Skip to content
Part 2 of 17 in the Series Jawaheer by Fatima Dan Borno

Ko kafin Mujaheed ya tunkare su, Jawaheer ta ƙaraso akan ƙaton mashin ɗinta mai kama da jirgin ruwa. Hular ta sake ƙwabewa yalwataccen gashinta ya watsu a bayanta, har yana rufe mata fuska. Siraran yatsunta tasa masu kyau, wa’inda suka ji ado da ƙumbunan kanti ta mayar da gashin baya, a lokaci guda ta ɗaure gashin ta ƙudundune. 

Riga da wando ne a jikinta masu ɗaukar hankali, tana yamutsa fuska kamar wacce bata taɓa kallon rana ba. Mujaheed ya rasa dalilin da a karo na biyu ya sake jin gabansa ya faɗi. Meyasa tun kafin ya haɗa ido da ita ya tsinci kansa a cikin damuwa? Meyasa ya tsinci kansa a cikin ƙunci?  

A lokaci guda Nayla ta faɗo masa a rai, a lokaci guda yanayin fuskarsa zuwa annurin fuskarsa suka ɓace ɓat! Yana jin alamun ciwon kansa yana son tashi, ya rintse idanu da ƙarfi, yana addu’a. A hankali ya ji natsuwarsa sun dawo sai wani irin zuciya da ke cinsa.  

Abin mamaki Jawaheer ta ƙaraso har gabansa tana dubansa, “Meyasa ka wulaƙanta ni zuciyata zata hanani ramawa? Meyasa zuciyata take bugawa da ƙarfi saboda ta ganka? Naso a yanzu ingaya maka na tsaneka. Wallahi! Tunda ka mareni, idan kai ne ubana Mai nasara sai na wulaƙanta rayuwarka, sai na mayar da kai abin kwatance a gari.” 

Ɗau! Ta ji ya ɗauketa da mahaukacin marin da tunda take bata taɓa jin azaba irinsa ba, haka ba a taɓa yi mata irin wannan marin ba. Cikin ƙanƙanin lokaci bakinta ya fashe, jini ya hau zuba ta gefen bakin.  

Wasu gardawan maza suka yo kan Mujaheed cikin huci da zafi. Sai dai kafin su ƙaraso Jawaheer ta sa hannu ta dakatar da su. Da hannu kawai tayi masu magana suka koma da baya.   

Mujaheed kuwa ya rasa dalilin irin wannan huci da ɓacin rai. Ko da yake duk ranar da yana cikin irin yanayin nan Nayla ta faɗo masa a rai, kowaye ke gabansa baya ji baya gani, sai ya aikata mummunar aiki. 

Bai yi mata magana ba kawai ya nuna ta da yatsa ya koma cikin motarsa a fusace. Jabir kuwa tuni ya tsuru, ya kasa furta komai, tunda ya gane Mujaheed ya shiga yanayin da duk wani masoyinsa ke tausaya masa, a duk lokacin da yake cikin irin yanayin. 

Da isarsu gida babu wanda ya yi magana, kowa ya shiga bashi hanya. Umma ce ta fito daga kitchen ganin yanayinsa yasa bata tsaya tambayar ba’asi ba ta wuce kawai tana girgiza kai.  

Kai tsaye ɗaki ya shiga ya rufe ƙofar.  Duk wani abun fashewa ya ɗinga jifa da shi da iya ƙarfinsa, jikinsa yana rawa. Hoton Nayla da ke manne a sama, wanda shi da kansa ya manna a ranar da ya iso garin na Kaduna, ya ɗauko ya buga da ƙasa. Komai ya dawo masa sabo. Kasala da zazzaɓi me zafi suka rufar masa, hakan ya sassauta masa fashe-fashen da yake yi kamar taɓaɓɓe. Ruf da ciki ya yi, a hakan wani mayaudarin barci ya kwashe shi. 

