Skip to content
Part 29 of 37 in the Series Fadime by Fulani Bingel

Ƙarar da wayar ta ɗauka da shi ne, ya saka ta tafiya da sauri ta ɗaga kiran tana sauke ajiyar zuciya.

“Ya har yanzu shiru ba ka iso ba?”

“Madam ki yi haƙuri, sai da na shigo cikin unguwarku wasu mazaje biyu suka tare ni da wuƙa suka kwace zoben. Yanzu haka sun kumbura mini ido.”

“Ya ilahil Alamina, ni kam na shiga uku! To yanzu kana ina?”

“Sun ce idan ina son ganin yarinyata ta gama Nursery da idanuwanta, kar na ƙara gigin takowa unguwarki, ko ma na ƙara samo irin Zoben. Madam ki yi haƙuri ba zan iya ba gaskiya, na gode, zan turo miki da sauran canjinki ta Account.”

Ƙitt ya kashe kiran.

Ta waigo tana kallon Linda da ta gama shirin fita ɗauko Barima.

“Ya taho da irinsa sun karɓe, suna cikin unguwar nan, ko waye ya gama shirya mana Linda, ya kuma sanni farin sani, tunda har tunaninsa ya ba shi ba zan bada nawa ba, zan nemi wani irinsa ne.”

Kafin Lindar ta buɗe baki ta yi magana wayar da ke cikin jakarta ta ɗau ƙara har sai da ta ɗan firgita kamar ba shi ne ringing ɗinta ba. Allah shaida, daga safiya zuwa yammacin ranar ta gama firgita da ko wanne irin Ringing musamman na ƙararrawa. Dan haka ta share kiran, har sai da ya katse, wani ya ƙara shigowa cikin shirunsu tamkar babu rayuka biyu a gun.

“Har ba na son ɗaga waya, gani nake kamar ina kaiwa kunnena za a ce You Are Under Arrest!”

Tsaki Faɗime ta je.

“Sa’adda duk kika shirya wannan ƙetar me ya sa baki yi tunanin hakan zai iya faruwa ba? Ki ɗaga kiran kawai, daga yanzu zuwa lokacin da kome zai ƙwaraire ba fa za ki samu barcin awa uku cikakke ba, ni damuwata kada dai ramin muguntar mun yi shi wawakeke ne da zai rufta har da mu. Koma dai menene, zan shanye ko meye da zai zama silar raba ni da ɗana. Allah ya tsayar mana haka.”

A hankali ta zuge jakar ta zaro wayar da ke ta ƙara. Ƙirjinta ya buga da ƙarfi ganin Private Number, a sannu sassanyan gumin ya yanko mata ya bi ta zirin hancinta yana ɗiga kan wayar. Runtse idonta ta yi da ƙarfi tana kai wayar kunnenta.

“Miƙa mata wayar!”

Aka furta a kausashe. Da sauri ta miƙe tana isa ga Faɗime ta bata.

“Ke ake nema.”
Karɓa ta yi ta kai kunnenta.

“Ki duba Whatsapp na aje miki kyakkyawan saƙo. Gama gani na kira ki.”

Buɗe whatsapp ɗin ta yi da sauri, sakonni rututu suka fara shigowa.
A sannu idanuwanta ya kai kan wata Number me ɗauke da Code din GHANA hotuna guda biyu sun shigo. Buɗewa ta yi ta ga abinda ya sakata lalubar kujera ta zauna tana ambaton Allah.

Hotan Yaya ne da Abbati a gefen wani haƙaƙƙen kabari yana ƙarasa warware farin likkafaninsa. Ɗayan kuma Yayane riƙe da hannun Abbati za su shiga cikin gidansu na Maƙarfi.

