Skip to content
Part 24 of 37 in the Series Fadime by Fulani Bingel

“Ba ni na kashe shi ba! Wallahi ba Ni ba ne! Haka na zo na same shi kwance a ofis din! Sagir ya furta da ƙaraji yana kallon murɗaɗɗen baƙin ɗan sandan da ke tsaye a gabansa. Awansu biyu da zuwa suna ta gwaje-gwajensu, suna ƙoƙarin saka shi ya amsa lefin da bai ji ba, bai gani ba.”

“Babu mai lefin da ke amsa lefinsa a karon farko…” Ya furta yana ɗora karan sigari a saman manyan laɓɓansa, ya kunna ya mata kyakkyawar zuƙa, ya ɗago yana mai fesar da hayaƙin a saman jiƙaƙƙiyar fuskar Sagir.

“Dole dai ka saka ni karya doka. Shan Taba a yayin a aiki ba. Sajen Luka! Me ma nake cewa?”

Wanda aka kira Sajen Luka ya matso da sassarfa gefen kunnensa.

“Cewa ka yi babu mai lefin da yake amsa ya yi lefi idan bai ji durum ba.”

“Yauwa! Na kuma daɗe da haddace kalmar nan daga bakin duk wani mai lefi irinka. BA NI NA AIKATA BA…Kiran mu da ka yi ka ba mu rahoton ka tsinci gawa a ofis dinka, ba shi ne zai hanamu tuhumarka ba, tunda dai gawa ba tada ƙafa balle ka ce takowa ta yi ta zo ta same ka. Kuma da ke kai take so da arziƙi, sai ta tsallake kaf malaman makarantar, da office din Headmaster ta zo naka. To a ƙa’ida ma kai ne na farkon wanda za a fara zargi. Kuma a laifi, kowa ma zai iya zama abun zargi har sai shari’a ta tabbatar da saɓanin haka.”

Ya yi shiru yana sauke kansa kan Sajan Luka, da sauri ya tabbatar da maganarsa ta hanyar gyaɗa kai tare da cewa

“Gaskiya ne Oga.”

Sagir ya ji rayuwar gabaɗaya ta masa zafi irin wanda bai san a ina zai saka kansa ba ko kuma da ace zai ga wata ƙofa da zai bi ta cikinta ya shige, to ko da lahira za ta kai shi zai bi ta a kan dai a ɗaura masa wannan lefin.

Oga ya bi ofishin da kallo na ƙurulla a karo na kusan goma, kamar wanda ke neman allurar da ta ɓace a cikin rairayi, sai dai  shi hujja yake nema, a crime scene kuwa komai zai iya zama hujja.

“Sajan Luka ka kira Forensic Team su zo su tattara duk wani evidence a je a yi analysis, amma kafin nan ka fara sakawa mutumen nan ankwa.”

Sagir ya ɗago a tsorace yana kallonsa, jikinsa har ya fara rawa, ankwa? Duk wannan girman da yake da shi, ankwa fa ? Bai za ci al’amarin zai kai haka ba, ya ɗauka suna zuwa za su taya shi binciken yadda akai gawar ta zo ofis ɗinsa, ashe dai lamarin ya zarce duk wani mummunan al’amari da ya taɓa riska a rayuwarsa girma.

Sajan Luka ya nufo shi da ankwa, a lokacin ne  ya ji nadamar kiransu ta sauko masa, ji ya yi kamar ya daka uban tsalle ya haure ta ƙofa ya bar gurin, kai da garin ma gabaɗaya, amma jikinsa ya ƙi ba shi haɗin kai, sai kawai ya sadda kai cikin rashin sanin abin cewa.

*****

Faɗime tana zaune ita kaɗai ta fara jin kamar ta yi kuskure da ta tabbatarwa Sagir bai isa komai ba, ta kuma bar Abbati ya koma makarantar nan. Haka kawai ta ji zuciyarta na mata guɗa da faruwar wani mummunan al’amari, gabaɗaya hankalinta ya ƙi kwanciya, da ta sani take dama ita ta kai shi ba Linda ba, yanzu idan ya sace mata yaro fa? Ba ta jin ko Dattijo Murad zai iya karɓo mata shi, ji ta yi ba za ta iya ci gaba da zama ba. Musamman da wata zuciyar ke da ɗa jaddada  mata ta yi wauta, ta tashi ta tafi makarantar su Abbati, idan ta je ta dawo da shi ba zai sake komawa makarantar ba, ba tare da sanin cewa ko ta je ko ba ta je ba Abbati ba zai sake komawa makarantar ba.

