Skip to content
Part 6 of 13 in the Series Fitsarin Fako by Sanah Matazu

Ɗakin taron cike yake da mutane mabambanta. Kowa da abin da yake gudanarwa; amma akasari fuskokinsu cike suke da farinciki mara misaltuwa. Ɗauke kanta ta yi gefe tana jin ƙwalla na taruwa cikinsu, ba ta hanata zuba ba duk da muhimmancin wannan ranar gareta sai dai ba don tana gudun yi wa rayuwarta rinton zunubi ta hanyar butulcewa Ubangijinta ba, da sai ta ce “Ranar ba ta da wani muhimmanci a duniyata.”

Kamar an ce ta ɗaga kanta ta hango kawunta, walwala ce cike a fuskarsa, gefansa kuma mutumin da ya zamowa duniyarta katanga ne, bayan zubewar dirkar da ta tabbatar ba za ra samu mai maye gurbinta ba.

Sake gyara rigarta ta yi, rigar da ta kasance duk wata irinta tana alfahari da ita, wato rigar lauyoyi. Jin ta take kamar ba ita ba, wai yau ita ce wacce za a yaye matsayin cikakkiyar lauya kamar uban goyonta (barrista) Abdallah Alhussain Gilɓowa.

Cikin ƙanƙanin lokaci aka soma gudanar da taron, abin gwanin burgewa. Kamar almara ta ji sunanta na amsa kuwa cikin abin magana, yayin da ɗakin taron ya ɗauki tafi tare da sowar abokan karatunta wajen kiran sunanta,

“Aufana Halima Labaran”

Maimakon ta tashi sai hankalinta ya nufi wani wajen daban. Tamkar maganaɗisu haka idanunta ya ja ta  zuwa ga wani saƙo na ɗakin taron, sake murza idanunta ta yi domin tabbatar da abin da ta hanga. Tabbas ba gizo ba ne, a wannan karon Annarta ta gani. Tabbas ita ce ta gani.

Kamar almara take jin komai, yayin da ta zamo tamkar mutun mutumi. Miƙewa ta yi tana ƙoƙarin zuwa wajen, murmushin kan fuskarta ya ƙi gushewa. Sake murza idanunta ta yi, ɓat ta nemeta ta rasa. Kanta ta ji yana juyawa, ba wannan ne karon farko ba, tabbas tana jin a jikinta Annarta ce.

Ba ta gama tantance mafarkinta ba, ta tsinkayi hannun Kamala cikin hannunta ya soma janta kamar wata ƙaramar yarinya. Abin mamaki hawaye ne suke zuba a idanunsa yana share su da hannunsa ɗaya wanda shi ne mai lafiyar.

“Kawu, Annata na gani!” Ta furta da muryar raɗa.

“Gizo ne Aufana Annarki ta tafi inda ba a dawowa.”

Jikinta babu inda ba ya rawa, saboda firgici domin ta tabbatar ita ta gani. Amma a yanayin da suke ciki babu damar musu. Hannunta ya ci gaba da ja har zuwa inda aka tanada domin ɗalibai masu ƙwazo.

Sai lokacin ƙwaƙwalwarta ta karantomata abin da ya kawota wajen. Ita ce ta karɓi kambun (fist class) ɗalibar da ta fi kowa ƙwazo, wasu hawaye ta ji sun kwaranyomata ta shiga waige-waige zuciyarta da jikinta na faɗa mata Annanta tana kallonta. kamar an tsikareta kalamanta suka shiga dawo mata a massarafar jinta,

“Aufana ke ce ƙarfin gwiwata a yanzu, na rasa komai sai ke.”

Ta ke ta ji wani karsashi ya zo mata, matattakalar ta soma hawa cike da ƙarfin gwiwa. Kwatanta abin da take ji ba zai misaltuba. Hannuta na rawa ta karɓi kyautar. Tana saukowa da gudu ta ƙarasa tare da faɗawa jikin barista, wanda shi ma hawaye ne kwance a idanunsa.

“Baba Barista wallahi na ga Annata, Anna na gani, wallahi!”

