Skip to content
Part 7 of 13 in the Series Fitsarin Fako by Sanah Matazu

Tun bayan kammala makarantarta sai ya zamana kaɗaici yana nema ya yi mata yawa. Tun asalinta  ba mace ba ce mai tarkacen ƙawaye ba, hasalima ƙawarta ɗaya ce Mardiyya, yanzu haka tana gidan mijinta tare da ɗiyarta Safna, suna zaune a garin Abuja.

Baba Barista in ya zauna a gida sai ƙarshan sati, kawu kuwa dama shi ba gwanin hira ba ne, yanzu ne ma yake ɗan janta da hira saboda bayanin da likita ya yi masa, kaɗaici zai iya asasa ciwonta.

Yau tun safe ta tashi da wani irin karsashi sakammakon mafarkin da ta yi da Anna. Gabaɗaya ta sauya ta yi wata irin cika ga kammala. Sai zuciyarta ta tsinke ta gasgata lalai gizo idonta yake yi mata a wasu lokutan mabanbanta. Amma kuma wace ce matar da ta ba ta takarda? A gefe ɗaya kuma tana tunanin Sadiya, yarinyar da aka kashe mai aikin gidan Alhaji Labaran. A taƙaice ma so take ta san waye Alhaji Labaran ɗin?

Lokaci ɗaya ta ji zuciyarta ta motsa da wani irin karsashi, Baba barista ya sha tambayarta kan yaushe za ta fara aiki a ƙarƙashin ofishinsa tana ba shi amsa da “Sai na huta.” Lallai yanzu ne ya kamata ta miƙe domin ƙwatar ‘yancin ‘yan uwanta mata.

Daga lokacin rasuwar Sadiya ta riski labarai sama da goma duk kwatankwacin hakan. Ta rasa wace irin rayuwa ake so mata su yi. Jin zuciyarta ta aminta da ƙudurinta ya sa ta miƙe ta soma shiri.

Kai tsaye ɗakin Baba barista ta shiga ta yi masa shara kamar yadda ta saba, gab da za ta fito taga littafin da ta gani kwanaki, cikin sauri ta ɗauke shi tare da fitowa. Haka kawai zuciyarta ta soma janta da ta ɗauke shi ƙila ya yi mata amfani. Ba ta wani tsaya jinkirtawa ba ta ɗauka tare da rufe ɗakin bayan ta kuna tsintsiyar ƙamshi.

Tana fitowa suka yi kiciɓus da kawu, saurin ɓoye littafin ta yi a bayanta amma ta makara domin ya gani kuma sai da ya tabbatar ya rabata da shi sannan ya ba ta hanya ta wuce. Ranta ya ɓaci sosai, don haka ma ko da ta fito Baba Laure na tsokanarta ba ta tsaya sauraronta ba. Tana jinta tana faɗin,

“Uwar ɗakina ina kuma za a je?”

Ko juyowa ba ta yi ba saboda yadda take jin zafin karɓar littafin, sai kuma ta soma mamakin kanta kan mene ne alaƙarta da littafin da za ta ji haushi har haka. Kai tsaye ɗaki ta koma ta shirya cikin shigar doguwar riga tare da yane kanta da mayafi. Wayarta ta ɗauka tare da karata a kunnenta bayan ta lallubo lambar da take nema.

“Assalamu alaikum”

Ya furta cikin nutsuwa, daga can ɓangaren aka amsa mata cikin shauƙi da kuma nuna kulawa,

“Baba Barista kana chamber ne?” Ta faɗa tana ƙasƙantar da kai tamkar yana gabanta,

“Ina nan ɗiyar albarka. Da wani abu ne?” Ya jefo mata tambaya.

“Babu kamai, kawai dai ina so in ganka saboda wata muhimmiyar magana!”

“Ba za ki bari sai na dawo ba?”

“A’a Bab….”

“Ok, shi ke nan! In shaa Allahu ina nan, ki ƙaraso.”

Da “to” ta amsa bayan ta ɗaga kanta kamar ƙadangaruwa. Da sauri ta ƙarasa haɗa duk wata shaidar karatu da ta san za a buƙata. Kai tsaye ta yi wa Baba Laure sallama tare da sanar mata Baba Barista ne ya ce ta zo yana nemanta. Gudun ta tsayar da ita da dogon jawabinta ya sanya ta zame ta yi gaba tana ta sauri.

*****

Lokacin da ta isa office shi kaɗai ta samu, kanta a ƙasa ta yi masa bayanin abin da ya yake tafe da ita. Take ta ga fuskarsa ta bayyanar da tsananin farinciki,

“Aufana dama ai ke kika ƙi soma aiki. Amma ba ya ga ni da nake san aikinki, akwai chamber da yawa na ƙungiyar lauyoyi da take maraba da ke. Musamman ta ɓangaren gwamnati, amma nafi so ki yi aiki a matsayin lauya mai ‘yanci ba wai ta gwamnati ba. Ba zan hanaki aiki da gwamnati ba domin gwamnati mu ne tun da mu take mulka, amma dole ki raba ƙafa. Dan haka kada ki damu kina da gurbi a nan”

 Dariya ta yi mara sauti. To ranar dai haka ta yini tare da Baba barista yana nuna mata abubuwan da suka kamata. Washegari ma haka. Sai dai bisa dukkan alamu kawu Kamala ba ya maraba da hakan, amma babu yadda zai yi. Cikin abin da bai gaza wata biyu ba, duk wani abu da take buƙata ya kammala. Da taimakon Babanta da kuma na ubangiji ta samu gurbi har ta soma gabatar da aiki yadda ya kamata.