Jawaheer ce zaune a ƙaton falon mahaifinta tana sanye da riga da wando masu adon pink tayi kyau sosai, tana latsa Laptop ɗinta. Mai nasara ne yake ta kumfar baki yana zage-zage yana faɗin sai annemo masa duk inda mutumin da ya taɓa masa ‘ya yake. Babu abinda zai baka mamaki sai yadda Jawaheer ko uhum bata ce masa ba. Da taga zai dameta sai ta miƙe ta zube komai a wurin ta wuce ɗakinta. 

Teddy ɗinta ta jawo ta rungume shi tsam a ƙirjinta, tana shafawa. “Me ya sa ya fusata? Dama ya sanni ne?” Akwai wani abu a ƙasa. Meyasa nake son damuwa da lamarinsa? “Saboda ki ɗauki fansa!” Wata zuciyar tayi saurin ankarar da ita.  

Mahaifiyarta ce ta shigo, don haka ta rufe idanun alamun barci take yi. 

Tana fita tasa hannu ta jawo tattausan bargon ta rufe jikinta da shi, tana jin wani yanayi me wuyar fassaruwa. A hankali ta sauke kafafunta kamar me tsoron taka wani abu, ta zare kayan jikinta, ta ɗauki ɗan tawul ɗin ta ɗaura. Samɓala-samɓalan cinyoyinta ne a waje, wanda suka gogu da gyara. Ƙamshi ya riga ya riƙe mata jiki, ta yadda ko tasa turaruka ko bata sa ba, indai zaka haɗu da ita sai ka rantse ta juye gwangwanin turare ne a jikinta. 

Banɗakin ta shiga ta fara aiwatar da brush wannan ƙa’idarta ce, sannan ta matso man miski da take tsarki da shi. Ɗaya bayan ɗaya take bin jikinta wajen wankewa.  

Sannu a hankali ta kammala komai, cikin shigarta ta ƙananan kaya, ta jawo timetable ɗinta tana dubawa. A dai-dai wannan lokacin ya nuna mata zata kalli labarai ne a BBC World. Haka zata yi kallon ne tare da markaɗaɗɗan inibi. Da gasasshen kaza. Kawar da kanta tayi daga barin kallon Timetable ɗin, ta fice zuwa kallon abinda zata kalla, kada ta ƙara wasu lokuta akan na cikin timetable ɗinta. 

A zahiri idan ka kalleta bata da wata matsala. Amma da zaka leƙa zuciyarta zaka ji tsoron sake shiga. Komai ta same shi a falon kamar yadda ta zata, don haka ta zauna tana latsa remot, ba tare da ta dubi abinda aka ajiye mata ba. 

Kiran Sallar Magriba ya farkar da shi. A hankali ya buɗe idanunsa yana ƙarewa ɗakin kallo. A hankali ya furta, “Astagfirullah! Allah na tuba, ka yafe min.” 

Cike da natsuwa, ya miƙe ya shige banɗaki ya fara yin wanka, sannan ya yi alwala. Sanye yake da jallabiya fara sol, ya fito falon. 

Ɗaya bayan ɗaya suka ɗinga tashi domin zuwa yin alwala, kasancewar babu yadda Umma bata yi ba, akan su tashi su je su yi Sallah, suka tsaya buga Game. Ganin Mujaheed yasa kowacce kama kanta. 

Jabir ya doso shi, “Ah yallaɓai an tashi?” Bai bashi amsa ba, haka shima bai tsammaci amsar ba. Kai tsaye suka wuce Masallacin, kowa da irin abinda yake tunani. 

Mujaheed Muhammad, wanda aka fi kiransa da M.D domin gajarta sunan, shi ne zaune da farin tabarau ɗinsa, yana buɗe jaridar da aka kawo masa ta yau, ya ci karo da hoton Nayla ɓaro-ɓaro dauke da wasu bayanai akanta. Yasan wannan aikin mahaifinsa ne. Rufe Jaridar ya yi cikin sauri tare da rintse idanunsa, ya sake buɗe su fes akan bangon jaridar. Ita ɗin ce take murmushi cikin shagwaɓarta aka ɗauki hoton. 