Kamar an turata sai ta fashe da kuka. Tsam ya matseta a ƙirjinsa yana da bubbuga bayanta. Bakinsa ya kasa furta komai. Hakan ya tabbatar mata da ciwon da yake ji a ƙirjinsa. Kawu Kamala ne ya ja su zuwa inda aka tanada domin zama, saboda idanun jama’a da hankulansu ya soma dawowa garesu.

Cikin ƙanƙanin lokaci aka gudanar da komai taro ya watse. Suna gab da fita daga ɗakin taron cikin taron jama’a ta ji an damƙi hannunta kamar za a tsinkemata shi, kafin ta farga wata mata da ta rufe fuskarta ta damƙa mata takarda a hannunta kafin ta yi wani yunƙuri ta ɓacewa ganinta. Ƙamshin turaranta ya sanya gabanta tsinkewa ya faɗi.

Da matsanancin sauri ta bita, amma ta kasa cimmata,

“Anna dan Allah ki tsaya!”

Haka ta bi hanyar da ta bi tana gudu tana kiran sunanta amma ba ta same ta ba, numfashinta ne ta ji yana sama-sama yayin da bugun zuciyarta ya ƙaru. Tun watanni biyu da suka gabata take fama da jin hakan, amma gudun kada ta ɗagawa Baba Barrista hankali ya sa ta ƙi sanar da su.

A sace ta je likita ya dubata kuma ya ba ta tabbacin jininta yana yawan hawa, ya shawarceta da ta rage tunani domin ya wuce ƙima. Sai dai ita ta san cewa tunani shi ne abokinta har ƙarshan rayuwarta matuƙar Anna ba za ta fito duniya ta san cewa tana raye ba kamar yadda zuciyarta take faɗa mata.

Tana makaranta aka ɗaukota aka kuma tabbatar mata da rasuwarta sai dai me ya hana a jira ta zo, aka haɗa gawar mahaifiyarta ba tare da ta ganta ba? Me yasa take ganinta a wurare mabambanta? Me yasa zuciyarta ta gaza gamsuwa kan rubutun da alƙalamin ƙaddararta ya wallafa a shafin kundin rayuwarta?

Idanunta ne suka soma ganin duhu, amma ba ta saki takardar da ta saka mata ba. Cikin ƙarfin hali ta buɗeta duk ƙoƙarinta na kokawa da numfashinta sai da ta himmatu wajen karanta takardar

“Ke ce ƙarfin gwiwata, ki tabbatar gaskiya ta bayyana”

Daga nan ba ta sake sanin inda kanta yake ba sai farkawa ta yi ta ganta a kan gadon asibiti.

*****

Da idanu take bin kawunta tare da Baba Barista, gaba ɗaya sun yi zuru-zuru. A hankali ta motsa laɓɓanta,

“Anna!”

Gabaɗaya suka yo kanta, suna kiran sunanta,

“Aufana”

Da idanu ta amsa musu, kawunta ne ya yi saurin fita sai ga shi tare da likita. Gwaje-gwaje ya yi tare da sakin numfashi,

“Gaskiya sai kun lura da yarinyar nan sosai. Bugun numfashinta na neman sauyawa daga tsarin yadda na kowane ɗan Adam yake. Jininta ya, hau fiye da ƙa’ida. A taƙaice dai ciwon zuciya ne yake neman kamata. Zuciyarta tana yawan bugawa kuma bugawar haɗe da firgici mai tsanani. Hakan ya haifar mata da hauhawar jini wanda idan ba ku yi da gaske ba zuciyarta za ta iya samun bugawa farat ɗaya.

“Kamar ya ya likita, ban fahimta ba?”

Kawu Kamala ya katse shi da hanzari, ɗaga kafaɗu ya yi,

“Kun san cewa shi ciwon zuciya suna ne a dunƙule na wasu cututtuka da sukan shafi zuciya. Wato dai ba ciwo ɗaya ne kan shafi zuciya ba. Akwai nau’o’in cututtuka iri-iri da sukan shafi zuciya.

Ciwon zuciya shi ne kan gaba wajen kawo ajalin mutane da dama a ƙasashe masu arziƙi, domin an yi ƙiyasin cewa a kowane rabin minti mutum guda na mutuwa a sanadiyar ciwon zuciya a ƙasashen Yamma, duk da ci gaban da suka samu wajen wayewa da fahimtar cututtukan zuciya da aikin tiyata na zuciya.