Kamar mai tsoron wani zai fisge wayar ya gani haka ta ƙanƙame wayar tana deleting hotunan. A sannan ne kuma kiransa ya ƙara shigowa ta ɗaga jikinta na rawa tana buɗe hands free

“Na san zuwa yanzu kin gane me magana da kuma manufar hotunan ba sai ina ɓata yawuna ba. A karo na farko na umarce ki da ki yi abu kina ƙoƙarin gwada mini duniyanci yadda kika saba. Idona a buɗe yake tar! Kan ki Fati. Ki cire zoben nan kamar yadda na baki umarni ki je ki ajiye shi a kan bolar. Shi kaɗai ne abinda na nema. Wallahi kin ji na rantse kar ki kuskura ki ƙara irin kuskuren nan. Watsa hotunan nan a duniya daidai yake saka Zare cikin Allura a gurina, kar kuma ki za ci suke nan, ina da su har kala goma, karkiyi mamaki idan na ce miki ina da har wanda Yayanki ke zirarawa yaronki Allurar ma! Ina fatan kin gane.”

“Wa..wa..waye kai?”
Kalmomin suka fito a kakkarye zuwa cikin kunnuwansa.

“Your Father!”
Ya furta a disashe yana kashe wayarsa.

Ba zagin ya fi mata ciwo ba, yadda kowacce gaɓa ta jikinta ta tabbatar mata da ta taɓa sanin muryar amma ta gaza tuna mamallakinta ya fi mata ciwo. Dafe kanta ta yi tana runtse idanuwanta da ƙarfi, ji take kamar ta fasa ihu ko za ta tuna, tabbas ta san muryar sai dai a ina? Ta gaza tunawa. Ganin kanta zai fashe a banza ya saka ta ɗagowa tana sauke dubanta kan Linda da ke can gefe ta takure jikinta. Wato tsoron Linda na bata mamaki. Gashi dai ita ta jawo kome, ba kuma ita aka nema da ta cire wani abu nata mai muhimmanci a rayuwarta ta bayar ba. Amma tafi kowa firgicewa da fita hayyacinta. Ji yadda yini guda ta yankwane kamar wata tsohuwa. Tsaki ta ja a ƙasan zuciyarta tana lalubar hannunta me zoben. A karo na farko da zafafan hawayen suka zobo mata, ta yi Allah wadai da wannan masifa da Linda ta ja musu. Ji take kamar jininta ake zuƙa a haka ta zare zoben tana damƙe shi cikin tafin hannunta.

Linda ta bita da kallon mamaki, lallai bala’i ya yi bala’i tunda ta yarda ta cire zoben nan.

Bata bi ta kanta ba ta buɗe ƙofar falon ta fice.

Sauke ajiyar zuciya ta yi tana godewa Allah da bata ce ta zo su je ba. Dan ita yanzu ko mutuwa bata fatan ta ɗauketa a wajen gidansu.

A hankali take takawa cikin sanyin maghribar da ke busowa a haka ta ƙarasa jikin abin sharar ta ɗora zoben akan tarin bolar tana runtse idanuwanta, hawayen na diga har a yatsar ƙafarta. Ji take ta gama tozarta masoyinta Mamuda duniya da lahira. Share hancinta da ke yoyo ta yi ta sunkuya tana ɗaukar kwalin sabulun da ta hango a ɗan saƙon durum din. Buɗewa ta yi, ga mamakinta mukullin ne da sabulun a haɗe, ke nan har sun yanko musu mukullin. Wannan ya nuna mata ba guda ɗaya suka yanko ba, suma suna da nasu. Wani murmushin takaici ya ƙwace mata. Ko waye ke wasa da su ya cika ɗan iska marar mutunci. Jifa ta yi da kwalin da sabulun ta wuce da mukullin zuwa inda ta fito.

L I N D A

09:04PM
Daidai ta wanzu a ƙofar gidan. Gyara zaman mini skirt ɗinta ta yi, ta taka a hankali zuwa jikin ƙofar. Sai da ta waiga hagu da dama ta tabbata babu wani mahaluƙi da ke lura da ita, tukunna ta zura mukullin, tana murɗawa sau biyu ya buɗe, ta cusa kanta zuwa ciki tana bayyana a tsakiyar falon. Lalubar makunni ta yi da sauri ta kunna, haske ya wadaci gurin.

