Skip to content

Fadime 1 | Babi Na Uku

2.3
(3)

<< Previous

Gishiri-gishirin da ta ji saman laɓɓanta ne ya ankarar da ita kuka take. Da sauri ta hau sharewa zuciyarta na tabbatar mata ba kukan tausayinsu take yi ba.

Da maghriba tana zaune zuciyarta cike da zullumi Malam tunda ya fita har yanzu bai dawo ba ta ‘ji sallamar Aminyarta. Da hanzari ta tashi tana washe baki duk wani ƙunci da take ji tana yana wucewa.

“Salame ina kika shiga ke kuwa yau kwana biyar nake cigiyarki ?”

Tutturnan bakar matar dake amsa  sunan Salame ta washe baki makaken wawulon dake bakinta ya bayyana.

“Hmm ke dai bari, Ɗan Hasan na tafi gidan sunan Binta, kinga yanzu ma naman sunan ne na taho miki dashi, kinsan ba zan iya ci ke baki ci ba.”

Ta furta tana kwance ƙullin Naman da bai fi yanka biyu da rabi ba, ta aje a gabanta. Da hanzari Uwale ta jawo ta dan nasu duka bakinta. Sai da ta hadiye ta dubi Salame dake ƙarewa ɗakin kallo cikin hasken wutar Aci bal-bal.

“Baki tambayi Fadime ba ?”  

“Hmm! Ita nake son tambaya kika riga ni , kin korata Marin halan?” 

“Ina fa ? Malam ya kasa ya tsare. Na kulle ta ne a ɗakin kaji.” 

“Dakin me ?” 

Salame ta furta tana dafe ƙirji. 

“Hmm!  Dole ce ta sa, kwana biyar ɗin nan da baki zo ba yarinyar nan ta kusa mai dani mushe…” Nan ta bata labarin duk abinda ya faru.

Salame ta doka salati tana gyara ɗaurin kallabi.

“To kuma shi ne dan sakarci kika barta haka nan bayan fitarsa me ya sa baki kirɓata ba ?” 

“Na gaji ne wallahi Salame, na gaji! Hannuwana har zafi suke saboda duka da ɗaga bokitin ruwa.” 

“Mtssw!” Ta ja tsaki.

“Wa ya ce mike dole sai da hannu ake horo?Bari ki ji wata dabarar.  Ba dai mahaukaciya ba ce ? Ai mahaukaci ma yasan ƙaiƙayi ince ko ? To samo shi maza ki sama shegiya cikin ruwa ki aje mata inda zatai wasa dashi ma ga ta hauka ai. Na tabbata daga ranar ba ta ƙara kuskuren yi miki ta’adi.”  

Uwale ta kwashe da dariya.

“Shi ya sa fa bana so ki yi nesa da ni ko na wuni guda ne, shi ya sa fa…”

Ta yi saurin yin shiru jin da tai kamar motsin mutum jikin tagarsu. “Wa ye anan ? Hansai ? ke ce ?” 

Ta ji shiru, hakan ya sa suka miƙe ita da Salame a tare suka fito, sai dai wayam babu kowa gurin sai Faɗime dake kwance har yanzu, dake ƙofar a buɗe take. 

“Ƙila to kunne na ne, amman fa kamar naji ƙusur-ƙusur ɗin Mutum.” 

“Ko kuma na ɓerayen da kike kiwo ba.”

Salame ta bata amsa, kafin kuma su bushe da dariya a tare. 

A daren kafin Salame ta tafi sai da suka san inda suka sami Karara, suka zuba cikin kwanan sha gami da sheƙa ruwa.  Ta aje shi inda ta tabbatar Faɗime na tashi za tai facaka da shi.

Wani matsattsen fitsari ne ya tada ita, ta fito tana doka tsaki da tunanin jan ruwa, gashi dare ne balle tace Hansai ta ja mata. “Wash!” Ta ambata lokacin da ta daga Butar ta ji ta cike da ruwa. A guje ta doshi banɗakin jin za ta iya sakinsa…

Da fari shiru tayi tana son tantance abinda take ji. Kamar wacce aka mintsila kuma sai tayi fatali da zanin jikinta ta hau soshe-soshe. A guje tayi ɗaki tana kwalama Malam kira wanda ke kan gyara kwanciyar daddaɗan barcin da yake yi.

“Menene kuma ?  Ke da daren ma baza ki bar mutum ya huta ba…?”

Ihun da ta daddage ta runtuma ne ya saka shi miƙewa tsaye a gigice yana karo hasken fitilar kwan.

“Malam matanci, matanci na Malam na rantse da Allah azabar da nake ji gwara haihuwar Hansai da shi. Zan mutu Malam.” 

Ta furta tana timuwa a ƙasa gami da goga bayanta jikin bango.

