Skip to content
Part 5 of 17 in the Series Jawaheer by Fatima Dan Borno

Umma, ta jima tana lallaɓa Jawaheer, sannan tayi mata sallama ta fice. Wanda ya yi dai-dai da shigowar Jabir. Sai da ya karya, sannan ya miƙe tsaye yana duban Jawaheer.

“Ya kamata ki daina zama a cikin duhu, ke kaɗai ce a yanzu nake sa ran zaki dawo min da farin cikin ɗan uwana. Haka idan kika ji labarin Jawaheer zaki hana kanki damuwa da kuma jin haushin Mujaheed, na tabbata zaki yi masa uzuri. Nasan ba zaki so kanki ba, zaki gane Nayla har abada ba zata bar rayuwar Mujaheed ba. A yanzu kuma idan na gama gaya maki wacece Nayla zan ɗauke ki insadaki ga Nayla. Daga yau zaki daina tambayar kowa labarin Nayla.”

Jabir ya yi kokarin ya riƙe hawayensa abin ya gagara, don haka kawai ya bar su suna ta zuba, ba tare da ya damu da ya goge su ba. Hakan yasa jikin Jawaheer ya yi matuƙar sanyi, har tana jin kamar ta ce ta fasa jin labarin. Sai dai ba zata yi wasa da daman da ta jima tana jira ba.

Yau Alhamis kamar kowacce juma’a a cikin gidan na Alhaji Muhammadu, fitaccen ɗan kwangila, wanda bama a jihar ta Kaduna ba, hatta duniya gaba ɗaya suna yaba masa, kasancewarsa wanda ya fita daban a cikin masu kuɗin mu da muke da su. Ga sunan da yawa, zaka ci karo da masu arziƙin amma taimakon talaka yana masu wahala.

Haka zai yi wuya su san a wani hali maƙocinsu yake ciki, kasancewar sun sa ƙaton katanga a tsakanin si da talaka.

Saboda mugun hali, idan suka ga talaka maƙocin su, sai su siye gidajen su su haɗe da nasu, gudun ma kada wataran su raɓe su. Shi talaka har gobe ba mutum bane a idanun ɗan uwansa mai kudi.

Alhaji Muhammadu, ya kasance mutum me sassauƙar rayuwa, duk ranar juma’a yana ficewa da shi da matarsa da gudan ɗansa, Mujaheed domin zuwa asibitoci, gidajen Marayu, da kuma sansanin ‘yan gudun hijira.

Haka yana zuwa gidajen almajirai da ke unguwarsu ya kai masu kuɗi da abubuwan amfani. Alhaji Muhammadu asalinsa ɗan mutanen Yola ne, da shi da matarsa Hajiya Saude. Yana da ƙaninsa me suna Alhaji Ma’aruf  da matarsa Hajiya Suwaiba, wanda suke zaune a Jihar Kaduna, a unguwar Mu’azu.

Shima ‘ya’yansa biyar, Jabir shine babba sai Salim, sai kuma Zara, da ƙannenta Hafsa da Ikram.

A natse suka gama shiryawa, da misalin ƙarfe goma na safe, domin farawa da wuri kuma su kammala da wuri. Mujaheed ɗan shekaru goma sha biyar a duniya, ya shiga gaba, yana latse-latsen waya, Ummansa tana baya, Abbansa ma yana baya, sai driver Malam Idi. Game kawai yake bugawa ba tare da ya ɗago ba, a hankali hirar mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya sami damar isowa har cikin kunnensa.

“Hajiya na rasa agurin wa Mujaheed ya samo miskilanci. Kwata-kwata baya son yara, ki kalli idan su Zara suka zo gidan nan, kamar sun ga mala’ikan ɗaukar rai. Hajiya ina tsoron yaron nan kada ya zama me girman kai, ina tsoron kada ya zama me wulaƙanta talakawa.”

Hajiyar tayi murmushi tare da kamo hannun mijinta kamar me son cire wani abu, “Haba Abban Mujaheed, ya kamata ka gane Mujaheedu mutum ne da baya son hayaniya, amma ya fi mu son talakawa. Mu bi shi da addu’a.”

Ko motsi bai yi ba, haka ya cigaba da buga Game ɗinsa.

A ƙofar makeken gidan marayun suka tsaya, tare da gaisawa da masu gadin, kafin suka harba kan motarsu ciki. Bayan isarsu Ofishin shugaban, yau dai Alhaji Mu’hd ya amince zai shiga domin ya dudduba marayun. Akan hanyarsu Mujaheed yana biye da su, suna kallon wasu yaran suna wasansu, kowanne da irin abinda yake yi.

Ƙafar wandonsa ta riƙe tana kyalkyatan dariya, hannunta duk datti, hakan yasa wandonsa samun rabonsa. Sunkuyawa ya yi, ya ɗaga ta, ba zata wuce shekaru huɗu a duniya ba. Duban juna suka yi, ya ajiyeta a gefe guda, sannan ya miƙe don ya cigaba da tafiya, kasancewar iyayensa har sun yi masa nisa.

