Skip to content

Fatalwar Sinu | Babi Na Uku

3.3
(3)

<< Previous

Turnuƙu faɗan Iblisai

Tuya sai mai ƙosai

Bakin wani zai kassai.

Yayin da Sinu ya ji waɗannan tambayoyi nawa, sai ya yi wani irin gunji tare da ƙarajin fusata, har sai da wani irin farin hayaƙi ya dinga fitowa daga bakinsa, hancinsa da kuma kunnuwansa. Can kuma sai ya nuna ni da hannu yana mai cewa,

“Kai ɗan bayan gari! Kada ka raina min hankali da waɗannan tambayoyi naka. Hausawanku basu iya samun sara ba, a duk lokacin da wata sabuwar sara ta fito, to ba za su tsagaita ba har sai sun gallabi jama’a da ita. Tun da aka fara wannan fassarar shikenan na zama abin zolayar kowa, a duk lokacin da kuwa aka zolaye ni ina jin duk abinda ake yi kuma raina yana matuƙar ɓaci, duba ka ga irin tsiyar da ka tsula min a cikin shirin Cinnaka har yanzu ba a daina zolayata akansa ba, hasali ma dai wannan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa na kasa kwanciyar kabarina lami lafiya.”

 Ko da Sinu ya zo daidai nan a zancen sa, sai na ce,

“A’aha, shin ashe dama binne ka aka yi ba ƙona ka aka yi ba?”

Wannan tambaya tawa ba ƙaramin harzuƙa shi ta yi ba, don haka cikin fushi ya ce da ni,

“Ya isa! Wannan Iskaranbarancin naka ya isa Hakanan, bana buƙatar wani bayani daga gareka, yanzu zan fara gana maka muggan azabobin da na tanada kafin daga baya in sheƙe ka kowa ya huta.”

Ko da na ji wannan batu nasa, sai dariya ta ƙwace min, hakan yasa ya yi shiru kawai yana kalllona yayinda baƙin ciki ya ƙume shi. Da na ga alamar ya nutsu sai na ce da shi,

“Ka yi min afuwa bisa dariyar da na yi, babu yadda na iya ne, amma tambayoyina ba su ƙare ba. Shin ta yaya aka yi ma har ka iya magana da harshen Hausa? Ta yaya aka yi ka san da wanzuwar masu fassara a ƙasata? Ta yaya kai da kake Fatalwa za ka iya azabtar da wanda yake raye?

Sannan kuma menene shirinka a kaina da kuma sauran masu fassara da harkar Indiya baki ɗaya a ƙasar Hausa? Erm… Kada ka yi min mummunar fahimta, kawai dai ina so in samu cikakken bayani ne dangane da dalilin da yasa kake son kashe ni bayan ka azabtar da ni. Hakan zai taimaka min wajen mutuwa cikin kwanciyar hankali.”

Yayin da ya ji na sake antayo masa waɗannan tambayoyi haka, sai ya sake kurɓar barasa sannan ya yi murmushi. Kamar daga sama kuma sai ga wata kyakyawar kujera fara tas ta bayyana a gabansa, zamansa ke da wuya kuma sai ga wani farin teburi ya bayyana a hannun damansa, ga kwalaben giya nan iri-iri an jera. Ya ɗauko wata kwalba guda wacce aka rubuta Star Larger Bear a jikinta ya buɗe ya kwankwaɗe ta kai tsaye sannan ya ajiye kwalbar. Ajiye kwalbar ke da wuya sai kayan jikinsa suka koma farare tas. Ya sake yin wani mummunan murmushi a gareni sannan ya fara magana da cewa,

“Duk da cewa ba zan so ka mutu cikin lumana da kwanciyar hankali ba, amma haƙiƙa ka yi tambaya wacce ke buƙatar amsa, domin kai da zaka mutu wani amfani ko rashin amfani amsar za ta yi maka? Manta ma dai da wannan, amsar tambayarka ta farko mai sauƙi ce, duk wanda ya mutu yana iya fahimtar kowane irin yare a duniya kuma yana iya magana da kowane yare. Amsar tambayarka ta biyu kuma ita ce, na san da wanzuwar masu fassara a ƙasar Hausa ne bisa irin yawan ambaton sunana da ake yi a yankin, sannan a matsayina na fatalwa ina da wani sihiri da zan iya aiki da shi a kan duk wanda na ga dama. Shirina kuwa a kanka tare da sauran masu fassara da harkar India baki ɗaya shi ne, da fari dai tukun zan ganawa kowannenku azaba mai raɗaɗi sannan daga baya in sheƙe ku kowa ya huta.”

“Don haka, a matsayinka na mutum na farko da zai fara fuskantar wannan waƙi’a, zan bai wa wani babban aminina damar gana maka azaba kafin in amsa daga inda ya tsaya.”

Har na buɗe baki zan tambaye shi wanene wannan abokin nasa kawai sai gani na yi wata ƙofa ta bayyana. Daga cikin ƙofar kuma sai ga wani mutumi ya bayyana. Bayyanar wannan mutumi yasa na kiɗime fiye da ganin Sinu. Me yiwuwa ku iya cewa “Haba Haiman, wannan ai yawa ne” amma ina, dole ce ta saka ni na kiɗime. Domin ba kowa na gani ba face babban azzalumin da duniya kaf ta yarda da cewa shi azzalumi ne. Wannan kuwa ba kowa bane face Amrish Puri, watau Mugyambo mugun boss.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×