Ta jagoranci shari’a kamar guda biyu kuma ta yi nasara, burinta na bincikar rayuwar Sadiya ya nan a ƙasan ranta. Sai dai baban tashin hankalinta ta lura kamar akwai wani abu ƙarƙashin hakan. Domin zuwanta ya kai uku neman mahaifiyarta ba ta samunta.

*****

Jingim Naman Jaki

Gabaɗaya fuskokinsu cike suke da farinciki. Alhaji Labaran ne ya muskuta,

“Alhaji Sammani kasan wani abu kuwa?”

“Sai ka faɗa Babban goro!”

“Ban taɓa tsamanin abin da Boka Jatau ya faɗa zai ɗauki tsayin shekaru haka ba. Ba mu taɓa samun yaron da taurarinsa kullum haskawa suke yi kamar Gundul ba.”

“Ba kai kaɗai ba, hatta ni ina mamakin baiwarsa, yana da saɓani fiye da tsamaninka, duk lokacin da wani hari kan kayanmu zai zo to sai ya bar wajen. Kuma baiwarsa ce a haka amma fa na lura kamar akwai ginshira a cikin idanunsa!”

“Ba ko kwanto kake yi ba Alhaji Sammani, ba don wani waigi ba da tuni Gundul ya suɓucewa muradanmu sai dai abin da be sani ba kifi na ganin mai jar koma.”

Ba su yi aune ba ya turo ƙofar ya shigo fuskarsa babu walwala. Gabaɗaya sun sha jinin jikinsu,

“Gundul mene ne haka za ka shigo mana babu izini?”

Sai da ya shaƙa sannan ya numfasa,

“Mutum da gidansu sai ya nemi izinin shigowa?”

Ya buƙata cike da ci da zuci, waskewa suka yi, Alhaji Labaran ne ya yi magana fuska ba annuri,

“Ina sadakin amaryar da Hamana ya biya?”

“Na manta in da na ajiye su…”

Wata irin zabura Alhaji Sammani ya yi, ya miƙe,

“Kana da hankali kuwa Gundul? Wannan maƙudan kuɗin za ka ce ka manta inda ka ajiye su….”

An zo in da yake so, don haka ya ƙara haɗe fuska kamar kashin shanu,

“Amma dai kai da bakinka ka sanar da ni ina da cutar mantau lokaci zuwa lokaci ko? To ƙila ita ce ta motsa na manta in da na jefa su”

Daga haka bai sake cewa komai ba, ya fita yana ciccila hannuwa. Da idanu suka raka shi, yana fita Alhaji Sammani ya buga benci yana huci kamar zai tashi sama. Zarginsa ya fara zama gaskiya, amma zai yi wa tufkar hanci. Wayarsa ya zaro tare da karata a kunnuwansa,

“Yaushe rabon da ka sakawa fatsarmu kifinta?”

“Alhaji tana zuwa tana farauta duk lokacin da kuka gindaya mata”

Aka faɗa daga ɗaya ɓangaren,

“Amma me ya sa take ƙoƙarin fita daga komarmu?”

“Ƙila dai zaren da kuka ɗaura mata ne yake neman tsinkewa”

Kiran ya katse bayan ya buƙaci a ƙara sama da abin da fatsar take buƙata. Alhaji Labaran na zaune, bai tanka ba, amma da alama akwai abin da yake shiryawa. A ɓangaren Gundul kuwa duk abin da suka tattauna a kan kunnuwansa. Murmushi ya yi tare da furta,

“Kun mayar da rayuwata turken jaki, ni kuma sai na zame muku ƙadangaren bakin tulu”

Kai tsaye gida ya nufa ya yi wanka tare da shiryawa cikin manyan kaya. Tsaye ya yi yana ƙarewa kansa kallo a mudubi. Ga shi dai mutum har mutum amma a zuciyarsa yana jin shi ɗin kura ce da fatar akuya. Wasu ƙwalla ya ji suna shirin zubo masa amma ya yi ƙoƙarin mayar da su.

Tun ɗazu ya shigo yana tsaye a bayansa amma bai san da wanzuwarsa ba, sai da ya yi magana,

“Kuka ai yanzu ka fara tun da rayuwar da ka zaɓa kenan!” Amon muryar ya bashi tabbacin mammalakinta, kuma yana da yaƙinin idan ba shi ba babu mai yi masa kutse haka. Dan haka ya ji zafin zuciyarsa ya ƙaru fiye da baya, a fusace ya juyo yana huci kamar matashin ɓauna yayin da yake diri kamar mahaukacin kare.

“Zuwa yanzu ya kamata a ce ka ɗauki na damo domin ba zan taɓa bin ra’ayinka ba. Rayuwarka ba rayuwata ba ce kuma ƙabarin kowananmu daban Abdallah”

“Duk da haka Gundule, ni ma na ɗana na kiranka da yaren da ka fi ganewa amma ka sani ramin ƙarya ƙurare ne. Kuma ina da yaƙinin sallamar ɗayanmu cikin ƙabari za ta maƙale a gurbin sallamar zuƙatanmu!”

Bai jira ya sake tankawa ba ya ɗauki jakarsa ya ratse gefansa ya wuce, har yana bangaje kafaɗunsa,

“Ka je ka dawo ka zo ka bayyana min lokacin da ka kashe Sadiya?”