“Ka jirani.” Sake dawowa ya yi da baya yana dubanta. “Me kike so inbaki?” Ya tsinci bakinsa da furta tambayar. “Nima ban sani ba. Menene sunanka?” Shafa gashin kanta ya yi, “Sunana Aboki. Kina sona?” Ɗaga kanta tayi duk da bata san me yake nufi ba ta ce, “Eh zaka bani sweet irin na Anti?”

“Eh zan baki, idan kin amince zaki dawo gidanmu.” Mamakin surutun  yarinyar yake yi, a lokaci guda yarinyar ta shiga ransa. Don haka ya riƙo hannunta suna tafe tana haɗa dukkan wani surutu da yazo bakinta, tana gaya masa.

Ganinsa da yarinya gaba ɗaya aka zuba masa ido. “Abba yarinyar nan kamar aba mu ita mu sami ‘yar yarinya, ta shiga raina.” Shugaban makarantar ya yi dariya ya ce, “Nayla. Wai yaushe ma har tazo wurinka ne? Ai yarinyar nan kowa yana sonta, sai dai ba azo nan ba, sai kaji ana maganarta. Alhaji idan kuna so ai babu matsala, abinda kake yi mana anan gidan ai sai dai mu ce Allah ya biyaka.”

Duban juna suka yi da Umma, ta gyaɗa masa kai kawai. Cikin abinda bai fice minti talatin ba, suka gama cike-ciken form. Mujaheed ya ɗan fito yana amsa wayar Jabir, Nayla ta dube shi ta ƙwala masa kira, “Aboki kada ka tafi ka barni.” Kasa yin wayar ya yi yana duban yadda take neman rikicewa.

Da baya ya dawo iyayen suna kallonsa, “Kada ki damu ba zan tafi inbarki ba insha Allahu.” Ita dai bata wani fahimce shi ba, illa riƙe hannunsa da tayi sosai.

Anan ake gaya masu yadda aka kawo ta, iyayenta aka kashe akan titin su na zuwa Abuja, iya bincike anyi amma ba a gano danginta ba, a cikin aljihunsa aka gano ma’aikacin nepa ne, don haka akaje har wajen aikinsa, mutane dai sun san shi, amma basu san kowa nasa ba. Don haka aka kawo ta gidan marayu. Mujaheed da iyayensa suka yi ta girgiza kai suna al’ajabi. Mafarin zaman Nayla a cikin zuri’ar Alhaji Muhd kenan.

Wata shaƙuwa ce me karfi a tsakanin Mujaheed da Nayla, wanda duk wanda ya san su yasan su ne da irin wannan shaƙuwar. Baya yarda Umma tayi mata komai shike yi mata. Hatta tsifar kai, shi yake yi mata, daga bisani ya rakata Saloon yana zaune ayi mata kitso. Cikin ƙanƙanin lokaci kyawun Nayla ya sake fitowa sosai. Haka da aka sanyata a Makaranta Mujaheed zai kaita har cikin Aji, sannan ya shafi kanta, suna ɗagawa juna hannu zai wuce nasa Makarantar. Ita kuma Nayla ta ƙware a shiga maƙota tayi ta wasa ta ɓata jikinta.

Yau ma kamar kullum Mujaheed yana fitowa ya hango Umma tana bin Nayla da bulalanta, ita kuwa sai tsalla take tana gudu tana ihun kiran Aboki. Mujaheed ya ƙaraso da sauri ya ɗauketa yana ɓoye ta, “Umma don Allah kada ki dake ta me tayi ne?”

Umma ta Harare shi, “Ni sai inhaɗa ku ku dukka inzane. Ka dubi jikinta yadda ta lalata, duka-duka ko awa biyu banyi da sauya mata kaya ba.”

Nayla ta haye bayan Mujaheed ta raɗa masa a kunne, “Kacewa Umma tayi haƙuri bazan ƙara ba.” Mujaheed ya ɗan marerece, “Umma kiyi haƙuri ba zata ƙara ba, yanzu zan gyara mata jikin.”

Umma ta koma tana harararsu. A banɗaki ya direta, duk ta ishe shi da surutu. Wani labarin ma bai san daga inda ya fito ba. Yana gama shiryata ta fito fes da ita, ya kamo hannunta suka koma ɗakin Abba.

Tuwo Abba yake ci da hannu, Umma tana zaune a gefensa. Nayla ta jawo hannun Mujaheed suka zauna, gaba ɗaya suka zira hannu a kwanon Abban suna ci. Abba ya dubi Nayla ya ce, “Anya ‘yar gidan Aboki yau baki yi wa Umma laifi ba? Naga tana ta harararki ne.”

Nayla ta haɗiye tuwo tana satan kallon Umma, “Wai kawai Abba daga na ɗan yi wasa kaɗan, a can gidan su Jamila shine Umma harda bulala.”