Mu ma nan muna da nau’o’in cututtukan zuciya irin namu na ƙasashe masu karancin tattalin arziki, waɗanda ba a jin ɗuriyarsu a kasashen da suka ci gaba. Misali: ciwon zuciya wanda ƙarancin jini kan haifar.

To sai ya kasance a yanzu sakamakon irin ɗabi’un rayuwa da wasunmu suka ara daga ƙasashen da suka ci gaba, wato rayuwar jin daɗi, mu yanzu kusan muna da kowane nau’i na ciwon zuciya. A wannan ƙasar an yi bayanin cewa ciwon zuciya shi ne ciwon da ya fi hallaka manyan mutane a wannan zamani.

Akwai ciwon zuciya wanda ake haifar jarirai da shi.  Irin wannan nau’i kan rabu kashi biyu; mai tsanani da marar tsanani. A mai tsananin sosai, waɗansu jariran ma ba sa kwana, da an haife su suke komawa. A nau’in da ba tsanani kuma, jariri kan girma da shi ya kai minzalin babban mutum ba tare da ma an gane ba.

Alamun da za a iya gani a ce jariri na da wannan ciwo ya danganta da tsanani ko rashin tsananin ciwon da kuma ko wane iri ne. Wani lokaci ba wata alama da ake gani, kuma hakan na nufin yaro zai iya rayuwarsa lafiya sumul. Wani lokaci kuma, akan ga wasu alamu ko ma a rasa yaron cikin ƙanƙanin lokaci ko watanni.

Alamun sun haɗa da: Yawan haki na jarirai. Wasu kuma a ga ba sa iya shan mama sosai. Wasu sai dai su sha kaɗan su huta, sannan su ƙara sha. Ko a ga leɓɓansu suna duhu ko baƙi-baƙi, maimakon ruwan hoda. Za kuma a iya ganin ƙirjin su yana ɓal-ɓal, saboda saurin da zuciyar ke yi wajen bugawa.

Idan yaro ya fara magana, yakan iya cewa yana jin ciwon ƙirji, kuma za a ga bai cika shiga wasanni irin na yara ba, don ko ya shiga, yana saurin gajiya. Ko kuma ganinsa yana yawan tsuguno don hutawa in ya shiga wasan yara, ko kuma ya yi wani ɗan gudu kaɗan. Za a iya ganinsa yana yawan tari, ko samun kumburin ciki. ko kumburin ƙafafu. Sannan, ba ya girma kamar sauran yara.

Waɗansu iyayen a ƙauye a wannan lokaci ne suke samo wanzami ya yi wa yaro mai wannan alamu ɓalli-ɓalli a ƙirji, musamman idan an ga ƙirji na harbawa da sauri-sauri. Mu kuma mukan ba da shawarar kada a yi haka, a samu a kai mai wannan matsala asibiti a duba shi.

Nau’in ciwon zuciya na biyu shi ne wanda Aufana ke shirin kamuwa da shi, wato wanda hawan jini kan zama sanadinsa.”

“Dr kana nufin wato hawan jini na kawo ciwon zuciya?”

Kawu Kamala ya katse shi, kai ya jinjina sannan ya furta,

“Ƙwarai kuwa. Amma hakan na faruwa ne idan hawan jinin ya daɗe a jikin mutum ba a sauko da shi ba ta hanyar shan magunguna waɗanda za a iya samu a asibiti. Mai wannan ciwo zai iya jin numfashinsa sama-sama, musamman in ya kwanta, wanda hakan kan sa mutum kwanciya da matashi biyu ko uku.

Numfashi sama-sama zai iya sa mutum ya kasa bacci, domin da ya kwanta sai ya ji kamar an shaƙe shi. Sai kuma a fara tari, da kumburin ƙafafuwa. Wani lokaci akwai ciwon ƙirji.

Bayan hawan jini kuma, ciwo na gaba muhimmi mai kawo ciwon zuciya shi ne ciwon Idan aka ce mutum na da ƙiba, ana nufin mai ya yi masa yawa a jiki ke nan.

A ƙasashe irin namu, waɗansu mutane har alfahari suke da mummunar ƙiba, saboda ba su san ciwo ba ne. Amma a ƙasashen da suka ci gaba, kullum za a ga masu ƙiba da ma marasa ƙibar, suna guje-guje don motsa jiki a filaye. saboda sun riga sun san illolin tara ƙiba.