Rufe kofar ta yi tana sauke ajiyar zuciya. Tunda ta fito sai yanzu ta ji a hankalinta ya kwanta. Siririn gyalenta ta zame daga kanta ta aje saman kujerar, ta duƙa ta zare dogon takalminta me Igiya. Tukunna ta bazama cikin gidan tana dube-dube. Ita ce kan gado, ita ce ƙasan kafet, ita ce jikin labulaye. Babu wani alamar barima a gun. Falon ta ƙara dawowa tana zama saman kujera, hannunta ya sauka kan tarharta da ta ajiye. Wani tunani ya ɗarsu a ranta, da sauri ta miƙe da tarhar a hannunta ta kama goge duk wani abu da ta san hannunta ya taɓa. A hankali ta isa ga banɗakin falon nan ma ta goge, ta buɗe ta shiga ciki, ta tsaya a madubin da ke jikin sink tana kallon kanta. A sannan ne ta ji ta taka wani abu me ɗan tsine, da sauri ta duƙa sai ga barimarta na dalle mata idanu. Wani farin ciki ya ratsa ta har sai da ta yi wani dan ihu ta yi sauri tana toshe bakinta.

Fitowa ta yi ta ƙara goge duk inda ta taɓa, ta cusa barimar a jaka da tarhar, ta zura takalmanta za ta fita, hankalinta ya kai ga kitchen, ƙishi take ji, rabonta da sa wani abu me kyau a cikinta tun daren jiya. Ƙarasawa ta yi ta zaro tarharta ta naɗe hannunta da shi ta buɗe fridge. Idanuwanta suka yi arba da SHANI (شاني) yawunta ya guda. Zaro shi ta yi ta aje kusa da sink, rufe fridge din ta yi ta warware tarharta ta ɗora a kai, ta ƙara gyara zaman vest din jikinta. Ta ɗauki lemonta ta buɗe ta kai baki, dadinsa ya ratsa ta, idanuwanta a lumshe a haka taji kamar an doka guduma a tsakiyar ƙirjinta, ta buɗe idanuwan tar! Tana kallon ƙofar da take ji ana motsi.

Aje gwangwanin lemon ta yi a hankali tana yin baya cikin rashin sanin abinyi. Idan ba kunnuwanta ke mata ƙarya ba, motsi take ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar gidan a shigo. Waige-waige ta fara yi tana riƙe mararta da take ji ta ƙulle, cikin ɗauke numfashi ta buɗe kantar ƙasa, bata jira kwalwalwarta ta gama lissafa girmanta ba ta cusa kanta ciki, wata ƙusa ta caki bayanta a haka ta toshe bakinta hawayen azaba na fita, da ƙyar take numfashi haka ta ja kofofin kantar biyu ta rufe. Ta dan wani layi siriri da ke tsakanin murfin biyu take hango hasken kitchen.

“In sha Allah ba za mu rasa wani abun ba, kar ka wani damu, Allah yana tare da mai gaskiya, haka tsakanina da ku babu godiya. Sagir ya wuce duk yadda ka ke tsammani a gurina.”

Cingam ta furtawa Yaya da ke ƙoƙarin buɗe ƙofar.

“Allah yasa. Godiya kam dole mu yi miki, kin mana kirkin da ba kowa zai iya ba. Bismillah shigo.”

Tana shiga falon ta baza manyan ƙofofin hancinta tana shaƙar iskar falon.

“Wow, kana Jin ƙamshin mutum?”

Babban Mutum ya yi sororo yana dubanta tamkar mai tunanin mayya ce, yo idan ba maye ba wa ke jin ƙamshin mutum?

“Oh sorry, I mean ka ji ƙamshin Turaren Pinky? Na mata ne, hala dai Sagir turaren mata yake sakawa?

