Skip to content

Fudayl | Babi Na Daya

4
(1)

‘Amna, wato a rayuwa kowa da kika gani da irin jarrabawar da Allah ke mai saboda haka ina so ki cigaba da addu’a kuma ki bar ma Allah zabi inshaAllahu zaki ga sakamako na alkairi kuma zaki ci ribar biyayya.” Kalaman ammi na kenan lokacin da abbu yayi maganan aure na.Madalla da uwa ta gari,Alhamdulillah.

*****

Lallai ammi kinyi gaskiya tabbas a rayuwa komai ya zo mai wucewa ne haka nan duk rintsi in kayi haquri kayi biyayya zaka ci riba da izinin Allah, a matsayin da nake a yau ina kara gode ma Allah.

*****

‘Ammi’ na kira sunan ta ina hawaye, na kasa cin abinci ammi, ni kadai fa yau, tace ‘Amna am meya sa baza ki dau kaddara bane uhm? aure fa kika yi kuma kowa da haka ya saba, kiyi haquri kinji?’

kuka nake kamar karamar yarinya, wanda aka kira da sunan miji na yana gefe yana kallo na. Allah kadai yasan me yake zuciyar shi, dan ni banga dalilin da zai sa ya raba ni da su ammi na da kanne na ba bayan kuma ba sona yake ba. Eh mana tunda ban ji ba sai aure kawai, ai sai kuka na ya dada karuwa naji na tsane shi ma.

Ammi tace, ‘ga su Nurain ma kin sa su kukan ai hankalin ki ya kwanta Amna kin ji ba.’ Ina kallonsu, kukan suke musamman Nurain da nafi shakuwa da shi. Nace ‘ishtaqat lakuma, (I miss you all) habiibi ka daina kuka am here for you always ina nan tare da ku, ka ji?’ Yace ‘aunt Amna wa zai ke mana abinci toh? I will miss your cooking so much,’ na kalli Hanan da ke hawaye ita ma nace, ’ke fa habibti ba zaki yi magana ba?’ Tace zanyi Aunt Amna and am missing you already.’

Abbu da ke zaune shima sai yanzu ya yi magana. ’Ku daina hawayen nan haka mana, binti ki zama mai hakuri kinji ko? inshaAllah zaki ga alheri. Kuma muna nan tare da ke always. Nima na fara missing abincin ki.’ Duk da larabci ya yi wannan maganar, sai naga Ammi ta kalle shi na yi dariya na ce ‘ammi kinji ba?’ Ta ce, ‘sai ka ke karbo nata din ai,’ duk muka yi dariya. Ya ce, ’tuba nake ai itan ma ke ki ka koya mata kinga kuwa tsohon hannu yafi.’

Na yi dariya nace, ‘ammi ban ga Haleefa ba, ina yaje ana dinner and he is missing.’ Tace kin san shi ai yana gyara wai an bata mai daki’ Nayi dariya nace, ‘he will never change ai ammi am, zan kira shi.’ ‘Tasbah ala khair,’ ta ce, ‘ki yi addua fa sai da safe.’ Muka yi sallama sai lokacin na lura har naci kusan rabin abincin ashe ban sani ba.

Lokacin da naga yazo daukan wayan shi na lura ashe bai bar falo din ba dama ganin naki cin abincin yasa ya kiramun su Ammi a wayan shi muka yi video call. Hakan yasa naji zan iya zama da shi ko da ba son shi nike ba amma yamun abun da raina ke so kuma naji dadi. Shukran na ce mai da sanyin murya, ya daga kai kawai bansan ko yaji mai nace ba ma, harshe na ya saba da larabci shi yasa tunda a gida ma Abbu na mana sosai shiyasa ba ko yaushe muke yin Hausa ba sai da Ammi. Ya shige bedroom din da nake zaton shi ne na shi.

*****

Ainihin suna na Hamna Nuhu Alkali amma an fi kira na da Amna wanda yaya na ya fara kira na da shi sai sunan ya bi ni daga Hamna na koma Amna, sunan kakar mahaifina na ci. Mu biyar ne a gidanmu, yaya na Ibrahim da muke kira ya Abba, shi ne babba sunan baban Abbu aka sa mai. Yana shekarar sa ta karshe a kasar India inda yake karantar medicine. Sai ni da nike bi masa amma shekara shida ne tsakanin mu, na kammala makarantar gaba da firamare shekara biyu da suka wuce zan iya cewa ma har da wata hudu kenan a makarantar High school da ke cikin garin Kano.