Ba zai mance ranar da aka ɗauki wannan hoton ba, ba zai taɓa mance a irin ranar fushi take yi da shi, irin fushin da bata taɓa yi da shi ba, ba zai taɓa mance yadda Nayla take turo ɗan bakinta idan tana jin shagwaɓa ba.  

Yatsunsa ya kai kan fuskarta, yana zagaye laɓɓanta. Kamar a zahiri yake ganinta. 

Yana jin wayarsa tana ƙara amma ya kasa ɗauka, sai da ya ji kiran tayi yawa, sannan yasa hannu ya zaro wayar tare da manneta a kunne, “Assalamu alaikum.” Ya furta cikin tsayayyar murya, me dauƙe da nagarta.  

“M.D wani hali ake ciki game da Mai nasara?” 

“A nemi wani a bashi aikin.” 

Ogan Mujaheed ya dubi wayar da mamaki, yana tunanin ko dai ba Mujaheed bane? Bayan da kansa ya amince zai yi wannan aikin yanzu kuma yana neman sauya zance? “MD ka natsu ka gane mahimmancin aikin nan, da irin amfanin da zai yi wa duniya gaba ɗaya. Kai ne mutum na farko da duniya ta amince da zaka iya, meyasa yanzu zaka sauya tunani?” 

Mujaheed ya fara ƙosawa da ogansa, don haka ya rufe idanunsa baya son ganin haske, ko kaɗan,   

“Oga idan ana son inyi aikina, a barni, a daina kirana ana tambayata, idan lokacin gama aikin ya yi da kaina zan kawo maku dukkan bayanan da kuke buƙata.” 

Kafin Ogan ya bada amsa Mujaheed ya sauke wayar, yana sauke ajiyar zuciya me ƙarfin gaske.   

Kwanansa biyu, bai fita ko nan da can ba, gaba ɗaya anrasa gane kansa, har ya sami abinda ake kira natsuwa, sannan ya shirya ya fice. 

Daga bakin Gate ɗin gidansu ta fito da mashin ɗinta zata fice. Mahaukacin da take yawan gani a kusa da gidansu, ta ƙura masa ido tana son yin nazarin mahaukacin. Kusan kullum idan ta fito ƙa’ida ce, indai zata haɗa idanu da mahaukacin nan sai ta ɗauki wani abu ta bashi. Yau ɗin ma kuɗi ta miƙa masa, amma ko kallonta bai yi ba, sai tsince-tsincensa yake yi. Cilla masa kuɗin tayi ta kama gabanta.  

Tayi nisa a wasan da take yi akan mashin ɗin, bata Ankara ba, ta buge wani tsoho, wanda ya faɗi ƙasa warwas.  

Parking tayi ta sakko tana ganin yadda mutane suka taru. Yamutsa fuska tayi, “Talaka har abada talaka ne. Ku ‘yan Najeriyan nan kuna da matsala. Menene dan na buge wannan zaku taru ku tsaya min akai? Shi baya ganine? Malamai ku ɗauke min shi daga nan tun kafin insake bin ta kanshi ya ƙarasa.” 

Mujaheed zai je wurin, Jabir ya dakatar da shi, ta hanyar riƙe hannunsa, yana roƙonsa. Mujaheed ya fizge ya ƙarasa gurin tsohon ya ɗaga shi yana duban fuskarsa yadda duk ta lalace. Jawaheer ta ƙaraso tana murmushi, “Shugaban masu fushi. Fushinka shi ya jawo maka matsala a duniya.”  

Dubanta yake yi, duba irin na tabbas na taɓa saninki. Amma a ina?  

