Skip to content
Part 3 of 13 in the Series Fitsarin Fako by Sanah Matazu

Mugunta Fitsarin Faƙo

Kamar kodayaushe da rashin walwala ya shigo gidan, ɗabi’ar da ta samu yayana ke nan a ‘yan kwanakin nan, wai a hakan ma an samu sauƙi saboda mun fahimci abin da yake damunsa. Da farko kafin mu ankare na ɗora alhakin hakan ne kan yanayin nakasar da ya samu kansa.

Akwai mutanen da ba sa iya tawakkali a kan ƙaddarar rayuwa, amma sai na fuskanci nasa abin yana neman yin tsamari. Wasu lokutan da na soma fahimtar sauyinsa shi ne, kasancewar ni ko Inna mukan yi ƙoƙarin zuba masa ruwa yana alwala sai na ga yana kuskure a wasu abubuwan. Sai na tuna masa sai kuma ya nuna kamar yanzu yake koyo. Inna na soma yi wa ƙorafi sai ta nuna na cika tsegumi dan haka na ja bakina na yi shiru amma abin na damuna.

Motsin da cikina ya yi ne ya katsemin tunanina, na lumshe idanuna tare da ajiye su kan turtsetsen cikina da ake saka masa ran haihuwa yau ko gobe. Tun satin da ya gabata likitoci suka ba ni tabbaci kan kwanakin haihuwata. Hakan ya sa muke zaman tsamanin warrabuka duk wani shiri Innata ta gama shi.

A wani lokacin na kan ji taradadi na ya ƙaranta, ba dan komai ba sai saboda muna inda ba kowa ya san asalinmu ba. Ba ni da fargaba kan abin da zan haifa sai dai na san duk runtsi abin ɓoye sai ya bayyana.

Idona na sake maidawa kan ƙofar ɗakin yayana, yanayin da yake ciki yana damuna matuƙa sossai, sai dai gargaɗin likita na hanawa zuciyata damuwa ya sa nake kauda kai ba wai dan abun ba ya mun ciwo ba.

Kimanin wata ɗaya ke nan da muka tashi a wata safiya gabaɗaya Yaya Kamalu ya nuna bai san mu ba. Ban manta yadda abin ya kasance ba a shigata ɗakinsa.

“Yaya Kamala Inna ta ce ka fito saboda yau ne za ku je karɓar tallafin nan na masu nakasa gidan ɗan majalisa.”

“Inna! Kamala!” Ya maimaita sunayen yana kallona tamkar bai taba ganina ba sannan ya ce, “Ke kuma wacece?”

“Lantana ce fa, Halimatu, ƙanwarka” na furta masa ainihin sunana ina jin wani tashin hankali na lulluɓe ni domin lokaci ɗaya na zuciyata ta rikito da wani bahagon tunani.

“Fita ki ba ni waje!”

Ya faɗa cikin tsawa, sai kuma ya dafe kansa kamar mai tuna wani abu, kamar kuma wanda yake wa ciwo a hankali ya tura laɓansa cikin bakinsa,

“Lantana”

Ya furta cikin wata ƙaramar murya sai kuma ya tafi taga-taga kamar zai faɗi ya dafa bango ya zauna. Jiki a sanyaye na fito, ƙoƙari nake wajen riƙe tashin hankalin daya rikito mini kamar aradu har na dangana da inda Inna take.

Babu jinkiri na yi mata bayanin yadda muka yi da shi, zani a hannu tana gyarawa muka sake rankayawa ɗakinsa. Amma dai jiya i yau haka Inna ta yi ta fama fafur yaƙi magana. Ƙarshe ma tambaya ya yi wace ce ita? Zuwa lokacin tsoro ya gama mammaye duk wani gurbi na jikinmu. Ranar haka muka yini sukuku, kuma amsar tallafin da ba a je ba ke nan.

Daga rana zuwa safiyar wanshekare duk wanda ya ganmu zai fahimci yadda tashin hankali ya samu wajen zama a dukkan motsi da fuskokinmu. Har zuwa lokacin Yaya bai sake magana da kowa ba, yana ɗakinsa. Amma ya ci abinci ya kuma yi sallah.

Da misalin goma na safe ne muna zaune kamar masu makoki Salisu yaran ɗan majalisa ya yi sallama a ba shi abinci. Sai dai ranar ma ba mu yi ba sakammakon halin da muke ciki. Ganin damuwa a fuskokinmu ne ya saka shi miƙe ƙafa ya zauna. Dan dama abin da yake muradi ke nan samun faɗa a gidan. Amma hakan ya gagara sakammakon tsare gida da nake yi haka ma Inna ina ƙoƙarin ganin ba ta saki jiki da shi ba.

Ɗabi’unsa kaf ba su yi mini ba, yana da yawan surutu da shiga sharo babu shanu. Ga shi ko abinci ya zo siya to idan zan miƙo masa sai ya yi ƙoƙarin hannuna ya taɓa nas. Akwai ranar da na wanka masa mari wanda a sanadin hakan sai da ya yi sati bai sake zuwa ba.

