Skip to content
Part 10 of 13 in the Series Fitsarin Fako by Sanah Matazu

Turka-turka

Ju yi take a ɗan ƙaramin ɗakin da aka yasar da ita, tun lokacin aka ɗauko ta. Gaba ɗaya jikinta ya yi tsami saboda ƙafaffunta da hannayenta a ɗaure suke. Ƙwalla ce ta ji ta zubo mata, bata san dalilinta na zama a wajen ba amma ta alaƙanta hakan da Alhaji Labaran.

Duba da yadda duk wasu file da suke hannunta babu wanzuwarsu. Hata da wayarta ma babu ita. Tashin hankalinta ɗaya shi ne duk wata shaida da ta mallaka tana cikin wayar.

Karaf! Ta ji an buga ƙyauren ɗakin da ƙarfi wanda hakan ya haddasa masa buɗewa. Idanunta ne ya soma gani kaɗan-kaɗan saboda hasken da ya ɗan ratso ta tsakanin ƙyauren.

Ƙafa wani jibgeggen mutum ya saka tare da dukanta. Ƙara ta saki me sauti,

“Wayyo Annata!”

Wata muguwar dariya ya saki, sai kuma ya fita jim kaɗan ya dawo tare da kwance mata duk wani ɗauri na jikinta. Zama ya yi tare da kafeta da idanu,

“Ke ƙwaruwa ko?”

Ya faɗa da wata irin murya, kallonsa take sossai gaba ɗaya tsoransa ne a tare da ita. Wani irin gabjeje ne ga suma tur-mus akansa kamar bamaguje. Idonsa ɗaya nanne yake da wani abu me ɗan faɗi wanda aka ƙawatashi da wani irin adon fulawa. Abin ya ɗan ja hankalinta sossai, ɗauke kai ta yi daga kallonsa.

“Ke ƙaramar ƙwaruwa ce, uwarki ma ta buga ta barmu ballanta wata ke!”

Kalmar ‘Uwa’ da ya ambata ya sa gaba ɗaya wani tsoro da kuma shakkarsa ya gushe a zuciyarta, bata san lokacin da ta yunƙura tana me furta.

“Bar raina allura ƙarfe ce, ai shi mugun nufi baya kashe ɗan kishiya. Kuma duk ƙanƙantar mage kukanta kaɗai ya isa firgita kakan ɓeraye ballanta kuma ya yi ido huɗu da ita!”

Dunƙule hannu ya yi da niyyar kai mata wani bahagon duka, da sauri ta runtse idanunta kawai tana tsammanin sumewarta. Ƙarar wayarsa ya dakatar da shi daga mugun nufinsa,

“Yallaɓai ga ta a gabana amma ina shirin lanƙwameta saboda na fahimci wannan ta fi uwarta taurin rai”

Cikin suɓucewar baki Aufana ta katseshi.

“Kadda ka sake zagarmun uwa wallahi domin ko wajen ubangiji ina yaƙinin ta fika daraja domin ita ba azzaluma ba ce!”

Wani mugun kallo ya watsa mata, ya cije laɓɓansa har gishiri-gishirin jini ya soma zagaya haƙoransa.

“Uwar ta ki ta gwal ce!”

“Ba ta gwal ba ce amma ƙima da darajarta idan aka ɗorasu a mizani ɗaya zata iya rinyar shi kansa gwal ɗin…”

“Ka na jinta ko yallaɓai?”

Ya furta tare da damƙar hannunta ɗaya yana murzawa, ai kuwa ta ƙwalla ƙara saboda azaba domin ji ta yi kamar hannun zai karye.

“Na faɗa maka kadda ka taɓata tunda dai kun karɓi hujojin wajenta ka ƙyaleta akwai abin da nake shiryawa”

Ogan na shi ya faɗa daga ɗaya ɓangaren. Ƙwafa ya yi tare da katse kiran wayar. Ransa gaba ɗaya a ɓace ba haka ya so ba, amma zai nunawa Alhaji Labaran shi ma shegen samane. Ƙafa ya sa ya fyaleta ta faɗi rumfa da ciki bakinta ya datse da haƙoranta sai ga jini. Take ya kuma sa ƙafa ya shureta ta yi walankeluwa kamar an buga ƙwalo ta bugi bango goshinta ya fashe. Kuka ma sai ya gagara zuwa a bakinta sai ajiyar zuciya da take yi.

