Skip to content
Part 34 of 37 in the Series Fadime by Fulani Bingel

Mintuna biyar kwarara suka shuɗe cikin kotun ana ta hayaniya da salallami. Daga can akwatin shaida kuwa mata biyu ne tsaye kan Linda da ke ta suma tana farfaɗowa cikin sambatu. Alƙalin kansa ya dawo ya zauna bayan an tabbatar masa yaron da ya gama shari’ar mutuwarsa ne ya dawo, haka suna da ishasshen lokacin da za su saurari abinda ke faruwa.

Gudumar da ke gabansa ya buga kotun ta yi tsit! Na tsaye duk suka zauna sai Faɗime kawai ta rage a tsaye tamkar wacce aka sassaƙata a matsayin gunki, tudun ƙirjinta da ke sama da ƙasa kawai zai tabbatar maka tana da sauran numfashi.

Babban Mutum da ya fara dawowa hayyacinsa ya matso ya riƙe hannunta ya zaunar da ita, ya ɗan kalli na kusa da ita sai ya tashi, shi kuma ya zauna a kusa da ita yana mai bubbuga bayanta, a zatonsa ta shiga wannan yanayin ne sakamakon dawowar ɗanta da ya mutu. Bin sa ta yi da kallo tamkar yau ta fara ganinsa, tamkar wacce hankalinta ya gushe haka ta damƙe hannunsa har sai da farcenta ya cake shi, sai dai kan ya zare hannunsa ya ji kalaman da suka dakatar da lissafinsa shigewa cikin kunnuwansa.

“Ban cancanci ka zauna kusa da Ni ba, na san Abbati na raye, Ni na boye shi dan na hukunta Sagir, ka matsa daga kusa da ni! Ni abar ƙyamace, na saka ka kuka na saka Hajiya kuka, na..!” Haka ta dinga jere su, a hakan kuma suka suke shigewa cikin kunnuwansa ba tare da cogewa ba. Zare hannunsa da ya yi da ƙarfi ya sakata yin shiru tana ƙara yin ƙasa da kanta.

Shi kam dafe kansa ya yi da hannu biyu ya rasa kalar tunanin da zai yi. “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel” da ya fara ambata ita ta dawo da shi cikin hayyacinsa. A sannan ne kuma ya ji ita ma ta ɗauka tana janta, yana ganin yadda hawaye ke ambaliya a saman fuskarta. Yawu ya haɗiya muƙut! A lokacin da tunani na farko ya wanzu a cikin kwakwalwarsa. ‘Mintuna goma da suka wuce take shirin kisan kai! Shi ne kuma a zaune yana kuka ba ita ba. A yanzu kuma har lamarin ya juye, ita ce a zaune tana kuka, shi kuma idonsa a bushe yana kallonta. Allahu Akbar Kabiran! Lalle ne babu taɓaɓɓe sai wanda bai yarda an halicce shi ba ne domin bautawa maƙaginsa! Wannan wani darasi ne a gabansa mai girman da baya taɓa shafewa.’ Buɗe baki ya yi zai mata tambayar da bai san sa’adda ta haɗa kanta ba, sai dai maganar Alƙali ta katse shi.

“Wannan shi ne yaron da aka ce ka kashe?”

“Eh shi ne ya mai Shari’a!”

Sagir ya furta da ƙyar yana riƙe da hannun Abbati da hannunsa guda marar Ankwa.

“Uncle Slim ni fa mafarki na yi na mutu, ai ban mutum ba, ka ga Aunty Linda ta bawa Yayan Ammy ni ya kaini garinsu gun Umma, ga sabon Uniform ɗina ma har an sakani a School.”

“Ohohohomiyoyo na shiga uku! Da Allah ku yi hakuri, Ni boye shi nasa ayi, kuyi haƙuri ba zan kuma ba, Sagir dan Allah kar a kaini prison wayyo! Iya Igweeeee!”

Linda da farfaɗowarta ke nan daga suma na huɗu ta ji muryar Abbati na ambaton sunanta ta furta da ƙarfi tana doka kanta a jikin kantar. ‘yan sandan biyu da ke kula da ita suka yi saurin riƙeta.

Alƙalin ya mata kyakkyawan gargaɗin da ta shiga nutsuwarta, kar kuma ta ƙara magana idan bai bata dama ba, kana ya maida kallonsa ga mutane biyun da suka shigo da yaron.

“A ina kuka same shi?”

