Skip to content
Part 32 of 37 in the Series Fadime by Fulani Bingel

M akarfi

“Yayan Ammy ni ma ka fesa mini turaren irin naka.”

Murmushi ya yi ya rage tsawonsa daidai shi, ya ɗaga hannunsa ya fesa masa turaren gurin hammata, suka kyalkyale da dariya a tare.

“Gashi nan duka na baka shi, maza kaiwa Umma ta saka maka cikin kayan ka.”

“Me za a kawo mini?”

Ta furta tana yaye labulen ɗakin. Sai kuma ta yi turus tana kallon yaron, ya yi kyau sosai cikin Uniform ɗinsa Ja da Fari, a sanyaye ta ƙarasa shigowa ɗakin.

“Ni kam banga dalilin da za a ce yaro kamar wannan da ko tsarkin kashinsa baya fita sosai wai makarantar kwana za a saka shi, ba ma a nan ba, sai an tafi wata uwa duniya Sokoto. Wannan abokin naka da ya yi sanadin karatun nan bai ji daɗin halinsa ba, ji wai wannan Uniform ne, sai ka ce na masu aiki a Mutuware, ja da fari, ina aka taɓa ganin kalar kayan makaranta haka?”

“Umma zamanin kenan ai. Ki daina damuwa Allah kuwa, kinga dai yanzu shekaru 8 yake ko, to sa’adda zai cika shekara 12 ya sauke Alkur’ani ya haddace rabinsa, Ni shi ne ma sha’awata da makarantar ba bokon ba ce zalla. Ki saka mana albarka kawai, ita muka fi buƙata.”

“Um um, ai gwara ka ce mini Makarantar Allo za ka kai shi, to suma yaran da ake kawo wa Allon sai su shekara biyar ba su gama Sabbi ba bare a tafi izifi guda.”

Dariya ya yi sosai, Abbati na taya shi.

“Ni dai Umma ki naɗe mana kajin sosai da Dambun Naman yadda dai ba za su yi kome ba. Can ɗin duk wani abu da kika san yaro zai bukata ko za a masa akwai masu yi. FADIL INTERNATIONAL SCHOOL Kenan, makaranta ce da babu ta biyun ta kaf! Nigeria.”

“Ai fa na ji. Ga kayan naku nan, Allah ya tsare ya kai ku lafiya.”

Ta furta tana shafa kan Abbati.

Fitowa suka yi gabaɗaya, sai da ta raka su har ƙofar gida tukunna ta dawo ranta fal kewar yaron.

“Yayan Ammy yanzu shi ke nan ba zan ƙara ganin Uncle Slim ba?”

Shiru ya masa yana jin wani yanayi a ransa. Fiye da sati kenan babu ranar da za ta fito ta faɗi bai ambaci Uncle Slim ba. Shi kam ko dan ya manta shi dole ya ƙara nesanta tsakaninsu.

“Ba ka tuna Ammynka sai Uncle ko?”

“Ina tuna ta ai nasan ita za ta zo, shi Uncle shi ne bai san zan tafi ba. Uncle nada kirki, yana so na yana son Ammy na.”

“Ni ma ina son ka, ina son Ammynka.”

Ya furta yana harba motar da gudu kan titi. Hankalinsa na ga mudubin motar ta waje, so yake ya gama fahimtar waɗanda ke bayansa. Sai dai bai ga alamar wani na biye da shi ba. Murmushi ya saki mai kyau. Ya sani yadda ya canja takunsa ko Aljani ne ke binsa bai isa ya gane ba. Duk wani abu da ya yi cikin satin ko mahaifiyarsa bai bari ta sani ba, kome da wani irin sirri ya aikata. Shiyasa hatta Sokoton ba a mota zai je ba, ba zai ma iya ba. Kano zai je su hau jirgi, ya riga da ya gama kome. Sanin hakan ya saka shi ƙara kwantar da hankalinsa yana tuƙinsa, jefi-jefi Abbati na masa surutu.

Ko da ya isa cikin ƙasa da minti talatin ya ƙarasa sauran abubuwansa suka zauna jiran jirgin da zai dawo daga Lagos.