Cak! Ya tsaya sai dai bai juyo ba, amma kuma kaɗuwarsa ta bayyana har kan dugadugansa da suka nuna alamar jikinsa ya yi musu nauyi,

“Ban san yaushe ka fara rinton zunubi ba!” Ya furta cike da juriya,

“Za ka tabbatar da hakan yayin da na bayyana maka inda ka je a ranar talatin da biyu ga watan da ya gabata da kuma takardun da suke nuna shaidar motar corolla mai lamba 3468 taka ce. Amma fa wannan ba komai ba ne, kawai wata ƙaramar shaida za ka ba ni ta goge wannan tun da ni kaɗai na mallaki waɗanan shaidun”

Zuwa lokacin duk wani ƙwarin gwiwarsa ya ƙwace, amma jin abin da ya furta sai ya samu wani karsashi. Ya tabbatar duk runtsi ba zai tozarta shi ba, kawai barazana ce,

“Barazana ce ko?” Ya buƙata yana gyaɗa kai.

“Haka ranka yake ba ka barazana nake yi maka ko, wallahil azim a wannan gaɓar zan yi komai dan tabbatuwar ƙimarka ta kwaranye a idon ko ma waye ko da kuwa zan rasa bugawar numfashina.”

Bai ba shi damar magana ba ya janye shi ya fita ya bar masa ɗakin. Jiki a mace shi ma ya bar ɗakin. Kai tsaye inda ya sa ran zuwa ya nufa zuciyarsa babu daɗi rabin farin cikin da ya samo na ƙuntatawa su Alhaji Labaran ya kwaranye. Tun da ya shiga mota yake tunanin kalaman Barrister Abdallah. A haka ya ƙarasa gidan marayun wanda yake a bayan gari sosai.

Shi ɗin ba baƙo ba ne a gidan, ya kai shekara biyar da fara gudanar da abin da yake ganin zai rage masa dakon zunubansa, sai dai a wani ɓangaren yana ganin wautarsa kamar yana nunka zunubansa ne ta hanyar ciyar da marayun Allah da dukiyar da yake da tabbacin haramcinta.

Kansa ya ji yana wani irin sarawa, haka ya daure ya fito nan da nan yaran suka zagaye shi. Farfajiyar wajen ya samu ya zauna wasu suka kewaye shi wasu kuma suna zaune a jikinsa. Ɗaya bayan ɗaya yake kallonsu wani abu na tsarga zuciyasa. Mukulli ya bayar aka soma kwasar kayan da ya zo da su. Duk wani nau’in buƙata ya yi ƙoƙarin samar da shi, kama daga kan; sabulu, omo, abinci, sutura har ma da kayan wasa ga ƙananun yaran cikinsu.

Nan da nan yaran suka shiga yin murna da farinciki,

“Baba Allah ya shiga lamuranka!”

Wata ƙaramar yarinya ta furta a cikinsu,

“Yadda ka faranta mana Allah Ya faranta maka!”

Wata ta sake faɗa, gabaɗaya sai suka karyar masa da gwiwa. Zuciyarsa ta tattare da wani irin yanayi da ya kasa fahimtar mene ne. Nan da nan ya yi musu sallama tare da nufar office ɗin mai kula da su ya cike wasu takardu ita ma ya yi mata sallama.

Yana shirin fita ɗaya daga cikin ma’aikantan ta shigo. Fuskarta ɗaure da niƙab ta sanarwa mai kula da wajen suna da baƙi. Tun da ta shigo yake kallonta, amon muryarta ya fi komai ɗaga masa hankali. Sai dai babu kafar da zai kalli daidai da farcenta domin bayan nikaf akwai hijabi dogo tare da safuna a ƙafa da hannuwanta.

Ratse shi ta yi ta wuce,

“Halima!”

Mai kula da wajen ta kira sunanta, amsawa ta yi da muryar da ta saka gabansa faɗuwa har ya lula wata duniyar kafin ya ankare har ta yi abin da ya kawota ta bar wajen. Har zai fita ta kira sunansa

“Baban yara kamar akwai damuwa?”

Ƙure ta ya yi da idanu, kamar zai tanka sai kuma ya girgiza kai,

“Babu na tafi” Ya furta tare da juyawa cikin sassarfa a kan dugadugansa yake takawa amma kowane taku yana nasar masa da wani irin tabo mai zafi a zuciyarsa. Yayin da sunan Halima ya ci gaba da amsa kuwa cikin kansa.

*****

Misalin ƙarfe biyar tana zaune kan kujerar office ɗinta wanda yake kusa da na Baba Barista. Tsam ta yi tana tunani tare da gode wa Ubangiji, kaf chamber ɗinsu yanzu babu matashiyar lauya mai ƙarancin shekarunta wadda take tashe tare da samun nasara kamarta.

Wannan kaɗai ya ƙara mata wani irin farinciki, musamman yadda ba ta taba haɗuwa da wata matsala ba a duk shari’ar da ta gabatar. Kai tsaye ta soma haɗa kayanta saboda ƙaratowar lokaci kuma garin akwai alamun hadari. Wani sashi na zuciyarta ne ya faɗo mata da batun Sadiya, ta taune gefan bakinta cike da takaici. Tun da ta fara aiki shi ne abu ɗaya da ta ƙwallafa rai kuma yana neman gaggararta.

Duk da ta san cewar tana da ci-da-zuci amma haƙurinta na neman gazawa. Tana jin kamar ta fito ta yi shela wa duniya. Kai tsaye abin hawa ta nema ta nufi hanyar gida. Tafiya suke a babur mai kafa uku, amma zuciyarta ta hau jirgin yawo ta lula duniyar tunani. A daidai kan kwanar titin da ke daura da gidan man fikra, danja ta tsayar dasu. Wasu gungun almajirai ne suka taho da gudu suka yayyaɓe motocin. Take wani takaici ya mammaye zuciyarta musamman ganin yadda ake hantararsu.

“Bayin Allah a taimaka fisabilillahi. Wai zai taimaka saboda Allah”.