Tunda na gama nike son wucewa wata amma Abbu ya hana ni , ni kuma gashi bani da tsayayyan saurayi ballantana ayi mani aure. Asali ma Abbu baya son tara samari, kuma ko da ka ga yar sa kana so sai dai ka turo kafin ma kayi magana da ita, haka tsarin shi yake, nikam dama ban taba kula wani a waje da sunan zance ba tunda nasan tsarin Abbu. Akwai wani Muhammad da ya ganni ya biyo yaga gidanmu sai ya turo wurin Abbu. Lokacin ma ina aji uku a sakandare ne, ammi ke ban labari ai Abbu yace musu karatu zanyi ba kuma hakan bane kawai ya san gidan su yaron ba masu tarbiyya bane shi kuma kullum addu’ar shi Allah ya bani miji na gari da ya fito a gidan mutunci.

Mahaifina Alhaji Nuhu Ibrahim Alkali sana’ar sa kasuwanci ne, babanshi dan Sudan ne ya dawo Nigeria da zama lokacin da ya rasa iyayen shi a gobara da gidan su yayi. Babanshi Alkali ne a can Sudan din, haka Abbu ya bamu labari. Ya baro kasar yazo nan Najeriya a nan kano, ya yi aure da matar shi Binta yar garin Maiduguri ce ita ma balarabiyar kasar Yemen ce, fara sol da ita, yaran su uku, Abbu ne dan autan su yana da yayyu mata biyu da suke aure a nan duka kuma sun hayayyafa suma. Shekarar da ta wuce Allah yayi ma babansu Abbu rasuwa bayan ya sha jinya.

Tun daga nan maman Abbu da muke kira Sitti (kaka kenan da larabci) ta dawo gidanta da Abbu ya siya mata a rijiyar zaki inda mu kuma muke GRA quaters. Abbu ya so ta dawo gidan mu ta ki saboda tace ita baza ta iya zama da sirika ba ta takura mata shiyasa ya kyale ta sai dai kullum zai je kuma ya dauko mata mai aiki dattijuwa ’ Iya’ da suke kwana tare. Muma muna zuwa duk weekends mu wuni a can.

Abbu na ba wani babba bane ba amma zai kai shekaru hamsin da hudu a duniya da haihuwa. Mahaifiyar mu kuwa sunan ta Hajiya Hafsat, muna kiranta, Ammi. Ita kadai ce a wajen Abbunmu yar garin Gombe ce kuma bafulatana, tana da kanne mata biyu da wan ta babba, zuwan Abbu service garin Gombe ne suka hadu cikin ikon Allah kuma ya nema auren ta aka bashi. Mu bakwai ne a gidanmu in ka hada da Abbu da Ammi. Gidanmu kuwa shine babba kuma na karshe a layinmu. Ina da kanne na uku kenan, Aliyu ne ke bi mani da muke kira da Haleefa sai Aysha ‘Hanan’ sai dan auta Usman Nurain.

Ni kuwa zan iya kiran kaina fara amma ba tas ba, gani mai dan karamin jiki ,jama’a da dama sukan yi mamaki in nace na gama sakandare wasu kan dauka aji uku nike a sakandare din saboda fuskar yarinta gare ni. Amma duk da karamin jiki na ina da diri mai kyau saboda irin mu ne bature ke kira ‘model’. Ba fa dan jikina bane ba nike kwada shi, a’a domin kawai ku fahimci ko ni Amna ya nike ne. Ina da hanci sosai ma, ga baki na yayi daidai da yar karamar fiska ta amma ina da gira mai yawa a saman idanuwa na wacce take a kwance da sai ka dauka mai nike shafa mata kuma baki sosai. Sai dai ni gajeriya ce amma bazan kira kaina da guntuwa ba sai dai in raba tsakiya.

Ba yaban kai ba ni kaina nasan bani da kwaramniya ma’ana yawan surutu amma in da kannena ne zaka ga ina hira sosai ma. Babu dai abinda zance sai Alhamdulillah kawai. Gashi na kuwa tamkar na larabawa ga laushi ko da yake tsatson larabawan ne, ko kitse shi bani iya yi sai dai inje a wanke mun saboda yawa. Ni ba ma’abociyar kwalliyar nan ba ce ta zamani, bar ni dai in nayi wanka zan shafa mai in goga yar powder sai insa man baki shima ba kala ba kuma ba mai yawa ba, kawayena a makaranta kan ce dan ina da kyau ne yasa bani son yin kwalliyan sai dai inyi dariya kawai tunda nasan ba hakan bane ra’ayina ne kawai.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×