Tunawa ya yi bai yi waya da su Fati ba, ya duba Account ɗinsa ya sai kati ntwrk ya ƙi, dan haka ya tashi ya fito ganin da sauran lokaci. Bai san Abbati ya biyo shi ba sai da suka fito reception, hannunsa ya riƙe ya zaunar da shi kan wata doguwar kujera ya ce ya jira shi ya dawo kar ya fito waje. Shi kuma ya juya ya fita.

Ba daɗewa ya dawo, idanuwansa na saitin inda Abbati yake sai dai wayam babu shi. Zagaya gurin ya fara yi babu shi babu alamarsa. Cikin tashin hankali ya fara tambaya har mai tsaron kofar reception sanin ba sa bari a shiga sai anyi da gaske, amma suka ce ba su ga fitar yaro ba, suma sun ganshi a zaune. Hankalinsa bai dugunzuma ba sai dai ya ga duk an bazama neman yaro amma babu shi babu alamarsa. Jikinsa karkarwa kawai yake yi. Bala’i yake yi da masifa ta ko’ina na sakacinsu. Wane irin shashanci ne da za a shigo har cikin Airport a yi kidnapping yaro. Wane irin rashin tsaro ne haka. Su dai kawai haƙuri suke bayarwa. Ƙarshe dole babbansu ya fito ya rarrashe shi da cewar tunda har yaron ya shigo ciki. To kuwa Camera za ta nuna kome, ya yi haƙuri za a duba aga inda yaron ya shiga, amma yanzu wanda ainihin ke kula da camerar baya nan. Ya bari zuwa gobe. Goben daya ambata ya saka shi shaƙe shi har sai da ya haɗa shi da wata ƙofar glass. “Saboda ba kai ka haife shi ba dole ka ce gobe, a sani na kai ne babba, har wani babba gare ku me kula da Camera, wlh summa tallahi Idan wani abu ya samu yaron nan gunduwa-gunduwa zan yi da sassan jikinka.”

Da ƙyar masu tsaron gurin suka ɓambare shi a hannunsa. Yana tari ya kalli wani dogon mutum. “Ka rubuta ya furta cewar zai yi mini wani abu. Idan wani abu ya same Ni daga nan har shekaru goma to shi ne, tunda bai ji kunyar furfurata ba. Bai kuma fahimci kowa da aikinsa ba. Ba muda haƙƙin duba Camera sai mamallakinta wanda ta rataya da a wuyansa ya zo. Da zan roka masa alfarma mu gani ko zai zo a yau, ko kuma goben ma mu samu tabbacin zuwan. Tunda ya yi tsageranci ku bar shi da iyawarsa.”

Daga haka ya yi juyawarsa, wasu na rokarsa ya masa uzuri ɗansa ne fa ya bace, ko waigowa bai yi ba bare su suka ran zai saurare su.

A ransa ya ji tabbas da haɗin bakin wasu a gurin aka ɗauke Abbati, ko kuma Abbatin ba zama ya yi ba, ya sake biyo shi, su kuma an gama biyansu suka ba shi hanya ya wuce, yana fitowar kuma aka ɗauke shi. Dan haka ya jawo wayarsa da sauri zai yi abinda ya kamata duk wani da aka tauyewa haƙƙi ya yi, wato shigo da Yan Jaridu cikin lamura. Yanzu za su sa labari ya fashe ya isa har London, ya sani cikin awa guda za a iya buɗe ɗakin Camera su ga kome, makawar suka ga yan jaridu sun watsa labarin kidnapping a cikin Airport.

