Skip to content
Part 28 of 32 in the Series Hakabiyya by Fulani Bingel

Sai ta ji maganar bambarakwai, wato shi ya zama mace ita namijin, shi ne yake faɗa mata abinda maza ake faɗawa, sai kawai ta taɓe baki kamar tana gabansa.

“Ba zan iya ba, da zan iya da ban kira ka cikin daren nan ba.”

“Ni kuwa kinga na iya, dan daga shekaranjiya zuwa yau kallon yar ƙaramar ƙanwata nake miki, kuma matar Babana.”

“Aww da wane kallo kake mini?”

Ya yi murmushi yana gyara kwanciyarsa jin ya kusa bambarama. Sai ya ji duk wani haushinta na ɗazu na yayewa, shi kaɗai yasan daɗin da ya ji da yaga kiranta.

“Kallon ɗalibata mana, mai masifar so na.”

“Ashe kasan ina son ka.”

“Kowa ma ya sani.”

“To me ya hana ka nunan naka son.”

“Babana, ke din rabonsa ce.”

Ta yi shiru tana jin kamar ta masa gorin ai ba Babansa ba ne, kawunsa ne, sai kuma ta kasa jin ita kanta maganar ta mata nauyi.

“Kin yi shiru? Ko tunanin Alhajina kike? Bari na turo miki Number ɗinsa ki Kira shi yanzu, shi ya dace ki kira dama.”

Kan ta yi magana ya kashe, sai ga number ta shigo, haushi yasa ta yi jifa da wayar gefe, ta ɗau fillo ta danne kanta da shi, so take barci ya kwashe ta ko ta yi mafarkin da za a nuna mata hanyar da za ta bi ta fidda kanta daga wannan masifar.

Washegari tunda ta tashi take ganin Mami nata hidimar dafe-dafe, a gurin Babanta take jin wai mai zubin ghost ne ya yi waya zai zo. Haka ta dawo tana taya Mamin tana mamakin yadda take rawar jiki kamar ba tada manufar auren. Har suka gama suka shirya kome inda ya dace, anan Mamin ta saka ta yin wanka ta zuba wata uwar kwalliya tamkar mai zuwa gasar fidda gwanin kyawu da iya ado. Mamin da kanta ta saka mata yari da sarka tana daɗa jaddada mata ta nutsu a gabansa banda yawan surutu da dariya. Daga nan ta fice tarbarsa kasancewar ya iso.

Tun daga nesa ya hango ta, ta yi masa kyan da ya saka shi juyowa ya kalli direbansa yaga shi ma ita yake kallo, bai san sanda ya talle masa ƙeya ba yana cewa “rufe idonka kada ta yi tuntuɓe, uwarɗakinka take zama nan da kwanaki, kai ban yafe ba ka ƙara mata kallon ƙurilla irin haka.”

Ya kalle shi baki buɗe yana dafe ƙeyarsa yana mamakin abinda ya samu ogansa, sai kuma ya basar yana juyawa da sauri zai buɗe motar ya fita dan ya buɗe masa shi ma, hannunsa na isa ga mabudin ya ji ya riƙe shi, “bar shi zan fita da kaina, yi zamanka cikin motar.”

Ya buɗe ya fito yana baza babbar rigarsa yana gyara zaman hularsa, ya harɗe hannayensa yana kallon yanayin takunta da ya rasa inda yasan irinsa, bai ɗauke idonsa kanta ba har ta iso ta masa sallama tana yatsine fuskar da ta zame mata ɗabi’a. 

“Baba an yini lafiya?”

Ta furta da sigar da ta saka shi hangame baki yana dariya.

“A’a ba a yi haka ba fa, ba dai Baba ba, ki ringa kira na yaya ko Hameedu na kawai, a’a ke, dinga ce mini Alhajinki ya fi daɗi.”

‘Ko surukina ba.’

Ta furta cikin ranta tana kallonsa a kaikaice tana jin kamar ta kakkatse shi da mari.

Ya mata kallo daga samanta zuwa ƙasanta, ya shaƙi ƙanshinta da jiyan nan ya je ya nemo irin turaren ya feffeshe ɗakinsa da shi, sai ya yi murmushi ya shafo gemunsa da furfura ta fara ratsawa ya ce, “kai, kai, Baby sarauniya kin yi kyawu. Ko dai mu zauna anan mu sha hira ne kafin na shiga, wabillahil azim baki san yadda kika cika nan ɗi na ba ne, ke ko ruwa nake sha fuskarki nake gani cikin kofin.”

Ya furta yana aje hannunsa a saitin zuciyarta.

Ta yamutsa fuska tana jin sabuwar tsanarsa na mata wani tsiron. Sai kuma ta narke fuskar tana kallonsa a marairaice. “Baba dan Allah ka rufa mini asiri ka bar maganar nan, ina da wanda nake so nake jin irin abinda kake ji kaina a kansa.”