Inna ba ƙaramar tunzura ta yi ba, saboda yana yi mana ciniki sossai kasancewar abincinmu akwai tsafta ɗan majalisa na aikoshi siyan tuwon dawa lokaci zuwa lokaci. Sai dai a wannan lokacin na gaza hana zuciyata yin komai sakammakon hango ƙila mafitarmu ta samu a hannunsu.

Inna ce ta warware masa komai na game da abin da yake faruwa. Abu biyu ne ya saukarwa Salisu a lokacin, a zuciyarsa tsantsar farin cikine domin nesa ta zo musu kusa, matuƙar abin da yake kintace ne ya tabbata. Abin ya yi masa daɗin da har hakan ya kusan bayyana kan fuskarsa, ya yi hanzarin gyara kwaɓarsa. Fuskarsa ce ta soma nuna tsantsar damuwa.

“Tabbas kuna cikin tashin hankali Inna, domin in dai ba tsarewar Ubangiji ba ina tunanin ya kamu ne da cutar amnesia.”

“Amnesia?

Muka furta bakinmu a haɗe, ba wai dan mun san ma’anar hakan ba sai dan ganin yadda yake gyaɗa kai kamar marayan ɗanta ya ba mu tabbacin abin babba ne.

“Ƙwarai kuwa domin cuta ce mai wuyar sha’ani da rikitarwa. Ni ma na taɓa jin labarinta ne bakin wani abokina kasancewar fanin ya karanta.”

“Mece ce ita Salisu?”

Na furta ina jin wani irin tsoro na nuƙurƙusar ƙasusuwana, sai dai in ba gizo idona yake min ba kamar murmushi na ga Salisun ya yi, amma sai na ƙaryata hakan da tunanin ko idona ne ya nuna min gaibu.

“Idan aka ce mutum na fama da cutar amnesia dai to ana nufin cutar da ke sa mutum ya manta abubuwa kamar abubuwan da suke zahiri, da kuma bayanai game da wani abu ko kuma manta abin da ya faru da su da makamanta ire-iren wannan mantuwa.

Mutane da suke ɗauke da wannan cuta yawanci sun san kansu wato ma’ana ba su manta ko su su wane ne ba. Babban matsalar su shi ne; koyon wani abu sabo ko tuna wani abu sabo a rayuwarsu.

Wannan cuta ta kan samu ne saboda wata illa da a ka yi wa ɓangaren ƙwaƙwalwa da ke da haƙƙin tuna abubuwa (areas of the brain that are vital for memory processing). A faɗin masana harkar kiwon lafiya, cutar amnesia na iya zama har abada a jikin mutum ba tare da ya warke ba sai dai idan amnesia ce ta wucin-gadi, ita tana warkewa, ita ce ake kira a turance da suna (Transient Global Amnesia)

A yanzu haka dai ba bu wani takamemmen magani da za a ce ga shi na wannan cuta to amma akwai ‘yan dabaru da ake taimakawa marasa lafiya domin inganta tunaninsu (enhancing memory) da kuma (psychological support) da ake ba su da su da iyalansu domin samun sassaucin wannan lalura.

A bayanin da ya yi min yawancin mutane da ke ɗauke da cutar amnesia suna fama ne da matsalar (short-term memory). Ba sa iya tuna sabbin bayanai ko abin da ya faru da su. Abubuwan da suka yi da bai jima ba sukan manta su amman idan an yi sa a sukan rike ko tuna abubuwan da suka sani da jimawa.

Za ku tarar wani lokacin mutum zai iya tuna abin da ya faru da shi yana yaro, amma kuma ba zai iya tuna abin da aka yi ba da jimawa ba kamar; zai iya tuna sunan tsohon shugaban ƙasa, amma sai ya manta sunan shugaba mai ci. Za su iya sanin a wani wata ake ciki da makamanci abu irin wannan.

Wannan (isolated memory loss) ɗin ba ya shafar basirar mutum, da kuma (general knowledge,) da dai abubuwa kamar wayewar mutum da kuma yananin hallayyansa (personality ko identity). Mutanen da ke da wannan cutar yawanci suna iya karatu da rubutu za su iya koyon skill kamar hawa keke da makamantansu.

Za ma su iya gane suna da matsalar mantuwa ɗin. Sai dai idan ta yi ƙarfi ta kan iya komawa wata cutar daban wadda ake kira (dementia)…”

Gaba ɗayanmu rushewa muka yi da kuka, saboda ba mu da tsumi bare dabara, fahimtar abin da muke nufi ne ya sa ya soma lallashinmu,

“Kadda ku damu ai tun da kuna tare da yallaɓai kuma ya nuna tausayinsa a kanku musamman ke Lantana” ya furta yana nuna ni ya ci gaba “In shaa Allahu zai ji da komai kuma zai zo da sauƙi. Kuma yanzu ba mu da tabbacin hakan har sai mun je mun ga likitan ƙwaƙwalwa.”