Sai dai wata gudumar tunani da ta dake shi a tsakiyar kwalwalwarsa ya saka shi lalubar kujera ya zauna a hankali bakinsa na ambaton Allah. Yana ji Ɗan Jaridan da ya kira na Hello! Hello amma ya sauke wayar yana mai tsura mata ido. Yana cikin tsaka mai wuya. Ba wai ɗan jarida ba, kai ko Social Media labarin nan ya je to fa kashinsa ya bushe, ya manta shaf, ya manta cewar yaron da ake maganar shi ma za a iya cewa kidnapping ɗinsa ya yi, haka matacce ne a gurin wata al’umma can. Kenan watsa labarin daidai yake da fallasuwar asirinsu, labari zai fita cewar yaron da ake shari’ar mutuwarsa a Lagos, gashi nan kuma a Airport ɗin Kano anyi kidnapping ɗinsa. Wani abu ne da ba kowacce kwakwalwar hankali za ta ɗauka ba. To ma ko menene su suka janyo. Dan haka shi kaɗai ne zai nemi masu aika-aikar. Shigar wasu cikin lamarin ba zai haifar musu da ɗa mai ido ba. Koma su waye ya sani ba zai wuce mutanen da ke bibiyarsa ba suka san kome kamar yadda Fati ta ba shi labari. Kenan ta can za a fara, dole can zai koma ya tatsiyeta ko za ta iya tuna wanene, abin ba na waya ba ne, haka gobe ne zaman kotu na ƙarshe, ya mata maganar batan yaron a yanzu ba zata nutsu ba, gwara ya je, ya samu zaman kotun shi ma. Dan haka a hankali ya tattara kome nasa ya sulale daga Airport ɗin ba tare da ya ƙara amsa tambayarsu ko guda ba. A ransa yake neman tsari da koma wanene, duk da yasan ba abinda za su yi da yaron, akwai dai wani abun da suke buƙata. A hankali wani tunanin ya sake burtso zuciyarsa, kar kuma ba waɗanda suke za ta ba, kar kuma ya zamana wannan Baristar ce da kullum kwanan duniya Linda ke jaddada masa tsanarta da ita, ta zo ta ɗauke yaron dan gobe ta samu kyakkyawar shaida da shi. Girgiza kansa ya yi da sauri ƙirjinsa na duka tuna hakan ba zai taɓa faruwa ba.

L A G O S

22 December 2019

Jan jambaki ta shafa ta ƙara kallon mudubin, sai kuma ta ganta kamar gajeruwar Rihanna, haka ba fa party za ta je ba, kotu za ta je, dan haka ta goge da sauri ta ɗauko pink, kalar flowers ɗin doguwar rigar da ke jikinta ta shafa, ta murza bakin ya zauna mata saisa-saisa, bakin ne ba fasali ita kanta ta sani, dan ma yarinyarta Lisa ta tabbatar mata irin manyan laɓɓanta maza ke ya yi yanzu. Rabbit Teeth ɗinta kuwa wasu mazan har googling suke yi suna neman mata masu irin sa. Wai arziƙi ne, kuma sun fi iya soyayya. 

Murmushi ta yi tana washesu a gaban mudubin, wani farin ciki take ji tunda ta gama haɗa dukkan bayananta, har abinda bata zata ba duk ta samu. Yau rana ce da za ta wanke masoyinta ta fidda shi kunya, ta tozarta wacce ta tozarta shi. Lumshe idanuwanta ta yi tuna ƙila jumma’a ta sama tana kwance ƙirjin Sagir a matsayin matarsa. Sakin tunanin ta yi ta ƙarasa ga rigarta ta lawyers ta ɗauka ta rataya a gefen kafaɗarta. Turarenta ta duba sai dai wayam babu shi, tsaki taja ta san Lisa ta ɗauke. Duk da ta fesa kusan kwatar gwangwanin Body Spray amma bai mata ba, ba za ta iya zuwa gaban Sagir tana kamshi ɗaya ba, babu ƙamshin wanda ta san ko wanine ya saka ya gifta ta kusa da shi zai tunata saboda tsabar yadda ya zauna a jikinta. Dan haka ta tattara files ɗin da sauran tarkacenta ta zari mukullinta ta fito da sauri dan ta isa shagon sai da turaren, daga can bayan ta fesa a mota sai ta ƙarasa kotun.

*****

Ƙarfe 11:00pm daidai aka zauna shari’arsu.

“Lauyoyi masu gabatar da ƙarar nan suna nan?”

Alƙalin ya furta bayan ya gama nazarin inda aka tsaya a shari’ar.

