Skip to content
Part 28 of 37 in the Series Fadime by Fulani Bingel

Ƙirrrrrrrrrrrrrrrrrrrrrrrrr!

Wata ƙarar kararrawar ta sake cika dodon kunnensu. A matuƙar firgice Linda ta runtse idanuwanta tana jan jikinta baya har sai da ta dangana da kujerar ƙarshe ta falon, tukunna ta buɗe su tar! A fuskar Faɗime da ke tsaye inda ta barta.

A cikin idanuwanta ta gane yanzu ko duniya za ta bawa Linda ba za ta je ta buɗe ƙofar ba, dan haka ta saki takardar hannunta da ta ɗauka ta karanta bayan Linda ta yi zaman ‘yan bori, ta taka a hankali zuwa baƙin ƙofar, ta buɗe.

Wannnan karon Maigadinsu ne baki ɗaya ya miƙo mata zungureriyar Ambulan ɗin da ta saka numfashinta ɗaukewa.

“Madam gashi wani me baƙar mota ya bayar ya ce a baki.”

Da ƙyar ta fisgo numfashin daga inda ya tafi, ta ce.

“Ban gane ba, ba yanzun nan Nike ya bar gurin nan da irin ta ba, ko minti biyar ba a yi ba, waye ne wai? Ka san shi?”

“A’a, ni banga ma sanda Nike ya zo nan ba, minti biyar baya ba na ƙasan gaskiya na ɗan kewaya. Ban san waye ba, yana ba ni ya ja motarsa ya tafi.”

“Okay, na gode.”

Har ya juya ta kira sunansa da sauri.

“Timbo! Ko waye ya ƙara kawo maka sako irin haka ka ce ya hawo sama ya same ni, ko kuma kawai ka cukwikuye shi ka kawo shi nan guna.”

“Okay Madam.”

Ya furta bayan ya yi shiru na ‘yan mintuna yana mamaki.

A kujerar da Linda ke jingine ta takure jikinta ta je ta zauna. Tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta hau warware takardar da ke fita da sautin bugun zuciyarta.

Na San Abbati Yana Raye!

Kar ki damu, ba wani abu zan yi da sanin hakan ba, kawai dai ina sha’awar sauraron bugun zuciyarki ne a lokacin da za ki karanta ‘Abbati Na Raye’ (smile).

Kin san me nake so da ke? Ki duba jerin ‘yan yatsunki guda biyar, ana biyun ƙarshe akwai wani kyakkyawan zobe irin na masoya (wink). Yauwa dai! To shi kawai nake so ki cire ki saka shi a cikin Ambulan ɗin da kika ciro wasiƙar hannunki. Ki sauko ƙasa can ƙarshen layinku akwai drum da kuke juye shararku, ki aje shi a saman sharar. Kar ki yi mamaki dan na nemi abinda bai da tsadar kome, wannan zoben ya fiye mini duk wani abu da ke duniya tsada. Sannan ki duba daga gefen drum ɗin, za ki ga kwalin GIV, to ki ɗauka, sabulun da zai sadaki da nasararki na ciki.

Na san ba sai na gargaɗe ki da ki yi abinda na umarce ki ba, kin san me nake nufi da Abbati na raye, kinsan kuma me zan iyayi kan hakan.

JWBilisco.

‘Tirƙashi! So yake ta ɗauki zoben soyayyarta da Mamuda da shi kaɗai ta gada a zamantakewarsu, shi kaɗai ne kyauta ma fi daraja da ta taɓa shiga tsakaninsu. Shi ne yau wani me warin kwata ke umartarta da ta je ta jefa a bola me ƙazanta ta gidajen da ke kafatanin unguwar, saboda mujiya ta sha yi mata fitsari a ka ko? Saboda ita jaka ce marar hankali, to ko waye, uban ubansa ma ya yi kaɗan balle shi kansa. Ya tuna mata ranar, ranar da har yau bata fasa mafarki da ita ba.’

Duƙe take tana wanke masa ƙananun kayansa ya mamayeta ya rufe mata idanuwa. My Blood! Zo ki ga abinda na kawo miki, abin burgewa ne da kaf cikin kwailayen samarinki babu wanda ya taɓa burge ki da irin shi.

“Ni kam ka ƙyale ni na gama wankin nan, anjima fa ka ce za ka saka su.”

“Allah ba zan ƙyale ki ba, ki zo ki gani kafin ya huce.

Janta ya yi har cikin ɗakin ya tsaida ta a tsakiyarsa, kana ya isa ga wandonsa da ya cire ya laluba Aljihun wandon ya ɗauko.

To ki rufe idanuwan mana, ban san ojoro fa.

Runtse idanuwanta ta yi tana murmushi, shi kuma ya lalubi hannunta ya saka mata. Ta buɗe idon da sauri sa’ilin da ƙyallin zoben ya cika mata su. Ba ta taɓa ganin zobe me kyansa ba, gashi ɗan siriri, da sauri ta zura a hannunta, ya kuwa zauna cif kamar ya aunata.

