Skip to content
Part 5 of 6 in the Series Fudayl by Aysha I. Ahmad

Kiran waya ta ne ya dawo da ni daga tunanin da na afka, sai da na tsorata ma ni dan na manta da wayar ma. A jikin kujera na same ta na tuna tun jiya ma a nan na barta kenan, bakuwar lamba na gani na yi mamaki dan ni ban cika son daukan numba ba suna ba.

Na daure na dauka a karo na uku da wayan ta sake kara, ‘Assalamu alaikum, na fada a hankali, ‘amin waalaiki salam,’ naji an amsa, ‘wa ke magana’ na tambaya sai da akayi shiru kafin na ji yace ‘Fudayl ne.’

Ni sai na fara tunanin ina na san mai sunan nan ne?’ Kin tashi lafiya?’ Nace ‘lafiya’ sai na ji ya ce, ‘Am dama akwai friends(abokai) na da suke son zuwa ku gaisa, sunyi insisting ne ma so nace barin fada miki if you are ok.‘ Ok kawai na iya ce mai ya ce, ’ok zamu taho tare around two, thanks’, ya ajiye wayan. .na sauke ajiyar zuciya, sai yanzu na gane sunan shi kenan dan Abbu ya fada lokacin amma da ke bani cikin natsuwa ta ko rike sunan banyi ba. Oh suna mai dadi kuwa amma mai shi bai yi ba.

Tashi na yi saboda in san me zanyi ko da ba son auren nike ba da shi kanshi maigidan dole in yima bakin wani abu tunda haka ake, ba dadi kuma ace su zo basu ci komai ba.

Kicin din na fara bincikawa inga ko akwai kayan abinci sai kuwa naga ba abin da babu, freezer din kicin din ma akwai nama da kaji duka, na fara shawarar mai zan dafa ne, na cire naman dai na ajiye ya sake daga kankara, kajin kam wanke su nayi na kunna gas na daura na sa kayan kamshi na yanka albasa na zuba na rufe. Dubawa na yi naga akwai mincer na markaden nama, sai nace barin yi sambosa saboda na saba ko a gida bama cin abinci ba tare da snacks ba, ana kiran hakan ‘deserts’ wato abun tabawa da ba abinci ba wanda ya danganci filawa haka. Ana cin desert da rana bayan cin abinci ko kuma a ci da yamma. Sambosa ya yi in na yi matsayin desert din sai na duba fridge karamin da ke kicin din naga akwai kayan marmari dangin su apple, kankana, abarba, lemo, na hada fruit salad sannan na yi GINGER CHAMPAGNE, matsayin lemon sha.

Kafin kace me wannan na yi ayyuka da yawa, shiyasa nike kara gode ma Allah da yasa Ammi bata bar mu haka ba yanzu ko Hanan zata dafa ma abinci kaci kana santi. Amma na tuna farkon yin ta wai zata yi tuwo ranan bana nan lokacin ta dora, ya dai nuna kam amma taurin da ya yi baa magana ga bai tuku ba muka yi ta dariyan ta, ita dama tafi son gyaran dakuna da saka turaren wuta abun da ni kuma ke bani wahala kenan sai da Ammi ta dage na koya dan tace kar inyi aure inje ban iya ba sai aikin kicin. Ina son gani na a kicin ina dafe dafe shiyasa su Nurain basu so in tafi saboda ana cin abubuwan dadi dan nifa ko a tv naga abu sai na kokarta na yi.

Sai wuraren karfe sha biyu har da rabi na gama komai na shirya abincin a kan dining lemon kuma nasa a fridge. Na yi sauri gaskiya da yake dai in da wuta nan da nan kayi amfani da inji kayi ayyukan ka ba wani bata lokaci. Na yi fried rice hade da pepper chicken, sannan na yi sultan chips, ga kuma sambosa for dessert da na rufe shi a tray mai kyau da foil paper. Diban abincin nayi na ci duk da ma ba yunwa nike ji ba amma dan in tabbatar komai yayi dai dai, haka naji kuwa, ina alfahari da Ammi na dan badan ita ba ba zan iya duk ayyukan nan ba, Allah ya saka mata da alheri, amin.

