Skip to content
Part 7 of 14 in the Series Ba'indiya by Haiman Raees

Hrithik Roshan

Gwani na gwanaye ne Hrithik

Baya tsoron mazan fama. 

Idan sun zo fa za su yi cik

Sarki na rawa ko ba lema. 

Mai lambobin yabo birjik

Agwanaye ko sai an nema. 

Ko birnin Landan ya je Hrithik

Labarin sa ya isa har can ma.

Idan zance na kafce ne

Ɗan Roshan babu mai i ma. 

Idan ko fage na dambe ne 

Anan sai dai a sara ma. 

Ina kuke masu so na rawa 

Kuzo ku ga mazari goga. 

Rijiya ta rawa lallai kai ne 

Mun gane kai ke da guga. 

Duggu kake dakalin mada

koo a kafce ka wuce ɗan wada. 

Gurin kyawu a nemo ka

A ƙyale batun su hankaka. 

Kyan ɗa dama an ce ya biyo mahaifi nai

To gashi ko har ya ma zarce mahaifi nai. 

Baya rigima da kowa nashi ne

Yana haƙuri ina ma a ce musulmi ne?

Allahu ka ceci bawanka 

kasa shi ya gano dai-dai

Ya karɓi shahadarka 

Ya zamo bawa akan dai-dai.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ba’indiya 6Ba’indiya 8 >>

2 thoughts on “Ba’indiya 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.