“Wai me ya faru ? Bangane ba ? Me ya samu gurin ne ? Ko cinnaka ne ya cije ki garin shegen wawan barcinki.” 

“Ƙaiƙayi Malam!  Wallahi da Karara nayi tsarki.” 

Da gaggawa ya karaso gurinta.

“Ƙarara kuma ? Me ya kawo ƙarara cikin b’Buta ? Kina lafiya kuwa Uwale…?”

“Kwankwanbilo ne kaina, ka sosa mini ni da Allah ko zanji sauƙi. Wayyo uwata Kakale na shiga uku. Kai! Allah ka tsinema Bashari da ya yi silar zuwan Faɗime duniya, na rantse ita ta zuba mini…”

“Wai wane irin hauka kike yi Uwale. Me Bashari ya miki tsakar daren nan kike roƙar masa tsinuwa.” 

“Ba lokacin zance ba ne wannan ka sosa mini na ce!!!” 

Ta furta tana ɗaga masa ƙafafuwanta sama.

“Allah suttara, haka kawai ni ma na samu rabona. Ke dai da kika samu can ki ƙarata da shi. Allah ko kusa da makwanci na karna ganki. ” 

Ya furta yana komawa gurin kwanciyarsa. 

“Yanzu Malam tsakaninmu akwai abinda zai same ni ka gujeni ?” 

Ta furta idanunta na kwararar hawayen azaba. 

Shiru ya mata yana juya mata ƙeya. Tun yana jin ihunta da ɓari da kwanuka har barci yayi awon gaba dashi. 

Uwale kuwa a zaune ta kwana bisa dandaryar ƙasa, bayan tama kanta tumbur tamkar mahaukaci sabon kamu.

*****

Sai da ya kai ludayin ƙarshe bakinsa, ya aje gami da gode ma Allah da ya wadata shi da abinda zai ci ba bisa tsuminsa ko dabararsa ba,tukunna yakai kallo inda take zaune ta doka tagumi idanuwanta sunyi jajur alamun ta ci kuka ta koshi.

“Umma ki yi hakuri dan Allah. Wallahi ni kaina ba bisa raina na tsaida shawarar nan ba, amman ba yarda zamu yi, banga wata mafita ba sama da wannan.” 

Ka mini shiru Yaya! Idan ba sakarci ba shekara nawa kuke tare me ya sa baka taɓa ba ni labari ba sai yanzu da kome ya lalace ? Sau nawa za ka same ni ina zubar da hawaye baka san duk saboda hakan ba ne ? Ashe har akwai wani abu zai shigo rayuwarka  baka sanar da ni ba, ni Mahaifiyarka ? Kai Innalillahi wa Inna ilaihir raji’un! Allah ka ji ƙan Falmata.”

Cikin rawar jiki ya motsa kusa da ita shi kansa idanuwansa kwallar suke zubarwa, riko hannunta ya yi ya fara magana a sanyaye.

“Umma ki yarda da ni, Allah shaidata Bansan Fatima ɗiyar ɗan uwanki ba ce, ban sani ba wallahi. Baki taɓa faɗa mana kina da wasu dangi a garin ba. Allah ne ya hada ni da yarinyar nan har na zama mai ba da garkuwa kanta. Banda sanadi ma mai zai kai ni can Umma ? Ki yi haƙuri na miki alƙawari duk inda Fatima take zanje na kawo miki ita, ki yafe mini dan Allah!”

“Na ji ya wuce. Yanzu ba ni labarin tun farkon haɗuwarka da ita. Ban kyautawa Falmata ba, ita kaɗai ta rage mini da take jinina. Tashin hankalin mutuwarsu da hanani yarinyar da wan mijinta ya yi ya sa ni ma na share su, ko zuwa ganinta ba na yi.”

“Umma na fa baki. “

“To bai ishe ni ba.”

Murmushi ya saki gami da sa kansa bisa kafaɗarta.

“To na ji Umma, amma fara ba ni naki labarin har zuwa sanda kika auri Baba.”

Rankwashi ta kai masa fuskarta cike da murmushi, hawaye kuma na zuba.

*****

Wai Uwale yau ma ba karin kumullon ne ?” Ya furta yana gintse dariyarsa, ganin dare ɗaya tayi wani mugun sanyi. Shi kam bai taɓa sanin akwai abinda zai shigar da Uwale cikin nutsuwarta ba. Lalle ba dan mugunta fitsarin fako ba ce, da ya yi ta roƙon Allah ta dinga tsarki da ƙarara daga nan har karshen  rayuwarsu.