Sai ya tsuke fuska yana jin farin cikinsa na komawa wani saƙon, sai kuma ya mata murmushi ya ce, “ba kome ai, da sannu ni ma watarana za ki so ni, ke dai bari a yi auren.”

“Da gaske nake wallahi ba na son ka! Ka ga kai Abokin Baba nane ina zan kai ka saboda Allah? Ka taimaka ka faɗawa Baba baka so na, ni ba zan iya faɗa masa ba.”

“Assha! Ai ko ba na ƙaunarki Bawa ya ɗauko ki ya ba ni ke ba zan iya turewa ba, bare kuma ina ƙaunarki, haba Baby saurayina ba fa tsufa na yi ba, Allah duka hamsin da ‘yan wasula nake, menene su samarin naki suka fini?”

Ta ɓalla masa harara tana ƙare masa kallo sai ta rasa abinda Huzaif zai nuna masa.

Sai ta juya ta ce masa ya taho babanta ya ce bai iya fitowa wajen.

Ya juya da sauri zuwa ga boot ɗin motar, ya buɗe ya zaro wani dogon abu da aka naɗe da wata leda mai zip. Ya bita da sauri har ya tadda ta suka jera.

“Yarinta mai daɗi, ki yi kome ba kome ba Baby sarauniya. Ina sonki a kome din da za ki yi,” ta yi kamar ta ja masa tsaki sai kuma ta tuna zai iya zama surukinta kar ta ɓata lamari tun yanzu, sai kawai ta tsuke fuska suka ci gaba da jerawa har ɓangaren Bawa. Anan falonsa suka tadda shi a zaune saman kujera gefensa kuma Mami ce.

Alhaji Hameed ɗin ma ya zauna, Haƙabiyya kuma ta juya ta fita saboda lecture da ke gare ta  ranar.

Suka gaisa da Zawwa tana ta shan ƙamshi, sai kuma ya juya ga Bawa ya masa murmushi ya taso da wannan abin ya zo ya zauna a gabansa.

“Gashi wannan ka saka, ina jin kunya, ina jinta sosai Bawa, ku dada haƙuri da ni dan Allah, Zawwa ke ma ki yafe mini abubuwan da suka faru da ku a dalilina.”

Ta yamutsa fuska tana harararsa ta ƙasan ido, sai kuma ta masa murmushin da iyakarsa fatar baki ta ce.

“Ba kome yawuce fa, dukkaninmu masu lefi ne sai dai na wani yafi na wani, Allah ya ba mu haƙuri baki ɗaya.”

Sai ya miƙo Mata abin ta karɓa ta hau zugewa har ta buɗe gabaɗaya. Ta ga ƙafar katako ce ya kawowa Bawa irin mai ƙarshen tsadar nan, sai ta ɗago ta kalli Bawa da dariyar farin ciki ke bayyana a fuskarshi, ta kalli Alh Hameedu da shima idonsa na kan Bawan, sai kawai taji hawayen baƙin ciki na cikowa cikin idanuwanta!

“Gaskiya na gode da wannan kyauta Hameedu, kasan ba yadda Haadiru bai yi in saka abin nan naƙi ba, amma tunda kai ne ka ba ni dole na saka, na gode sosai surukina Allah ya dawwamar da zumuncinmu har jikoki.”

Hameedun ya yi murmushi yana jin kamar ya sauke wani haƙƙine da ya hau kansa, sai kuma idonsa ya kai kan Zawwa da ta dangwarar da ƙafar ta tashi da sauri ta bar falon. Ya ji wani abu ya daki ransa har ya waigo ya kalli Bawa da shi ma ya bita da ido, sai Bawan ya masa murmushi cikin son basarwa ya ce, “kasan mata lamarin nasu sai haƙuri, tunda ta ce ma yawuce, yawuce ɗin, kawai dai ka yi haƙuri da yadda za ka dinga ganinta, abin ne ta masa riƙon da sai a sannu zai bar cikin ranta.”

Ya sunkwiyar da kansa yana jin haushin halinsa yana kuma son tambayarsa abu sai dai ya gagara buɗe bakin jin harshensa ya yi masa nauyi. Har Bawan ya matso ya dafa kafaɗarsa, ya ɗago suka haɗa ido da shi, sai ya kwashe masa da dariya yana nuna fuskarsa.

“Kai Hameedu baka da kunya wallahi, ji yadda fuskarka ta koma ja? Haƙabiyya kake tunanin za ta hanaka ko? To ba za ta hana ba, tana son lamarin sosai fiye da zatonka, dan haka kar ka wani damu, ita kanta yarinyar bata san kome da ya faru gabaɗaya ba balle ta ƙika kansa.”

Fara’a ta wadatu a fuskarsa har yasa Bawan riƙe baki yana mamakin irin son da yake mata da bai iya ɓoye shi ko a gabansa, sai ya ji ya bashi tausayi kuma, a cikin ransa ya hau yi masa fatan Allah Yasa Haƙabiyyar ma ta soshi kamar yadda yake sonta.

