Skip to content

Fatalwar Sinu | Babi Na Daya

4.8
(4)

Baki mai yanka wuya

Tabbas an sha wuya

Jiki ya yi talata.

A yayin da dubun dubatar jama’a ke murnar shagalin ƙaramar Sallah a wurare mabanbanta a cikin duniya, ni kuwa Haiman cike nake taf da taraddadin abinda ya same ni tamkar randar da aka cika ta da ruwa. Hausawa kan ce ‘ƙaddara ta riga fata.’ Haƙiƙa wannan batu haka yake, domin kuwa duk iya addu’o’i da fatan alheri da mutane suka yi ta aiko min bai hanani fige kazar wahalar da na yanko wa kaina ba. Amma na san duk wannan bai shafe ku ba, don haka bari in ja ku zuwa ga labarin kai tsaye.

Da fari dai ya kamata ku sani cewa, tun ana jibi bikin Sallah na yi wata kasassaɓa ta hanyar bayyana ra’ayina dangane da irin kyautar da na fi so a bani matuƙar dai so ake a burge ni, inda na zana abubuwa uku a matsayin waɗanda na fi so. Waɗannan abubuwa kuwa su ne alƙalami, littafi da kuma turare. Kasancewar mai duka ya haɗa ni da ‘yan uwa da abokai nagari, da yawansu sun aiko min kyautukan abubuwan da na ambata a baya, wasu ma tun daga birnin Dabo suka antayo min nasu, wasu kuma daga ta Dikko, kai har ma da mutanen birnin Zaman-fara.

A taƙaice dai, na samu sinƙi-sinƙin wagagen littatafai tare da zabga-zabgan alƙalumma gami da ribɗa-ribɗan kwalebanin kayan ƙamshi. Shin ‘yan uwa, yanzu anan fisabilillah ina da laifi? To amma bari ku ji yadda ‘yar wannan maganar ta zama makekiyar gaske.

A washe garin sallah ne, ina zaune a ɗakina da ke ƙofar gida (kun san har yanzu ban shiga daga ciki ba tukun), sai na ji an rafka sallama, bayan na amsa sai na yaye labule na leƙa domin in ga ko wanene. Kwatsam! Sai na ga wani yaro tsaye da akwati ɗan ƙarami a kansa. Ko da ganin wannan yaro sai na tambaye shi lafiya? Sai ya ce aiko shi aka yi wai ya kawo wa Haiman wannan akwatin. Na tambaye shi wa ya aiko shi, sai ya ce min wani mutum ne, ina mutumin yake? Wai ya fece amma ya ce in duba cikin akwatin zan taras da dukkan bayanan da na ke buƙata. Tun a sannan na ji ni fa ban yarda da wannan lamari ba, to amma da yake ina da rabon shan duka, sai na amshi wannan akwati na shige ɗaki, har da yi wa wannan yaro tukuici kuwa.

Bayan na koma cikin ɗakina, sai na samu kujera na kame sannan na sheƙe duk kayan da ke kan ɗan teburina. Daga nan sai na jawo wannan ɗan akwati na buɗe shi domin in kashe ƙwarƙwatar da ke idona. Ko da na buɗe wannan akwati, kwaram sai na yi arba da wani wagegen littafi mai kama da littafin Tarihin Duniya. A jikin littafin kuma, an liƙa wata ƙaramar takarda wacce take ɗauke da wani rubutu a jikinta. Ban yi wata-wata ba wajen yakito wannan takarda domin ganin abinda ke rubuce a jikinta.