Na sake gyara ko ina na kunna turaren wuta sai gidan ya dau kamshi, na shiga daki na sake wanka na yi alawla na fito na sa kaya na wata atamfa mai manyan filawas kalar ja tamun kyau sosai dinkin da na kalli madubi sai da na yaba ma telan nan, na murza yar hoda da dan mai a labbana sannan na ji ana kiran sallar azahar a masallaci watakila kusa ne dan radau na ji kiran na saka hijab na tada sallah. Ina idar da sallah kenan naji tsayuwar mota na duba lokaci naga har biyu tayi lallai time ba wuya.

Hayaniyar su da naji shi ya tabbatar mun da cewa sun shigo falo, nace suna da yawa kenan tunda na ji hayaniyar nan. Knocking kofa ta naji anyi nace’shigo’ sai naga Fudayl ne ya shigo ‘Assalamualaikum’ na amsa da ‘wa alaiku massalam’ ya ce ‘bakin sun zo ‘na ce ‘toh’a zuciya ta ina mamakin shi da baya dogon magana ko da yake ba masoyiyar sa bace ni ai da zaiyi magana yanda ya kamata.

Na share wannan tunanin na tashi na dauko mayafi na babba kalar atamfar na lulluba na bi bayan shi muka fita falon suna zazzaune su hudu ne ma ashe amma suke hayaniya haka, na samu kujera daya daga can gefe na zauna muka gaisa suka mana Allah sanya alkairi na ce ‘mun gode’ dayan da ke zaune kusa da Fudayl da na lura duk yafi su surutu shi ya ce ’bari mu miki introducing kanmu as closest friends ga mijin ki our very own Matawalle,’ Suka yi dariya shi kam Fudayl murmushi kawai yayi ya cigaba da danna wayar shi.

Ya cigaba da cewa ‘ni suna na Aminu Kamal,’ sauran suka ce AK in short, na yi murmushi, ya nuna na kusa da shi ‘ni suna na Nasir’ suka sake cewa Nas kenan, sannan dayan da suke su biyu a zaune yace ‘Khalid suna na ba wani nickname’ suka ce karya ne ‘gentle’ kenan kin ganshi nan baya son magana, nima na lura dan tun da muka gaisa bai sake wani magana ba nike ga halin su daya da Fudayl, na gefen gentle ne yace’ni kuma suna na Yusuf’ suka amsa da ‘cele ba’ Ak ne ke cewa ‘shi lokacin muna makaranta babu wanda bai sanshi ba saboda shige shige irin nashi yasa ake cemai celebrity mu kuma muka mai da shi ‘cele’ in short, na yi dariyar su sosai nace ‘toh an gaishe ku da sunaye haka, ku shiga ku ci abinci yanzu kam.’

Ak ya ce, ‘toh amarya mun gode,’ kallo na naga Fudayl yayi da alamun tambaya a idonshi da na fahimta so yake yace ‘kin yi abincin ne?’ gyada mai kai nayi kawai shima ya mike suka nufi dining room din, na bi su dan in ciro musu lemon daga fridge, na riga na fitar da cups daman, na ajiye Ak yace ‘ki huta amarya zan zuba ma kowa na karbe ki.’ Na ce ‘toh na gode Ak.’ Nas ne naji yana mai tsiya’ai dole kace zaka zuba tunda kai mayen abinci ne’ yace waye bai son abinci toh ha’an ,ku ji ka fa, Matawalle kaima layinmu daya ai ko? Sai lokacin naji Fudayl yayi magana’ kai dai dayan ka nikam bani da ci kowa ya sani, na fita ina dariyar su Ak na daga murya yana’ amarya kin ji shi ba, zaki ban labari in an kwana biyu sai kin dafa kwano biyu kullum.’ Nayi dariya nikam na fita na bar su.