Kai kawai muke jinjinawa, a raina ina yi wa wannan Ubangida nasa addu’a ban taɓa ganin ɗan siyasa mai tausayi da jin ƙai kamarsa ba. Zuciyata ta rika ƙisima tarin mutuntakarsa. Sai dai abin da muka kasa fahimta ashe akuya ce da fatar kura. Ba mu fuskanci hakan ba sai da ya kai mu ramin halaka tsumu-tsumu.

*****

Kwana biyu muna dakon zuwan Salisu amma kuma gaba ɗaya babu shi, zuwa lokacin yaya Kamalu na fama da matsanancin ciwan kai, idan ya tashi tamkar zai suma haka ya ke yi. Gaba ɗaya hankalinmu ya tashi. Ranar haka muka yini kamar marasa lafiya saboda har zabure-zabure ya soma yi. Mun yanke cewa washegari zamu je asibiti saboda duba lafiyarasa.

Wani ikon Allah da yammaci sai ga baƙuncin Alhaji Labaran Tanimu, cikin mutunci da karama juna suka gaisa da Innarmu. Daga nan Salisu ya kora mata bayani game da tallafawa Yaya Kamalu. Bakunanmu har kunne, ba mu gushe ba Inna ta rusuna har ƙasa,

“Alhaji Allah ya kare ka daga dukkan shari. Ubangiji ya zamo madogararka…”

Katseta ya yi ta hanyar ɗaga hannu, “Haba baiwar Allah! Kamar wanda na ba ku kyautar rai? Ai kare haƙƙin al’ummata tare da kulawa da su a wuya na yake alƙwarin ne na yi wa gwamnati na da kuma Ubangiji don haka kada ki ji komai”

Ya faɗa yana sauke idanunsa a kaina, da sauri na kauda kai saboda kallon da yake min ya yi min nauyi har ya soma tsinkamin zuciya.

“Wannan ma ta wajenki ce.”

Rau ta yi da ido, “ɗiyata ce da ƙaddara ta faɗawa, ‘yanta’adda ne suka haike mata….”

“Inna mana….”

Yaya Kamala ya faɗa da tsawa, wanda tun zuwan da Alhaji ya yi yana wajen amma bai ko gaishe da shi ba ba ballantana ya tanka, hakan ya yi min daɗi ƙwarai da gaske na lura kamar Innarmu na neman zaƙewa. Fuu ya tashi ya bar wajan yana bal da kwanon garin da na gama tankaɗewa.

“Sai kun bi shi a hankali duk da ba mu tabbatar da cutar a kansa ba, amma alamu me na masu ciwon yadda yake nuna zafin rai haka, idan kin lura idanunsa sun yi ja kuma jijjiyoyin kansa sun ɗaga tare da fitowa”

Kai Inna ta jinjina, ta kasa tankawa, gaba ya yi Salisu na binsa a baya, sai kuma ya juyo ya saci kallona na ɗauke kai ina ƙunƙuni.”

*****

Kwana biyu tsakani suka sake dawowa, aka ɗauki yaya Kamala zuwa asibiti. Bayan gwaje-gwajen da suka dace likitoci suka tabbatar da yana ɗauke da wannan cuta ta mantuwa amma ba ta yi tsanani ba. Hasalima tana motsawa ne lokaci zuwa lokaci wanda idan aka ɗorashi kan magunguna tare da kulawar da ta dace in shaa Allahu za a yi nasara.

Ba Inna ba hatta ni ranar sai da na yi wa wannan bawan Allah godiya. Daga wannan lokaci sai ya zamana yana kawo mana ziyara duk lokacin da ya bushi iska. Hakan na matuƙar takura ni sosai.

A kuma tsakanin ne na yi sabo da wani maƙocinmu matashi ne duk da cewa ya girmeni zai yi tsaran yayana Kamala. Mun shaƙu da shi sosai da sosai. Domin shi ɗin yana karatune ɓangaren shari’a (law)  kuma mahaifinsa ɗan takarar jami’iyar adawa ne ta su Alhaji Labaran.

Kusancina da shi ya samar da ci gaba da yawa ga rayuwata, ta fanin lafiyata da kuma hidindimunmu na yau da kullum har ta kai ta kawo har karatu yake koya mini. Ranar da ya san cikakken labarin rayuwarmu a ranar na ga tsantsar tausayi da karamci a fuskarsa. A kuma ranar ne ya yi mini alƙawarurruka da dama ciki kuwa hadda zama uba ga abin da zan haifa mace ko namiji.

Mahaifiyarsa Hajiya Rakiya mace mai tsananin kirki da kuma yakana. Ta ɗauke ni kamar ɗiyar cikinta, kasancewar Abdallah shi kaɗai suka haifa suke nuna ƙauna ga duk abin da yake muradi. Haka ma mahaifinsa Alhaji Alhussain Gilɓowa. Mutum ne mai karamci da kyauttatawa maƙotansa.