“Ni sunana Sergeant Luka, ina cikin ‘yan sandan da suka karɓi wannan case ɗin da aka shigar gun Ogana, da Ni ma aka fara ganin gawar yaron cikin makarantar. A jiya ne cikin Airport na Kano naga wasu mutane na faɗa da yaron. Suna hilatarsa da ya zo su tafi mamansa na kiransa, shi kuma ya ce a’a, Yayansa ya ce kar ya je ko’ina. A zatonsu babu wanda ya ankara da su dan haka suka cukwikuye yaron suka jefa a motar, to kafin su tashi da motar ne, Ni kuma muka sha gabansu a tamu motar. Anan ne kuma na ga fuskar yaron wanda a gabana aka rufe gawarsa cewar ya mutu. Na sha to ko yan biyu ne, amma kuma da na tuna yadda uwarsa ke kuka kunga kenan shi kaɗai gareta, da na tambaye shi sunansa ya faɗa mini na ga ya yi daidai da na yaron da aka ce ya mutu. Na tambaye shi a Kano yake ya ce a’a, a Lagos har ma ya faɗa min makarantarsa Little Angels, anan ne na gane wani abin aka ƙulla, dama kuma ina tune da lokacin da Malamin ke iƙirarin bai kashe shi ba, ina kuma tune da lokacin da Uwar ke kukan cewar yana son rabata da ɗanta shi ya sa ya kashe shi, kenan za a iya ƙulla wani abin dan bawa Malamin lefi. A saboda haka na kira ogana wanda case ɗin ke hannunsa na faɗa masa, shi ya ban umarnin da kar na nemi wanda ke tare da yaron, na hawo jirgi kawai na taho da shi nan Lagos, tunda a yau dama za a karkare shari’ar.

Su kuma waɗanda muka kama za su sace yaron bayani ya nuna basu ne suka kawo shi Kano ba, ba kuma su suka kirkira masa mutuwa ba. Suma amfani suka yi da damar hakan su cika umarnin ogansu wanda yake son yin amfani da yaron domin cimma muradinsa kan uwar yaron, saboda haka yake bibiyar dukkan motsinsu, inda sai a jiya ne suka samu damar ɗaukar yaron, kafin su tafi Allah ya toni asirinsu. Sai dai sun ƙi kama sunan ogan nasu sai ɗazu da safe da suka ji azaba suka iya faɗin inda yake anan Lagos. Babban Ɗan ta’adda ne, yana kuma cikin mutanen nan goma da suka taɓa harbin Commissioner of Police na ƙasa. A yanzu haka an tura waɗanda za su kamo shi.”

Kotun ta yi shiruu kowa na jinjina lamarin cikin ransa. Ita kanta Linda ta kaɗu, wato da tuni aikin nasu ya yi kyan kai, da tuni suna nan suna nadama marar amfani. Da ace wani abu ya samu Abbati a dalilin wannan shirin nata da ba za ta taɓa yafewa kanta ba. A sanyaye ta yi ƙasa da kanta. To ita ma Faɗime haka, nadama kawai ke ƙara mamayeta tana godewa Allah da ya kare mata yaro. Shi kam Sagir ƙara damƙe hannun Abbati ya yi yana jin kamar za a zo a ƙara tafiya da shi. 

“A ɗazu yaronki ya ambaci ke ce kika sa a kai shi wani garin. Ko menene hujjarki na aikata hakan?”

Alƙalin ya furta ga Linda.

Gabaɗaya Ido ya dawo kanta, jikinta babu inda baya rawa, a haka ta runtse idanuwanta ta fara magana.

“Na yi kuskure ku yafe min, Sagir ka yi hakuri. Mun yi maka wannan sharrin ne saboda kar ka ɗauki yaron, mu kuma rama abinda ka yi. Saboda kai Ammy har a cikin Yan Ta’addan BH ta zauna. Ta sha matuƙar wahala ta yadda ba ta ji zata yafe ma ba, saboda ka ji kwatankwacin zafin da ta ji ya sa muka yi haka. Ka yafe mana kar a kaini prison, I swear ba zan ƙara ba.

A karon farko da Alƙalin ya sunkuyar da kansa da wani guntun murmushi yana girgiza kai. Bayan ya gama rubutun ya sake ɗagowa yana kallonta.

“Kenan ke da uwar yaron kuka shirya hakan?”

Sagir da idonsa ke kan Abbati ya ɗago da sauri yana kallon saitin Faɗime da ta runtse idanuwa tana hawaye. Da matuƙar mamaki ya dafe saitin zuciyarsa da yake jin za ta faso ƙirjinsa, wannan wace irin tsana ce? Fati ta kashe ɗan ta a baki saboda ta nesanta shi da duniyar ma baki daya? Anya da Zuciya A Ƙirjinta?

A lokacin da Linda ta buɗe baki za ta amsa, shi kuma ya yi wuf! Ya miƙe tsaye cikin tarin mutanen da ko Faɗime bata san da wanzuwarsa gurin ba.