Kalolin muryoyi ne kawai suke tashi a tsakanin danjar, motoci da babura duk tsun cake. Makafi, guragu, kutare, da wasu da kallo ɗaya za ka yi musu ka tabbatar da lafiyar su, amma haka suke bin motoci da babura suna neman taimako.

Wasu na ture wasu masu kananun yara sai zabga ihu suke saboda yanayin zafin rana da ya ƙwale a titin.

“A taimaka bayin Allah…Hajiya Alhaji a taimaka, Rabbi ya sauke ku lafiya, Rabbi ya kare ku daga sharrin karfe”.

Muryar wata dattijuwa ta da tsaya jikin wata mota kirar Benz mai kalar baƙi sai ɗaukar idanu take gilasanta duk baƙaƙe ba ka ganin wanda yake ciki sai dai na cikin ya ganka. Dattijiwar duk da ba ta ganin na ciki amma hakan bai hana ta ci gaba da neman taimakon ba hannunta jikin gilashin.

Wani abu ne ya tsarga mata har babban yatsan ƙafarta. Sai ta samu kanta da sanar da me napep ɗin a nan za ta sauka. Kai tsaye wajansu ta nufa, a daidai lokacin da danja ta saki hannu wata mota ta kwaso a guje ta yi gaba da wata matashiyar yarinya.

Da gudu ‘yan uwanta almajirai suka yi kanta, motar kuwa sai ma ƙara mai da ta yi cikin sauri ta saka idanunta kan lambar motar sai da ta tabbatar na ɗauketa a kanta sannan ta samu nutsuwa tare da mayar da hankalinta inda abin ya faru.

Ƙarasawa ta yi wajen, jikinta babu inda ba ya rawa tsabar mamaki da takaici da kuma tashin hankali sai dai kuma rai ya yi halinsa,

“Allah Ya ƙara muku, mutane sai jarrabar tsiya babu tawakali me ake da bara?’

Wani mutum ya furta yana buga babur ɗinsa, ta ji zafin maganarsa duba da yadda mahaifiyar yarinyar take kuka kamar ranta zai fita. A wannan yanayin ta juyo tana dubansa,

“Ina roƙon Ubangiji da kada ya ƙaddara wa ko maƙiyina kwatankwacin rayuwar da muka fuskanta har ta kai mu ga zuwa wannan bigiren. Baka san ƙaddara da ta faɗa mana ba, kuma ba ma buƙatar ka sani domin da alama akwai raunin imani a zuciyarka!”

Take jikin mutane da yawa ya yi sanyi, ƙoƙarin kama yarinyar take wadda ta kasance cikin jini. Sai ga jami’an tsaro sun iso wajen. Nan da nan suka fara yin abin da ya kamata. Wani da na lura kamar shi ne babba cikinsu wajensa ta nufa. ID card ɗinta ta zaro tare da nuna masa,

“Sunana Aufana Halima Labaran. Ni ma’aikaciya ce  da ta shafi ɓangaren shari’a (law) na yi karambanin ɗaukar muku lambar motar da ta bige yarinyar”

Tsananin farinciki ne ya bayyana a fuskarsa,

“Tabbas kin yi aiki mai kyau, kuma da alama ke ɗin jajjirtaciya ce tun da har ki ka iya wannan ƙoƙarin. Bayan an tabbatar da motar tana bige yarinyar ta ƙara gudu lallai ya kamata a yaba miki!”

Murmushi ta yi bayan ta miƙa masa, ta kuma tabbatar da ta adanata (save) ɗinta cikin wayarta, har ta juya za ta tafi ya furta,

“Ko zan iya samun lambar wayarki?”

Sanin hakan zai iya faruwa ya daɗe da zuwa kanta, domin ta san dole sai an buƙaci ganinta a gaba. Ba ta jinkirta ba ta ba shi tare da barin wajen cikin sauri. Tana ƙoƙarin hawa wani napep ɗin ta ji an dafa kafaɗata. Juyawa ta yi suka yi ido biyu da ɗaya cikin almajiran,

“Kin kyauta ƙwarai da gaske, tabbas albarka ita ce za ta jiɓance ki, sai dai akwai wani duhu da yake manna da mafarin ƙaddarar rayuwarki. Ki yawaita sadaka akwai haske na nan zuwa…!”

Kafin ta buɗe bakinta ta yi wuf ta bar wajen, ƙoƙarin bin ta ta yi a baya amma kuma ba ta ganta ba. Ba ta buɗe fuskarta ba amma akwai abin da take gani cikin idanunta waɗanda suka yi mata kama da idanun da ta sani,

“Anna!”

Wani sashi na zuciyarta ya faɗa mata cikin raɗa, kanta ta girgiza da sauri tana jin bugun ƙirjinta na ƙaruwa.

‘Ina wanda ya mutu ai ba ya dawowa.’

Ta yi furucin a zuciyarta.  Jin mai napep ya balbaleta da faɗa taƙi shiga sai kawai ta shiga suka fara tafiya, amma kuma rabin hankalinta ya tafi kan tunanin wacan matar. A haka suka ƙarasa unguwarsu ta sauka jiki babu ƙwari.

Haka ta yini zur da tunanin mutane uku a ranta. Na ɗaya wannan jami’in tsaron da take tsammanin kiransa kodayaushe. Na biyu kuma tunanin wannan matar da ɗiyarta, yayin da almajirar da ta dafata a kusa da napep ita ma ta hanata sukuni cikin ranta. Sai kuma tunanin Anna. Gabaɗaya sai ta ji gidan ya gundureta. Lokaci zuwa lokaci takan duba wayarta domin tsamanin kiran wannan jami’in tsaron, amma shiru.