Duk sati yana rabon abinci, ga famfuna da ya yi a ƙofar gida ana ɗiban ruwa. Akwai marayu da suke ƙarƙashinsa da yawa. Haka kuma da yawa yaran unguwar matasa ya sama musu aikin yi ta hanyar takardun karatunsu. Wanda kuma bai yi karatu ba yana ba shi jari. An yi ittifaƙin takara ma da ya shiga tilastawar makusantansa ne saboda yaba hallayensa na kirki. Duk ina samun wannan labari ne a bakin mazauna unguwar da suka san shi tun tale-tale.

Takanas mahaifiyar Abdallah take sa a kawo min abinci mai rai da lafiya irin na masu larurar ƙaramin ciki. Sutura akai akai take aikomin da ita. Kuma masu tsada, idan na fito sai a rantse ni ɗin ɗiyar wani hamshaƙi ce. Babu jimawa soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanina da Abdallah wanda a lokacin yana gab da kammala karatunsa.

*****

Rabin rayuwar Abdallah tana makaranta ne wadda yake yinta a garin Abuja shi ya sa ba su taɓa haɗuwa da Alhaji Labaran ba. Ranar wata Lahadi da ba zan taɓa mantawa da ita ba cikin jerin ranakun rayuwata. Na fita in yi tattaki kamar yadda na saba duk safiya sakammakon likita ya tabbatar min cewar hakan zai taimakawa lafiyar jikina da kuma sauƙaƙamin haihuwa. Gab da zan shiga soron mu na ji zantukan da suka ɗaga min hankali. Muryar Salisu da Alhaji Labaran ce ta daki dodon kunnuwana,

“Ya Alhaj ta fa faɗi gassasa.”

Ya faɗa yana sosa ƙeyarsa, dubansa ya yi daga bisani ya kwashe da dariya irin tasu ta ‘yan duniya.

“Alhaji ka yi ƙasa-ƙasa mana a soronsu ne fa” ya faɗa yana waige-waige alamun rashin gaskiya.

“Salisu ki ki makaka zakara mai neman suna. Kai dai ko ina aka ganka an ga samu, guntsu mai bakin guntso alkhairi da akasinsa yau da me kazo mana”

“In da rabbana ai ba wahala yallaɓai, wannan dai dilan da muke shirin jefawa fatsa to Allahu ya gajarta mana dakon zunuban.”

A tsaye yake amma tsabar farin ciki sai gashi yana neman zama, danƙo hannun Salisu ya yi, tamkar ba Ubangida da yaro ba. Farincikin fuskarsa ya ƙi ɗaukewa.

“Ban fahimta ba Salisu kasan ni wata rana kamar kwarkwar nake.”

“Magana nake maka a kan wannan Gundul ɗin ya kamata mu yi wani abu a kansa”

“Kamar me fa?”

Sai da ya sake waigawa, na yi sauri na ɓuya a bayan buhun da ya raba tsakaninmu da gidansu Inna Sahura.

“Za mu yi amfani da damarmu ne wajen nema masa magani, yanzu dai ba likitoci sun bada maganin da zai sami sauƙi ba. To na zauna da Dr Badamasi mun yi shawara zai sha na watanni ne yayin da danginsa suka ga alamun sauƙi za su ƙara yadda da mu su saki jikinsu. A wannan gaɓar za mu ce za a nema masa aiki. A taƙaice dai  Gundul zai zama babban yaronka mai yi maka hidimar fataucin ƙwaya.

Takardunsa na shaidar ciwo za su rika yi mana amfani duk sa’ilin da tsautsayi ya sa aka kama shi, domin yana da shaidar takardar asibitin gidan masu taɓin hankali. Idan ya nemi yi mana gaddama za mu yi masa barazana da ahalinsa.”

Wata irin dariya ce ta suɓuce masa, damƙar kafaɗar Salisu ya yi tare da furta,

“Lallai watan bakwai ya kama, damunar bana shuka za ta yi yabanya. Tsutsa ba ta cin ragwan goro. Za mu shirya kaya yadda ya kamata amma kafin sannan za mu yi yadda za mu ja shi a jiki, za mu yi wa ahalinsa alƙawarin samun lafiyarsa ta hanyar tallafinmu. Za su shiga komar mu kamar yadda muke jefa fatsa yayin kamun kifayanmu mu kuma lanƙwame su hankali kwance.”

Ya ƙarasa yana wata irin dariya mara tushe da daɗin ji.

“Inda rabana ba wahala yallaɓai. Ba za mu ja jiki ba, da zafi-zafi ake dukan ƙarfe.”