“Ba ta sani ba, da ni aka haɗa, da hannuna na yiwa yaron Allurar Anesthesia, da hannuna kuma na tone kabarin na fito da shi na kai shi Maƙarfi ba tare da sanin Uwarsa ba! “

“Allah ya wadaranka.”

Wani fusataccen tsoho da ke gefensa ya furta.

“Baba Ƙauna Ce Sila.” Ya furta masa a hankali.

“To Allah ya wadaran soyayyar da za ta sa ku ƙagawa mutum Sharrin kisa.”

“Ku fito da shi!”

Alƙalin ya furta.

Faɗime kam wuf! Ta yi za ta miƙe ta ƙaryata Yaya sai dai wani abu da ya kasheta da mamakin kwana ɗari da ashirin, shi ne damƙeta da Babban Mutum ya yi ta hanyar take ƙafafunta yana riƙo hannunta. Kallonsa ta yi baki buɗe, shi kuma ya girgiza mata kai, “Yayana ne fa ya yi karya dan ya kare Ni, na sani wallahi, wallahi na san kome!”

Shiiii! Ya mata alamar ta yi shiru. A cikin idanuwansa ta gane karatun. Wato idan Allah ya baka dama ko yaya take, ka yi amfani da ita. Amma kuma shin wace irin ƙauna waɗannan mutanen ke biyu ke mata. ‘Me ya sa Yaya zai ɓoye lefinta, me ya sa kuma Babban Mutum da gudan jininsa aka yiwa sharrin zai hanata tona kanta?’

“Ya ya sunanka?”

“Ibrahim Ya’aqub Maƙarfi (Yaya).”

Wato ku biyun kuka shirya kome ba tare da sanin Uwar Yaron ba?”

“Eh ya mai Shari’a, a tunaninmu ta wannan hanyar kawai za mu nuna mata ƙaunarmu, ta hanyar ƙuntatawa wanda ya ƙuntata mata… Daga haka ya zarce da labarin duka, tun daga ranar da Sagir ya ga Faɗime.”

“Wane ya canja file ɗin Barr. Zubaida?”

A matuƙar firgice Linda ta Kai kallonta saitin Oboy, ta sani ko da za a musu rangwame wannan zai iya hanawa. Runtse ido ta yi a hankali zafafan hawayen na ɗumama mata ƙunci.

“Ni ce My Lord, Ka mini Afuwa dan Allah, kar ka kaini prison ba zan ƙara ba.”

Tsai ya yi yana nazarinta Alkalin, kafin kuma ya girgiza kai, ta yiwu ƙananun shekarunta ya ƙiyasta.

“Ku kenan masu hannu a lamarin?”

“Eh mu ke nan!”

“Ina shi likitan da ya baku allurar?”

“Baya ƙasar wai ba zai dawo ba sai bayan shekara biyu.”

Linda ta furta a hankali.

Alƙalin ya duƙar da kansa yana rubuce-rubuce, kafin kuma ya ɗago.

“Linda da Ibraheem, a sakamakon kama su da laifin cosipiracy, forgery giving false in formating da causing false injuries da attempt to commit culpubale homicide a section 88 penal code, kotu ta yanke musu zaman gidan yari na shekaru goma sha huɗu (14). Shi kuma Likita kotu za ta fidda takardar sumame da kuma wacce za a kai wajen aikinsa.”

Wani ihu da timuwa da Linda ta fara ya ja hankalin ɗaukacin jama’ar gurin, kuka take tana roƙar Alƙali da ya rage musu shekarun, tana roƙar Sagir da ya saka baki bata san cewa shi kansa bai da hakkin saka bakin ba, criminal ne wanda jaha da society ke da haƙƙi dan ya zama izna ga ‘yan bawa.

Sai a lokacin tsakin da Zuby ta maƙale a zuciyarta ya fito, ta miƙe da sauri ta isa ga Sagir suka yi magana ƙus-ƙus.

A karo na farko da ya ji ba zai gwaleta ba, dan haka ya saci kallon Faɗime, ransa ya ƙara tuƙuƙi sanin da ya yi da ita aka shirya, masoyin nata dai ya kare ta ne, nan da nan ya bawa Cingam damar da ta nema a shigar da civil suit saboda a biya shi damages for tourtious liability da aka yi, sai dai kuɗin da ta ambata bai wani girgiza shi ba, dan haka ya ƙara mata. Ai da sauri ta washe masa fararen Rabbit Teeth ɗinta tana dawowa gaban Alƙalin bayan ta ƙara gyara zaman rigarta.