*****

Kwana ɗaya, biyu, uku, har huɗu, bai kirata ba, hakan ya sa ta fitar da tsammani, a ranar kwana na biyar ne ta kasa haƙuri ta ziyarci matattarar almajiran abin tausayi suna zaune sun yi layi ɗoɗɗar wajen ya zamto musu kamar gida. Masu ƙwari cikinsu ne suke kwasa da gudu zuwa wajen motoci, yayin da sauran suke zaman jiran tsamanin warrabbuka.

Ƙarasawa ta yi tana ware idanu, a can saƙo na hango mahaifiyar wannan yarinyar da hanzari ta ƙarasa bayan sun gaisa take tambayarta kan yadda aka kaya. Amma ga mamakinta sai ta ga ta fashe da kuka har ajiyar zuciya take yi, sai kuma ta miƙe zumbur ta bar wajen.

Duk yadda ta so ta yi mata bayani ƙin tsayawa ta yi ta saurareta. Haka ta haƙura ta koma gida amma kanta ya ɗaure. A taƙaice sai da ta jera kwanaki huɗu tana zuwa amma ba ta saurarenta ƙarshe ma da zagi suka rabu tana kiranta da ‘annoba’.

Zuciyarta ta yi zafi sosai sai dai ta kasa fahimtar dalilinta. Dan haka ta ƙuduri niyyar kai wa Baba Barista matsalar. Da daddare ta same shi a zaune yana duba wasu takardu. Zama ta yi a kusa da shi tare da dubansa,

“Baba wai kuwa kana ganin me zai kawo wanda aka yi wa laifi ya dinga ƙoƙarin ɓoye abin da aka yi masa”

Sai da ya ɗan yi jim sannan ya furta,

“Me ya faru ne Aufana?”

Ba ta tsaya wani kwana-kwana ba ta bayyana masa komai da ya faru. Ajiye abin da yake yi ya yi ya mayar da hankalinsa gabaɗaya kanta. Sai da ya tabbatar ta gama sannan ya fuskance ta,

“Idan har kintace na ya zama gaskiya Aufana, ‘yan sanda sun gano mai laifin, sai dai kuma ina tsammanina yana da wani matsayi da matar ba za ta iya ja da shi ba. Za su yi amfani da wannan damar su yi mata barazana ciki kuwa hada gargaɗi kan alaƙarta da ke tun da sun san wace ce ke da matakin karatunki”

Sai yanzu wani haske ya shigo cikin kanta. Tabbas batun Baba na kan hanya,

“Yanzu Baba idan har hasashenka ya zama gaskiya ran yarinyar nan ya ta fi a banza ke nan?”

“Bai tafi a banza ba Aufana, matuƙar za ki ƙarfafa mata gwiwar karɓar ‘yanci.”

‘To ba za ta yi ba.”

Kawu Kamala ya furta a zuciya, da kallo suka bi shi gaba ɗaya. Ya cigaba da magana kamar zai ta shi sama ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Gabaɗaya ya ɗaure musu kai. Sai ta ga Baba Barista ya ƙi kulashi har ya yi ya gama, ya fita. Tsam ta yi tana mamakin bambancin ra’ayin da ake samu tsakaninsu. Tun tasowarta ba ta taɓa samunsu a kan bigire guda ba.

“Kada ki damu kin ji Aufana, kin san kawunki akwai tsoro da yawan fushi”

Kai ta ɗaga masa ba don ta yadda da hakan ba, domin tun tasowarta ta san kawun nata ba matsoraci ba ne, hasalima shi sai ya yini a gida amma kuma da dare ya tsala zai fice ba kuma zai dawo ba sai goshin asuba ko safiya. Ta yi duk wani naci da ƙoƙarinta ta kasa fahimtar abin da yake fitar da shi.

“Haka ne Baba yanzu mene ne abin yi?”

Ta tambaye shi don san kawar da maganar da ba ta da tushe,

“Abu na farko da za ki yi shi ne, sai kin yi haƙuri. Matar na buƙatar kulawa da lallashi tare da ƙrfin gwiwa har ki ji abin da ya wakana. Amma me ya sa ki ke san dole sai kin ji abin da ya faru?

“Baba kada ka manta, matsalarta ta shafi ɓangarena ne, wato kare haƙƙin wanda aka zalunta. Kuma ka san burina na haɗe ne da burin Anna. Annata ta tsani zalunci da azzalumai, wannan yana ɗaya daga cikin dalilina na karantar ɓangaren shari’a!”

Ta ba shi amsa kai tsaye, kai ya jinjina tare da ci gaba da ƙwarara mata gwiwa. Sun jima suna tattauna matsaloli irin haka har ya tabbatar ta samu gamsuwar da ta dace, sannan ya ba ta umarnin tashi.

Ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen amfani da shawarwarinsa, cikin kwana uku ta samu matar ta soma sakewa da ita. Ranar Litinin da wuri ta shirya ta je wajenta. Misalin ƙarfe biyu da rabi na rana bayan sun fito daga wata shari’a ta same su a zazzaune. Wajen da babu yara sosai suka nufa, a kusa da wata dattijuwa suka zauna sai kuma wata mace da kai tsaye za a iya sakata a sahun matsakaita. Dubanta ta yi cikin kulawa,

“Ki daure ki bayyana min abin da ya faru?”

Sai da ta juya kamar tana neman wani abu, sannan ta yi ƙasa da murya,

“Yaron da ya bige ta ɗa ne ga wani babban ɗan siyasa mai suna Alhaji Labaran Tanimu. Ɗan sanda da ki ka ba lambar motarsa shi ne ya tabbatar min da hakan bayan sun yi ƙwaƙwaran bincike. A ƙarshe ya gargade ni da idan ina son na tsira da raina, to na haƙura da batun rasuwar ‘yata!”