Idanu ya zare sossai tare da nunata,

“Sa’arki ɗaya bana tsallake maganar yallaɓai wallahi da sai na turaki ƙiyama kamar yadda na tura gyatumarki!”

*****

Kai kawo kawai Baba Baristar yake yi, duk inda rashin nutsuwa take to tana tare da shi. Gaba ɗaya tunaninsa na ga ina Aufana take? Shin me suka yi mata a wane waje suka ajiyeta? Ga shi ya rasa wayar Kamala gaba ɗaya tun bayan rabuwarsu.

Kwana biyu kenan yana tunanin mafita game da lamrin sai dai bai hango koda ɓurɓushin nasara ba. Zuciyarsa ce ta doka lokacin da wani ɓangare yake bashi tabbacin kan inda ya kamata ya sami mafitarsa. Gaba ɗaya ya manta da agogon da yake a hannunta wanda in da ya so na’ura zata iya saita masa har inda take.

Cikin sauri ya shirya tare da fitowa, Baba Laure da ta ga ji da tambayarsa ina Aufana da Kamala suke ya samu zaune ta buga tagumi, har zai wuceta ya dawo tare da sunkuyawa. A shekarun da suka ɗauka da matar kaɗai ya isa damuwarsu ta zama tata. Tun bayan rasuwar Halimatau ita ta kasance tare da su kuma duk wata ɗawainiya da uwa take yi wa ‘ya’yanta to kuwa Baba Laure tana yi musu ba tare da nuna ƙyashi ko hassada ba. Dan haka be ga alfanun ɓoye mata komai ba,

“Ki yi haƙuri Baba uwar ɗakinki tana nan cikin kariyar Ubangiji In Sha Allahu!”

“Allah ya tabbatar babban mutum amma akwai abin da baka so na sani.”

“Ba wai bana so ki sani bane, tashin hankaline ba na so in saka ki fatana kawai ki cigaba da yi mana addu’a baki ɗayanmu.”

Sai da ya tabbatar ya sama mata nutsuwar da ta dace sannan ya fita zuwa in da zuciyarsa take bashi tabbacin zai sami haske. Kai tsaye office ɗin abokinsa Dr. Badamasi ya nufa, kasancewarsa sananne ya sa babu wani neman izini sakatariyarsa ta ba shi damar shiga. Yana shiga wayar abokin nasa ta yi ƙara, haɗa idanu suka yi kowane ya saki murmushi me ɗauke da ɓoyyayiyar ma’ana. Wuri ya samu ya zauna yayin da Dr Badamasi ya kanga wayarsa a kunnunwana. Kasancewar wayar me amo ce yana iya jiyo abin da me kiran yake faɗa.

“Duk abin da ka ke ka sameni a office domin akwai muhimmiyar maganar da za mu yi.”

“In Sha Allahu ya Alhaj!”

Cewar Dr Badamasi yana me ƙasƙantar da murya kamar yana gabansa. Yana sauke wayar  ya kalleshi a lalace,

“Allah ya yi wadaran naka ya lalace. Nasan ba kowa ne ya kiraka ba face wannan maƙiyin Allah…”

“Idan kana so mu shirya Abdallah ka fita gonata da yallaɓai, wannan runton zunubine kawai, ina ruwanka da rayuwar wani?”

Kai kawai ya girgiza, zuciyarsa na zafi. Duk lokacin da Alhaji Labaran zai kira Badamasi yasani ba wai abin kirki zasu shuka ba. Dan haka ya sassauta zuciyarsa saboda yana san cimma ga ci a tafiyarsa. Sai ya yi murmushi tare da shafa gemunsa. Kafin ya yi magana ya katseshi.

“Me ka zo yi min a office?”

“Sada zumunci da kuma neman lada ko hakan aibune?”

“Allah ya sa da gaske ka ke, ni dai nasan wanda fatsarsa ta ɓace har cikin yashi ma lallubenta yake saboda doɗewar kai.”