Cikin maganarta ta izgilanci ta dawo da shi daga duniyar tunani, “Ko zaka sake dukana ne?” Mujaheed dai bai ce mata komai ba, hankalinsa yana kan tsohon nan. Sai dai abinda ya ba Jawaheer mamaki yadda ‘yan sanda suka halarci wurin cikin gaggawa. Da idanu kawai Mujaheed ya nuna masu Jawaheer wata mace a cikin su ta riƙe ta. “Madam muje Office.” Abinda Jawaheer ta iya fahimta kenan. Shi kuma wanda aka buge Mujaheed yasa aka wuce da shi asibiti. 

“Kina wasa da ni, amma zan koya maki hankali.”  

Tunda Jawaheer take, ba a taba ci mata mutunci irin na wannan ranar ba. Tana ji tana gani aka kaita Police Station aka rufeta. A karo na farko ta fara tunanin ko dai dan sanda ne? Sai dai bashi da alamu da ‘yan sanda.   

A fusace Mai Nasara ya shigo bayan gama waya da IG yana gaya masa wulaƙanta shi da akayi. Cikin abinda bai shafe minti talatin ba, hankalin duk wani ɗan sanda da ke wurin ya tashi. Babban tashin hankalin wanda ya bayar da izinin a kawo Jawaheer Police Station, babu shi babu dalilinsa.   

Haka anyi iya bincike ba a gane ko waye ba. Jawaheer tana ganin mahaifinta kawai tasa kuka me tsuma zuciya. A maimakon ta ji tsanar Mujaheed sai hakan ya gagara, kawai takaicin wulaƙanta ta da ya yi ta fi ji. Rungumeta ya yi yana bata haƙuri tare da yi mata alƙawarin sai ya nemo shi da kansa.   

Motoci a ƙalla sun kai biyar, wa’inda suka je dauko Jawaheer daga cikin Police Station, don haka ne ana zuwa dai-dai bakin Gate ɗin su, ta dakatar da direban, tana jikin mahaifinta ta zuge glas. Da hannu ta kirowa shi, amma ko dubanta bai yi ba, hakan yasa ta bude motar ta sakko. Shuru tayi tana kallonsa, daga bisani ta ajiye masa kuɗi kamar yadda ta saba, sannan ta dawo ta shiga motar.   

Suna sakkowa, mahaifinta ya ce, “Meyasa kike taimakon mahaukacin can?” Ware kafaɗa tayi ta ce, “Dad! Narasa dalili, kawai dai zuciyarsa tana yi min shige da zuciyata, kamar yana da alaƙa da zuciyar aro.”  

Shuru ya yi bai bata amsa ba, ya shige wajen baƙin da ya yi yana sanar masu ba za su sami daman yin meeting ba, ‘yarsa babu lafiya.  

*****

Tsugunne yake a cikin maƙabartan idanunsa jajir kamar wanda ya yi kuka. Kansa a ƙasa. Shi kaɗai yasan me yake zuwa yi a duk ranar juma’a kuma a gaban ƙabari ɗaya tak! Haka yakan shafe fiye da awanni a wannan wuri, ba tare da tsoro ko wani tunani ba. 

Tsugunne yake a gaban mahaifinsa tun bayan ya gaida shi, ya gaza miƙewa. Kansa a ƙasa. 

Ɗago kansa ya yi, yana duban saman ɗakin Abbansa, gani ya yi kamar Nayla tana shirin faɗowa ƙasa, dan haka ya miƙe tare da miƙa hannunsa, ya ƙwala mata kira da ƙarfi, *”Naylaaaa…”* Riƙe goshinsa ya yi, idanun nan kamar jan gauta. Ummansa zata yi magana, Abban ya girgiza mata kai. “Ka shiga ɗakinka ka samu ka huta.” 