Falo na koma na kunna tv ina kallo, ina jiyo hirar su Ak suna ta santi dan har naji yana cewa’ lallai Matawalle ka gama morewa fa, nas ke cewa’nikam kyan tebir din ma kadai ne ya fara burgeni komai a tsare, gentle kam sai yanzu naji maganar shi yana’ Matawalle amma balarabiya ka auro ko? Duk suka sa dariya, shi dai Fudayl bani jiyo maganar shi, a raina nace Allah ya zuba ma mutumin nan yanga, nasan dai namiji komai rashin maganar shi zaka ji shi cau in da abokan shi ne amma ban da wannan. Wata zuciyar tace to ina zaiyi magana tunda ba masoyiyar sa ake yaba ma ba. Shiru na jii su kuma sai karan cokula,nace toh yanzu ne ake bama ciki haqqin sa kenan,kai wannan in ka zauna da su na awa daya musamman AK sai cikin ka yayi ciwo. ‘ko zuwa na London fa ban ci irin abincin nan ba Matawalle’ abun da na jiyo wani ya fada a cikin su kafin in tantance waye ne na ji ihun su suna’ ho cele’ dole kace haka banza kana ta santi da Allah kar ka cinye mata faranti’ AK ne mai wannan maganar, ‘toh kai kuma ka ajiye mata cokali kar ka hadiye’ dariya suka ta bani nikam ,na manta da tv na kunna ma, waennan yan cafta ne gaskiya. har na manta yaushe rabo na da dariya haka nike ga tun maganar aure na da Fudayl. Sai naji wani iri amma ba komai haka Allah ya so.
Fitowar su na ji na sake gyara mayafina na amsa masu sallamar, nace kun fito kenan, suka ce mun fito amarya, nan Ak ya ciro kudi ya ajiye mun kan tebir din falo yana na sha ice cream. Nace ‘wannan dawainiya ce gaskiya ku bar shi, suka ce ‘ina amarya, dole ma ki amsa in kuma ba kin raina ba, nace ko daya na masu godiya. AK ya ce ‘sune da godiya ai, kin ga ni yanzu da abinci sai gobe, Nas ya ce wuce muje dan Allah kar ka zama Faisal, kai din da abinci ne sai gobe? Ashe da anyi ruwa da qanqara.

Muka yi dariya na sake masu godiya suka fita da Fudayl zai raka su, nikam falon na sake dawowa na zauna, kudin da AK ya ajiye na dauko naga dubu goma ne nace lallai suma masu hali ne. shigowar Fudayl ne yasa na dago na kalle shi, falon ya shigo nace ‘Am ga kudin nan da suka bayar.’ Ya ce, ‘No, naki ne ai, ki rike and Amna, sai da naji wani iri dan ban taba jin ya kira suna na ba. Wato dama yasan sunan nawa kenan kuma sai naji yayi dadi a bakin shi kamar shi ya rada mun, jin shi nayi ya ja numfashi kafin yace’ thank you for ehm..’ katse shi nayi da cewa ‘ba komai’ na fahimci akan abincin da na masu yake son fada amma ya tsaya kame kame, oh ni ban taba ganin namiji mai yanga irin shi ba.

Har zai shiga na ce ‘ina son magana da kai na dan lokaci’ juyowa ya yi amma mamaki ne a fuskar sa wanda nasan hakan ba zai rasa tunanin wace magana zanyi da shi din ba. Zama yayi sannan ya zubo mun ido yana son jin mai zan ce,’ina so ka yi haquri da ni, I wont be able to love you( ba zan iya son ka ba) a yanzu saboda ban san meye so ba sai dai bansan ko gaba ba, amma na ma alkawari I will be a good wife (zan zama mata ta gari) insha Allah zan maka biyayya ‘shiru na yi ina so inji mai zaice, ya dau kusan sakan uku kafin na ji yace, ‘ban taba so ba nima Amna, ban san ya so yake ba ya fada da raunin murya, ya cigaba da cewa’ naji dadin yadda kika karbi abokai na, kin mutunta ni hakan kuma ni a wurina so ne, bani bukatar wani abu kuma bayan nan’ kallon shi nike da mamakin kalamanshi, fuskar shi ta canza alamun ya shiga wani yanayi dan kamar maganar ma da kyar ya yi ta,toh yanzu akwai namijin da zai ce bai san so ba? kai anya kuwa? Nike ga dai fada kawai ya yi. ‘barin je sallah’maganar shi ta katse ni, ‘ok’nace ya mike ya fita nima na tashi jin ana ta kiran sallar ta la’asar na shiga inyi alawla inyi sallah.

Bayan na idar na fito na shiga gyaran wurin da su Fudayl suka ci abinci Allah yasa ma na wanke duk kayan da na bata kam bayan na gama, yanzu farantai da kofunan da suka bata ne sai kulolin, naga ma fried rice din ce ta saura sai sambosa din amma sultan chips din kam sun cinye shi, tattara su nayi na kai kayan wajen wankewa a nan kitchen din, sink ne babba shima da famfo a jiki, ina goge kan dining table din ne sai ga Fudayl ya shigo,’Assalamu alaikum’ na juyo na amsa mai da ‘wa alaiku massalam.’