“Za ki fini sani ai, ke da kuka yi karatu tare?”

Ya furta yana aje mata murmushi.

“Ohhh kamar ba a Naija ba…”

Ta furta tana kai hannunta ga makunnin falon ta kashe, ta kuma ƙara kunnuwa.

“…Ina nufin kamar ba Nepa ba kuke barin wuta a kunne alhali ba ku cikin gidan. Ganganci ne wannan, a kowanne lokaci za su iya kawo wuta me ƙarfin da za ta haddasa gobara. Ni idan zan fita daga gidana meter gabaɗaya nake rufewa.”

Shiru ya yi yana nazari kafin ya ɗago da sauri yana kallonta.

“Ai kuwa da na zo da safe babu abinda na bari a kunne sai fridge, na kashe duka kwayayen gidan nan. Kai! Ba dai…”

“Wani ya shigo ya kunna, hakane.”
Ta ƙarashe masa zancen.

“Shi ne kuma ƙamshin da na ce maka na ji ina shigowa, akwai alamun ko waye bai yi nisa da mu ba.”

“Amma ai Key yana guri…”

Dariyar da ta yi ya saka shin yin shiru yana ƙarewa takunta na gajeru kallo, kayya! Ga muni har muni amma sai dai kwanya. Jifa ya kusa ninka shekarunta amma bai iya tunanin da ta yi ba.

Zama ta yi kan kujera tana ɗora guntuwar ƙafarta me ɗauke da dogon takalmi kan ɗaya.

“Ai ba abun mamaki ba ne idan ka yi la’akari da yadda aka shigo har cikin gidan aka ɗauki motarsa, wannan ƙarami ne cikin shirinsu. Ko waye kuma ya yi inkarin zan zo, akwai kuma abinda ya manta anan ɗin, shi ya sa ya dawo ya ɗauke dan idan na zo kar na samu kome. Wannan ƙamshin turaren da na ji kuma shi ya sake ba ni tabbacin akwai mata a cikin shirin.”

“Amma me ya haɗa Sagir da mace da har za ta ƙulla masa wannan kaidin?”

“WHO knows?”

Ta furta tana ƙara zaman tabaronta da ke taimakawa nanannan hancinta tsayi.

“Kasan ance rana dubu ta ɓarawo, rana guda ta mai kaya. Idan da rabo sai ka ga Allah ya toshe musu wata basirar sun yi kuskuren da zai fallasa wani abin, bari dai mu gani.”

Ta miƙe tsaye tana kewaye falon, Shi kuma ya take mata baya. Tun daga uwar daki har toilet bata bari ba, sai dai babu wani abu da zai nuna wani ya shiga gidan. A haka harta gangara kitchen, idanuwanta suka sauka kan gwangwanin Shani da har yanzu da sauran raɓa jikinsa. Wani sassanyan murmushi ta saki tana isa ga lemon.

“Ka ga tun lemon safe da kasha har yanzu da sanyinsa.”

“A’a, ni da na shiga babu abinda ya haɗa ni da fridge, kai! Amma fa da mamaki, ace duk iya takun nan nasu su bar abu mai muhimmanci irin wannan?”

“Toshewar basirar ke nan.”

Ta furta tana saka Safa a hannunta, ta ɗauki gwangwanin tana ƙare masa kallo.

“Amma Barr. Anya kuwa mu kaɗaine a cikin gidan nan? Kin ga fa kamar yanzu aka sha shi?”

“Zo ka ga! ya rabbi, dole Baba ya dawwama shi mini Albarka.”

Matsowa ya yi yana duba abinda take nuna masa.

Shatin jan jambaki ne ɓaro-ɓaro a bakin gwangwanin.

“Ka ga zance na ya fito ko? Akwai mace a cikin a lamarin.”

“Na yarda kam, amma yanzu ta yaya za ki gane wanda ya yi amfani da wannan din alhali ba ki da shaidar wani abu nasa?”