Ƙara kallonta yayi ganin tana nan zaune ko kwakwkwaran numfashi bata son yi. Kaɗa kansa ya yi gami da dosar kofar fita daga gidan. Zuciyarsa cike da godewa Allah yadda yau ba a tashe shi da harara ba, ba a kuma raka shi da ita ba. 

Ganin ya fita ya sata miƙewa da hanzari ta leƙa wajen, sai da ta tabbatar  ya karya kwana ta dan nawa ƙofar sakata. 

Kai tsaye inda Faɗime take ta yi, ta  finciko ta hadata da bango da wata irin bahaguwar maƙura. Yarinyar tun tana dariya harta fara kuka tana son kwatar kanta. Sai da ta tabbatar ta galabaita sannan ta wancakalar da ita gefe tana haki. Wani baƙin ciki ya ƙara kwasarta ganin ta miƙe gami da komawa gefe tana wasa da gashin kanta tamkar ba ita aka gama maƙura ba. Kwafa ta yi, sai kuma ta shige ɗaki da hanzari. Can sai gata ta fito da Igiya kakkaura. Ɗaure ta ta yi irin ɗaurin da sai anyi da gaske zai kwantu. Tukunna ta jawo Turmin daka ta watsa Barkono da kayan ƙamshi ta barbada toka ta fara dakawa.

“Kashe ki zan yi! Yadda Bashari ya bar duniya ba a ga ko tokarsa ba kema yau hakan zanyi da ke. Ban taɓa tsanar wata halitta a duniya sama da yadda na tsani Bashari da Falmata ba. Amman a yau dukkan tsanar ta koma kanki shegiya baƙar annoba baƙar Akuya da silar haihuwarki duk wani buri na ya ruguje.”  

Gama da kan ta yi, ta miƙe da hanzari ta isa ga Faɗime ta gwale kafarta za ta zuba Barkonon. Ihun da ta fasa da dukkan karfinta ya yi dai-dai da bugun ƙofar gidan kamar za a ɓallata.

“Aminiya ba kya nan ne na kama gabana? Wannan rufe ƙofa haka kamar mai wanka a  tsakar gida.” 

Jin muryar Aminiyarta yasa ta miƙewa da hanzari ta je ta zare sakatar.

Idanuwan Salame basu sauka ko’ina ba, sai kan Faɗime dake ta mutsu-mutsu cikin murtukekiyar Igiya.

Ta kuwa kwashe da dariya tana duban Uwale.

“Wace wainar kuma kike toyawa haka? na ga duk kin shirɓa uban gumi, kamar ma kin rame.”  

“Hmm! Ba dole na rame ba. Waccar baƙar annobar ta mayar mini Ƙaiƙayin kaina. Sam jiya ban runtsu ba, tsarki fa nayi da shi.”

Salame ta zare ido tana salallami ?

“Garin ya ya to ? Ta yaya ta san mene ciki ta juye mikin,? Yanzu wane mataki kika ɗauka? ”  

“Garin haukanta mana ta juye ruwan a Butar Ni kuma azal ɗin ta hau kaina. Mataki ya wuce wanda zan mata yanzu.”

Ta furta tana mai nuna mata cikin turmin da baki.

“Wai da kwaɗon Yaji zanyi da matancinta, kin san Allah ni da kaina ma ya kwance  har ‘yar guntuwar Citta da Masoro na jefa.”  

Salame ta kwashe da dariya sai da tayi mai isarta, kana ta kwance mayafin jikinta gami da daure shi a kugu.

“Bari to na taya ki, buɗe kafafuwan.” Ta furta tana dosar Faɗime.

“Wa za a buɗe ma ƙafafu ?” Suka ji Muryar Malam a bayansu. 

Da hanzari ya doshi Faɗime yana doka salallami. Ita ma ganinsa ya sata sakin ihun kuka. Shan gabansa Uwale tayi tana kaɗa jikinta cikin tsantsar tashin hankali.

“Kwanceta daidai yake da amincewarka wucewa da ita gidan Malam Musa Mai Mari yanzun nan!” 

Shiru ya yi yana kallon Faɗime. 

Tabbas gwara gidan Mari da wannna izayar da ya tarar za’a ma marainiyar Allah, shi ko mai zai hana shi yarda, dan haka ya nisa cikin son bagarar da kome ya ce. “Yauwa Uwale ai abinda ya dawo da ni ke nan, na zo tafiya da itan ne.” 

Ya sami bakinsa da mata ƙarya. 

“Ayyiyrurii yau buri ya cika.” Ta doka shewa gami buga hannu cinya. Da hanzari ta fara kwance Faɗime tana yi tana mintsilinta ganin ba idon Malam.

 “To dai ƙarshen duk wata muguntarki ta zo, ba sai kin bita da mintsili ba.”

Kifta ido ta farayi sai kuma ta hanƙada masa Faɗime gabansa, ya yi hanzarin taro ta jikinsa ganin za ta fadi.