Barr. Jagazi ya miƙe ya gabatar da kansa. Barr Zuby ma ta miƙe ta gabatar da kanta suka zauna.

“Muna saurarenku, ko kuna da wata hujja da za ku gabatar gaban kotu dan tabbatar da tuhumar da kuke masa?

Barr. Jagazi ya miƙe.

“Akwai mu da wasu hujjojin gamsassun ya mai sharia, muna neman alfarmar kotu dan mu gabatar da shaidarmu ta uku.”

“Muna saurare.” Alƙalin ya furta yana ci gaba da rubuce-rubucensa.

Madam Chiboke, doguwa, zabiya me faffaɗar fuska, ita ce ta taso ta tsaya a akwatin shaida. Clerk (magatakarda) ya biya mata rantsuwa, ita kuma ta ɗaga hannunta na dama tana maimaitawa.

“Madam Chiboke, ko za ki yiwa kotu bayanin inda kike zaune?”

“Ina zaune a C. Low-cost.”

“Ko kin san wannan da ake tuhuma?”

“Na san shi sosai, maƙocina ne, gidana na jikin nasa.”

“Madam, ko za ki iya maida zuciyarki baya zuwa ranar Tara ga watan Satumba ki yiwa kotu bayani akan ranar?”

“Ranar na tashi Chiboke ya mini fitsari, dan haka da sassafe na fito na wanke kayan. Na je Balcony shanya na ga fitar Sagir a motansa. Lokacin bai fi 6:40am, bantaɓa ganinsa a irin lokacin ba. Sai na yi mamaki da na sake ganinsa wurin 9:15 zai sake fita, a lokacin ina kofar gida Chiboke na wasa da Ball ya bi motar ta kan Ball ɗinsa ta wuce.”

“Ke nan ba ki ga lokacin da ya dawo ba bayan fitarsa ta ƙarfe bakwai, sai wata fitar kika ƙara gani ?”

“Gaskiya ko ƙarar mota ban ji ba.”

“Madalla.”

Ya furta yana komawa gaban Alƙali.

“Ina roƙar kotu ta yi duba da wannan shaidar ta yi hukunci bisa adalci. Anan ya nuna Sagir yasan Madam Chiboke na sane da shige da ficensa, dan haka ya yi amfani da wannan duku-dukun safiyar domin ya fita ba tare da wani ya ankara da shi ba, duk da sai 7:30am ya isa makarantar. Inda ita kuma Allah ya bata sa’ar ganinsa ta dalilin fitsarin da yaronta ya mata. Haka ya dawo gidan a sace, hakan ya nuna sai da ya daidai ci babu kowane mahaluƙi kusa tukunna ya ƙarasa. A fitarsa ta biyu kuma sai da ya daidai ci tana waje, ya fito domin ya tabbatar mata da lokacin ya fita, bai san cewa ta ga waccan fitar ba. Idan aka yi duba da haka za a gane barin irin su Sagir a ƙasa irin tamu ba ƙaramar annoba ba ce, tunda har ya san ya shirya ta’asa irin haka ta hanyar canja dukkan tunanin wani da zai zarge shi. Dan haka ina roƙon kotu da ta ɗauki hukunci mai tsauri kan Sagir, a bayan ta gama duba wannan shaidar mai ɗauke da tambarin yatsunsa da ke bada tabbacin Sagir ne ya yi kisan.”

Ya furta yana aje file ɗin gaban Alƙali.

Alƙali ya yi nazarin takardun.

bayan kammala ‘yan rubuce-rubucen shi, sai ya bawa Barr. Cingam dama dan gabatar da nata tambayoyin ga Madam Chiboke.

Miƙewa ta yi ta ƙarasa inda take.

“Madam, shin ko kin haɗa ido da Sagir a lokacin da zai yi fitar farko?”

“A’a, ai bai ganni ba.”

“Ba ki ga fuskarsa ba?”

“Ban gani ba kasancewar ya saka facing cap.”

“A matsayinki na makociyarsa ma fi kusanci, kenan kina kiyaye da dukkan shigarsa. Ko kin taɓa ganinsa da facing cap?”

