Skip to content
Part 3 of 32 in the Series Hakabiyya by Fulani Bingel

“Idan zan rufe gidan nan sau goma sai ta fita sau goma, wannan sakacinki ne da iya ɗaurewa ƙarya gindi. Na ce shi wankan dole ne? Idan za ki kauce daga gabanta me ya sa ba za ki rufe ta a ɗaki ba?”

“Haba Maigida, a mari take ne da zan dinga kulle ta ko a gidan mahaukata? Ina dalilin da za ka matsa har haka, na faɗa maka bana sanin za ta fita, yanzun ma zaune muke tana gyaran zogale na ce bari na kewaya kafin na fito ta fice, idan tsaron dole ne ka ƙara tsayin katangarka mana. Amma Allah ba zan zauna ina maka gadin ƙatuwar budurwa kamar Hamdiyya ba.”

Motsin da suka ji a ƙofa ya saka su waigawa gabaɗaya suka yi arba da ita tsaye tana ta zare idanuwa kamar Barewa a bakin Zaki.

“Daga ina kike, ba saboda ke na rufe ƙofa yau ba?” Kawu ya furta.

“Can baya naje, ka yi haƙuri dan Allah.”

“Wanene shi yaron?”

Ji ta yi hantarta ta cure guri guda jin tambayar daga sama. Yaushe Kawu yasan abinda nake yi?. Da sauri ta gayyato juriya ta aza saman fuskarta.

“Tambayarki nake ko, a ina kuka haɗu.”

“A asibiti, tun sa’adda aka kwantar da Baba.”

Ya bi ta da kallo daga sama har ƙasa yana mamakin yadda ta bashi amsa ba gargada.

“Shekararku guda ke nan? Ba ki taɓa faɗa mini ba balle ma na yi matsayin da zai nemi izinin nemanki a gurina, kike fita da shi ko’ina a cikin Kano, har sai da mutunen waje suka ankarar da ni, wai ni Sahabi ɗiyata ke yawo da wani  ƙato a gari.”

“Ka yi haƙuri…”

“Zan haƙura, amma faɗa mini, wacce wasiyya mahaifinki ya bar mini?”

Shiru ta yi tana raba idanuwa.
“Tambayarki nake yi ko!?”
“Umm…Cewa ya yi ka kula dani, kar ka bar Ni na kula kowa a waje.”

“Saboda me ya ce haka?”

“Saboda kaine jininsa guda ɗaya da ya rage, kuma yana so ka haɗa ni aure da Yaya Haruna.”

“Shi Yayan wanene shi a gurina?”

“Ɗan ka ne.”

“Ke kuma fa?”

“’Yar ka ce, ‘yar amana.”

“Da mahaifinki ya roƙi hakan gurina me na ce masa?”

“Ka yi masa alƙawarin za ka yi duk abinda ya furta koda kuwa shi ne abu na ƙarshe da za ka gabatar a rayuwarka ba Ni da miji sai Yaya.”

“To yanzun da kike kula wani me kike son mai da ni?”

Ta yi shiru, dauriyar tata ta gama kaiwa ƙarshe.

“Tambayarki nake Hamdiyya!!”

“Kawu wallahi…Ina…ina son sa ne.”
Ta furta hawaye na rige-rigen isa gurbin wuyanta.

Baki kawai ya buɗe daga shi har matar tasa, ya tsura mata ido yana jinjina girman zamanin da yake ciki.

“A’a, share hawayenki, kinsan me za a yi? Na fasa jira Harunan ya dawo daga Kwaleji, nan da wata guda zan ɗaura muku aure, dan haka ki ɗauko son da kike yiwa wancan ɗin ki maido shi kan Haruna, ki kuma haƙura da shi ki ba ni haɗin kai mu cika burin marigayi.”

Zuciyarta ta buga tamkar za ta tarwatsa allon ƙirjinta ta fito, ji ta yi ruhinta na ƙoƙarin arcewa daga gangar jikinta, sai dai hakan bai hanata riƙe kanta ta fasa ihun da amsa kuwwar sa ya ratsa sabon ginin nasu ba.

“Wallahi Kawu ba na son Yaya shi ma baya so na, Ni Huzaif nake so idan ban same shi ba mutuwa zan yi.”

“Babanki ma sa’adda ya auri Babarki baya sonta ba ta son shi, wanzuwarki anan yanzu shi zai tabbatar miki da cewar bayan auren sun so juna har suka samar da ke. Babu abinda ya kashe su Hamdiyya.”

Kawu ya furta yana sunkutar buta ya fice daga gidan.