Gabaɗaya jikina babu inda ba ya rawa, yayin da marata ta ɗaure ta yi wani bala’in murɗawa. Ban san lokacin da na saki ƙara ba na manta ma da wai ɓuya na yi a wajen. Ban sake sanin inda kaina yake ba sai farkawa na yi nagani a ɗakin asibiti. Gefe na Inna ce da kuma Salisu da yaya Kamala. A hankali nake bin su da idanu na tsaida su tsaf a kan yayana. Tausayinsa ya cika zuciyata. Yana cikin tsaka mai wuya amma bai sani ba. Hannu na kai na shafa cikina, sai lokacin komai ya shiga dawo min. Ɗan Adam kayan Allah, mutum mugun itace.

Da rawar jiki Salisu ya fita kiran likita, wanda na ji sun kira da Dr Badamasi mutumin da duk duniya bayan Alhaji Labaran babu wanda na tsana kamarsa domin na haƙiƙance shi ne wanda Salisu yake faɗar ya bada shawara kan yayana.

Da ƙyar na tsaya ya duba ni. A lokacin Inna na jera min sannu har suka ƙaraso bayan gwaje-gwaje ya tabbatar musu da komai lafiya. Sai a lokacin na ji wai haihuwar na yi saboda na shiga wani yanayi da ya tilasta min naƙuda lokacinta bai yi ba, duk da cewa cikina ya shiga wataninsa na haihuwa, amma kwanakin (EDD) ba su cika ba.

Duk da yayana ba ya a hayyacinsa na ga tsantsar tausayina a idanunsa. Kwana na biyu Alhaji Labaran ya zo, sai dai na yi iya ƙoƙarina matuƙa wajen ɓoye tsanarsa ko wani abu makamancin hakan. Domin na lura shi ɗin mutum ne mai matuƙar haɗari. A kuma ranar ne idanuna suka sauka a kan mutumin da zuciyata ta sami dokawar da ba zan manta da ita ba.

Wani matashi da Alhajin ya zo da shi da sunan ƙaninsa ne sosai fuskarsa ta yi min yanayi da wanda na taɓa gani. Zuciyata ta shiga kai kawo sosai wajen tantance in da na san fuskar. A ƙarshe dai na tuna ɗaya daga cikin ‘yanta’addan da suka shigo garinmu na ga lokacin da shiramin ɗaya ya zame. Tabbas na shaidashi amma ban yi garaje ba na barwa zuciyata zan jira dawowar Abdallah.

Hajiya Rakiya ta taka muhimmiyar rawa sosai wajen kula da ni a jinyata, takan zo da rana da kuma yamma amma ba su taɓa haɗuwa da su Alhaji ba. Haka ma Alhaji Alhussain ya zo duba ni sau ɗaya a wayarsa ne ma muka yi magana da Abdallah ya ba ni haƙuri tare da sanar da ni suna jarrabawa ne.

A lokacin na sanar da shi na gano wani cikin waɗanda suka kawo hari garinmu amma idan ya dawo za mu yi magana. Tamkar zai fito daga cikin wayar saboda farin ciki ya kuma gargaɗe ni da kada na sanar da ko Inna.

Ranar da muka cika kwana huɗu a asibiti, ina kwance na ɗan yi kwanciyar giciye jaririyar a gefena tana shan mama ina mitar hanamu bacci da ta yi jiya saboda kwana ta yi kuka. Dr Sabrina ta shigo. Likita ce mai faran-faran da jama’a sossai. Ita take kula da ɓangaren yaran da aka haifa. Kuka jaririyar ta sake saki me ƙarfi, ɗagota na yi ina jijjigata, amma kamar na tunzurata. Haɗe fuska ta yi sannan karɓeta tare da furta,

“Halima na sha jan kunnanki kan bawa yarinyar nan abincinta daga kwance kin ƙi ji ko?”

Ɗan haɗe fuska na yi tare da furta,

“Wallahi Dr na gaji ne, kuma dama ina nemanki ki dan dubata jiya ta kwana kuka ba mu samu bacci ba.”

Bata tankamin ba, ta sa hannu ta ɗauketa, baki ta saka ta hura kunnanta sai kuwa ta motsa ƙafafu ta saki kuka. Sake hura kunnan ta yi sai ga shi ta yi luf tana ajiyar zuciya. Harara ta galamin tare da yin ƙwafa,

“Ga abin da nake faɗa miki nan ai kin ƙi ji. Illar bawa jarirai nono a kwance. Shi ne dalili na farko da yake hadasawa ƙananun yara ciwon kunne musamman me ruwa. Abin da ku ka kasa fahimta shi ne, akwai mahaɗa tsakanin kunnen yaro da kuma maƙoshi wadda bata gama haɗuwa sai an ɗauki wani lokaci. Wannan bayar da nonon a kwance yakan haifar da suɓucewar wani kaso cikin mahaɗar sai ya tafi ya kwanta wanda shi ne yake zama wannan ruwan mugunyar da za ki ga yana kwaranyowa a kunnan yaro…”

“Ya Allah yanzu Dr yarinya ta kurmancewa zata yi?”