Tayi kwaɓa-kwaɓa da fuska kamar zata yi kuka. Umma ta zaro idanu, “Au daga kin ɗan yi wasa? Lalle yarinyar nan, gobe ki sake fita ki ɓata jikinki ki gani.”

Kallon Mujaheed tayi ya kashe mata ido, tayi dariya. Abba ma da yake dubansu dariyar yake shaƙa. Abba ya dubi Umma ya ce, “Kinji Nayla ƙyale Ummanki, duk barazana take yi, da anƙyaleta ba zata iya dukanki ba.”  Gaba ɗaya suka yi dariya, banda Mujaheed da yake faman lumshe idanu, alamun yana jin barci.

Tsalam ta cire hannunta ta miƙe tana faɗin “Jirani nima barcin nake ji.” Mujaheed ya girgiza kansa, ya sani sarai idan Nayla tana nan barci sai dai yaga wasu suna yi. Ƙaramin aikinta ne ta kunna film tayi ta tambayarsa abinda ake kallo a ciki, dole ko baya kallo sai ya bata amsa. Juyowa ya yi ya riƙe kafadunta.

“Friend kije gun Abba, fita zai yi gara ki bishi kada ya yi maki wayo ya gudu.” Ta juyo tana dubansa, “Wai haka Abbana?” Abba ya girgiza kai, “Wayo yake yi maki maza ki bishi.”

Abin mamaki sai suka ga ta dawo gun Abba, “Duk abinda aboki ya ce min da gaske ne.”

Abba da Umma suka riƙe haɓa suna mamakin yadda kwata-kwata Mujaheed baya laifi agun Nayla. Mujaheed ya yi murmushi ya shige ɗakinsa. Tunani ne fal a ransa, na yadda zai gina rayuwar Nayla. Kukanta ya ji, don haka ya miƙe cikin sauri ya fice yana leƙawa. Ɗaure fuska ya yi sosai a lokacin da take tunkaro shi, “Aboki kaga maigadi ya samin kaɗangare.”

Mujaheed ya fice jikinsa har yana rawa, ya fizgo mai gadin nan, ya shiga dukansa ko ta ina. Abba ya ƙwace shi da kyar. Da hannu ya nuna shi.

“Yau ka gama aiki a gidan nan, tunda baka da hankali. Sau nawa ina gaya maka ka daina tsorata yarinyar nan? Wallahi sai ka bar gidan nan.” Abba ya dubi yadda idanun Mujaheed ya sauya a lokaci guda, ya kamo hannunsa suka shige ciki Nayla tana biye da su.

“Haba Mujaheed meyasa zaka duke shi?” Kasa magana ya yi, sai Nayla da ta haye tsakiyarsu ta zauna, ta karkace kai, “Abbana Kaɗangare yake cinna min, sai inyi ta kuka.” Abba ya dubeta ya ce, “Meyasa baki zo kin gaya min ba, zaki gayawa wannan abokin naki sarkin zuciya kamar kuturu.”

Ɗaure fuska tayi ta ce, “Abbana Abokina ba kuturu bane.”

Gaba ɗaya suka yi murmushi harda Mujaheed ɗin. Miƙewa ya yi ya ce, “Abba a sallami Isma’il a gidan nan, ba yau ya fara yiwa Nayla wannan abin ba, zai iya sakewa ni kuma zanyi masa illa.” Abba ya gyaɗa kansa kawai.

Ɗakin ta biyo shi, ta kunna tv, bai ce mata komai ba ya kwanta kawai dan yana fama da ciwon kai, Nayla ta kunna kallo bai san wani film take kallo ba, sai jin muryarta ya yi a tsakiyar kansa, “Aboki yanzu har ankasheta ko?”

Amsawa ya yi da Eh ba tare da ya ɗago ya dubi abinda take tambayar ba, ta sake yanko masa wata tambayar, “Yanzu daga nan ina za su je?”

Ya ce, “Sama.” Ta ɗan dube shi ta leƙa fuskarsa, “Aboki a bango kake kallo?” Jawo ta ya yi ya kwantar da ita kusa da shi, “Rufe ido kiyi barci yanzu, idan ba haka ba, babu zuwa yawo.”

Rufe idon tayi, tana son yin kallo, tana kuma son zuwa yawo. Kamar kuma antsunguleta ta ce, “Zaka jira in haifi Muhibbat ɗina, itama ta haihu, idan ta haihu sai ka..”

Riƙe kansa ya yi, “Eh da uwar Muhibbat ɗin da tattaɓa kunnenta duk zan tsaya inrene su, sannan in mutu.”

Rufe idanun tayi a hankali barci yana kwasarta. Da ido ya kafeta yana ƙarewa halittarta kallo.