Ƙiba tana lahani ga zuciya idan daskararren mai ya toshe magudanan jini da suke zagaye da zuciyar, don su ne suke ba ta nata kason na jini. Idan hakan ta faru ɓangaren da abin ya shafa a jikin zuciyar zai iya mutuwa, ya kuma jawo matsala ga zuciyar baki ɗaya. Yawancin masu ƙiba kuma suna da hawan jini, wanda hakan kan haɗu ya ƙara wa zuciya ciwo.

Babbar alamar da ake ji idan irin wannan ciwon ya kama mutum shi ne ciwon tsakiyar ƙirji, daidai saitin da zuciya take. Ciwon ya fi tashi idan aka dan yi wani dan kazar- kazar, ko aka ji mummunan labari.

Yakan lafa idan aka ɗan zauna aka huta. Za a iya ganin mutum yana zufa ko gumi idan ciwon ya yi tsanani, wanda hakan alama ce ta cewa dole a kai mutum asibiti cikin gaggawa kada zuciya ta buga.

Sai ƙwayoyin cuta. ƙwayoyin cuta daba-daban kan samu damar shiga cikin zuciya su samu wurin zama idan jini ya kwaso su daga wasu sassan jiki musamman waɗanda suke daga baki da maƙogwaro, su sa wa zuciya. Akwai irin wannan ciwon zuciya da ƙwayoyin cuta kan kawo har iri biyu, wato (Rheumatic Valvular Heart Disease) mai kama murafan zuciya da (Infectibe Endocarditis) mai kama tsokar naman zuciya. Bari na ɗan baku taƙaitacen bayani kan mafi hatsarin ciki domin shi ne ya fi yi wa yara illa sossai da sossai. Kasancewar ba a ganeshi kai tsaye matuƙar ba gwaji aka yi da wuri ba, wato me kama murfin zuciya.

Rheumatic Valvular Heart Disease. Cutace da take kama murfin zuciya. Kamar yadda masana suka faɗa zuciya tana da kusurwa guda huɗu ne wato (chambers). Ita zuciya tana da murfi guda huɗu ne, biyu a hagu biyu a dama. Bayan (chambers) kuma tana da rasa guda huɗu su ma biyu a hagu biyu a dama. Rheumatic valvular Heart disease tana farawa ne da wani zazzaɓi wanda ake kira Rheumatic fever wanda yake farawa daga maƙogoro. Wanda akasari ya fi kama yaran da suke da shekara shida zuwa sha biyar.

Sau tari mutane basa sanin yaushe suka kamu da shi. Yana farawa da zazzaɓi me zafi tamkar zazzaɓin cizon sauro. Yana sanya ciwon gaɓoɓɓi sossai. A hankali yake cin jiki har ya zama Rheumatic valvular Heart disease. Yanayin al’ummarmu wajen ƙarancin kula da lafiya ya sa ba a fahimtar asalin abinda yake damun yaro har sai ya kai wannan matakin.

lokacin da ya kai ga ciwon zuciya ya kan fara da mitral stenosis (tsukewar ƙofar da ke sadar da jini tsakanin ramukan zuciya biyu na hagu ) ko kuma mitral regurgitation ( ya kasance jini yana tafiyar gaba da baya ) saboda ƙofar bata buɗe da kullewa yadda ya kamata.

Lokacin ne alamomin kasawar zuciya za su fara bayyana kamar su numfarfashi, saurin gajiya daga yin aiki kaɗan amma kasancewar abun is a gradual process yakan ɗauki shekara ko shekaru kafin mai matsalar kanshi ya ankara. Idan abin ya yi tsanani ne har ta kai ka yaro ya fara tari da kakin jini, wanda shi ne abu na farko da a lokuta mafi yawa yafi saurin ankarar da mutane da kuma neman agaji daga babban asibiti. Wannan ciwo da zaran ya fara idan ba a ɗauki matakin dakatar dashi ba ci gaba yake daga ƙofa ɗaya har ya shafi sauran ƙofofin zuciyar ɗaya bayan ɗaya zuwa matakin kasawar zuciya gaba ɗaya.