Wata zuciyar kuma na faɗa mata cewa kafin ta tafi ta nemi makami, da gudar zuciya ta farko da na biyu duk suka rinyayeta ta miƙe a tsaye ta nufi kitchen ta ɗauko wuka.

“Amma me zan yi da wuka?”

Tambayar da ta yi wa kanta kenan, tambayar da ba ta da amsa, ba  ta jira ba ta fice daga gidan.

Kirjinta ya ruɓanya bugawa, zuciyarta kamar ta faso kirjinta ta fito waje a lokacin da ta isa jikin gate ɗin makarantar, tana ƙoƙarin shiga kuma wata motar ‘yan sanda da aka rubuta forensic unit a jiki tana ƙoƙarin cuso kai, ta kauce ta ba su guri suka shige kafin ta bi bayansu.

Duk da cewa makaranta ce da a irin wannan lokacin ake samunta shiru ba hayaniya kamar sabuwar unguwa amma ta cika da mamaki lokacin da ta ji hayaniya a farfajiyar makarantar kamar a gidan kwallo.

Ta tafi da sauri, jikinta na rawa, zuciyarta na ci gaba da raya mata abubuwa marassa daɗi.

Sajan Luka ya cukumo kugun Sagir kamar ya samu gayan fura a lokacin da ‘yan sanda uku biyu maza ɗaya kuma mace daga Forensic Department suka ɗuro gurin.

“Yauwa Musa kun zo? Nan ne crime scene din, ga wanda aka kashe can, wannan kuma…”  Ya nuna Sagir

“Shi ne suspect ɗinmu na farko.”

“Wallahi ba ni na kashe shi ba. Ga sauran malaman nan ku tambaye su mana, koda ba su ga shigowata ba na tabbata ba za su ƙi ganin shigowar yaron ba. Wai malami ne zai iya kashe ɗalibinsa?”

“Aww aikinmu za ka koya mana, a garin Lagos uba na kashe uwarsa ma bare malam da ɗalibi.”

Sajan Luka ya furta yana shirin ɗaga hannu ya kwaɗa masa mari, Faɗime ta duro gurin ta katse masa hanzari.

Jikinta na rawa, wuƙa a riƙe a hannunta tsirara kamar an haska fitila an ɗauke haka ta kalli abun da ke faruwa a gurin, da hanzari ta nufi Sagir.

‘Yar sandar da ke gurin ta yi saurin riƙe ta.

“Shi kenan, burinka ya cika ka kashe mini Abbati, ka kashe ɗanka na cikinka wanda dama ba ka sonsa, ka daɗe kana son ka kashe shi tun yana gudan jini, shi kenan sai ka kashe ni ni ma, ko kuma bari na kashe mu tare.”

Ta furta  cikin rashin hayyaci da tsananin baƙin ciki, idanuwanta sun zaro kamar su faɗo ƙasa, ji take kamar ana kaɗe tunaninta, kamar ba a tsaye take a raye ba, kamar cin hatsin tsuntsaye haka take saurarar maganganunsa, ga bakinsu na motsi amma bata fahimtar me suke cewa. ‘Yar sandan ta yi baya a tsorace tana kallon yanayin ta. Faɗuwar wuƙar suka fara ji kafin ita ma ta bi bayanta.

Malaman huɗu har Headmaster da ke gurin suka dubi Sagir da ɗumbin mamaki.

“Ko kun gane me wannan ke faɗi?”

Ya furta yana sauke idonsa kan Luka.

“Oga tana ba da tabbacin ɗansa ne ya kashe, dama yana da burin kashe shi, tun yana ciki.”

“Amma ka ma raina mana hankali. Kai dama kasan kai ne ubansa kake ta mana yawo da hankali?”

“Wallahi ba ni na kashe shi ba, ya za ai na kashe ɗa na? Ni kaina yadda kuka samu labarin ɗa na ne, a yanzun na samu, bansan ina da wata alaƙa da shi ba.” Ya furta cikin rashin sanin madafa, tun sa’adda Faɗime ta tabbatar Abbati ɗan sa ne ya ji duk wani fatar duniya kuma ya kau daga zuciyarsa. A tsaye ƙeƙer yake magana.

“Amma ba a taɓa cin mutuncina irin haka ba, kai ban ma taɓa samun mutumin da ya laƙanci rainin hankali ba irin ka. Ba ka san ɗan ka ba ne sai yau? Saboda ka ɗauke mu abokan wasa? Sajan Luka mu tafi da shi yana ɓata mana lokaci. Kana kai shi ka tabbata an masa wankan ruwan gishiri kafin na ƙara ganinsa, lefin ka ne idan anjima kuma ya ce bai san ya kira mu ba. A ladabta shi sosai yadda zai koyi magana.”

