Skip to content

Fitsarin Fako | Babi Na Biyar

0
(0)

<< Previous

Rashin Sani Ya Fi Dare Duhu

Sosai Abdallah ya mayar da kai wajen aikinsa. Nan da nan sunansa ya zagaye alƙarya sakammakon duk shari’ar da ya sa gaba sai ya cimma nasara. Kuma ba ya tsayawa kan rashin gaskiya. A wanan tsakanin ne maganar aure ta kankama tsakanina da shi. Aufana ta fi kowa farinciki da walwala.

Yaya Kamala kuwa ƙiri-ƙiri ya nuna ba ya murna da hakan. Katon gida ya gina mana mai kyau da tsari. Bayan an ɗaura aurena  da shi aka yi gajeriyar walima mai ƙayatarwa. Daren ranar ba zan iya fayyace farincikin da na yi ba. Ban taɓa tunanin zan ga wannan rana ba sai da shekaruna suka ja ga Aufana har ta zo aji biyar a sakandire.

Zaman lafiya da kwanciyar hankali shi ne abin da ya gudana a zamantakewarmu. Kasancewar ana kan ƙadamin siyasa, Abdallah ya soma yunƙurin samar da dalilan durƙusar da Alhaji Labaran.

Mun haɗa dabara da shi ya sa na dauko wayar Yaya a ɓoye, ya yi amfani da fasahar da ya koya a kasashen waje, ta yadda duk wayar da Yaya zai yi yana saurarensa ba tare da ya sani ba. Duk lokacin da yaya ya amsa kiran karɓo wasu kaya kafin ya je sai dai su riski jami’an tsaro sun kai sumamme wajen.

Haka ya yi matuƙar ɗaga hankalinsu sosai, gabaɗaya dukiyar Alhaji Labaran ta soma yin ƙasa. Sai dai duk iya hangensu sun kasa gano dalilin afkuwar hakan. Sossai Alhaji Labaran ya tashi hankalinsa. Ya kuma tsananta bincike kan abin da yake faruwa.

Rabuwa Da Masoyi

Ranar wata littanin da safe muka tashi da tafiyar da Abdallah zai yi zuwa garin Abuja domin hallatar wata shari’a a kan fyaɗe. Ransa a ɓace yake sosai, domin yadda ake haikewa ‘yanmata a ɗan tsakanin ya ta’azzara. Ganin yadda duk yake a hautsine ya sanya na rika binsa da lallashi da nasiha har ya sauko ya soma fara’a. Lokacin da muka fito domin mu karya na riski Aufana a kan table ta shirya komai.

Ba ni da matsala da hakan domin na yi ƙoƙarin ganin ɗiyata ba ta tauyu da ko ɗaya daga cikin abin da zai tauye ƙimarta ta ɗiya mace ba. Cikin ladabi ta gaishe mu gaba ɗayanmu muka amsa mata da fara’a. Ganin Babanta cikin shirin tafiya ya sa ta kwaɓe fuska,

“Abba ina kuma za ka je bayan ka san gobe ne muke kammala jarrabawa?”

“Ki yi haƙuri ‘yar Abba kamawa ta yi babu yadda zan yi tafiyar nan”

“Idan ma ba ta haƙura ba me za yi? Za ka fasa kare haƙƙin al’umma ne saboda muradinta?” Cewar Halima tana dubansu.

“Babu ruwanki Ummu Aufana, Ummina ta daban ce”

Ya bani amsa yana murmushi. Daga bisani gaba ɗaya muka zauna, wajen cin abincin sai tsokanarta yake har ta ware. Ni dai idanu kawai na saka musu domin gaba ɗaya ji na nake babu daɗi. Sallama ya sake yi mana a nan na roƙeshi zan je in ga Yaya ya kuma barni na tafi cike da gargaɗi in kula da kaina”

*****

Dogon numfashi ya ja tare da dafe saitin zuciyarsa. Ƙirjinsa ne yake masa zafi sosai. Ya tabbata jininsa ya hau a yanayin da yake jin idanunsa sun yi nauyi. Daga wannan rana bai sake sanin yaya rayuwar Halima ta kasance ba sai kiransa aka yi aka sanar masa ta rasu har an bunneta yayin da Aufana take kwance a gadon asibiti.