“Ba za ta kurmance ba amma gaskiya sai kin sa lura sossai. Bari tunda ina da lokaci in bambance miki nau’in ciwon kunnen da ya fi adabar yaranmu. Ƙananan yara tsakanin wata shida zuwa shekaru uku sukan yi fama da wani irin ciwon kunne da ake kira (Otitis media) shi (otitis media) ciwo ne wanda yake ciwo a tsakiyar kunne. Ciwon kunnen yafi faruwa da damina kuma yana zuwa da zazzaɓi wani lokaci mai tsanani sai dai sau da dama bai cika zama abun damuwa ba.

Akwai kuma wani ciwon kunnen da ake kiransa (otitis external), wanda shi kuma yake shafar wajen kunne. Koda yake yara basu cika kamuwa da shi ba  kamar na farkon ba. Yawanci ƙananan yara suna fama da ciwon tsakiyar kunne musamman ƙananan yaran da suka kasance daga cikin wannan jerin:

Yaran da aka haifa basu kai lokacin haihuwa ba. Akwai yaran da suke yawan jin sanyi sosai. Sannan akwai yara waɗanda basa son wari, kamar hayaƙin taba da sauran su. Ko kuma yaran da ba’a basu nono ba wato waɗanda basu sami shayarwa daga mahaifiya ba. Da kuma yaran da aka baiwa abincin gwan gwani. Mafi saurin kamuwa daga cikinsu su ne irin yaran da ake shayar da su abincinsu daga kwance.

Wasu ƙwayoyin cuta suke kawo ciwon tsakiyar kunne. Ƙwayoyin cutar na tafiya daga bayan maƙogoro yayin da (Eustachian tube) ta lalace. Wannan ne yake kawo ciwon tsakiyar kunne. Shi yasa yara masu yawan jin sanyi ko masu fama da ciwon maƙogoro ke kamuwa da ciwon kunne. (Otitis external) shi kuma yawanci yana faruwa saboda rashin tsabtar fatar jiki da ƙwayar bacteria…”

“To Dr ya alamominsa yake?”

“Kai Halimatu zalƙun muzalaƙo ɗa daga ciki roƙon uba kwabo. Ki bari na mutu sai ki bineni mana. Ai zan kai ki inda ki ke san zuwa. Alamun ciwon: Ciwon cikin kunne (Otitis media), yawancin manyan yara suna fama da ƙaiƙayin kunne da kuma zafi. Ƙananan yara basa iya magana, amma zasu kasance da zazzaɓi marar misali. Haka nan zasu kasa yin bacci su riƙa sosa kunnen su.

A wasu lokutan har ya yi jinni, kuma sukan kasa iya sauraron ƙara ko amo me ƙarfi. Za’a iya samun fitar ruwa mai ƙwayoyin cuta daga kunnuwan. Ciwon bayan kunne shi ma yana da zafi sosai, yana sa ƙuraje sossai a bayan kunnuwa. Wanda a hausance muke kira da ‘ƙimi’.

Ana iya ba yara ‘yan  ƙasa da wata shida maganin kashe ƙwayoyin cuta (Antibiotics). Shan maganin rage zafin ciwon.Yara suna jin sauƙi yayin da suka fara amfani da maganin kashe ƙwayoyin cuta. A nan yana da muhimmanci ga iyaye su kiyayye umurnin likita har ƙarshe.

Shan (Topical antibiotics) da man shafawa suna maganin (otitis external). Sake ganin likita na da amfani idan yaron yana da ciwon kunne ko yana amai sossai. Idan kuma yana zazzaɓi fiye da sa’a araba’in da takwas da kumburi bayan kunne, idan yana bacci sosai, ƙuraje a kunne, baya ji sossai ko gaba ɗaya.

Kunne yana ɗaya daga cikin sassa masu muhimmanci sosai a jikin ɗan Adam. Wanda ba kasafai ake gane muhimmancinsa ba, sai ya kamu da wata matsala. Kuma amfaninsa ba wai kawai a jin magana ya tsaya ba, a’a yakan taimaka wajen sa dai-daito idan mutum ya miƙe tsaye ta yadda ba zai faɗi ƙasa ba.

Kunne na da ɓangarori uku, na waje da tsakiya da kuma can ciki. Fatar kunne da ƙofar kunne ta waje su ne ɓangare na waje ɗin. Amfanin wannan sashe shi ne tare iska da amo ya saita su zuwa cikin kunnen. Wannan ɓangare bai cika samun ciwo sosai ba, sai dai akan iya yanke shi a haɗari, ko kuma da abubuwa masu kaifi idan wata tarzoma ta tashi misali. Ita kuwa ƙofar kunne ana iya ganin dattin kunne a ciki a fitar ta wannan ɓangare.

Ɓangare na tsakiyar haɗe yake da maƙogoro ta yadda ƙwayoyin cuta daga maƙogwaron kan yi saurin shiga kunne, musamman ga yara tunda hanyar da ta haɗasu gajeriya ce. Ruwa ma kan iya shiga wannan ɓangare na kunne a yayin wanka ya hana mutum sakat.