Ya juya gefensa ya ɗauko wayarsa ya kira Haadiru, nan ya bashi labarin kyautar ƙafar da aka kawo masa, ya kuma ce masa ya zo ya saka masa, ya kuma nuna masa yadda ake sawa da cirewa dan idan ya gaji ko idan zai kwanta ya ringa cire abarsa.

Anan suka ɗan tattauna kan gidan da Hameedun ke son siya cikin unguwar tasu, sai kuma ya sake ɗaga waya ya kira Zawwa dan ta turo ma Hameedu, Haƙabiyyar, ta faɗa masa ita ma data dawo bata tadda ta ba ta yi tafiyarta makaranta, sai kuma ta yi ƙwafa ta kashe wayar alamun cikin haushin hakan take ita ma.

Ya waiwaiya ga Hameedun ya faɗa masa ta tafi makaranta sakamakon lecture gaggawa da ta ta so musu.

Hameedun ya yi murmushin yaƙe ya nuna masa ba kome shi ma sauri yake zai tafi. A cikin ransa kuwa jinsa ya yi baƙiƙirin ga wani ɓacin rai dake taso masa musamman da ya tuna cikin uwar kwalliyar da ya taddata, yanzu haka gyale ta saka ta fita, ta sake bulbula mayen turaren nan nata, tuna hakan yasa ransa ƙara ɓaci har ya fito a fuskarsa, ya ja siririn tsakin da ya maido da hankalin Bawan kansa, “to Malam zumuɗi za ta dawo ai ba sai kana tsaki ba.” Sai kuma ya yi dariya ganin Hameedun nata ɓata fuska ya miƙa masa hannu suka sake musabaha ya tashi ya tafi da zummar sai bayan kwana biyu zai dawo.

Koda ya fita ji ya yi hankalinsa ya gaza

Kwanciya, sai kawai ya bawa direban umarnin su tafi makarantar da take. 

Ɓangaren shugaban jami’ar suka yi inda yasan nan zai samu Alhaji Bilyaminu kasancewarsa ƙani yake ga shugaban, haka shi ya saka ya binciko masa har department din da take a makarantar tun farkon saninsa da ita. Anan ɗin kuwa ya tarda shi, suka cafke bayan sun gaisa, sai kuma ya hau kallonsa daga sama har ƙasa kafin kuma ya tuntsire da dariya, “a’a malam zumuɗi hala amaryar aka biyo nan, irin wannan kwalliya haka, wai ma ko kunya ta baka ji kamar ba nan na baka ɗiyata ba ka ce ka mata girma, yanzu gidan ubanwa ka kai girman naka da za ka maƙale ma yarinyar nan?”

Hameedu ya yi dariya yana sa hannu ya zare hular kansa ya aje, sai ya ji haushin da yake ji na gushewa cikin ransa sai kuma ya harare shi ya ce.

“Wai ku menene naku da Ni ne, yanzu ma surukina ya gama kirana malam zumuɗin nan kai ma gashi ka ɗora, ku barni ni ma na ci lokaci na, ku sanda kuka yi taku soyayyar waya takuraku saboda Allah? Sannan ɗiyar taka a lokacin nasha na tsufa ai, bansan ni ɗin matashi ba ne sai yanzu da na fara son wannan ɗin, to menene lefina?”

Haji Bilya ya shafa ƙaton cikinsa yana dariya ƙasa-ƙasa yana kallon furfurar da ke sajen Hameedun, da wacce ke kwance a gemunsa.

“Duniya mai yayi! To ai shi ke nan bari na yi shiru, yanzu itan ka zo gani ko kuwa begena ya cika ranka ka zo ka ganni.”

Baisan sanda ya tuntsire da dariya ba yana ƙare masa ƙallo.

“Allah ya tsare ni da hakan, tura wanda za ka tura ya kawo mini ita nan ni.”

Sai kuma ya ɓata fuska sanin halin abokin nasa.

“Idan ta zo banda kallon ƙurilla dan Allah, ku gaisa kawai sai ka tashi ka fita kaga yarinya ce kar kasa ta mana kallon dattijan banza.”.

“Baka isa ba wallahi, ba za ka haɗa ni da yaya ba yaga shegantaka cikin makarantarsa, muje na nuna ma inda za ka jira ta, banda shegen zumuɗi ma ka bari mana ta koma gida ba sai ku yi hirarku a natse ba.”

“Na ji, kai ni gurin sai ka yi tafiyarka ba ma sai kun gaisa ba.”

Daga nan suka fita, ya tura wani Halliru da ke kula da tsaftar office din, ya kwatanta masa department ɗin da take, ya ce ya je can ya kira masa Haƙabiyya Bawa Malle.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Hakabiyya 27Hakabiyya 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×