Ya ji zafin maganar kuma yasan saboda ya kunashi ya yi ta amma sai ya kanne. Hasalima sai ya ɗauki wani file yana dubawa. Daga bisani kuma ya ɗauki wayarsa ya cigaba da dannawa kawai.

Shiru ya ratsa tsakaninsu babu me tankawa wani. Kowa da abin da yake ƙiyastawa cikin rnasa. Miƙewa Dr ya yi ya shiga banɗaki da wannan damar ya yi wuf ya maƙala abin ɗauka jikin bironsa. Wanda duk ƙwaƙwar mutum be isa ya fuskanci wani abu ba. Ya sa ni ba ya rabo da biron dan haka yake ganin zai zame masa wani tsani na cimma muradinsa.

Yana fitowa ya miƙe tare da bashi hannu,

“ni zan wuce Badman.”

Kallonsa ya yi yana dogon nazari alamun tuhuma, murmushin gefen baki ya yi irin na ‘yan duniya. Hakan ya sanya gabansa ya faɗi yasan Badamasi akwai ƙwaƙwalwa baya san kwaɓarsa ta yi ruwa. Dan haka ya saki dariya yana shafa gemunsa,

“kai ka kamaci zama (barrister) ba ni ba Dr wannan irin kallon tuhuma haka?”

“Nasanka ya yunwar cikina Abdallah, baka jaurar banza kadda ka yi abin da zamu yi nadama ni da kai, domin kadda ka yi mamaki na ajiye abota a gefe na taɓa mutuntakarka. Ka sani a kan kuɗi zan iya koma mene ne!”

“Nasani Badamasi, zaka iya koma mene ne tunda har ka iya bayar da jinin ɗiyarka ta farko sadaukarwa wa nuna ƙauna ga Alhaji Labaran domin hayewa takarar gwamna!”

Ya furta yana me sake riƙe hannunsa cikin nasa yayinda yake murzasu da wani irin sallo na sanya shakku a zuciyar wanda aka ɗaure da jijjiyoyinsa. Baki a hangame yake dubansa, tsananin mamaki ya sa ya kasa tankamasa. Yana kallo ya saki hannunsa ya juya yana tafiya kan duga-dugansa cike da izza da kuma karsashin da be san ina ya sameshi ba har ya kai ƙarshan ƙofa. Ganin kamar idan ya ƙyaleshiɓ ya ci shi da yaƙi ya sa ya aro juriya ya yafa,

“Daɗin abar mallakina na bayar wani kuwa ba shi da ko sili bare a saka masa ran zai iya sadaukarwar, sai dai koda yake an fake da guzuma ne ana harbin karsana uwa ta tunkuyi burji ana shan lagwadar ɗiya.”

Gabansa ne ya yi wata irin  dokawa zuciyarsa na wani iri zafi,

‘Me kalaman Badamasi suke nufi?’

Ya yi furucin a zuciyarsa, be bashi damar kammala tunaninsa ya sake furta,

“Ka adana sirrina Abdallah domin zan iya yin komai dan watsa rayuwar wanda ya shiga hancina.”

Be yi mamakin kalamansa ba har cikin ransa. Saboda  yasani sarai gaskiya ya faɗa, cikin abin da zai iya shaida nasa a alaƙarsu da juna  hadda faɗin abin da yake ransa gaba gaɗi. Amma ba ya jin hakan zai karya guiwarsa daga karɓar ‘yancin al’ummarsa. Dan haka ya aro juriya ya yafa, muryarsa wasai ya ɗaga kafaɗa,

“Baka da damuwa yadda ka ke kaifi ɗaya haka ma Abdallah yake. Ƙafafuna suna tsaye tamkar turakun dabino matuƙar akan gaskiya ne.” Ƙofar ya buɗe ya fita daga office ɗin, ba tare da ya sauriri ko da kalma ɗaya daga gareshi ba. Zuciyarsa ta yi zurfi wajen tunanin rashin imanin da yake zagaye da zuƙatan wasu mutanan. Sam ya kasa fahimtar amfanin baɗi babu rai.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fitsarin Fako 9Fitsarin Fako 11 >>

1 thought on “Fitsarin Fako 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×