Gyaɗa kansa kawai ya yi, ya miƙe tare da shigewa ɗakinsa. Wanka ya fara yi, ya sami sauƙin gajiya, sannan ya shige ƙaton Garden ɗin gidan. Hannunsa riƙe da wata sarƙa yana ta jujjuyata. Daga bisani ya mayar da sarƙar cikin ƙirjinsa da ke bugawa da ƙarfi. 

Addu’ar da ya saba yi ita ya sake maimaitawa a yanzu, “Allah ka gajarta min rayuwata a duniya.”  

“Abokiii, Walh ba Ameen ba. Ka ga zaka tsaya a duniya sai na zama kamar Umma, na haifi ‘yar Muhibbat ɗina, ka taya ni renon ta, kamar yadda ka taya Umma renona ko? Sai kuma ka tsaya ka aurar min da ita, sai kuma ka jira itama Muhibbat ɗin ta haihu daga nan…”  

Hannu yasa ya murɗe mata kunne har sai da tayi ƙara, sannan ya bata amsa, “Daga nan sai insake jiran ‘yar Muhibbat ta yi aure ko? Idan tayi aure sai injira itama ta haihu. Ohh Nayla yaushe zaki daina shirme ne wai? Komai naki shirme ne.”  

Turo baki tayi sai kuma hawaye har da shessheƙa, yana nan zaune yana dubanta, haka ba shi da ninyar yin abinda take so wata lallashi, “Zanje ingayawa Abbana kace zaka mutu ka barni.”  

Shan mur ya yi, “Maza ki gaya masa. Amma kafin nan zo intambayeki wani abu.”  

Ƙarasowa tayi ta sunkuya ta dafa guiwowinsa. “Yauwa my Friend, ina Mamar Umma? Kinsan kakar Umma?” 

Taɓe baki tayi, “Ai sun tsufa shiyasa suka mutu.”  

“To ni meyasa ba zan mutu ba har sai na ɗaurawa Muhibbat da jikokinta aure?”  

Buɗe ‘yan kananan haƙoranta tayi, “Nidai gaskiya ba zaka mutu ba, sai kayi dukka abubuwan da na lissafa. Idan ba haka ba idan ka ajiye ni a Makaranta infita mota ta bigeni intafi inbarka, kayi ta kuka Nayla ta mutu. Ka ga ba zaka sake samun Friend ba ko?”  

Ohh shirmen Nayla yana sa masa damuwa, don haka ya ce, “Oh hakane Gaskiya. To yanzu a bar maganar zo muje ki raka ni wani wuri.” 

Miƙewa tayi tana dubansa harda riƙe ƙugu, “Nawa zaka bani idan na rakaka? Ko kuma muje daga nan ka siya min Ice Cream.”  

Miƙewa ya yi yana ware hannu, “Ni na gaji da wannan abotan da ke Walh. Haba duk idan zaki rakani wani wuri sai na biyaki? Yanzu nawa kika tara a cikin irin kudin da nake baki?” 

Ɗaga kai tayi sama tana ƙirga, “Za su iya kai dubu biyar.”  

Idanu ya ware, “Je ki kwaso ki bani aro, insiya maki Ice Cream a ciki.” 

Cike da gamsuwa tayi cikin gida da gudu. Umma ta biyo bayanta tana tambayar ko lafiya? Bata bata amsa ba, sai da ta duba bata ga kuɗin ba, sannan ta ɗago tana son yin kuka, “Ummana ina kuɗina da na ɓoye su? Zan arawa aboki zai siya min Ice Cream.”  

Umma ta zabga mata harara, “Baki da hankali wayo yake yi maki yana kwashe maki kuɗin.”  

“Ummana ni dai ki bani kada ya qi fita da ni. Ni ai dai komai na samu dama shi zan baiwa saboda ya ce zai tsaya ba zai mutu ba, sai ya aurar da jikokin Muhibbat ɗina.” 

Firgigit ya yi, a lokacin da wayarsa ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula. Jabir ke kiransa don haka ya ɗauka kawai ba tare da ya iya furta komai ba.  