Daga can ciki kuma akwai wani ɓangaren, inda dodon kunne yake wato (cochlear) da wasu ƙasusuwa ƙanana guda uku. Jijiyar da ke da alhakin sa mutum jin magana a jikin dodon kunnen take. Wato ke nan dodon kunne shi ne ke da alhakin jin magana. Su kuma ƙasusuwan sukan taimaka wa jiki wajen daidaito.

Abubuwa da dama kan taɓa lafiyar dodon kunne har a rasashi ta hanyar hujewa;abubuwan su ne ƙwayoyin cuta (kamar sanƙarau) ko wasu magunguna, na nasara ne (kamar gentamicin) ko na gargajiya, ko kuma a huɗa shi ta hanyar susa da abu mai tsini.

Ko kuma ta hanyar faɗawa ruwa da ƙarfi, ko buguwa ta sanadiyar haɗari. Ko ta yawan jin ƙara fiye da ƙima, ko ma abin ya faru tun a ciki, a haifi mutum haka ba ya ji. Akan iya yin dashen wani dodon kunnen idan buƙatar hakan ta taso. Idan ruwa ya  shiga kunne, misali kamar a lokutan wanka, za a iya sa tsinke mai auduga a goge.

Idan bai fita ba a bari bayan kamar kwana biyu zai tsane da kansa. Sai dai idan ba a ji ya tsane da kansa ba ya kamata a je asibiti. Masu aiki a kamfanin da suke da injina masu  ƙara ko filin tashin jirgin sama, dole su riƙa toshe kunnensu a kullum. Domin kiyaye lafiyar dodon kunne. Irin wannan ƙara ma takan iya fasa dodon kunne. Masu aiki a irin waɗannan wurare yana da kyau su riƙa zuwa wurin likitocin kunne a kalla sau ɗaya a shekara don kula da lafiyar kunnensu.

Haƙƙinsu ne su nemi kamfanin ya samar musu abin rufe kunne da kuma likitoci domin kula da lafiyar kunnensu. A ƙasashen da suka ci gaba, idan babu irin wannan a kamfanin ma’aikata za su iya kai kamfani ƙara kotu don a tabbatar an samu yanayin aiki wanda ba zai taɓa lafiya ba.

Waɗannan su ne hanyoyin da za su iya sa a kamu da ciwon kunne, dama wasu hanyoyin daban-daban.

“To Dr hanyoyin kariya fa?”

“A mafi yawan lokuta ba sai an fitar da dattin kunne ba, dattin da kansa yake fita. Wato kunne shi ke wanke dattinsa da kansa. Yakan wanko shi ya turo shi ƙofa kunne. Za a ga dattin launin ruwan ƙasa a naɗe a jikin wani abu mai danƙo. Idan har ta kama sai an cire wannan abu mai danƙo, to kada a yi amfani da abu mai tsini. A sa irin abin goge kunnen nan mai auduga a bakin kunnen a fito da shi a hankali.

Wanke hannuwanka da na yaro kodayaushe. Shayar da yara da nonon uwa. Dena ba yara abincin kwalba lokacin suna kwance. Ko shayar da su a kwance. Daina amfani da kayan susa masu tsini. Daina shan taba a ɗakin da ƙananan yara suke.

Yiwa yaro rigakafi  yana rage wannan ciwon. Yin allurar rigakafin mura mai zafi (Fluvaccine) kowacce shekara. A ƙarshe, idan yaro ya kamu da ciwon kunne: Kada ayi amfani da auduga a kunnen, domin zata iya ƙara girman ƙwayar cutar. Kada a ɗiga maganin kashe ƙwayoyin cuta a kunnuwan yara, zai iya kawo fashewar kunne .Kada a share kunne da auduga domin kauda danƙon kunne”

Ta ƙarashe tana murmushi me sauti,

“Gaskiya na gode likita kuma insha Allahu zan kiyaye”

*****

Mun ci gaba da samun kulawa ni da ɗiyata har aka sallame mu bayan shawarwari daga likita kan yadda za ta samu kulawa yadda ya kamata. A ranar da za a ba mu sallama ne kuma na sake jin abin da har na koma ga Ubangiji tabonsa ba zai daina mintsinin zuciyata ba.

Ina kwance a gadon asibiti kasancewar ɗakina VIP ne kamar yadda na ji sun faɗa, Alhaji Labaran ne da Salisu da kuma Yaya Kamala suka shigo, ni kuma lokacin na rufe idanuna kamar ina jin bacci.

“Salisu burinmu ya cika yau ɗan Gilɓowa da cingum ɗinsa sun wula. Na so ace haɗe da ɗan kaɗafinsa  amma ba komai shi ma zai iya zama kifin cikin fatsarmu”

Haka kawai na ji kaina ya ɗaure game da kalamansa, ban fahimci sauran zantukan ba har suka gama. Da haka suka fita cike da farinciki da nishaɗi. Ina buɗe idanuna muka haɗa idanu da Yaya na ga tashin hankali sosai a cikin idanunsa sai dai kalmar Gilɓowa ita ce taketa yawo a kwanyata amma na kasa haɗa komai. Sai na haƙura.