Yau Mujaheed ya makara zuwa ɗauko Nayla daga Makaranta, hankalinsa gaba ɗaya a tashe yake, yana isowa Makarantar ya sameta tana durƙushe taci kuka, idanun nan sun yi jazir. Da sauri ya riƙo hannunta, ta saki wani irin ƙara, hakan yasa ya gigice da tambayarta ko lafiya?

“Aboki Malam ne ya dukeni duba ka ga hannuna.” Mujaheed ya rintse idanu, yana jin kamar ya fasa ihu. “Nayla wani malami ne wannan?”
Ta kasa kiran sunan Malamin, saboda tsoronsa da ya riga ya shigeta. Gurin Maigadin ya ƙarasa yana magana cikin ɗaga murya, “Ka gayawa malamin da ya taɓa Nayla ya gama dukar wata yarinya a cikin makarantar nan.” .Mai gadi ya mika masa cikakken address din inda zai sami malamin, domin shi kansa ya tsane shi. Kai tsaye Mujaheed ya wuce Police Station ya kwaso ‘yan sanda. Suna tsaye da malamin ana magana, zuciya ta dinga cin Mujaheed bai san lokacin da dunkule hannu ya zuba masa duka a hanci ba, nan da nan jini ya bata masa fuska. Da kyar ‘yan sandan suka janye Mujaheed.

Haka ya dawo gida cikin ƙunci, a ranar babu wanda yaga fara’arsa. Ita kuwa Nayla, abin nema ya samu, idan zai taɓa mata hannun sai ta sa ihu. Abba dai da Umma sai ido suka zuba masu. Sai da malamin nan yayi kwana biyu sannan Abba yasan abinda ke faruwa. Don haka Nayla tana zaune a gaban Mujaheed yana ɗaure mata ‘yar babynta, Abba ya shigo yana masifa,

“Mujaheed wani irin zuciya ce haka gareka? Meyasa ba zaka rage ba? Yanzu abinda kayi ya yi dai-dai? Ashe dalilin da yasa ka sauyawa Nayla Makaranta kenan? Kana ƙirga adadin Makarantun da kake sauyawa yarinyar nan?”

Nayla ta dubi yadda ran Mujaheed ya ɓaci, kawai sai tasa kuka, ta miƙe ta wuce can wajen Gate. Shima Mujaheed ya wuce ɗakinsa. Abu kamar wasa Nayla taƙi cin abinci, ta ƙi kula kowa, haka taƙi tashi daga  bakin Gate.

Umma tayi lallashin duniyar nan amma ko a jikinta, haka Abba shima yaje ya lallasheta fir ta ƙi kallon su. Nan da nan hankulan mutan gidan ya tashi, dole Abba ya je ya sami Mujaheed ya ce, “To ai sai ka tashi kaje ka lallashi Nayla, anyi maka faɗa ta karɓe fushin, ko abinci bata ci ba.”

Da sauri ya fito, ya je ya sameta. Hannu ya miƙa mata ta dube shi, taga yana murmushi, sannan ta miƙa hannun, sai kuma tasa kuka. A jikinsa ya rungumeta, “Sorry Nayla, ki daina kuka kin ji? Mu je ki ci abinci inkaiki wajen wasa.”

Taɓe fuska tayi tana duban su Abba, “To ni dai ka cewa su Abba su baka haƙuri.”

Har Umma zata zageta, sai kuma suka tuna yadda fir taƙi dubansu, don haka Abba ya riƙe kunne, “Abba ya tuba ba zai sake yiwa Mujaheed faɗa ba.” Murmushi suka yi gaba ɗaya suka miƙe suna tafe ana hira kamar ba su bane, ɗazu kowa ke cikin fushi.

Rayuwar Family ɗin akwai burgewa da shiga rai, suna matuƙar son junansu.

Yana kwance a ɗakinsa ya ji muryarta ta windo “Aboki ka fito na je nayi wasa jikina duk ƙasa, kuma su Umma suna falo zata dake ni.”

Miƙewa ya yi ya shige ɗaki ya ɗauko mata wasu kayan, ya ɓoye ba tare da su Umma sun gani ba, yana fitowa ya jawo hannunta can wajen Garden ya miƙa mata ta sauya, ya karɓi wanda ta ɓata suka zagaya ya wanke su tas, ya shanya sannan ya kamo hannunta. Ta bayan Mujaheed ta ɓoye Umma tana ɗagowa ta ruga gudu ɗakin Mujaheed tana ƙyalƙyaltan dariya.

Yana shigowa ta dafe goshi, ta miƙa masa hannu suka tafa ta ce, “Ummana bata ganni ba, yau da na sha duka.” Wautan Nayla da manyancenta suna bashi mamaki.