Ta ƙarashe tana kuka, da ido ta bi ta, gabaɗaya tausayinta ya kamata. Mamaki da takaicin al’ummar ƙasarta ya baibaye ta. Wai jami’in tsaro guda shi ne yake umartar ɗan ƙasa da ya binni zaluncin da aka yi masa. Wannan wace irin ƙasa ce?

“Za ki iya kwatanta min wane sitation ne?”

“Ki yi haƙuri, sun gargaɗe ni a kan alaƙata da ke, tare da yi mini barazana me ƙarfi, domin har yaron da ya aikata laifin na gani. Na so ace ina da muryar faɗa aji, da na ƙwatarwa ɗiyata ‘yancinta sai dai hakan ya gagara.

Ban ƙara tsanar rayuwar bara ba sai ranar da ɗan cikina ya ɗauki hannu ya tsinke ni da mari da sunan barazana kan rufe bayanin wanda ya kashe min ɗiyata. Lallai wannanƙasa tamu ta tabbata ƙasar da ba ta san ‘yanci ƙima da darajar talakawanta ba. Masu madafun ikonmu sun….

“A’a Mama kada ki ce haka shugabaninmu suna ƙoƙarinsu matuƙa, sai dai kowane waje akwai na kirki akwai na banza. Tabbas kisa a ranki akwai ranar da hawayenku zai daina zuba. Amma kuma ya kamata ku yi wa rayuwarku kyakkywar makoma. Bara ba ta kama ce ku….”

“‘Yar nan,” Ta katse ta sannan ta ci gaba. “Ba za ki fahimta ba, ba za ki fahimci raɗaɗin da muke ji a yayin yin bara ba. Kalmar ‘bara’  kalma ce da ta kasance abokiyar gaba, ga duk wanda ya san ciwon kansa da kuma abin da kalmar take nufi na ƙasƙanci da rashin martaba, da mai yin ta ake nuna masa.

Al’umma da yawa suna yi wa bara kallon abin yi, ga waɗanda suke da matacciyar zuciya. Wato zaɓi ke nan. Wasu kuwa ana yi musu kallo ne a matsayin wanda ƙaddara ta zaɓa musu yin barar, suna yin ta ne ba a son ran su da zuciyar su ba. To kamar haka ne a kan kaina da rayuwar ɗiya ta da ta salwata.

Kamar yadda alƙalamin ƙaddararmu ya mallaka mana wannan babbin a cikin shafukan kundin da muka rungumo. Haka muka saka hannuwa bib-biyu muka karɓe shi duk da zuciyarmu ta daɗe da tsanar wannan kalmar a ko wa ce daƙiƙa.

Sai dai kash! Sai kalmar ta ‘bara’ ta yi wa rayuwarmu ɗaurin talala, wacce muka rasa ta yadda za mu warwareta. Rayuwar bara ta kasance mana tamkar rigar siliki a duk lokacin da muka yi ƙoƙarin daƙile kanmu a cikinta, sai wani abu mai girma mai karya mana ƙwarin gwiwa da zuciya ya gifta, ya ƙasƙantar mana da duk wani ƙokarinmu. Kuka sai ya maye gurbin komai….”

Kuka ne ya ci ƙarfinta, wanda zuwa lokacin da yawan matan sun zagaye su suna suraranta,

“‘Yata ‘yar shekara goma mai mota ya kashe min ita. Ba wanda ya dube ni bare ya tallafa mini, mutane da yawa cewa suke da ni matacciyar zuciyata ta ja mini. Ba ni da kowa bayan ita tun da muka baro garinmu dalilin ‘yan ta’adda da suka kashe mana mazaje….”

Jikinta ya yi sanyi matuƙa, sai yanzu ta fahimci asalin wacce ce matar. Kalamanta suka kasa barin zuciyarta.

“Ina jin ciwo a duk lokacin da na sanyo ƙafa da sunan zan fito bara, zuciyata ji nake tana ƙonewa”.

Yanayin muryar matar ya raunana, zuciyar Aufana sosai. Har ta ji wani tsoro mai firgitarwa ya saukar mata lokaci guda. Kallon matan take, tana hango ciwuka masu girma da suke kewaye da rayuwarsa. Sai dai rashin matallafi da rashin inda za su dosa bara ta kanannaɗe masu rayuwa.

“Mijina guduwa ya yi ya bar ni da ‘ya’ya takwas, duka mata. Iyayena duk sun rasu. Danginsa ba mai taimaka mini, bare na ji a rai ina da abin  dogaro da kai da zan tallafi marayun nan.”

Wata ta sake faɗa a gefanta. Hawaye suka zubo mata a kunci, ta shiga gyaɗa kai murmushi mai ciwo na bayyana a fuskarta.

“Ba zan iya sai da mutuncina da martabata da darajata  ba. Ba ni kaɗai za ta kanannaɗewa rayuwa ba, har da ‘ya’yana, wasu mutanan suna da son zuciya. In za su taimaka maka sai sun so bukaci raba ki da mutuncinki, shi ya sa na rike a matsayin zaɓi, zabi a saboda ba ni da wani zabin bayan ita.

Da mamaki Aufana take dubanta duk da shekarunta ƙanana ne ta fahimci kalmomi da ma’anoninsu sosai na matar nan. Nan da nan zuciyarta ta shiga rawa, wani tsoro mai girma yana naɗe mata rayuwa.

A ranta ta ji ba za ta iya  barin rayuwar waɗannan bayin Allah ta gurɓace ba tana kallo.  Barin ma yadda take jin labarin yadda wasu marasa tausayi suke wa matasa ‘ya’ya mata  marabata ta  tabbata komai zai iya faruwa. Don haka ta ware murya tare da dubansu baki ɗaya,

“Kuna buƙatar ‘yanci?”