Shigowa kicin din yayi sai na tsaya kallon shi da mamaki, ‘Ki kawo in taya ki gyara wurin’ na ji ya fada, ’am ki yi hakuri zuwa gobe zan ce ma Duddu ta dawo kawai, ita ta tafi da mai aikin lokacin biki akan sai wata sati su dawo’ dariya na yi da bansan yaushe ta zo ba, na ce ‘waye Duddu kuma?’Dariyar shima yayi kadan da ban taba gani ba yace ‘kema sunan ya baki dariya ko? Nace ai kam fa’ ,yace’ granma nawa ce fa, I called her Duddu only, Hajja ake kiran ta. ‘ nace ‘ok ayya,‘ yace,kawo in taya ki din’ nace’ ka bari zan karasa…’ ai kafin in gama magana ma ya wuce wurin sink din yana kokarin hada ruwan omo, zuwa na yi na karba’ kawo ka ga ba aikin maza bane wannan.’ yace ni fa sai nayi’ ganin ya dage nace ‘toh ka bari sai ka dauraye, haka muka fara ina wankewa yana daurayewa har muka gama ba dai mai magana cikin ni da shi, falo muka dawo na kunna tv shi kuma ya wuce ciki ya dauko laptop ya dawo ya samu dan kujera mai hade da tebir da ke gefe a falon wanda na lura saboda irin haka aka ajiye kujeran ,irin ta biyu ce a falon a kusurwa kuma su ke ,dora laptop din yayi a saman tebir din sannan ya zauna tare da budewa ya fara aiki, yanda yake sarrafa komfuta din sai ya birge ni ba kadan ba, ko aikin me yake sai Allah.

Wayar shi ce ta yi kara naga ya dauko ta amma sai bai amsa ba har ta katse sannan ya kira, ‘Duddu ina ta kewar ki fa, gaskiya gobe zaku dawo,’ shiru naga yayi bansan mai aka ce a daya bangaren ba na dai ji ya sake cewa’a’a gidan yayi shiru ne fa kuma ita wancan zata yi aiki kinsan, shirun ya sake sannan na ji ya ce’toh naji nikam bansan mai sunan ta ba ma. Dariya na ga yayi daya mai kyau sosai, ko da abokan shi ma banga ya yi dariya haka ba, ‘to to na ji Duddu yanzu dai zaku dawo goben please, eh ita ma gidan zai mata shiru kin ga ba zama nike ba, shiru ya yi sannan na ji yace ‘toh sai kun iso din zamu yi magana, Allah ya kaimu, zata ji insha Allah, dariya na ga ya sake yi, Duddu mana, sai dai kin dawo, bye bye.’ Annan naga ya ajiye wayan, juyowa ya yi nayi saurin maida ido na tv kar ya kama ni ina kallon shi, ‘Amna my grandma on the line, ta ce a gaishe ki’ oh saboda yaga Hausa na ba sosai ba shine yake mun turanci, toh cemai nayi banjin Hausan ne? oho dai, na amsa da’ina amsawa, zasu dawo goben? ‘ ‘eh kawai yace ya mike , nace ‘Allah ya kawo su lafiya’, ‘’amin ‘ya amsa yana nufar dakin shi. Ajiyar zuciya na sauqe, Allah gani gare ka, ko ya zaman nan zai kasance? Sai goben in Allah ya kaimu inga ya Duddu take, kai abun dariya ma, wai Duddu, ko mai yasa yake kiranta haka oho, zan so jin inda ta samu suna duddu din nan, da gani kuma sun shaku da ita tunda har dariya yake da suke wayan nan, ni fa ba zance ga labarin Fudayl ba ma dan ni bansan komai akan shi ba har yau, toh duka duka a wata guda fa akayi bikin nan kuma tun gani na da shi sau daya ban sake ganin shi ba, in ba kiyayya ba kam ai kazo kaga wacce zaka aura ko da a kurarren lokacin ne. Duk yanda na tsara rayuwa ta da mijin da zan aura hakan bai yiyu ba, in da ace ma Fudayl na sona toh ba laifi zan so shi nima amma ba zan taba son mutumin da baya sona ba gaskiya har ga Allah. Wata ranan litinin ba zan manta ba shine zuwan shi gidanmu, gashi ya zamo sanadin dagula mun tsarin rayuwata ko kuma dama an dade da shirya hakan ban sani ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fudayl 4Fudayl 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×