“Goodness me!” Ya furta yana ɗaga ta sama ya fara juyawa a ɗakin. “Ban za ci zai miki daidai ba, gabana nata faɗi idan na tuna hakan. Ko kinsan shi kaɗai ne zobe me kyau da ɗaukar hankali a duk kasuwar? Mai zoben kan shi cewa ya yi, a shekara biyar, bai fi sau ɗaya ake samun irinsa. Haka ko a zobban zinari babu irinsa. Azurfa ce me kyau Fati, ki riƙe ta amanata ce, zuciyata ce, ina so ki dawwama da ita, ko kin tsufa ki ɗaura ta sarƙa a wuyanki! Ni wai idan mutum ya mutu ba a binne shi da zobe ko?” Dariyar da ta tuntsire da ita ne ya ankarar shi ba ta ɗaukar zancen nasa serious.

“Ni to ina zan san yadda ake wa gawa?”

“Ke Allah da gaske nake, da ana binne mutum da zobe, zance kema kar ki bari a cire zoben.”

“Ok, ok, tsaya ka ji yadda za a yi. Idan kana mini wankan gawa da ka zo daidai yatsuna za ka cire zoben, sai na gartsa ma cizo a kunne.” Ta ƙarasa tana lalubar kunnensa ta gartsa masa cizon.”

“Ai da sauri ya dire ta, kafin ta tashi ya bi ta ya danne. “Ai da yake na ce miki ke za ki riga ni mutuwa ko? To ni ne zan mutu na bar…”

“Ka yi hakuri dan Allah, na fa cije ka ne dan ka dawo hayyacinka, na ga sai wani murna kake kamar wanda aka bawa kyautar Amarya.”

“Dole na yi murna Fati! Wannan ce kyauta ta farko da ta taɓa shiga tsakaninmu. Sai dai ba irin ta naso ba, wannan me arha…” Da sauri ta rufe masa bakin tana kallon cikin idanuwansa. Hannu ya sa a hankali ya ɗauke hannunta da ke bakinsa.

“Ki bar ni na faɗa, ta yiwu daga wannan ranar ba zan ƙara samun dama irin ta ba. Abu mai matuƙar tsada da daraja naso ya fara shiga tsakaninmu, sai dai wannan ma na ji daɗinta, dadi irin wanda na shafe shekaru ban ji irinsa ba. Kinsan me ya sa?” Ya furta yana kissing lumsassun idanuwanta.

_”Saboda da kuɗina na siya, da halalina, ba da kuɗin Imam ba. A masallacin da muka yi sallah jiya ne a garin Gombe, wani Attajiri ya sa a rabawa kowa dubu biyar. To nawa kason ne na ɗauka duka na siyo miki zoben da ko bayan raina ina roƙanki da ki bar shi a hannunki, ki bar shi ya dawwama a gunki, ko da sarƙa ne ki yi da shi ki rataya a wuyan…” Rufe bakinsa da ta yi da nata bakin ya hana shi ƙarasa maganar, kawai ya lalubi harshenta yana karɓar saƙonnin da ke cunkushe da su. A cikin kunnuwansa ta raɗa masa kalmomin.”

“Wannan zoben ya fiye mini duk wani abu da ke duniya tsada!”

Hawayen ta share, tana tuna kalmominta da ke cikin wasiƙar. Wato kowaye yasan alaƙarta da zoben. Saboda ya san ya faye mata duniyar ya sa yake umartarta da ta je ta jefa shi a shara, wane irin cin mutunci ne hakan a gareta, wane irin kuma tozarci ne ga Mahmuda da ke kwance a kabarinsa. To amma waye ne? Me yake so da ita? Tun yaushe yake bibiyarta? Me ya sa duk tarin gwala-gwalanta bai nema a su ba sai zobe na Azurfa. Ɗagowa ta yi tana sauke rinannun idanuwanta cikin na Linda da ta gama duba takardar, a tare suka yi tambayar.

“Waye Bilisco a rayuwarki?”

A taren suka ƙara maganar.

“Ke fa nake tambaya?”

“Ba mu san shi ba ke nan, amma shi ya san mu, ya san kome namu, ta yiwu har …”

“…ranar da aka haife mu ya sani!”

Linda ta ƙarasa mata a hankali, tana tsiyaya ruwan sanyi a cup ta miƙa mata.

“Me kika yanke yanzu? Na ga me yake nema, ko waye tabbas akwai alaƙa tsakaninsa da zuciyarki. Ya kuma san ki sosai. Sai dai abin tambayar shi ne, yaushe har aka ɗauki jakata aka zare sabulun ban sani ba? Ban tsaya a ko’ina ba daga gidan Sagir, ban kuma tuna na haɗu da wasu a hanya ba.”

Ta yi shiru cikin zurfin tunani.