“Muna buƙatar ‘yanci”

Da murya mai amo suka amsa mata, hakan ya haifar mata da wani irin karsashi a ranta. Ta ci gaba,

“Sai kun kawar da tsoro, sai kun yadda cewa bara ba ita ce madafar rayuwarku ba!”

A taƙaice Aufana ba ta bar wajen ba sai da ta tabbatar ta gina da yawansu kan abin da zai amfani gobansu. Haka kuma sai da ta samu cikakken bayani game da sitation ɗin da case ɗin matar nan yake. Ta kuma ƙuduri a niyyar zuwa domin tabbatuwar ‘yancin su.

*****

Da wannan burin ta kwanta yayin da rayuwar mabaratan ta yi tsaye cikin ranta. Misalin ƙarfe shabiyu na dare ta farka da wata irin matsananciyar yunwa. Mamaki ne ya kamata ganin kwanaki biyu ke nan tana fama da irin wannan yanayin. Hakan ya tabbatar mata da sakacin da take wajen cin abinci ciwon yunwa na neman kamata.

Kai tsaye ɗakin girki ta nufa, domin ta duba ɗakinta ko ɗan biskit babu. Gab da za ta shiga kicin ta jiyo nishi sama-sama a ɓangaren ɗakin Baba Laure. Ƙirjinta ya buga, ta nufi wajen cikin sanɗa har ta kai ƙofar ɗakin. A lokacin nishin ya ƙaru fiye da baya, da hanzari ta tura ƙofar ɗakin tare da kutsa kai. Ganin Baba Laure a sassandare, hakan ya sa ta ƙwala ƙara, wadda ta zamto silar jawo hankalin Baba Barista da yake gabatar da sallahr nafila.

A guje ta fito suka yi karo, yana tambayarta abin da yake faruwa ɗakin kawai take nuna masa da hannu. Shiga ya yi ta bi bayansa nan suka same ta ko motsi ba ta yi. Da hanzari ya tambayeta,

“Aufana me ya same ta?”

“Baba ban sani ba na fito zan shiga kicin na ji yo nishinta….”

Shigowa Kamala ya yi, sai dai bai yi magana ba ganin halin da take ciki. Nan da nan suka kinkime ta suka saka ta a mota. Kafin su je asibiti gabadaya ta daina motsi. Aufana ban da kuka babu abin da take yi, gani take kamar za su rasata ne. Suna zuwa aka karɓe su aka wuce da ita ɗakin taimakon gaggawa. Ban da kai wa da komowa babu abin da Baba Barista yake yi. Sun share kusan awa ɗaya sannan likitan ya fito, kwantar musu da hankali ya yi tare da ba su tabbacin za ta samu lafiya. Daga bisani ya ba su tabbacin za su iya tafiya.

Aufana ce ta dage kan ita sai ta kwana wajenta. Dan haka suka tafi suka bar ta da sharaɗin za su dawo da sassafe. Haka ta kwana ba ta runtsa ba, gabaɗaya gani take idan ta runtse idanu kamar za ta rasa Baba Laure.

Tun bayan rasuwar mahaifiyarta ita take buɗar idanu ta gani matsayin uwa. Baba Laure ce ƙawarta, ita ce abokiyar shawararta, dan haka take ji kamar za ta rasa wani ɓari na jikinta ne. To shi ma Baba Barista ta ɓangarensa kasa runtsawa ya yi, wanda rabin tunaninsa na ga yadda Aufana za ta shiga damuwa ne. Dan haka bai wani yi baccin kirki ba. Kiran farko kuwa ya miƙe a masallacin asibitin ya yi sallah. Daga bisani bayan gari ya waye ya shiga wajen nasu.

Ya samu Aufana tana zaune tana gyangyaɗi, da ganinsa ta miƙe ta isa wajansa muryarta ta yi sanyi sosai ta gaishe shi. Amsawa ya yi yana dafa kanta,

“Kada ki damu kin ji Aufana, Baba za ta samu lafiya!”

Kai ta jinjina masa kawai tana share ƙwalla. Bayan sun zauna yana ɗan janta da hira a haka Kamala ya same su, hannunsa niƙi-niƙi da kayan abinci. Sai da ya ajiye sannan ya ɗan harari ɓangaren da yake,

“Ka kyauta da ka baro ni ai ba gurgu ba ne!”

Yana shirin ba shi amsa likita ya shigo bayan sun gaisa ya janyo file ya dudduba abin da ya kamata. Daga bisani ya nemi ganin Baba Barista a office ɗinsa. Ganin Babar bacci take ya sa ya ja hannun Aufana suka rankaya tare Kamala na biye da su a baya. Suna shiga office ɗin ya zauna, Aufana na tsaye hakama Kamala. Dubansa Dr. ya yi,

“Kai kaɗai na nemi gani ka shigo min da mutum har biyu, ka karya min dokar aiki!”

Murmushi ya yi,

“Dukanmu babu bare, mara lafiyar mahaifiyarmu ce!

Ya ba shi amsa kai tsaye, kafaɗu likitan ya ɗaga tare da furta,

“Is ok, dama abin da ya sa na kiraka magana ne kan mara lafiyar da kuka kawo. Yaya aka yi kuka yi sakacin barinta ta kwanta a ɗaki me zafi ana wannan yanayin na tsananin zafi?”

Gabaɗaya sai suka rasa bakin magana, domin abin ya ba su mamaki. Ɗakinta akwai fanka akwai na’urar sanyaya muhalli (air condition/AC). Don haka Baba Barista ya yi saurin katse shi,

“Likita anya kuwa domin babu abin da babu na buƙatar sanyaya waje a ɓangarenta?”