Jabir ɗin ya fara koro masa bayani, “Jawaheer ta sa annemo ni. Yarinyar nan da gaske take yi tana son ɗaukar fansa akanka. Wani abin da yake bani mamaki, tana da irin ayyukan Nayla. Bambancinsu ita ta cika ji da kanta ne. Ka bari idan ka dawo Kaduna akwai shawarar da ya kamata muyi.”  

Mujaheed baya fahimtar dukkan abinda ɗan uwansa Jabir yake gaya masa, don haka kawai ya cire wayar a kunne yana dafe goshinsa. 

Abbansa ya gani tsaye akansa, ya miƙa masa glas cup cike da ruwan zam-zam da ya tofe da addu’o’i. Duban juna suka yi ya gyaɗa masa kai, hakan yasa ya karɓa kawai ya kai bakinsa ya shanye tas. Sake ɗagowar da zai yi yaga hawaye kwance a idanun Abbansa.  

Mujaheed ya duƙar da kansa kawai jikinsa ya ƙara yin sanyi. Dukkansu anrasa me ƙarfin halin da zai iya furta ko da kalma ɗaya.  

***** 

Jawaheer ce take ta faman motsa jiki, ta hanyar yin abubuwa kala-kala. Mace ce da take daraja jikinta, bata son wani ƙiba yazo ya sauya mata halittar da take tinƙaho da shi. Ita kanta tasan ta haɗu. Jabir ne suka ƙaraso da wasu mutane da suke yi masa jagora. Tunda yake bai taɓa shiga gidan Mai nasara ba, sai dai daga waje, don haka ganin gidan yasa ya yi matuƙar firgita, zai iya rantsewa gidan gari ne guda, haka kamar ba a cikin ƙasar aka yi ginin ba. 

Duban Jawaheer ya yi, wani abu me ƙarfi ya fizge shi. Cikin ƙanƙanin lokaci ta susuta shi. Ƙugunta kaɗai idan ka duba, sai kaji kana neman sumewa, bare akai ga ƙirjinta da ke cike da dukiyar fulani. Haka rigar da tasa sun bayyana ƙirjin sosai. Jabir ya kawar da kai, baya son ta gano loggonsa.  

“Jabir ina son sanin tarihin wannnan mutumin da bai da mutunci. Zuciyar aro tana yawan yi min ƙarya da cewar tasan waye shi. A zahiri bansan shi ba, ya shigo ya lalata min komai nawa. Kayi sauri kayi min bayani, lokacina ya kusan yi, idan ya yi dole zamu datse maganar, saboda bana shiga lokacin wani.” 

Jabir ya taɓe baki, “Kiyi haƙuri shi ba kowa bane bare sanin tarihinsa ya burgeki. Na barki lafiya.”  

Da idanu ta bishi, sannan ta zari tawul tana goge wuyanta. Dubansu tayi a lokacin da ta fara tafiya, “A gaggauta nemo min mutumin nan, idan zai samu a sato min shi a kai shi gidan gona, a wahalar da shi kafin inzo. Dole ko zan ƙyale shi sai nasan me ya taka.” 

Gaba ɗaya suka amsa cikin girmamawa. Tana shiga ciki ta sami Mom ɗinta da Dad suna kallo, ta ƙarasa ta ɗan rungume Mai Nasara ta bashi fake kiss a kumatu haka, tayi wa mahaifiyarta. “Hie Mom Hie Dad.”  

Bata jira cewarsu ba, ta shige domin lokacin wankanta ya yi. 

Latsa wayarta take yi, ba tare da ta dubi inda ƙawarta Suhaima take ba. Ita kuwa Suhaima ta dage tana gaya mata irin shagalin da za ayi a bikinta, da kuma irin ankon da ya kamata ayi. 