Rarrafawa ta yi ta faɗa ɗaki cikin gunjin kuka, auren wani ba Huzaif ba nan da wata guda abu ne da bata taɓa zaton faruwarsa ba. Da girman Allah ta yi rantsuwa idan ba shi ba sai dai ta mutu ba aure, rabin kukanta tana yi ne dan tausayin Kawu da kanta sanin rabuwarsu ta zo, ta sani tunda ya furta babu kuma wani abu da zai tada zancensa, haka idan har ita jinin Kawu ce da gaske to kuwa tunda ta furta Huzaif take so ita ma babu wani abu da zai tada hakan. Ta tuna adanannun kuɗaɗenta da Huzaif ke yawan bata tana ɓoye su cikin kango, ba ta zaci amfaninsu zai zo mata da wuri haka ba, tabbas sun ishe ta ta yi duk abinda za ta yi, ta tafi duk inda take so ita da masoyinta suyi aure, idan yaso bayan ta haihu sai ta zo gun Kawu ta bashi haƙuri. Da wannan tunanin ta ji hankalinta ya ɗan kwanta, sai dai fa ba za ta iya jira har zuwa ranar haɗuwarsu nan da sati guda ba. Dole ne ta neme shi a gobe, amma ta yaya? Sau ɗaya ya taɓa nuna mata layin gidan da yake. Da wannan tunanin wani zazzafan zazzaɓi ya silalo ya lulluɓeta.

Idan lissafinta na tafiya daidai wannan shi ne mutum na goma da ta tambaya ko yasan Huzaif yana bata tabbacin bai sani ba.

“Malam, bai fi shekara fa da zuwa nan ba, za ka ganshi dogo fari mai yawan suma? Yauwa a sabon Bankin nan Silver da aka buɗe yake aiki.”

Ta furta cike da sarewa.

“’Yan mata na faɗa miki ban san shi ba, ni nan unguwarmu ce anan aka haifeni, ke idan da baƙo cikin unguwar nan ni zan fara sani saboda tsabar sa idona, Ni fa baƙo guda na sani anan unguwar shi kuma ya fi shekara guda nan, haka ba Huzaifu sunansa ba. Ki dai yi tunani ko dai ba haka sunansa yake ba? Kina ta Banki-Banki wai shin menene ma shi bankin ko wata sabuwar gonar shinkafa ce?”

Rashin sanin me za ta ce masa ya saka ta wucewa gaba kawai. Sai kuma ta dakata tana sauke numfarfashin gajiya. Ta ɗaga kanta sama idanuwanta suka dallare da zazzafar ranar da ta haska doron duniyar, ta sanya siraran yatsunta ta ɗauke gumin da ya taho ta silin hancinta yana ƙoƙarin shige mata baki. A lokacin ne kuma ƙofar wani gida da ke can nesa da ita ta buɗe ya fito cikin shirinsa tsaf na jamfa da wando.
“Huzaif!” Ta furta da wata marainiyar murya, kafin kuma ta ɗaga ƙafa da sauri ta isa gare shi. Bai ji zuwanta ba sai ji ya yi ta shige tsakiyar ƙirjinsa. Hakan wani abu ne da bai taɓa shiga tsakaninsu ba a tsayin lokutan da suka yi tare. Da hanzari ya jata cikin gidan yana maida ƙofar ya rufe gudun idanuwan mutane.
“Na wahala sosai, tun safe nake walagigi cikin unguwar nan ina nemanka, me ya sa babu wanda ya sanka?” Tana jin yadda bugun zuciyarsa ya canja, sai dai hakan bai hanata sake ruƙunƙume shi ba tana sakin gunjin kuka.

“Ya isa…Shiiiiiiiiii, ki yi shiru haka bansan kuka fa, me ya faru da har zai saka ki wahalar da kan ki kina nemana, me ya sa ba za ki iya jira zuwa satin da za mu da haɗu ba.”

Ya furta a hankali cikin kunnuwanta yana shafa bayanta.

“Kawu ne wai aure zai mini da Yaya Haruna nan da wata guda.”

Tamkar an saka baki an bushe wutar aci bal-bal haka tunaninsa ya bushe a cikin kwalkwalwarsa. Sakinsa ta yi a hankali jin shirun ya yi yawa ta lalubi idanuwansa da suka kaɗa jajur da ɓacin rai.

“Kar fa ka damu, na gama yanke mana shawara mai kyau, ka gudu da ni can garinku ayi mana aure, bayan na haihu sai mu zo gun Kawu mu bashi haƙuri, kaga a sannan ba zai raba mu ba.”

Ya bita da kallo yana gyaɗa kai tamkar marayan ƙadangare.