Caraf Aufana ta katse shi,

“Baba ka yi haƙuri zan saka muku baki. Wallahi Baba kashewa take yi ta ce wai ita ba za a sakata yin mura ba, ko labulan ɗaki ba ta bari a ɗaga sai ta ce wai ƙuda zai dame ta”

“Amma kin taɓa faɗa min?”

“Ka yi haƙuri gani na yi….”

Katse ta ya yi tare da duban likitan,

“Yanzu mene ne aihinin matsalarta?”

“Abin da yake damunta gaskiya shi ne anobar nan ta cutar sanƙarau”

“Sanƙarau!”

Suka haɗa baki su duka ukun, kai ya jinjina,

“Ƙwarai kuwa cutar sanƙarau kuma ciwo ne mai haɗari da illa babba”

“Kamar yaya ke nan likita?

“Ba zan jaku da nisa ba, amma zan muku bayaninsa a taƙaice. Ciwon sanƙarau wani nau’in ciwo ne da ƙwayoyin cuta ke mamaye mayafin da ke lulluɓe ƙwaƙwalwa da lakar wuya da kuma gadon baya wato (meninges) a turance. Akwai nau’o’in ciwon sanƙarau daban-daban wanda ƙwayoyin cuta iri-iri ke kawowa.

Ƙwayoyin cutar bacteria ne da ake kira (Neisseria meningitidis) ke kawo nau’in sanƙarau ɗin da muka fi sani. Su waɗannan ƙwayoyin cuta suna nan a cikin iskar da muke shaƙa mai zafi. Hasali ma kashi ɗaya cikin biyar a cikinmu masu lafiya na ɗauke da waɗannan ƙwayoyin a hancinmu da maƙogoaronmu ba mu sani ba.

Ta haka ake yaɗa su in an yi kaki an tofar ko kuma ta iska a wuri mai cinkoso. Ƙwayoyin cutar mutuwa suke da sun ji sanyi. Don haka da wuya a yi sanƙarau lokacin sanyi. Idan aka shaƙe su ta hanci ƙwayoyin na samun shiga jiki har jini ya kwashe su ya kai mayafin ƙwaƙwalwa. Nan da nan alamomin cutar suke bayyana….”

Cikin hanzari Aufana ta ce,

“To ya alamomin ciwon suke? “

“To zalƙun muzalaƙo ɗa daga ciki roƙon uba kwabo. Ai kya jira ya ƙarasa ko?”

Kawu Kamala ya katseta yana ɗaga hannu kamar zai make ta. Baya ta yi ta ɓuya bayan Baba Barista. Sai suka ba likitan dariya, ya yi murmushi tare da furta,

“Ta kyauta da ta tambaya don ni a ra’ayina nan zan tsaya da bayani na amma tun da ta tambaya ba zan watsawa garinta ƙasa ba. Alamomin ciwon sanƙarau ya fi kama yara ‘yan shekara biyar zuwa goma. Amma a lokaci na annoba zai iya kama kowa ma. Alamomin ciwon suna da yawa amma ga kaɗan daga cikinsu:

Da farko dai a kan ji ciwon kai mai tsanani. Zazzaɓi, sai sanƙarewar wuya. Wasu lokutan kuma akwai amai, rashin son ganin rana ko haske. Wasu kuma sukan suma tare da ɗaukewar numfashi akai-akai wanda yakan sa a rasa mutum.

Akwai hanyoyin kariya domin gudun afkawa wannan ciwo musamman a lokacin annoba. A tabbatar akwai wadatar iska a ɗakin bacci ta hanyar  tagogi buɗaɗɗu a kalla biyu masu kallon juna. Idan taga ɗaya ce abar ƙofa a buɗe musamman idan mutane fiye da biyu ne a ɗakin kuma ya zamana babu abin sanyaya waje kamar fanka ko AC.

Idan yanayin zafi ya kama a yawaita zuwa asibiti domin a karɓi allurar riga kafin ciwon sanƙarau. Sai face majina inda ya dace ba a cikin mutane ba. Idan wani na kusa a gida ko wurin aiki ya kamu da ciwon to duk mutanen wurin ko da ba su yi ciwon ba su je su karɓi magani a asibiti.

A yi saurin kai wanda ya kamu da wannan ciwon asibiti don gudun yaɗa cutar ko ya galabaita. A yawaita cin abinci mai gina jiki da shan kayan itatuwa na marmari masu tsabta musamman ga yara don ƙara ƙarfin garkuwar jiki, masu iya kashe ƙwayoyin cutar tun kafin su isa ƙwaƙwalwa.

Sanƙarau yana haifar da ɗaukewar ji na tsayin lokaci, ko kuma ɗaukewar muryar mai ciwon ya zama ta shaƙe matuƙa har ba’a iya jin sautin mai magana. Wannan kaɗan ke nan daga bayani kan sanƙarau”

Godiya suka yi wa likitan tare da baro office ɗin. Suna shiga suka samu ta farfaɗo amma har zuwa lokacin wuyanta bai gama daidaita ba, domin da filo take jingina. Sannu suka yi mata yayin da suka zauna. Aufana ce za ta soma mitar kashe fanka da Babar take yi Kamala ya tsawarta mata. Cikin kwana biyu sai ya zamana zaryar asibiti ta sanya tilas Aufana ta ajiye komai a gefe ta mayar da hankalinta kan lafiyar Baba Lauran. Cikin ikon Allah ta sami lafiya aka sallame ta, suka dawo gida. Nan kuma suka mayar da hankali matuƙa wajen kulawa da ita yadda ya kamata. Sai da ta ware sosai sannan Aufana ta koma bakin aiki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fitsarin Fako 6Fitsarin Fako 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×