*****

Yau kamar kullum yana dawowa daga Makaranta ya sami Nayla ta tara almajirai, tana raba masu sweet. Don haka ya shiga layin masu karbar sweet ɗin ba tare da ta ganshi ba. Tana basu tana masifa, “Idan baku bi layi ba, zan shige da abuna cikin gida.” Hannunsa ya miƙa, tana miƙo masa, ta kafe hannun da idanu, sai kuma ta ɗago cikin matsanancin farin ciki, “Lahh Aboki!” Watsar da Sweet ɗin tayi ta rungume shi fuskarta ɗauke da tsantsar farin ciki, “Aboki…” Shima shafa kanta ya yi, “Na’am Friend. Nayi kewarki.”

“Nima haka Aboki.”

Suna tafe tana bashi labarin abubuwan da suka faru. Tana zaune ya sauya kaya, ya ɗauko key ɗin mota, suka fice daga gidan gaba ɗaya.

“Kinsan ina zamu je?” Girgiza kanta tayi, “Wata budurwa nayi, shine nake son ki raka ni taɗi.” Dariya tayi ta miƙa masa hannu suka tafa.

“Daga wurinta kuma sai muje ka siya min alawan nan me daɗi ko?” Hancinta ya jawo har sai da ta gangaro ta faɗo jikinsa, “Shegen kwaɗayi shiyasa ga haƙoranki nan ƙanana kamar masara. Duk abinda kike so zan siya maki Friend.”

Dariya ta sake yi.

Suna isowa gidan su budurwar ta fito daga ita sai riga da wando, tana ta yatsine. Nayla ta ɗan saci kallon Mujaheed, shima ita yake kallo, suka taɓe baki. Da ido ya tambayeta ko budurwar tayi? Kai ta ɗaga masa, sannan ta ware babban ɗan yatsanta alamun tayi. Wanda a zuciyar Nayla ko da take yarinya sam Saudat bata burgeta ba.

Suna cikin hira, Nayla tayi tsalam tasa masu baki, sai shima ya koma hirar da ita. Saudat da ta gama kula da rainin wayo a cikin Nayla kawai ta miƙe tayi masa sallama.

Matsalar da Mujaheed ya fara samu da ‘yan matansa, shi ne duk hirar da za ayi Nayla tana tsakiyarsu ta zauna. Sai hira tayi nisa, zaka rantse bata jin abinda suke cewa, sai dai kawai kaji ta tsomo baki. Don haka da yawan ‘yan mata suke cewa basu yarda da Nayla ƙanwarsa ce uwa ɗaya uba ɗaya ba, shi kuwa da zarar aka taɓa Nayla duk irin son da yake maki ya haƙura da ke kenan. Mujaheed baya taɓa yiwa kowa uzuri akan Nayla.

Yau yana zaune a tsakar gida shi da Nayla, asuwaki suke yi, wanda ya zame masu kamar ibada, ƙa’idane kullum sai sun yi asuwakin nan. Nayla ta buɗe masa ‘yan haƙoran wai ya cire mata itacen ya maƙale mata a haƙori. Don haka yasa hannu ya cire mata sannan ya bata ruwa ta kurkure bakin. Tana zubarwa taga jini, ai sai ta gigice da ihu, “Aboki jini jini jini wayyoooo Aboki jini..”

Haka take idan har taga jini ko a jikin waye sai ta hau ihu tana faɗin jini. Riƙe mata hannayen ya yi ya ce, “Ki natsu babu abinda zai yi maki.” Asuwakin da ba a ƙarasa ba kenan ya shige da ita ɗaki yana lallashi.

Ranar da Mujaheed zai tafi Training ɗin zamowarsa ɗan sanda, ansamu matsaloli, ta fuskar Nayla. Da ƙyar ya iya lallashinta, sai dai shima kwana biyu kacal ya iya yi babu ita ya sato hanya ya fito. Kai tsaye Makarantarsu ya nufa, ya ce, a kirata. Tana fitowa, ta ganshi a guje ta ƙaraso ta faɗa jikinsa, tana goge hawaye.

Tarkacen su Biscuit ya ciro mata yana shafa kanta, “Nayla gaya min sau nawa kika kasa barci da bana nan? Yanzu a wurin Umma kike barci ko?”

“Aboki ina ta kuka ina ta kuka, Umma da Abba suna bani irin abinda kake bani, amma ni nafi son naka. Aboki kada ka sake tafiya ka barni kaji?”

Biscuit ɗin ya buɗe ya ce, “Friend bude bakinki.” Ta buɗe ya saka mata a baki, gaba ɗaya suka yi murmushi. Ya dubeta ya ce, “Akwai daɗi?” Gyaɗa kanta tayi tana lumshe idanu. Shuru ya yi yana tunanin ta yadda za su rabu, “Friend idan kika koma gida kada ki sanar da su Umma nazo gurinki kin ji? Zan rinƙa satar zuwa ina ganinki. Tashi kije ki samo min ruwa insha.”

Babu musu ta miƙe tana ta tsalle-tsallenta sai dubanta yake. Tana wucewa ya fice daga Makarantar gaba ɗaya.