*****

Motar da Salisu ya ɗauko mu a ciki na tsayawa na soma ganin jerin gwanon motoci suna fitowa daga ɓangaren gidansu Abdallah. Kai na ya ɗaure da mamaki na dubi Inna,

“Inna taron siyasa ake yi ko?”

Da sauri ta ba ni amsa da “eh”

Yayin da Salisu ya yi caraf ya furta,

“A’a Lantana ai wannan mai neman sunan Alhaji Alhussain Gilɓowa ne ‘yanta’adda suka shiga har gida suka kashe shi da matarsa da kuma maigadinsa. Ɗansa ne kaɗai ya tsira….”

Ban sake sanin inda nake ba sai farkawa na yi na gani a kan gadon Innarmu, gefena kuma ɗiyata ce da Inna. Hawaye ne suke bin fuskata ɗaya bayan ɗaya yayin da zuciyata ke mugun suya kamar za ta faso ƙirjina. Lallai sai yanzu na tara na kuma ɗebe kalaman Alhaji Labaran.

“Ɗan Gilɓowa ya wula tare da cingum ɗinsa. Wato Ummun Abdallah ce cingum yayin da Abdallah ya zamo ɗan kaɗafi.

‘Lallai kuwa sai ɗan kaɗafi ya ɗafewa duk wani jin daɗin rayuwarsa matuƙar ina numfashi’

Na yi furucin a zuciyata, haka na yini sur ba magana, Inna ta yi bambakin ta yi nasihar amma gani nake da na buɗe baki zan magana kamar zan faɗi abin da na ji ne ni kuma na ƙuduri babu mai jin hakan bayan Abdallah. Ita kanta mutuwar ta dake ta kawai tana nuna min babu komai ne saboda in dawo nutsuwata.

Ban sa Abdallah a idanuna ba, ban kuma sa ran hakan ba domin nasan duk inda yake ina ransa. Haka kuma duk inda yake ina da tabbacin kwanciyar hankali ta yi ƙaranci gare shi.

Ranar kwana bakwai da asuba muka tashi da bugun ƙofa, Inna ce ta yi ƙarfin halin buɗewa domin ranar Yaya bai kwana gida ba, haka muka kwana cikin zullumi. Inna na tunanin a wane hali yake ni kuma ina tunanin su Alhaji Labaran sun soma gudanar da ƙudirinsu a kansa.

Tana buɗewa sai ga Abdallah ya shigo, sanye yake cikin doguwar jallabiya fara, hannunsa riƙe da carbi da kuma kwalin biscuit. Bayan sun gaisa Inna ta yi masa gaisuwa domin zuwanta ba ta samu ganinsa ba. Juyowa ya yi gare ni, yayin da Inna ta fita ta bar mana ɗakin. Ina buɗe bakina zan yi masa magana sai kuka. Bai hanani ba, hasalima hannu ya saka ya ɗauki ɗiyata ya rungumeta a ƙirjinsa. Har sai da ta yi ƴar ƙara,

“Yi haƙuri Ummina kin ji.”

Ya furta da muryar da ta ƙara karyarmin da zuciya, gaba ɗaya tausayinsa ya gama nuƙurƙusa zuciyata. Hannu ya sa yana shafa kanta, ta yi luf da ita kamar me bacci. Dubana ya yi a tausashe.

“Ki yi haƙuri Lantana zan miki karambani ki yi min alfarma in san ya wa ɗiyarki sunan Ummina amma za mu riƙa kiranta da Aufana.”

“Kana da iko a kaina da komai nawa Abdallah, ballantana kuma ɗiyar da ba ni da takaimaman sanin mahaif….”

“Kar ki kuma matuƙar ina raye ba za ta yi kukan rashin mahaifi ba.”

Kuka ne ya kwace mun,

“Ga kwalin biscuit nan ki rarrabawa maƙota ni zan koma sabida sadakar su Abba”

“Yaya Abdallah na san wani abu game da rasuwarsu Abba duk da kokwanto nake yi amma akwai alamun lauje cikin naɗi.”

Da sauri ya dawo ya zauna, ban ɓoye masa komai ba game da farkon alaƙarmu da Alhaji Labaran da Salisu har ma da abin da na ji da kuma wanda nake zargi kan yaron da suka zo da shi. Gumi ne ya shiga tsattsafo masa, “Halimatu lallai kin zo da babban lamari amma ki riƙe wannan sirrin a zuciyarki ki kuma ba ni lokaci domin gudanar da bincike yadda ya kamata. Amma abu na farko da za mu soma yi dole mu kuɓutar da Yaya Kamala.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fitsarin Fako 2Fitsarin Fako 4 >>

1 thought on “Fitsarin Fako 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×