“Aa, gaskiya, shigarsa na yarensu yake yi. Ban taɓa ganin shi da hula ba.”

“To ta yaya kika tabbatar shi ne a motar?”

“Saboda shi kaɗai ke kwana gidansa, ban kuma taɓa ganin wani da motarsa ba. A fitansa na biyu ai mun haɗa ido da shi.”

“Okay kenan Sagir bai da abokaina?”

“Gaskiya ban taɓa ganin wani ya zo masa.”

“Na gode.”

Ya furta tana komawa gaban Alƙali.

“Iya tambayoyin mu ke nan ya Mai Shari’a, sai dai idan an ba mu dama za mu gabatar da wata shaidar. Wato Mr. Samuel”

“Muna saurare.” Alƙalin ya furta.

Mr. Samuel ya fito ya tsaya, aka sake bashi rantsuwa ya maimaita.

“A baya ka ce daga ƙarfe Tara zuwa Goma Sha Ɗaya kana ta sintiri zuwa banɗaki shi ya sa har Sagir ya shigo ba ka sani ba, ko za ka iya tuna abinda ka ci na ƙarshe a ranar?”

“Eh zan tuna, Cake na ci, ban fi mintuna arba’in da ci ba na fara zarya Toilet.”

“A ina ka sai Cake ɗin?”

“Ba siya na yi ba. Yaron da ya mutu ya ba ni. Na tuna lokacin da Auntynsa ke ce masa ba zai ba Ni Cake ɗin ba. Sai ya miƙo mini duka.”

“Wace Auntyn tasa?”

“Wacce ke yawan kawo shi makarantar. Linda Sunanta, mun saba da ita.”

“Okay, kafin ranar ko akwai wata rana da yaron ya taɓa baka cake ɗin?”

“Gaskiya bai taɓa ba ni, gun yara ma nake ji Uncle Slim(Sagir) yake yawan kaiwa ya saka masa rikici su ci tare.”

“Da kyau, na gode.”

Ta furta tana komawa gaban kotun.

Ina roƙon kotu da ta ba ni dama domin kiran Linda ta amsa wasu tambayoyin.

Kotun ta yi tsit, da yawan mutanen tunaninsu ya nausa na abinda za ta yi kuma. Shi kansa Barr. Jagazi juya bironsa kawai yake yi ya kasa gane kome. Haka Sagir da ya tsura mata ido yana mata duban mamaki.

Linda kuwa tunda Samuel ya ambaci sunanta ta fara gumi. Sai da Faɗime ta matse hannunta ta fara shiga hankalinta. Da ƙyar ta iya miƙewa tana taku da ƙyar bayan an ƙara kiran sunanta ta je ta tsaya a kanta, aka biya mata rantsuwa ta maimaita.

“Ko za ki faɗawa kotu sunanki?”

Barr. Zuby ta furta bayan ta isa ganta.

“Linda Oboy Oyororo.”

Ta furta tana tattaro ƙarfin halin duniya ta ɗora a fuskarta.

“Madalla, Linda ko za ki iya maida zuciyarki baya zuwa ranar Tara ga watan Satumba ki yiwa kotu bayani akan ranar?”

“Ba zan taɓa mantawa da ita ba ai, ranar yaron yar uwata ya rasu, Ni ce kuma da kaina na kai shi makarantar da ta yi silar mutuwarsa.”

Ta ƙarashe tana rushewa da kuka.

Barr.Zuby ta yi murmushi tana miƙa mata hankacif.

“Bari kuka haƙuri za a yi, share hawayenki.”

Ƙirjinta ya buga ya sake bugawa ganin hankacif ɗin ta sak! Cikin ƙarfin hali ta karɓa ta share hawayenta tana harararta ta ƙasan ido.

“Kusan kullum ke kike kai shi makaranta kuna wucewa ta gaban Samuel ba ki taɓa masa wani alheri ba. Ko menene dalilin da yasa ranar kika umarci Abbati da ya bashi cake ɗinsa?”

“Saboda dama ba na Abbatin ba ne, shi Ammy ta yiwa ta ce idan mun je a bashi.”