Maganin wannan ciwo shi ne tiyatar zuciya wanda zaɓi biyu ne ya danganta da matakin da aka tari cutar. Abin bai tsaya nan ba bayan tiyatar akwai buƙatar shan magani wanda kusan yakan zama iyakar rayuwar mutum ya dawwama akan maganin kenan.

Sai kuma hanyoyin kariya a lokacin da aka lura yaro ya kamu da cutar sore throat (da ke kama maƙoro) kar ayi sanya wurin neman magani. Mutane da dama basu cika bashi muhimmanci ba domin yawanci yaro zai fuskanci zafi ne yayin haɗiyar abinci wani kuma yakan haɗa da ɗan zazzaɓi ba mai zafi ba. To irin haka sai kuga mutanen mu sun ɓige da shan panadol wanda ko tabbas zai tafiyar da wannan zazzaɓin da zafin haɗiyar. Wanda treatment ɗin kwata-kwata a wannan lokacin antibiotics na kwana biyar kacal yaro yake buƙata wanda ko ɗari biyar hakan ba zai ci ba.

Ƙwayar cutar bacteriya ita ta fi samun sukuni a jikin zuciya, duk da cewa ƙwayoyi irin su virus da fungus sukan iya sa wa zuciya ciwo.

Akwai kuma nau’in ciwon zuciya wanda ke damuwa silar ciwo a huhu. Idan aka samu matsala a huhu, matsalar takan iya shafar zuciya. Cututtukan huhu da za su iya sa ciwon zuciya sun haɗa da ciwon tarin fuka, da ciwon daji na huhu, wanda ya fi kama mashaya taba sigari.

Akwai ma ciwon zuciya wanda na ce karancin jini kan iya kawowa, musamman a mata masu ciki ko masu shayarwa waɗanda suke da karancin jini. Yawancin cututtukan zuciya ba sa warkewa sai an kawar da abin da ya haddasa su, ko a yi dashen wani ɓangaren da ciwo ya taɓa, ko a yi ta shan magani har tsawon rayuwa”

Gabaɗaya jikinsu ya yi sanyi, tana daga kwance tana iya hango yanayinsu mai tattare da damuwa. Ba ta san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ita ba. Kwananta biyu aka sallame ta, duk wani gata da tarairaya tana samunsa daga wajen kawu da Baba Barista. Ranar da aka sallame ta sosai ta ji ƙwarin jikinta, sai dai har zuwa lokacin zuciyarta na maƙale da tunanin Anna.

A mota suna tafe babu mai tankawa wani har suka isa gida, sai dai fuskokinsu sun isa shaida ga kowa na karantar abin da ke zuƙatansu. Suna isa gida sallah ita ce abin da suka fara gabatarwa, sosai take ƙarewa gidan da suke kallo wani tunani na ɗarsuwa a ranta.

 Ya kamata kawu ko Baba barista su samar da cikar mutuntakar gidansu ta hanyar mallakar mata. Sai dai  ta san da kamar wuya, har yau sun gaza manta tabon da ya ruguza duniyarsu.

“Abdallah bai kamata a ce mun bar Aufana na girbar shukar da mu muka das….”

Da sauri ya katse zancen sakammakon sallamar da ta yi, murmushin cikin zuciya ta yi ta tabbatar akwai abin da suke ɓoye mata. Amma za ta bi komai a hankali tabbas sai ta gano ko mene ne. Sai da ta tabbatar ba ta dasa musu zargin komai ba sannan ta shiga.

A zaune ta same su kan kujeru, ƙarar talabijin ɗin can ƙasa yayin da duk suka maida hankalinsu kanta. Hoton da aka nuno kan alon talabijin ɗin ya haddasa ɗaukewar numfashinsu na wucin gadi baki ɗaya, yayin da bayani ya biyo baya kamar haka.

“A yau ne aka sami gawar Sadiya Sani ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan Alhaji Labaran Tanimu, bayan dogon bincike likitoci sun tabbatar da an haike mata ne, daga bisani kuma aka ka….”

Ƙarar fashewar talabijin ɗin ita ta hana su jin ƙarshen bayanin, kafin ta tantance mene ne ya faru ta hangi Baba barista a tsaye yana huci tare da buga hannunsa a bango. Talabijin ɗin da ke wargatse a ƙasa ta bi da kallo.