 “Babbar Nasihar da zan ma idan ka kaita ita ce, karka kuskura a saka ta inda za ta samu damar kuɓcewa tabar garin nan!”

 Ta fadi gami da juyawa gurin Salame wacce ke tsaye kamar ace ƙyat! Ta arce.

*****

 “Ga ta Malam Amanata ce, karka sata inda za ta wahala, kar kuma a sata aikin da ba za ta iya ba. Haka kar a bari wani abu ya samu lafiyarta. Bayan kwana biyu da kaina zan zo na ɗauketa na kaita inda za ta ji daɗinsa.

Dan Allah Malam Musa ka riƙen Amana…”

“Ban karɓa ba! In dai Amana ce ba na karɓarta anan. Mari ka kawota ko gidan renon yara ? Kasan zuciyarka na mata wannan son to ka je kayi haƙuri da abar ka. Ban da ma kirki irin nawa akwai riƙon da zai bada wahala ne ma irin na mahaukaci ? ai har gwara na gagararre, amma Ni da haka na karɓeta, kai kuma ko kunya kana mini wasu zantuka masu kama da gargaɗi, haka…” 

Dariyar da Faɗime ta kwace tana nuna fuskarsa da hannu ya saka shi yin shiru yana shafa fuskar.”

“Ka gani ko ? Tun yanzu ta fara raina gemuna da na daɗe ina tanada shi. Akan bai kai kamu ɗaya ba, Sahura taƙi aure na. Kuma… “

“Ya isheni haka Malam Musa, ba hirar zawarcinka na zo muyi ba.” Malam  ya faɗi cikin damuwa.

“Na ji ba ka riƙe amana , to amma dan Allah karka saka mata waɗannan ƙarafunan na gabanka. Ka ga har ƙarzuwa suke saka wa yaro…” 

“Idan ba ka so a saka biya kudinsu yanzu.”

 Ya yi hanzarin tare sa yana mai miƙa masa hannu.

“Ai kasan ba ni da shi. Sai kuma abu na gaba da Uwale ta ce na sanar maka shi ne; kar kai ragon riƙo da ɗiyar mutane. Ka tabbata ta dawwama nan har zuwa sanda zan zo na tafi da ita…!”

“Yo dama nan gidan ai an shigo ke nan, in ba iyayenka sun fidda kai ba, to gawarka, itama gawar na kusa mata MAKABARTA anan. Dan haka karka damu.”

Malam girgiza kai ya yi sai kuma ya miƙe hannunsa riƙe da na Faɗime. Kallonta ya yi yana son maida kwallar idonsa.

Ki yi haƙuri Faɗime, ki yi haƙuri. Ban isa zama Babanki ba, ban kuma cika mutum ba da na kasa riƙe Amanar Bashari. Ki yafe mini, na miki alƙawari nan da yan kwanaki zan zo na dauke ki na kaiki can gurin Innarki kin ji ?_

Ya furta kamar wanda ke tunanin mahaukaciyar ‘yar za ta amsa masa. Sai dai ga mamakinsa cika hannunsa tayi gami da kanƙame shi tana kuka sosai. Jikinsa ya ƙara sanyi. Da ƙyar ya cika ta ya fita yana mai waiwayenta.

Malam ya dube ta, tashi ki shige ciki sai gobe zan kaiki can, yanzu bazan iya fita ba. Banza ta masa hakan ya saka shi tunawa dawa yake magana. Kaɗa kai ya yi gami da kwala ma ɗaya daga cikin matansa kira, ta zo ta shiga da ita ciki.

Da misalin ƙarfe 4:30 Na dare.

Tashi ke, tashi maza na taimake ki. Faɗime ta buɗe ido tana son kwashewa da dariya matar tayi saurin toshe mata baki.

“Shiga hankalinki, Indo ce ni matar Malam. Zan buɗe miki ƙofa ki fita ki yi ta gudu kinji. Wallahi kika tsaya har Malam ya kaiki gidan mari to idan baki fito da goyo ba, zaki fito da wannan annobar cutar mai karya garkuwar jiki. Tashi maza ki mini shiru kuma”.

Faɗime ta yi tsit tana zare ido cikin duhun ɗakin..

Da sauri matar ta ringa fincikar hannunta har zuwa ƙofar fita daga gidan. A hankali ta zare sakatar ƙofar tana kallon Faɗime cikin tausayi.

 “Ki yi ta gudu kinji. Karki tsaya a ko’ina sai kin fita daga ƙauyen nan.” 

Ta furta tana hankaɗa ta wajen, ta mai da sakatar ƙofar. Runtse ido ta yi hannuwanta bisa ƙirji tana maida numfashi…

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×