Shi ya sa har gobe yake alaƙanta mutuwar matarsa da ɗan uwanta Kamala domin gidansa ta ce masa ta tafi. Kuma shi ne mutum na ƙarshe da ya yi waya da ita a binciken da ya gabatar. Sai dai bayan hakan ba shi da wata ƙwaƙƙawarar hujja. Ya yi iya bakin ƙoƙarinsa amma ya gaza samu. Bincike ya nuna ta je gidan ta fito amma har yau ya kasa sanin abin da ya faru da ita wanda sai kabarinta aka nuna masa.

Bayan rasuwarta sun ɗauki tsayin lokaci basa magana ko hanya ba ta haɗa su ba, da taimakon Allah da naci da kukan da Aufana take masa ya sa da kansa ya nemi Kamala tare da neman ya zauna tare da su ko dan saboda Aufana ɗin kasancewar shi ba ya wuni a gida.

Baba Laure ita ce aka samo domin taya Aufana zama kuma babu laifi tana matuƙar ƙoƙari wajen kulawa da ita. Zaman Kamala a tare da ita ya rage mata kaɗaicin mahafiyarta sosai domin a farkon abun kusan zaucewa ta yi.

Jin yadda kansa yake juyawa ya sa ya haƙura. Alama ya saka a shafin littafin ya ajiye shi ya kwanta.

Sai dai gaba ɗaya bacci ya gagare shi, juyi kawai yake yi. Daga bisani bacci mai ƙarfi ya ɗauke shi.

*****

Sarƙaƙiya

Wani ƙaton fili ne mai yalwar duwatsu masu santsi da mulmulewa, suna da ɗaukar idanu da ban sha’awa. Ga mamakinsa rabin fillin wani irin duhu ne mai kashe zinariyar idanu daya ɗumamme wajen. Rabin kuma haske ne mai kyau da armashi ga wata ni’ima luf-luf da ita. Daga in da yake zaune cikin korayen ciyayi idanunsa na mamakin duhun a ransa yana jin yana san ya taka akan diga-digansa ya isa wajen amma kuma kamar an ɗaureshi.

Wani abu yake hangowa cikin duhun ta wata kafa da ba ta fi kafar allura ba wanda shi kaɗai ne hasken da ya ratsa tsakiyar duhun. Abin acure yake yana murƙususu kamar mai neman agaji. Sake yunƙurawa ya yi a karo na biyu ya nufi wajen amma gam ya ji ƙafaffunsa sun riƙe.

Wani farin dattijo ne ya bayyana gabansa, fuskarsa ƙwar cike da tashin hankali,

“Ka je gareta ka zamo WANI HASKE a lamuranta. Kai kaɗai ne ka rage mata bata da kowa!”

 Kafin ya tantance waye dattijon ya ji kamar an kwance masa sarƙoƙin da suka kewaye shi. Ya yunƙura da dukkan ƙarfinsa ya nufi wajen. A kan dugaggansa yake takawa ya yi har zuwa bakin inda DUHU da kuma HASKEN suka yi shamaki.

Yana ɗora ƙafarsa a sashin duhun wata ƙara data kusa kashe masa doddon kunne ta firgitashi. Yayin da wani zafi mai raɗaɗi ya ratsa jijjiyoyin jikinsa. Ya kuma kasa cire ƙafarsa daga wajen kamar wanda aka hankaɗa haka ya cigaba da bin wannan siririn hasken da ya zamo masa FITILA a tafiyar.

Duk zafi da raɗaɗin da ke ratsa shi haka ya cigaba da tafiya yana gab da ƙarasawa wajen wani dunƙulallan abu ya taho a sukwane, sai da ya zo gab da ahi sannan ya fahimci wata makekiyar mikiya ce. Kafin ya yi aune ta dira gabansa tare da buga masa fuka-fukanta ya yi taga-taga sai ya faɗi rub-da-ciki.

Cikin sa’a hannunsa ya sakalo wani abu kamar hannun mutum yana ɗagowa sai ya ga hannu sanye da wani zoɓe na azurfa mai tsanin haske da ɗaukar idanu.

Firgigit ya farka, kansa ya sara tare da dafewa. Ji yake tafin ƙafarsa yana masa wani irin zafi da ciwo. Idanunsa ya runtse yana kiran sunan Allah. Ya fi karfin mintuna goma yana tunani amma ya kaso gano maƙasudin mafarkin.