Murmushi ta yi idanuwanta na sauka saitin da Linda ke ɓoye, gun ta ƙurawa ido kai ka ce tasan da wani a ciki. A hankali kuma ta juya tana ƙare damƙe gwangwanin a hannunta.

“Kar ka damu, akwai waɗanda na daɗe ina zargi dama, zo mu tafi, wannan kawai ya ishe ni. Sagir nake son gani yanzu.”

“Su waye?”

“Lokaci zai zo da za ka san su.”

Ta furta tana mai ficewa daga kitchen din.

Sai dai, da ace ta ƙara sakan biyu tana kallan drawer, da ta kula da wani ruwa me yellow-yellow da ke fitowa ta ƙasan yana malala a ƙasan kitchen ɗin. A tun lokacin da Linda ta ji ta ɗauki gwangwanin lemonta, mararta ta gaji da riƙon fitsarin ta sake shi, ba dan ta yi ƙoƙarin toshe bakinta ba, da babu abinda zai saka su jin saukar numfashinta da ta fara jansa kamar me athma. Kuskure ne ta yi, sai dai fa ko karen haukane ya cije ta ba za ta yadda Ammy ta san wannan wautar da ta yi ba, za ta yi ƙoƙarin ganin Cingam ba ta samu wani shaida na hannunta ba ko wani abu nata, da za ta haɗa da gwangwanin ya zama iri ɗaya. Ta tsinewa kanta ya fi sau hamsin na kwaɗayin da ya sakata taɓa Fridge har ta kai ga ɗaukar wani abu a ciki. Sai dai ta rasa gane dalilin da yasa take ta aikata kuskure, a haka ta fito tana dafe bayanta da ƙusa ta fasa. Sunkuyawa ta yi da ƙyar tana goge fitsarinta. Kafin kuma ta tattara ya nata ya nata ta fice daga gidan. A ranta take jin bata fatan wata ƙaddarar da za ta ƙara haɗata da ilahirin unguwar.

S A G I R

Sai da ya gama ƙare mata kallo, kana ya ƙarbi ‘yar cooler hannunta da ta gama shan bincike kafin a yadda ta iso masa. Buɗewa ya yi, daddaɗan ƙamshin abincin ya daki hancinsa. Dambun Shinkafa ne irin wanda yake so. Lumshe idanuwansa ya yi yana jin anya akwai wanda ya gama sanin lagwansa irin Zuby? Tattare hannun rigarsa ya yi ya fara kai loma.

Sau uku tana buɗe baki za ta yi magana sai ta fasa. So take ta maƙe murya yadda za ta yi daɗi a kunnensa amma ta gaza, tun daren jiya ta zauna gaban TV ta kamo tashar Turawa tana saurararsu tana gwada muryar da za ta yiwa Sagir magana yau wacce za ta ɗau hankalinsa ya bata dukkan nutsuwarsa. Ta kuma samo guda ɗaya, sai dai ga mamakinta da ta iso gabansa kome ya kwace mata. A hankali ta yi gyaran murya tana yin ƙasa-ƙasa da idanuwanta.

“Fatan zuwa yanzu ka tuna wanda ka haɗu da shi a wannan dar…?”

Ƙwarewar da ya yi ya sakata tashi da gaggawa tana miƙa masa ruwa. Allah ya sani ita ta kwarar da shi, ji ya yi tana magana kamar an shaƙe Ɓera. Ban da ƙeta ya yana cin dambu za ta maƙe masa murya, ai sai ya shaƙe shi.

“Haba Zuby yau muke tare? Dan ALLAH ki yi magana yadda zan fahimta.”

Kar ku manta comment da like dinku shi ne ribata. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fadime 28Fadime 30 >>

4 thoughts on “Fadime 29”

  1. Masha Allah da ina ta tunanin a ina zan samu littafin nan complete sai gashi cikin sauki da wasu kudi ƴan kalilan na samu kai bakandamiya duniya ne wlh

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×