. Ya furtaa yana mai barin office ɗin.

Ganinsa ya sa Sagir tashi da sauri yana masa magana. “Dan Allah Ya…” “Tasss! Ya ɗauke shi da wani wawan mari, sai da ya ga Taurari suna wulga masa, ya yi saurin dafe kuncinsa, yana kallonsa.

“Kana da nutsuwa kuwa? Kasan illar abinda ka aikata? Yaushe ka fara hauka ne bansani ba Sagir? Wane irin abu ta maka da zafin sa zai sa ka azabtata da ruwan sama ? Tsaya ma mai kake son ce mene. Ba kai ka yi ba da yake indararo gareka cikin motar ko? Bari kaji Sagir! Idan kana tunanin wannan shi ne iyakar kiyayyar da zaka nuna mata, to wallahi ta yi kaɗan. So nake naga ka ɗau wuƙa ka mata gunduwa gunduwa ka aje mini ita saman mota nan ne zansan ka haifu a Turai. Ka ɓace daga gabana kafin na yi rugu-rugu da kai. Allah zai saka mata muna nan da kai.”

Ya furta cikin ƙunar rai gami da shigewa ɗakin da Faɗime take. Sagir dai kam shiru ya yi cike da ɓacin rai yana shafa inda yasha mari. Ko kaɗan baya nadama sai dai ma zafin a dalilinta an mare shi. Ƙarshe ma barin asibitin yayi gabaɗaya ba tare da ya ƙara leƙata ba.

Ko bayan farkawarta jiya e yau dai. Sai ma wani shiru da ta zama duk dan wasan da ‘yar fara’ar ta tafi. Sai dai ta zauna ta yi shiru kamar mai tunani ba um ba um’um , wannan abin ne ya ƙara ta da ma kafatanin mutanen gidan hankali, idan ka ɗauke Sagir da ko kallo bata ishe sa ba, yana ta fushin Yayansa ya ki amsa gaisuwarsa duk a dalilinta.

Sau uku Babban Mutum yana tuntuɓar Dr kan hakan yana ce masa ba kome karya damu, akwai yiwuwar za ta dawo cikin nutsuwarta gabadaya ne. Shi dai kam hankalinsa ya gaza kwanciya, gani yake ko wani ciwon ke damunta ba a sani ba. Yau ma dai haka nan ya saka ta gaba sai takalarta yake sai dai kawai ta bishi da ido har hajiya ta zo ta tar dashi yayi zurfi cikin tunanin yadda zai gyara rayuwar Faɗime.

Dafa kafaɗarsa ta yi inda yayi firgit yana kallonta. Cike da tausayawa take dubansa.
“Ka saki ranka Babban Mutum, ka ɗauka cewa wanann duk yana cikin jarrabawar rayuwarta da mu da muke riƙeta baki ɗaya. Allah yasan abinda bamu sani ba, don haka yafi mu sanin dalilin faruwar hakan, mu yarda da ƙaddara, mu kuma jira mu ga ikonsa.”

Jikinsa ne ya yi sanyi yana kallon Hajiyar.

“Abun ne da taɓa rai Hajiya, na rasa me mutane ke nema a duniyar nan da basu gudun zalunci. Ki duba fa ki gani babu wani mataki da ta taka na cigaban rayuwa. Amman a hakan aka samu wanda ya rushe mata ɗan ginin rayuwar. Me ta yiwa wanda ya mata da zai ɗau wannan matakin?”

“Allah Masani Babban Mutum, haƙuri kawai za kai kama dai na tunano irin wadatnnan ɓacin ran. Samun lafiyarta shi ne kawai babban burinmu.” “Hakane Hajiya, To Allah ya rufa Asiri.” Ya furtaa yana mai barin wajen.

Rayuwar Faɗime ta miƙa cikin zuri’ar cike da kwanciyar hankali, ga wani irin girma da take yi na ban mamaki kai kace kazar Agric  ake kiwa ta wa. Idan baka santa shekara ɗaya da rabi baya ba, ka ganta yanzu zaka ɗauka ta kai shekara goma sha takwas sabida cikar da ta yi. Wanda ba kome ya ja haka ba sai tsabar jin daɗin da Hajiya ke wadata ta da shi.

Ga Hajiya ko har bata son tuna Faɗime ba ɗiyar ta ba ce. Wata nagartacciyar ƙauna  ke tsakaninsu, ƙaunar irin wacce duk wata Uwa ke ma ƴaƴanta. Ga Faɗimen ma haka ne, dan ko fita Hajiya ta yi ta rasa sukuni ke nan har sai ta dawo. Ita kanta Hajiyar bata son nisa da ita. Ga babban abinda ke ƙara faranta musu rai, yadda wata nutsuwa  ke mamayarta. Duk wani sakarci, yawan magana, tsokana ta dai na. Cikin shekara guda har haddar izifi Asharin na alƙur’ani mai girma da suke yi da Hajiyar ta yi. Ga waɗansu ƴan ƙananan littattafan addini da ake koya mata nan ma. Game da larurarta kuwa tun tana rufa sati abin bai motsa ma ta ba, yanzu tana kai har wata cikin nutsuwarta. Sai dai idan abin ya motsa kowa sai yasan akwai marar lafiya gidan. Dan ko ta dinga koke-koke ke nan da ba da labarin Uwale. Wani abun mamakin duk sanda take cikin hankalinta in kwana zakai kana mata tambaya game da labarinta na baya ba zata faɗa maka ba. In ka faye matsa mata ma ta sa maka kuka sosai, karshe ta ma yi yajin cin abinci gabaɗaya.

Dalilin ke nan yasa Hajiya ta rufe a mata tambaya kowacce iri ce. Da ma Babban Mutum ne ke yi ko iyalinsa in sun zo, ko kuma Kande. Abu ɗaya ne ta kasa barinsa wato kwana ƙasan gado, da tana cikin nutsuwarta da bata ciki haka nan zata hanƙada ta shige cikinsa. In kaso ganinta kwankwasa mata yanzu zaka ga ta mirgino tana ma kyakykyawan murmushinta.

Sagir kuwa tun ranar da ya mata izayar ruwan sama har zuwa rana irin ta yau Faɗime ba ta ƙara ɗaga kwayar idonta ta dube shi ba. Kai ko tangamemen hotansa na falo ba ta kalla. Haka indai yana dining cin abinci da ta zauna ta gwammace ta ɗauke abincinta ta tafi can gurin Kande ta ci. Shi ydin ma da fari abin ya tsayama sa rai, ganin kamar yarinyar ta ƙulla ce shi ne. A hankali kuma sai ya share ko dan ganin ya samu lafiya, duk da can kasan zuciyarsa yana kewan wasu abubuwan na ta. To karshe ma dai tattara ya nasa ya nasa ya tafi can Ghana yin wani (Course) na shekara guda kan  (Computer Science). Wanda sai da Alhaji ya sa baki tukunna Babban Mutum ya yarda. A hakan ma sai da ya sashi yiwa Faɗime shopping mai tarin yawa cikin Aljihunsa. Wannan ke nan.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×