“Ki ka ce kar na damu?Koya mini yadda ake hana damuwa tasiri a zuciya dan Allah. Hamdiyya, ke zan rasa fa gabaɗaya ki tafi ga wani na amma kike cewa karna damu saboda kina da wata gurguwar shawara..?”
“Ba gurguwa ba ce da ƙafafunta wallahi, ni ce na baka damar ka ɗauke ni ka kai ni koma ina ne ayi mana aure, ba zan taɓa rayuwa da wani idan ba kai ba. Ya kamata ka haddace hakan…”

Yadda ya danƙo kafaɗunta da hannuwansa yana buɗe mata manyan idanuwansa ya razanata.

“Aurenki nake son yi a gaban iyayenki da waliyyanki ba auren da zan zo ina nadama ba. Son ki nake da dukkan zuciyata ba dan na rabaki da kowa naki ba saboda son zuciyata. Ki ajewa ranki ni Huzaif ba zan taɓa aurenki ba da yardar Kawunki ba.”

“Ina jin zafi sosai.”

Ta furta tana cije bakin riƙon da ya mata.
Sakinta ya yi gabaɗaya ya juya mata baya yana ɗauke kwallar da ta fara tarar masa.

“Mu yi haƙuri da juna, ki manta da Ni, ki kuma fice daga nan.”

Cikin wani irin tashin hankali ta shawo gabansa jikinta na karkarwa.

“Hu…Huzaif ni na haƙura da kai kake cewa?”Sai kuma ta ƙarasa gabansa tana dunƙule hannuwanta ta fara dukansa a tsakiyar ƙirjinsa.

“Baka isa ba, saboda Ni aka halicce ka, saboda mu dawwama tare, ka sha furta mini haka, wallahi baka isa ba.”

Sai kuma ta durƙushe a ƙasan ƙafafuwansa tana bubbuga kanta.

Da sauri ya ɗago da ita yana share mata hawayen cikin ƙarfi hali. A hankali ta saka kanta a kafaɗarsa tana sauke ajiyar zuciya.

“Me kike so na yi? Ina kike so na kai dumbin soyayyarki, ina kike so in sanya rayuwata a sa’adda wani zai nesantani da ke? Ya ilahi! Dama zan iya dawo da ranar da na fara ganinki…”

“Na tsani kalmar dama, ka sani ko?

“…Da na ɗauke waɗannan kalmomin uku da suka haɗa ni da ke na furtawa wani su, wanin da ba zai taɓa barina ba.”

“Ba zan taɓa barinka ba, ka daina wannan zaton, ka yarda kawai da shawara…”

Ta yi shiru jin saukar wani abu me ɗumi a dokin wuyanta.

A gigice ta ɗago da ɗumbin mamaki da tsoro tana duban idanuwansa da suka yi caɓa-caɓa da hawaye. Wasu shuɗaɗɗun zantukansa suka wuce cikin kunnuwanta.

Hamdiyya ban taɓa kuka ba ko da ina yaro. Na sha ganin Innata na kuka saboda yunwa amma ni ba na yi. A gabana yunwa ta kashe Abbana da Baffana da Yayuna biyu kowa yana kuka amma ni ina gefe ina kallonsu.

“Huzaif ka ga kuka fa kake, menene ya yi girma haka da har ya fi mutuwar Abbanka?”

“Ki barni na yi suna da daɗi sosai, ina jin wani irin sanyi yanzu haka, matsalarmu da tawa na neman kaɗar da hankalina daga jiki na.”

Zare ido ta yi gabaɗaya tana dubansa da mamaki.
“Wace matsala ce gareka? Yanzu dama akwai abinda ke damunka baka taɓa faɗa mini ba? Wannan ne son da kake ikirarin kana mini? Har akwai wani abu naka da zan gagara sani?”

“Ki yi shiru dan Allah, kin sani ba na son abinda zai tada miki hankali, abin ne yana da matuƙar girma, ban jin a ‘yan shekarunki za ki iya ɗauka…”

“Wai mene ne, ka faɗa mini dan Allah, ko da ba zan iya kome ba zan maka addu’a ai, menene ke damunka da zai iya zautar da kai har ka zubar masa da hawaye?”
“Hamdiyya ki bar…”

“Ta sanya hannu ta rufe bakinsa da sauri tana kaɗa masa kai.”

“Shi kenan idan ba ni da matsayin da za ka iya faɗa mini damuwarka wallahi na juya na tafi ba za ka ƙara gani na ba.”

Ta juya da sauri tana sharce kwalla ya riƙo ta Yana juyo da ita gabaɗaya.

“Ki yi hakuri ba na so ki kalle ni wani mutumin banza ne.”