Jawaheer ta ɗago tana dubanta, “Suhaima dole mu bambanta da mu masu kuɗi, da kuma su talakawa. Angon dubu Hamsin ya yi kaɗan. A samo mana kaya wanda idan muka sa sai anjuyo ansake duban mu. Ayo order ɗin laces na a ƙalla dubu ɗari uku da hamsin. Kowacce ta zuba zinare a hannu, da ƙafa, kunne da wuya. Kin dai san yadda nake son biki ya kasance ko? Idan ba haka ba, ba zan je wurin ba.” 

Suhaima dai lallaɓa Jawaheer take yi, domin ita ce babbar ƙawarta don haka komai ta ce sai ta amsa mata kawai. 

Shirye-shiryen biki ya kankama, a yau za ayi dinner don haka, tun safe Jawaheer take gyara kanta, kamar ita ce amaryar. Haka kowacce ta tafi a cikin motarta. Dukka ‘yan matan suna ji da kansu, ta fannin kuɗi da suturu. Jawaheer ce akan kujerar babban ƙawa, don haka ita ta bayar da tarihin Suhaima cikin natsuwa. 

A ƙalla ta sawa mutane da dama ƙaunarta.  

“Yanzu Mujaheed Muhammad wanda aka fi sani da MD, zai zo ya sawa auren nan albarka, zai kuma yiwa ango da amarya nasiha.” 

Shuru babu Mujaheed babu dalilinsa. Har wasu masu gajen haƙuri sun fara ƙosawa. Sanye yake cikin shadda me ruwan toka, kansa yana sanye da hular da tayi matuƙar dacewa da shi. Farin glas ne manne a cikin idanunsa masu ɗaukar ido. Gaba ɗaya sai kallo ya koma kansa. Jawaheer tabi yatsunsa da kallo suna da kyau. Hannun yana sanye da wani zobe wanda tana gani ta shiga kallon zoben, tasan zoben kamar ma nata ne, a ina ya samu? Idan nata ne ya akayi ya zo hannunsa? 

Yana tsaye da abin magana, har sai da wurin ya ɗauki shuru, sannan ya yi Sallama. Juyowa ya yi, ya zura idanunsa a cikin na Jawaheer, rana ta farko da wani ya yi mata kwarjini har ta kasa jurewa haɗa idanu da shi. Sannan ya dawo da kallonsa ga amarya da ango da suke ta walwali. 

“Aboki wai duk wurin nan mun fi kowa kyau ne da naga ana ta kallon mu? Aboki kayi kyau sosai ni fa?” 

“Yau mun fi kowa kyau, yau mun fi mutane da dama martaba, yau mun samu cikakken ‘yanci. A yau zamu dawwama cikin farin ciki. Friend mun fi kowa kyau, musamman ma ke.”  

“Aboki ina jin fitsari ka zo mu je ka rakani inyi sai mu dawo.” 

Babu musu ya kamo hannunta suka fice a cikin dumbin jama’a. 

A hankali ya sauke abin maganar ya kasa furta ko da kalma ɗaya. Sai da ya ɗan fara jin magana sama-sama sannan ya fara magana cikin wata natsuwa. 

“A yau kun fi mutane da yawa daraja, a yau zaku dawwama a cikin farin ciki. Duk soyayya dole akwai samun matsala. Rayuwar aure gaba ɗayanta idan aka dunƙuleta fahimta ce da kuma kulawa. Namiji ma yana son kulawa bare kuma ‘ya mace da kullum take kallon kanta a ‘yar ƙarama, duk girmanta kuwa. Idan kuka kore shaiɗan a cikin ku zaku fi kowa jin daɗin aure. Allah ya baku zaman lafiya.” 

Zazzaɓin da yake ƙoƙarin kayar da shi, yasa ya yi saurin ɓacewa a wurin ba tare da wani ko wata sun san inda ya bi ba. Da yawa ‘yan mata sun fito suna nemansa dan tallata kansu, sai dai tuni ya shige motarsa, yana riƙe da ƙirjinsa da ke faman suya. 