Dawowa tayi da ruwan a hannunta, tana ganin babu shi ta saki ruwan, ta riga ta gane guduwa ya yi. Haka ta koma aji tana kuka. A ranar taƙi yiwa kowa magana, haka taƙi faɗin dalili.

Ranar Asabar ya shigo gidan, yana tsaye daga bakin ƙofa ya hangota, tana gudu Umma na binta da bulala. Ji tayi tayi tuntuɓe da abu, tana ɗagowa ta ganshi tsaye, ya sake kyau, da wani irin kwarjini. Farin ciki ya kama ta, ta maƙalƙale shi tana dariya. Ita kanta Umma ƙarasowa tayi ta rungume shi tana kyalkyaltar dariya. Shi kuwa sai faman duban Nayla yake yi, yarinyar kullum cikin sauya masa take. Tana da sassanyar kyau.

A ranar a falo suka baje suna ta ciye-ciye. Hatta Abba bai fita ko nan da can ba, yana cikin su ana hira. Haka idan ka shigo zaka hango Nayla a tsakiyar su Abba ta raba su ta zauna. Ta dubi Mujaheed ta ce, “Aboki akwai wata da tace tana sonka, har ta bani wasiƙa inkawo maka. Ni na amsa mata kawai.”

“Kai Friend wai mata nawa zan aura ne?”

Yatsu ta ware masa, “Mata biyu zaka aura Aboki. Ko Ummana? Ni kuma lokacin na haifi Muhibbat ita kuma Muhibbat idan ta haihu sai ka aurar da…”

Gaba ɗaya suka tuntsure da dariya, hakan ya hanata ƙarasawa. Wautan Nayla yana sanya su cikin nishaɗi.

Abba ya ce, “A’a ni ban taɓa ganin inda ƙanwa take cusawa yaya ra’ayin mata ba. Kuma irin wannan lissafin su Muhibbat ɗinnan ina kika samo su ne Nayla?”

Duban Abban tayi kawai ta kama dariya. Ya kamo hannunta tare da miƙewa, “Akwai magana a bakin friend kwana biyu mun rabu da yin gulma, zo muje ki bani labari.”

Umma tana dubansu har suka ɓace, sannan ta dawo da dubanta ga Abba. Dukkansu tunanin su guda ne, don haka ya ce, zai kira ƙaninsa Alhaji Ma’aruf su tattauna.

Da shigarta ta karkace kai ta ce, “Wai kaji su Umma wai idan ka dawo za su yi maka aure, da wata yarinya. Kana sonta? Kuma da baka nan, naga jini a jikina, ina ta kuka da ƙyar Umma ta lallasheni ta ce min na girma ne, indaina bari namiji yana taɓa ni, nace mata harda Aboki? Kawai sai tayi shuru. Ni ko ta ce min harda kai, tasan bazan yarda ba, kuma dama kasan ko menene kai nake gayawa shima wannan dan baka nan ne na gaya mata.”

Cire kayayyakinsa yake yana jefarwa, ita kuma da zarar ya jefar sai ta kwashe ta ajiye masa a wurin da ya dace. Dakatawa ya yi yana dubanta, sai kuma ya kaɗa kansa, “Friend ni bani da zaɓi, idan har kina son yarinyar nima ina sonta. Zan iya rayuwa da aljana a matsayin mata, idan har ke kika bani ita. Maganar jini kuma da gaske kin girma. Zan sake sa idanu akanki insha Allahu.”

Girgiza kanta tayi ta ce, “Nidai babu ruwana, duk wacce kake so ita nake so.”

Gashinta ya kaiwa duba, duk ya yi datti, ya ce “Friend meyasa ba a wanke gashin nan ba? Zo muje inkaiki wajen wankin kai, bana son datti sam.”

Nayla ta ɗan yi yaƙe, kasancewar ta tsani a taɓa kan, amma tunda Mujaheed ne ba zata iya yi masa musu ba.

Suna fitowa yake gayawa Umma inda zai kaita, Umma ta ce, “Ni da na kama kan Nayla, ta nemi ta tara min jama’a? Ihu fa tsakaninta da Allah ta ɗinga yi. Wannan yarinya da ‘yar riƙo ce da na shiga uku.”

Mujaheed ya yi murmushi yana duban Nayla tana ƙwalawa Abba kira tana faɗin sai sun dawo.

*****

Nayla tana da shekaru sha shida, komai na budurci ya gama bayyana a jikinta, haka shaƙuwarta da Mujaheed tamƙar sake haɗe su ake yi. Har yanzu Mujaheed bai amince akwai wata alaƙa da ta wuce ‘yan uwantaka da Nayla ba, haka itama Nayla. Musamman ma yadda ko alama bata da kishi akansa, indai ya ce yana son abu, to ko menene itama tana so. Haka a lokacin tuni ya yi nisa da aikinsa. Wataran da ita yake zuwa Office ya ajiyeta har ya tashi.