“A matsayina na mai kare wanda aka wanke yanzu, ina neman kotu da ta bi ma Sagir hakkinsa na ɓata masa suna da aka yi da lokaci, da zaman gidan yari, ya sha wahala ya wulaƙanta, an tozarshi, abin ya taɓa shi sosai ta yadda har mahaifiyarsa sai da ta kwanta a gadon asibiti, dan haka yana neman da a biya shi Million 300 sakamakon hakan. Ina fatan kotu za ta duba.

Hayaniya ta ɓarke jin maƙudan kuɗin da ta ambata, ƙalilan ne suke ganin hakan ya yi daidai, Linda Kam ai sandarewa ta yi sanin ko kwatarsu ba ta tada. ita kanta Faɗime sai da ta cire kai ta dubi Sagir suka haɗa ido ya wulla mata wani mugun kallo. Duk da tana da kuɗi, sai dai fa wannan kuɗin kamfaninta na Lagos duka shi ne zai kawo shi. A yanzun da ta fara kyamar talauci, gashi tana ƙoƙarin muguwar ƙaryewa. Ta gama da Murad bare ace za ta koma gurinsa ta nema. To amma ko duka abinda ta mallaka ne za ta ba shi. Za ta iya, tana jin hakan. Za ta biya domin Yaya domin Linda, domin ƙaunarsu gareta, kome suka yi ita ce sila. Wasu hawayen masu ɗumi suka sake zubo mata. Ashe dai baka taɓa rasa masu ƙaunarka kome mugun halinka.

Alƙalin ya buga guduma aka yi shiru.

“Sai kuma magana ta biyu. Idan aka yi duba da dalilin Ibrahim da Linda na aikata wannan lamari, to fa bai kamata a karɓi hujjarsu na cewar su kaɗai suka aikata hakan ba tare da sanin uwar ba, tunda soyayya tasa suka yi hakan, kenan soyayyar ita za ta saka a yanzun ma su ɓoye lamarinta. Dan haka ina nemar kotu mai adalci da ta nemi shaida ta uku. Wato wannan mutumin da Sergeant Luka ya ce yasan kome da suke shiryawa. Ina fatan kotu za ta duba.”

Alƙalin bayan ya gama nazarin maganganunta ya bawa Sergeant dama da a kawo dan ta’addan kotun domin ya bada shaidarsa. Anan ya bada dama da a tafi break na mintuna arba’in kafin ya zo.

B ayan Cikar Lokaci

A lokacin da ake bada labarin wani Ɗan ta’adda da dama ‘yan sanda na nemansa ruwa a jallo ke ƙoƙarin sace Abbati, tunaninta ko kusa bai bata cewar ta taɓa rayuwa da shi ba, koma ta san shi, sai a yanzun da ya wanzu gabanta a tsakiyar kotu jina-jina alamun an sha gumurzu kafin ya kamu, cikin kamanninsa da ba zata taɓa mantawa ba ko da kuwa duka hannaye ya rasa da kafafuwa, a sannan tunaninta ya ruga da gudu ranar da ta yi waya da shi, da zobenta da ya nema. Jabiru wato shi ne J Bilisco. Tirƙashi! Ko da wannan izinar aka barta ba za ta ƙara kuskure irin wannan ba, wato da tuni a dalilin ta tozarta Sagir, ita ce za ta tozarta ta hanyar rasa yaronta gabaɗaya, ko kuma tursasa rayuwa da Jabiru, mutumin da ya zama silar mutuwar mijinta saboda makauniyar soyayyarsa. Sai dai fa ta kuma fidda duniyar a ranta a yanzun da ya tsaya zai bada shaida game da saninta, ta sani ko dan ya nesanta Abbati da ita zai bada shaidar cewa ta san kome, da kanta ma ta ɗauko mukullin gidan Sagir. Duƙar da kanta kawai ta yi tana girgiza kai, yaya ne kawai ke haskawa a zuciyarta sanin duk ɓata lokacin da bayyana kansa da ya yi domin kare ta ya tashi a banza.

“Ku yafe min dan Allah, ka nemi Hajiya da ta yafe mini. Ka ba ta Abbati ta riƙe, na roƙe ka da girman Allah kar ka taɓa gaya masa ina prison.”

Ta furta ga Babban Mutum a hankali sa’ilin da ta ji ya dafe hannunta, idanuwansa cike da ƙaunar nan da bata gushe ba duk kuwa lefin da ta aikata gare su.

A sannan ne Alƙali ya jefa tambayarsa ga Jabiru.

“A abubuwan da ka sani game da yaron nan. Ko kana da tabbacin uwarsa tana da masaniyar boye shi da aka yi?”

Ku yi rating stars din da ke kasa dan nuna godiyar ku gare ni.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fadime 33Fadime 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×