Ya juya kallonsa kan ‘yar sandar “Madam Merry ki bar su Musa su yi aiki a nan, ki taho mana da sumammiyar matar nan, mun samu evidence na farko. Sannan ko tsuntsu ne in dai ya shekara 16 a gwada Thumb print ɗinsa.  A rufe makarantar zuwa lokacin da za a gama duk wani bincike.”

*****

Zuwa dare ya bar rantsuwar da ba shi ya yi ba, ya koma zubawa sarautar Allah ido.  Sai yanzu ya san duk dadinka da mutum, kuskure ɗaya tak! Za ka iya iya yi ka gane waye shi a rayuwarka. Faɗime dama ba shi da wani hope kanta, yaronta a kashe, yaron da silarsa ta bar rayuwar dadi ta tafi inda bai sani ba, amma bai za ci har abokan koyarwarsa ba. Gabaɗaya sun maida shi dodo, mai makarantar kansa ya furta nadamar ɗaukarsa aiki yake tunda gashi rana ɗaya yasa an rufe masa karanta. Ya kuma aje masa tarihi mai muni na kisan yaro Ɗalibi a cikin shahararriyar makarantar tasa. Sai dai shi yanzu duk ba wannan ne damuwarsa ba. Abu biyu yake fata ace sakamakon kome ya fita babu shaidar yatsunsa jiki. Ya tabbata a lokacin ne duk wani cin kashi da yan sandan ke masa zai ƙare. Kai bai taɓa ma sanin haka lefin kisa ke da girma ba irin yau da aka cakume shi aka jefa shi a wani a kurki shi daya tal! A bayan an jirkita masa kamannin fuskarsa saboda yana ba da amsa iyakar gaskiyarsa. Ga wasu can nasu case ɗin wani yaro suka kwakwalewa ido amma aka haɗa su cikin ɓarayin kajin unguwa. Shi kuwa da ke bahaushe ne ba yoroba ko igbo ma sai aka cusa shi a wani ƙazamin ɗaki da ko numfashi baya iyayi sosai. Abu na biyu kuwa tausayin Faɗime da ya cika zuciyarsa. Tun bayan da ta farfaɗo ta daina magana sai bi da ido, ko da wata fara ta zo da yake yawan ganin tana kawo Abbati makaranta babu abinda ya canja. Dole tasa yanzu aka yi babban asibiti da ita. Abin ya cukurkuɗe masa gabaɗaya, burinsa guda ace kar ya kwana gun nan. Fatansa guda ace zuwa dare duk wani gwaji ya ƙare, an sallame shi, an kuma tabbatar masa da za a gano me kisan, ko waye ya kashe Abbati ya kai shi ofis ɗinsa wallahi ba zai yafe ba. Ko waye kuwa sai ya saka shi ya girbi abinda ya shuka.

Ƙarfe 8:00 daidai aka dangwarar da shi gaban murɗaɗɗen ɗan sandan safen nan. Sai dai wannan karon fuskarsa da yar rahma yake dubansa, yana nazari kamar mai lissafa masa kwanakin da suka rage masa a duniya.

“Ba dan zaman kotu dole ba ne da na ce daga nan kawai ka ce a wuce da kai in da za a rataye ka. Abin naka sam ba dabara. Kyakkyawa kamar bai kamata ka ƙare a rataye ba.”

Luka ya furta a daidai kunnensa sa’ilin da ya ga hankalin ogan na ga kan takardun gabansa.

Shi kam sadda kai ya yi yana ƙara mamaki. Luka ba ta inda yake kama da Hausawa, amma hausar bakinsa ko jakin Kano albarka. Kodayake zaman Lagos kamar bariki ne, ƙalilan ne ba zuwo ne.

“Ba sirinjin ne kawai ne ya fito da zanen hannunka ba. Har takalmin makarantarsa da uniform ɗinsa tambarinka ne kawai a jiki. Kome da kome ya nuna shaidar yatsunka. God forbid! Me yaro ƙarami ya maka da za ka masa mummunan kisa haka. Ya kamata ka amsa lefinka ba sai kana wahalar da jama’a ba.”

“Oga ai kamar ya suma.”

Luka ya furta yana leƙa fuskar Sagir da ke sanƙame, babu wani alamar bugun zuciya a tattare da shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fadime 23Fadime 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×