Amon muryar da zoban yake tuna inda ya taɓa jinsu amma ya gaza tunawa. Miƙewa ya yi ya ɗauro alwala ya soma jera nafilfili har zuwa goshin asuba. Da safe haka ya tashi sukuku da shi, lokacin da ya fito da Aufana ya soma cin karo.

Cikin ladabi da biyayya ta gaishe shi ya amsa mata cike da kulawa,

“Baba dama….”

“Dama me ɗiyar albarka, faɗi abin da ya ke tafe da….”

Maganarsa ta maƙale sakammakon ganin irin zoban da ya gani a mafarki hannun Aufana. Gabansa ya ci gaba da faɗuwa amma ya daure ya furta,

“Ina sauraranki”

“Dama ina tuna maka ne batun graduation, na ga kamar ka manta”

Ta faɗa tana sunne kai ƙasa, murmushi ya yi har sai da gefan kumatunsa ya loɓɓa. Ya dubeta,

“Aufana ban manta ba, idan na manta da lamuranki ai tamkar na manta da duniyata ne. Kada ki manta ke ɗin amanata ce!”

Daidai lokacin Kamala ya ƙaraso,

“Uba da ‘ya!” Ya furta da muryar tsokana,

“Kawu Kamala ina kwana”

Ta katseshi tana murmushi, murtuke fuska ya yi,

“Tun kina tsumanki gyatumarki take faɗar Kamala har ki ka haddace gashi nan raɗau a bakinki kamar karatun sallah. Ki wa Allah ki dinga cewa Kamalu!”

Dariya ce ta so ƙwace mata amma ta gimtse,

“Idan na ce maka hakan ina tunawa da Annata!”

Kalamanta sun sanyaya gwiwar mutanen dake wajen, har hakan ya so taɓa walwalarsu dan haka cikin hanzari Kawun nata ya yi dabarar kawar da yanayin,

“To Uba da ‘ya na fahimci wannan ƙusƙus ɗin naku ba zai ƙare ba ni na yi nan”

“Ya san ranka?” Ya ba shi amsa da wani irin yanayi.

“Wasai kuwa Baban Aufana. Ni zan wuce akwai abin da zan gabbatar mai muhimmanci”

“Ka ji ra na sauke ka”

“Bana buƙata!”

Ya faɗa da sauri kamar mai tsoron wani abu, kuma bai juyo ba ya yi gaba. Gabaɗaya suka rakashi da idanu har ya ɓacewa ganinsu. Dawo da hankalinta kan Baba Brr. ta yi suka ƙarasa maganarsu. Amma a ƙasan ranta tana mamakin abin da yake faruwa tsakaninsu wasu lokutan kamar masu yi wa juna shaguɓe.

Kai tsaye ɗakin Baba Barista ta wuce domin gyara masa kamar yadda ta saba. Cikin mintunan da ba su gaza sha biyar ba ta kammala. Littafin da yake ajiye kan drower ta bi da kallo wani abu ya ja hankalinta game da shi sai dai kafin ta kai hannu ta ɗauka ta ji Baba Laure ta ƙwalla mata kira dan haka ta juya ta fita a hanzarce. Abin haushi ba wani takamaiman kira ba ne face tana so ta nuna mata yadda za ta yi markaɗe a blander. Baki ta turo tare da furta,

“Duk laifin Baba da kawu ne da sun yi aure da ba ki firgitani da kira ba kamar na mafarauta”

Tana dariya ta ce,

“`Yar kirki ‘yar nema ai sai ki samo musu matan”

Hirar da ta ɗauke ta da ita ne ya sa kwata-kwata ba ta kuma tunawa da littafin ba. Ta shirya ta tafi makaranta. Lokacin da ta isa sai ta riski abin da ya fi ƙarfin tunaninta. Ba komai ba ne face samun labarin abokiyar karatunsu da aka nema aka rasa tsayin kwana huɗu. Wanda an tabbatar da saurayinta ne ya fita da ita wajan fati amma kuma da aka bincika sai ya nuna shi sun rabu tun a ranar.

Hankalinsu ya tashi sosai domin Shafa’atu yarinya ce wadda babu ruwanta. Hasalima ba su taɓa kawo tana irin wannan tsale-tsalen ba. Sai dai ba a shaidar mutum. Nan da nan aka kira meeting na gaggawa tsakanin ƙungiyoyinsu na tsofaffun ɗalibai sai dai har zuwa yamma babu wani gamsasshen bayani game da ita. Haka duk suka rabu jiki babu ƙwari.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×