Watarana Mujaheed yana gun aiki, ya rasa dalilin da yasa hankalinsa yake kan Nayla da ke Makaranta, gabansa sai faɗi yake da ƙarfi. Cikin lokaci ƙalilan ya miƙe ya bayyana a cikin Makarantar. Har ajin su Nayla yaje aka ce bata nan, sai wata ƙawarta ce take kwatanta masa Office ɗin da Nayla ta je, wanda yake da ɗan nisa da cikin makarantar. Hakan yasa ya ƙarasa har Office ɗin gabansa yana faɗi.

Ji ya yi kamar kukan Nayla, a hargitse yasa ƙafa ya tokari ƙofar da ƙarfi, ya buɗe. Malam Musa ya gani yana zarewa Nayla idanu sai ta amince da shi, Wani irin zuciya da ke cinsa, yasa ya zari addan da ya gani a Office ɗin, ya damƙi yatsan da yake sawa Nayla a baki alamun tayi shuru, yasa adda ya datse yatsan nan. A take Malam Musa ya saki fitsarin azaba. Ya sake sa addan nan a tsakiyar maƙogoronsa, “Sai na kasheka! Nayla zaka taɓa?

“Aboki kada ka kashe shi.” Siririyar muryarta ya ziyarce shi, a hankali ya sassauta irin riƙon da ya yi masa, ya damƙo shi ya fito da shi.

Sanadiyyar barin Malam Musa Makarantar kenan, haka wannan abu yasa Malam Musa ya riƙe Mujaheed a ransa, ya ci buri kala-kala akansa.

Mujaheed ne kwance ya yi rigingine, Nayla tana faɗowa ɗakin ta shiga tashinsa, ya taya ta cire rigarta ta matseta. Baya cikin walwala, yana buƙatar zama shi ɗaya, amma Nayla ta hana hakan. Dole ya tashi yana lumshe idanu, ya kama rigar kawai ya kwaɓe mata. Sai a lokacin ya dawo hayyacinsa, da idanunsa suka ci karo da wani abu, da ya yi sanadiyyar tayar da duk wani abu da ke kwance a cikin jikinsa. Wani irin shokin ne ya taso masa tun daga saman kai har ƙatsan tafin ƙafafunsa.

Yanayin da ya shiga, ya yi dai-dai da haɗuwan fatan jikinta da hannayensa, hakan yasa mata wani irin faɗiwan gaba, wanda tunda take bata taɓa jin irinsa ba.

Luma idanunta tayi a cikin nasa, dukkansu suka yi tsit kamar masu nazari. “Nayla tashi kisa kayanki.” Abinda ya iya furtawa kenan ya mayar da kansa ya kwanta.

Tun daga wannan ranar zuciyar Nayla ta sauya tunani akan Yayanta Mujaheed, salon soyayyar da take masa ya rikiɗe zuwa wani sashe, wanda ta kasa fassara wannan sashen. Sai ta koma zama shuru-shuru, Garden ya zama wurin zamanta tayi tagumi. Shi kansa ya sauya, amma sauyawar Nayla yafi komai bashi mamaki. So yake ya tabbatar da abinda yake zargi, don haka yana zaune yana wanke ‘yan ƙananan kayansa, ta shigo ta sunkuya suna wankin tare. Ruwan kumfar ya ɗiba ya watsa mata, ada can baya idan ya watsa mata ruwa, sai ta rama, wannan ƙa’idarta ce, amma sai ta ɗago ta riƙe hannunsa, tayi masa ƙuri da idanu. Girgiza kai kawai ya yi ya ce, “Friend idan kika canza zan shiga damuwa irin wanda baki taɓa tunani ba. Bana cikin farin ciki kwana biyu saboda rashin farin cikinki. Ki gaya min menene matsalarki kin ji? Gaya min yanzun nan innemo maki maganinsa.”

Nayla ta tsame hannunta, ta buɗe rigar da tasa me ɗauke da botira, shacin ƙirjinta duk suka bayyana, ta nuna masa ƙirjinta. Gani ya yi kamar wani irin haske me kashe ido ya haske fuskarsa, hakan yasa yasa hannu ya kare fuskarsa. “Me ya faru da wurin Nayla?”

Girgiza kai tayi, “Nima ban sani ba Aboki, wurin ke min ciwo, yana bugawa da ƙarfi, kullum ina jin ƙunci a raina, kamar ina son wani abu, kuma bansan mene ne ba.”

“Aboki kike so, kuma gashi a gabanki. Ki daina damuwa kin ji? Idan kina damuwa zan kasa aiwatar da komai. Zanyi tafiya idan na dawo zan gaya maki wata magana.”

Kada kanta kawai tayi. Haka washegari ya bar garin zuwa wani aiki, a lokacin ne kuma Nayla take jin ciwonta yana ƙaruwa. Yau tana kwance kanta a jikin Umma ƙafafunta a bisa jikin Abba, sai ta ce, masu nan na ciwo, anjima ta ce, can yana mata ciwo. Gaba ɗaya sun rasa gane kanta.