Ko da na duba jikin wannan takardar, sai na ga an yi rubutu kamar haka:

‘Zuwa ga Haiman, ga kyautar jinjina nan gareka daga shugaban makafta wato M.S Narayana’. Ko da na karanta wannan rubutu sai na yi murmushi, domin a wancan lokacin na yi tunanin ɗaya daga cikin abokaina ne ya kafto min wani kafce domin ya sa ni nishaɗi, sai dai kamar yadda za ku ji a nan gaba, na yi babban kuskure. Daga nan sai na zaro wannan wagegen littafi tare da wangame shi. Abinda na fara arba da shi bayan na buɗe wannan littafi shi ne rubutun harshen telugu, ni kuma wannan tafiyar tanar ba wani gane shi nake yi ba, don haka sai na yi tunanin lallai kowanene wannan makafcin, tabbas yayi ƙoƙari matuƙa gaya.

Tun da ba iya karanta yaren na yi ba, kawai sai na antaya shafi na gaba. Wannan karon kuma sai na ga hoton jarumi M. S. Narayana a jiki, watau Kwarkwar Sinu kenan. Sa’ilin da na ga haka, sai na fara tantamar anya ma kuwa wannan saƙon ni aka aiko wa da shi? Anya ba kuskure aka yi ba? Ko dai yaron nan ɓatan kai ya yi ne? Na dai daure na ci gaba da buɗe shafukan wannan littafi. Sai dai wani abin mamaki, duk shafin da na antayo sai in ga hoton Sinu, wasu hotunan tun yana makaranta ne, wasu hotunan tun yana saurayi, wasu hotunan shi da iyalansa ne, wasu da abokan aikinsa ne wasu kuma a yayin gudanar da kafcen shirye-shiryensa ne. Haka dai na ci gaba da kallon waɗannan Hotuna har na zo kan hoton gawarsa yayin da aka fito da gawar sa bayan ya mutu.

Ko da na zo kan wannan hoto, sai na tsaya cak na kasa yin gaba balle baya, zuciyata kuma sai ta hau dukan shida-shida yayin da idanuwana suka tsaya car a kan hoton ba sa ko ƙiftawa. Ba komai ne ya jawo faruwar wannan al’amari ba kuwa face ganin kaina da na yi a jikin wannan hoto. Na san cewa ku kanku za ku yi mamakin jin wannan batu, amma ko rabi na ba ku kai ba. Gani na yi gani nan tsaye cikin tawagar masu raka gawar tasa a daidai lokacin da aka kafta wannan hoto. Nan fa na ƙurawa wannan hoto ido ƙuriiii… Ina mamakin faruwar wannan al’amari, domin ko da yake na san cewa ana samun mutane da dama su yi kama da junansu, abin da mamaki ace akwai mai kama da ni a ƙasar Indiya har ma ace ya bayyana a jikin hoto irin wannan. Bayan na daɗe ina kallon wannan hoto tare da ƙoƙarin ganin cewa na gano ko ni ne ko ba ni bane ba tare da na yi nasara ba, sai na kai hannuna na taɓa wannan hoto wai ni a tunanina hakan zai sa in fahimci ko akwai wata alaƙa a tsakanina da wannan mutumi da ke jikin wannan hoto ko babu. Hannuna na sauka a kan wannan hoto, sai na ji kamar daga sama an ɓarke da wata irin mummunar dariyar mugunta, kafin in tantance ko daga ina ne wannan dariya take fitowa, kawai sai gani na yi wasu ƙananan igiyoyi sun fito daga cikin wannan littafi sun ɗaure ni tamu, har sai da ta kai ga bana iya motsa ko ɗan yatsana. Kwatsam! Kuma sai ga wata iska mai ƙarfi ta biyo bayan waɗannan igiyoyi tana kaɗawa da ƙarfin gaske, nan take ta ja ni da ƙarfin tsiya ta dunƙule ni har sai da na koma ɗan ƙarami tamkar kiyashi sannan ta antaya da ni cikin wannan littafi, kamar dai abin da ya faru da su Jafaru a cikin littafin Kundin Tsatsuba. Duk ihu, magiya da kururuwar neman taimako da na yi ta antayawa sun tashi a banza domin kuwa babu wanda ya ko jiyo ni balle ya kawo min ɗauki.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×