Game da Mu

Hikaya taska ce da aka kirkira don masu sha’awar rubuce-rubuce da karance-karance da kuma manazarta litattafan Hausa su samu dandali na musamman don ilmantarwa, nishadantarwa da karar juna.

Don haka, kowa na iya yin rajista don karantawa ko rubuta labari. Mutum na iya yin tsokaci bisa labarin wani, haka shima za a iya yin tsokaci bisa labarinsa. Ta yin haka ne masu sha’awar rubuce-rubuce za su samu damar habaka rubutunsu har su wallafa.

Muna gayyatar malamai da daliban jami’o’i da kwalejoji har ma da sakandare masu nazartar labarun zube da wasan kwaikwayo da wake da su yi amfani da wannan taskar wajen bunkasa nazarinsu. Dalibi dama duk mai sha’awa na iya bunkasa rubutunsa ta hanyar bawa wasu dama su karanta kuma su yi tsokaci.

Baya ga bangare na yin rubutu da karatu da kuma tsokaci, akwai sashe na azanci inda mu ke sanya kalaman hikima irin su karin magana, habaici, arishi, nasiha da ma hikimomi na mutane daban-daban don karuwar sauran jama’a.

Har ila yau, Hikaya na dauke da kasuwar sayar da littattafan Hausa har da sauran littattafai. Mutum na iya shiga kasuwar, ya zabi littattafin da yake so, ya biya kudi sannan ya sauke littafin a wayarsa ko komfutarsa. Akwai kuma littattafai da dama da mutum zai iya saukewa kyauta.

Masu sha’awar wallafa littattafansu na iya tuntubarmu ta hanyar latsa wannan wuri. Zamu wallafa musu littafinsu kuma mu sanya musu a kasuwar Hikaya don su sayar.

Don wani karin bayani, shawari ko tambaya da ya shafi wannan taskar, kuna iya tuntubarmu ta hanyar latsa nan, ko kuwa ku je ‘menu’ dake kasa da nan, za ku ga ‘Tuntube mu’, sai ku latsa nan.

Sai mun ji daga gareku..