“Oh My God! Ammy sanda zan kai Abbati kinsan mun manta cake ɗinsa? Na kusa fita daga gate din layin nan na tuna, sai na bar shi a motar na dawo da ƙafa nan gidan na ɗau Cake ɗin. Kenan sa’adda na bar jakar a motar wani ya hilaci Abbati ya buɗe jakar tawa ya ɗauke sabulun. Damn It! Ina ta aikata kuskure, but please ki taimaka ki tuna waye Bilisco a rayuwarki? Saboda ko waye Abbati ya san shi, yana da wayo, da bai san shi ba ba zai yarda a shiga motarsu ba, idan na zo kuma zai faɗa mini ko da ya ce kar ya faɗa.”

“Na rasa tuna waye Bilisco a baya. Ban tuna wani me suna irin haka ba. Ko zaman da na yi a Ƙaryar Imam babu kowa Bilisco, duka sunayensu na Musulunci ne. Abbati kuma dan ya san shi ba mamaki, kar ki manta, da irin haka ma ya san Sagir, waya sani ko wannan din ma a makarantarsu yake. Ko ma dai waye, ban yanke shawarar rabuwa da Zoben Masoyina ba saboda tsoratarwarsa.”

“Amma ya san Abbati fa yana raye, me kike tunanin zai yi kan hakan?”

“Ba mu san iya adadin abinda ya sani kan mu ba, idan muka fara yi masa abinda yake so tun yanzu, to ba fa zai fasa neman wasu abubuwan ba, ta yiwu ma wataran kan mu zai nema.”

“Idan kuma ba mu yi masa abinda yake so ba ya je ga ‘yan sanda ya tona mana asiri fa? Haƙuri za ki yi ki ɗauki zoben kamar yadda ya buƙata ke jafa masa a sharar. Ni kuma in je a yanko mini mukullin da zai sadani da cikin gidan Sagir na duba barimata, wannan ne damuwata kaɗai, a cikin kwakwalwata nake fahimtar ramar da wuyana ya yi cikin daƙiƙan da ban ganta ba. A kaf! Rayuwata, babu abinda nake tsoro irin zaman prison!”

“Wallahi ba zan yi hakan ba!”

Ta furta da kaushi tana tashi zuwa ma’ajiyar Landline ɗin su.

Bugu biyu aka ɗaga.

“Zan turo maka hoton wani zobe yanzu. Ina so cikin awanni biyar ka zagaya duka kasuwannin garin nan, ka nemo mini irin sa sak! Shi, idan ma babu aka baka tabbacin akwai a wani garin, ka yanki ticket din jirgi ka tafi can ɗin. A yau nake so ba gobe ba, ko nawa ne zan siya!”

Ta aje wayar tana sauke idanuwanta cikin na Linda.

A tare suka yi murmushi.

Linda ta ɗaga hannu biyu tana mata jinjina. Sai dai, a cikin wani saƙo da ke can cikin zuciyarta, take jin kamar wani kuskuren za su sake yi.

***** *****

Dungulmin hannunsa ya ɗago yana kallo, a hankali ya saki murmushin da bai kai fatar baki ba, ya dire kallon nasa kan karyayyen yatsan ƙafarsa da ficewarsa ya saka shi zama mai yatsu huɗu. Ɗaya hannun me lafiya ya miƙa ya ɗau kofin Coffee ɗin da ke gabansa na tururi, ya kurɓa, ya ji yajin cittar da aka dafa da shi ya wuce har cikin kansa, kana ya waigo yana sauke manyan kwayoyin idanuwansa kan na yaron da ke tsaye a gabansa.

“Yaushe za a yi zama na biyu a kotun?”

“On 22 Oga.”

“Na Maƙarfi fa?

“Kamar ya fara ankara ana bibiyarsa, kafin ya fara tunanin aiwatar da wani abin, ya kamata mu gama namu aikin.”

“Good! Haka nake so dama ya gane ana bibiyarsa.”

“Kamar ya Oga? Hakan ai kuskure.”

“Kuskuren nake so ya faru. Ya wasiƙun duk sun isa gareta?”

“Eh sun isa, na san zuwa yanzu ta yanke shawarar bin umarninka. J dai yana kewayen unguwar yana kula da kowane motsinsu.”

“Hmm! Ba za ta yi abinda nake so ba, tsakanin ni da ita bansan wanda ya fi buƙatuwa da Zoben ba.”

“To ya za ta yi? Alhalin mun san abinda babu wani muhaluƙi da ya sani nata.”

“Za ta nemi wani irinsa, she is very smart…”

“Amma ba ta san hakan kuskure ba ne ga rayuwarta?”

“Kuskuren nake so ta yi ai, za kuma ta yin. Saka mini sabon sim ɗin a jikin wayata ka ba Ni.

Ya furta yana ƙara kurɓar coffee ɗinsa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fadime 27Fadime 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×