Ana haka Mujaheed ya yi sallama. Yana tsaye ya zuba mata idanu, yana kallon yadda duk ta rame. Abin mamaki tana ganinsa ta ware murya, “Aboki…” Da gudu ta tashi, sai dai tana ƙoƙarin rungume shi, ya yi dabaran riƙo hannayenta, ba tare da ya bari ta rungume shi ɗin ba.

Umma ta dubi Abba, shima ita yake kallo. Tuni ta warware kamar bata da wata matsala. Ƙoƙari take ta duba me ya kawo mata a leda.

A gaban su Umma ta buɗe komai, har da sabuwar waya. Ta ɗauki komai ta miƙawa Abba da Umma, ta ce su cire ɗaya su ajiye mata sauran. Abba ya yi dariya. Mujaheed ya dube su ya ce, “Umma anyi min transfer zuwa Abuja, bansan yadda zan yi inbarku anan ba.”

Nayla ta ce, “Sai mu tattara mu koma Abujan gaba ɗaya. Ba zan iya rabuwa da kai ba, haka ba zan iya rabuwa da su Ummana ba. Ko Abbana?” Mujaheed ya miƙa mata hannu suka tafa, “Maganarki dutse Friend, Abba dole gaba ɗaya zamu koma Abujan nan, sai musa a sake gyara mana gidanmu.”

Abba ya ce, “Kana bani mamaki da kai da ƙanwarka. Shikenan sai kuyi ta juya mu kamar mune yaran naku? To babu inda zamu je, kayi tafiyarka. Haka kuma babu inda zaka tafin min da ‘yar auta. Babu yadda ban yi da kai ba, kada kayi aikin Gwamnati amma ka ƙi ji na, ai ga irinta nan. Haka za ayi ta maka transfer mu kuma muyi ta binka?”

Nayla ta turo baki kawai ta mike ta shige ɗaki ta rufe. Shuru-shuru babu Nayla babu dalilinta. Bugun ƙofar duniyar nan anyi amma fir taƙi buɗewa. Sai da Mujaheed ya ƙaraso ya tabbatar mata su Abba sun amince, sannan ta buɗe ƙofar tana ƙyafta idanu.

Cikin hukuncin Allah suka tattara suka koma Abuja, wannan ne mafarin zaman su a Abuja.

Zaune take a cikin Garden ɗin idanunta a rufe, da littafi, tana jin wani abu a zuciyarta. A hankali ya ƙaraso ya zare littafin daga fuskarta, hakan yasa ta buɗe fuskar ta washe baki tana dariya. “Aboki yaushe ka dawo? Kasan tunaninka nake yi?”

“Yanzu na dawo. Naga Abba yana nemanki.”

Zaro idanu tayi ta ce, “Na manta ya ce intsinko masa Gwaiba, ni kuma nayi zamana anan. Yau na shiga uku da Abbana.”

Miƙewa ya yi ya je ya tsinko Gwaiban ya wanke, sannan ya kamo hannunta suka fito a tare. Ganin Abba yana harararta, yasa ta zagayo ta sunkuya ta riƙe kunne, “Allah ba zan ƙara ba. Nayi alƙawari.”

Mujaheed zai yi magana, Abba ya Harare shi, suka kalli juna suka yi murmushi.

Suna zazzaune a falo, aka hasko wani yaro yana shan giya da taba, Abba ya ɓata rai ya ce, “Wannan ne kuskuren da yarona zai aikata inyi masa mafi munin hukunci. Ko sigari bana ƙaunar inga jinina yana shanta.”

Mujaheed ya ɗan yi tsam, domin yakan sha jefi-jefi musamman idan tunani yana neman yi masa illa. Haka babu wanda ya sani, don haka ne ya yi fuska kawai.

Suka dubi juna da Nayla gaba ɗaya suka taɓe baki. Da ido tayi masa magana suka miƙe. Can ɗakinsa suka shige, ya ce mata ya yi sabon budurwa, da farin cikinta ta miƙa masa hannu suka tafa, har ya ciro mata irin kayan da ya siya domin kaiwa hudurwar. Ta duba tana faɗin sun yi kyau. Har zuciyarta ta ji daɗin yadda Mujaheed yake gaya mata yarinyar tana sonsa sosai, don haka ta dame shi da dole sai anje gidan su yarinyar.

A mota ya ɗauketa suka nufi gidan su Rukayya. Tun daga nesa Nayla ta ce, “Wai wai Aboki wannan me tsada ce. Komai ya yi.” Shi dai kawai Nayla yake kallo, hakan yasa Rukayya ta ɗan shaƙa. Bata wani sakarwa Nayla fuska ba, hakan ya fusata Mujaheed shima ya sake tamke fuska ya yi mata sallama kawai.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jawaheer 4Jawaheer 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×