“Ba zan taɓa kallonka haka ba ko me za ka aikata ka sani ai, wai menene? Ko giya kake sha kake son ka bari ka kasa?”

Wani ɗan guntun murmushi ya ƙubce masa. “Ta fi ƙarfin shan giya, kin gane ne…”

Sai kuma ya yi shiru yana kallon rinannun idanuwanta, da za ta yi kuskuren matsawa jikinsa sosai za ta iya jiyo bugun zuciyarsa da ya sauya cike da tashin hankali, ya runtse ido da ƙarfi ya buɗe yana ƙara tauna maganar.

“Zan faɗa, amma…Kin gane, ina sabon aikin da na ce miki shi ya kawo ni garin nan yau shekara guda ko…?”

“Ta kaɗa kai da sauri tana matsowa kusa da shi.”

“…To ban daɗe da fara aikin ba na saba da manager din Bankin gabaɗaya, yana matuƙar yaba kwazona, ya ɗauke ni kamar yaronsa na jini. To, yau wata guda ke nan ƙaddarar ta faru gare ni. Wasu maƙudan kuɗaɗe ya ba ni cikin jaka in kaiwa wani babban Attajiri gidansa, ya kuma ba ni ne dan kar kowa ya farga zan iya riƙe wannan kuɗaɗen, sannan shi Attajirin shi ya nemi da na yi shiri kamar Almajiri a yayin da zan kai masa saƙon saboda baya son a san yana da ajiya ma a bankin, sai dai dabararsu ba ta yi ba, dan kuwa ina gabda isa ga gidan wasu mutane da bansan su wanene ba suka rufe ni da duka da saran wuƙa, ƙarshe suka kwace jakar suka tafi da ita, kin ga..?” Ya furta yana buɗe kafaɗarsa sai ga wani babban yankan wuƙa ya sha ɗinki.

Ta yi baya da sauri tana toshe bakinta, duk da ciwon ya warke bata taɓa ganin mummunar yanka irinsa ba.
“T.. t…to cewa suka yi ka biya musu?”

Ta furta gabaɗaya jikinta rawa yake.

“Kusan hakan, amma ta hanyar ɗora mini wani aiki mai mugun wahala da haɗari…”

Ya yi shiru yana sanya hannunsa a Aljihu ya zaro wani farin kyalle mai zanen kan Mujiya.

“Kin ga wannan shi ne damuwata Hamdiyya, shi ne tashin hankalina da rashin nutsuwata. Manager ne ya je gun wani Malaminsa kan batun kuɗin, to shi ne ya bashi wannan farin ƙyallen da cewar idan har aka zuba jinin mace na haila a jikin wannan ƙyallen a take wannan kuɗin za su dawo duk inda suke, to shi ne Manager ya ba ni alhakin samo jinin tunda Ni ne silar ɓatarsu. Ya kuma gargaɗeni da idan har ban samo ba nan da cikarsa wata uku a baƙin aikina kenan, zai kuma yi mini zagon ƙasa yadda ba zan ƙara samun aiki a yankin nan ba. Hamdiyya, aikin nan shi ne dukkan rayuwata, da shi nake ciyar da mahaifiyata nake siyan magungunanta nake kula da Maraya.”

Ya furta yana ɗauke kwallar idonsa.

Ita kam gabaɗaya tunaninta ya ɗauke, tana ganin wani abu mai kama da tsafi ƙiri-ƙiri a gabanta, da ƙyar ta haɗiye wani bushasshen yawu ta ce da shi. “Amma shi ne baka taɓa faɗa mini wannan matsalar ba, ai da tuni na sama maka mafita, Allah banfi sati biyu da yin wanka ba…”

Ganin yadda yake zare ido yana yin baya ya sa ta yi shiru.

“…Kana mamaki ne? Wai ni har sai yaushe za ka yarda ina maka son da zan iya mallaka maka dukkan rayuwata?” Ta ƙara takunta gabansa, kafin ya farga ta fisge ƙyallen hannunsa.

“Bari mu gama da wannan matsalar kafin na aurenmu. Na tafi, ba zan dawo ba sai da abinda kake so a jikin wannan ƙyallen.”

Daga haka ta juya, ya bi bayanta da kallo har ta ja masa ƙofar gidan a fuskarsa.

Wata juya ya ji ta kwashe shi ya yi taga-taga ya dafe bango yana sauke nannauyan nishi. A can ƙasan zuciyarsa wani abu ke cure masa yana zungurarsa da wani mummunan kuskure da zai jawo cikin rayuwarsa!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Hakabiyya 2Hakabiyya 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×