“Duk abincin duniya a rasa me za a masa sai cake? Kuma a saka a cikin lunch box na yaro?”

“To ai, um to, ai ganin ana yawan yiwa yaron yana gani shi ya sa aka masa nasa ranar.”

“Sai aka zuba masa abin gudawa ciki? Shi ya sa kika hana yaron ci?”

” Flour da aka yi amfani da shi ne ya ɓaci, amma babu wani abu da aka sa ciki. A wane dalili ma za ai hakan?”

“Good! Kenan dai kin yarda cake ɗin ya lalatawa Mr Samuel ciki tunda gashi kince flour Bai da kyau. Kin san bai da kyawun kenan?”

Shiru ta yi cikin rashin sanin abin cewa.

“Okay to a bar batun Cake. Ko za ki iya tuna inda kike da misalin ƙarfe 6:40 na ranar?”

“Ina gida ina barci.”

“Motarki kuma na UTurn na biyu da zai sadaki da C.Low cost?”

Ɗif ta yi jin yawun bakinta na kafewa.

“Ban gane ba.”

“Za ki gane, yanzu zan miki dalla-dalla.”

Ta furta tana komawa tsakiyar kotun.

“Ya mai sharia, wannan da kuke gani ita ce ta aikata kisan tare da sa hannun wani da ban a san wanene ba sai dai ita ta fito da shi. A washegarin ranar ta haɗu da Sagir a gidan abinci wanda dama saboda shi ta je. An kawo musu abinci inda ita kuma ta tashi ta karbo musu lemo anan ne ta zuba masa abinda ya fitar shi hankalinsa har bai san sa’adda ya je gida ba, inda ya bar ƙofar gidansa a buɗe. Da duku-duku ta je gidan ta ɗauki mukullin motarsa ta kuma yi amfani da safar hannu gurin sakawa Sagir sirinjin a hannunsa ya taɓa a halin barci, anan wanda ke taimakonta ya kare fuskarsa da facing cap shiyasa Madam da Mr ba su ga fuskarsa ba. Ya shigo makarantar da karfe 7:30 dan kowa ya za ci Sagir ne, inda ya zauna a can har Linda ta kawo masa yaron suka yi masa Allurar suka aje sirinjin agurin, kana ya sake fitowa ya dawo gidan Sagir ya aje masa motarsa, suka tafi. Sai dai ya yi kuskuren barin rigarsa ta sanyi a cikin motar, mai dauke da kuɗi adadin dubu goma. Gasu. Ta furta tana aje rigar gaban Alƙali.

“Kai I swear ƙarya ne, ya za ai na kashe yaro na!”

Linda ta furta da ƙarfi.

Ba ta saurareta ba ta ci gaba.

“Ita kuma ta yi kuskuren manta wani abu da bansan mene ba, inda ta koma gidan ta hanyar mukullin da ta yi irinsa, ranar da nima na je gidan ta. Anan kuma tasha lemo ta barshi, na ɗauka na haɗa da hankacif ɗin ta da mukullin da ta jefar a ƙofar gidan ya zama iri ɗaya. Irinsa ne kuma aka gani a wani sassan jiki na yaron da ke nuna ita ce ta yi Allurar da hannunta. Ga shaidar kome a cikin file ɗin nan.”

Ta furta tana ɗaukar file ɗin ta aje a gaban Alƙali.

Alƙalin ya buɗe file ɗin, a hankali ya sa hannu yana zare gilashi me ƙara karfin gani dake fuskarsa.

“Dan haka ina roƙar…”

“Ɗaga mata hannu da Alƙalin ya yi ya sakata yin shiru. Ɗago file ɗin ya yi gabaɗaya ya juyo shi kowa na ganin. F*CK YOU! Shi ne abinda ke rubuce a takardar da manyan baƙi dara-dara.

 Kotun ta ruɗe da hayaniya. Wani gumi ya tsargoma Zuby tun daga farkon tsiron gashinta take jinsa har cikin rigar mamanta. Ba Sagir kaɗai aka taɓa ba, hatta aikinta an taɓa!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fadime 31Fadime 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×