 Hucin da yake ya ba ta tsoro. Rabonta da ganinsa haka tun rasuwar mahaifiya. Jikinta na rawa ta fita daga ɗakin da gudu.

“Aufana!”

“Aufana!!”

Amma ina ko juyowa ba ta yi ba ta afka ɗakinta hadda saka kuba. Numfashi ta dinga ja da sauri da sauri. Tabbas koma mene ne wannan ya taɓa Baba Barista yana da yawa. Tana jin kawu na faɗa masa ya tsoratata. Sai dai amsar da ya ba shi ta girgizata,

“Kamala ka yi min shiru, kadda allura ta tono garma”

“To sai me?” cewar kawun sannan ya ci gaba,

“Kai ka san bana tsoron ta mutu ko ta yi rai”

“Ba girin girin ba dai ta yi mai!”

Bata ji amsar da ya ba shi ba, haka kuma ba ta sake fitowa ba,  ba ta kuma san yadda ta kaya ba har zuwa dare.

Haka ta yini a ɗaki tana tunani, lamarin ya tsoratata sai dai kuma a gefe ɗaya tana jin tausayin yariyar da aka kashe, ƙwaƙwalwarta ta sake haskomata hotanta (innocent face) a yanayinta babu ruwanta.

Sai dai ta so su kawu sun bari sun ƙarasa jin bayanan domin a gefan yarinyar ta ga wata mata tana kuka wanda hakan ya mintsini zuciyarta sosai da sosai.  Jin zazzaɓi na neman rufe ta, ga ciwon kai mai zafi da ya mata dirar mikiya, shi ya sa ta haƙura domin ba ta manta da bayanin likita ba,

“Aufana ki taimaki kanki, ki rage damuwa da tunani domin ciwonki abu ne me haɗari sosai”

Ko wajen cin abinci Baba Laure mai aikinsu nata tsokanarta, amma ta ƙi sakin jiki, ba komai ne ya ƙara dagula lissafinta ba face ganin har lokacin kawunta bai saki ransa ba. Ganin yanayin damuwa a fuskarta ya sa suka soma janta da hira har ta warware sosai. Abincin kansa tsattsakura ta yi ta tashi.

Komawarta ɗaki ya ba ta damar yin nutso wajen tunanin rayuwarta, cikakken sunanta shi ne Aufana Halimatu Labaran. Mutane da yawa na tambayarta ya aka yi take amfani da sunan mace a madadin sunan mahaifinta sai dai amsarsu ta gaza samuwa daga gare ta sakammakon ba ta san amsar ba,  kuma ba ta same ta daga bakin kowa ba, ciki kuwa har da mahaifiyarta har ta koma ga mahallicinta.

 Gwargwado ta samu tarbiya da ilmin addini, haka ma ilmin boko. Ta yi karatunta na primary da kuma secondary duk da taimakon mahaifiyarta. A daidai lokacin da ta kammala karatunta na secondary a lokacin ne babin da ba za ta manta ba ya buɗe wa rayuwarta.

Domin a daidai wannan lokacin ne ta rasa babban jigon rayuwarta, tabon da har gobe ya kasa cikewa. A lokacin tana da  shekaru goma sha bakwai cif. Da taimakon Baba barista da kuma taimakon Allah ta samu gurbin karatu a jami’ar Bayero, ta karanci fanin shari’a (Law) shekara biyar, daga nan ta tafi (school of low) makarantar fanin shari’a dan zama cikakkiyar lauya mai lasisi.

Inda ta sha gwagwarmaya a (law school) ta fannin shiga (law chamber). Cikin ikon Allah ta yi (attachment). Nasara ta samu domin tana cikin ɗaliban da suka ci jarabawar call to bar da ake wa lauyoyi, inda ta samu matsayin da duk wani barrister ya taka ake saka ma shi rigar su da kuma wig da suke sawa ya zama cikakken (barrister). Bayan nan ta yi NYSC ɗinta cikin kariyar Ubangiji. Burinta ya cika, hakama mahaifiyarta, sai dai kuma babu wanzuwarta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fitsarin Fako 5Fitsarin Fako 7 >>

1 thought on “Fitsarin Fako 6”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×