“Amma dai kamar kana da matsala? Shiyasa kake tare mutane kana dukansu kamar an aiko maka da jakai ko?” 

Bai dubeta ba, haka bai sa wa kansa ran zai iya tanka mata ba. Shi kaɗai yasan halin da yake ciki. Haka yana addu’ar Allah ya hana ta fusata shi. Buɗe ƙofar motar ya yi, ya rufe tare da wuce wa can baya yana jin wani irin zafi a cikin ransa. Hannunsa ya kaiwa wani gini duka da iya ƙarfinsa, cikin rashin sa’a ya fasa hannun sai jini.  

Jawaheer tana ganin jini ta gigice ta cire siririn gyalenta ta ƙaraso wurinsa da sauri tana girgiza kai, sai kuma hawaye, “Wayyoo jini, jini, jini…” 

Dubanta ya tsaya yi, yadda take nannaɗe masa hannun da gyalenta jikinta yana rawa. Ayyukanta sak Nayla. 

“Aboki! Jini, jini bana son jini wayyo jini.”  

“Allah zan zane ki idan baki natsu ba. Ni na saki kije kiyi wasa da reza? Ba zaki tsaya ba?” 

“Wayyoo jini, jini… Abbana Ummana jini jini.”  

Haka take idan taga Jini na ciwo tana iya sumewa. 

Yana kallon Jawaheer ta gama ɗaure masa jikinta na rawa ta bar wurin. Ƙamshin turaren da ke jikin gyalen sak irin wanda Nayla take amfani da shi. 

Jabir ne zaune a gaban malamin. Bayan sun gaisa ne ya yi masa dukkan bayanin da ke tafe da shi, tare da zube masa maƙuden kuɗaɗe akan kawai irin bayanin da suke son ya yi wa Jawaheer. Babu dogon jayayya malami ya amince, suka yi sallama ya fice.  

Sai da biron nan yayi kwana biyu agun Alhaji Mai nasara, kafin ta ɗauko ta dawowa mahaukacin nan da shi, har tana yi masa godiya. Tunani ne fal a ranta na yadda zata yi ta je gun malamin nan. Da gaske take son Mujaheed, bata taɓa faɗawa tarkon soyayya ba sai akan Mujaheed. Ji take yi kamar zata yi hauka idan bata gan shi ba. Don haka ta kira malamin kawai ya kwatanta mata gidansa, sai gata cikin tashin hankali. 

A gabansa ta zube tana roƙonsa da ya dubeta ya taimaka mata tana son Mujaheed. Malami ya ɗauki maganin ƙarya, ya miƙa mata ya ce ta zuba masa a cikin abin sha. Girgiza kanta tayi tana sharce hawaye, 

“Wannan aikin yafi ƙarfina, bani da hanyar da zan iya aikata abinda kake tunanin sanya ni. Ka sauya wata hanyar. Ni ko aurensa ba alkhairi bane na amince zan aure shi.”  

Malamin ya yi matuƙar tausaya mata, haka kuma yana mamakin dalilin da yasa Mujaheed zai ce ya bata magani. Kawai sai ya sauya wani maganin ya ce ta je gabansa ta saki ledan maganin a ƙasa da zarar ya taka shikenan. 

Jawaheer ta zube masa kuɗaɗe tana godiya. Ta amince ko yau ya aureta asirin da tayi ya karye zata iya jurewa. A wahalce ta koma gida, hakan ya tashi hankulan iyayenta, babu tambayar da basu yi mata ba, amma amsar babu komai ne. 

A cikin ƙaton ɗakin Mujaheed ne da Jabir suka mayar da komai dake cikin biron zuwa Laptop suka kunna suna kallon ikon Allah. Babu abinda basu gani ba, hatta shiga ɗakin da tayi, sai dai sun so ƙwarai su ga takardun da kyau, sai dai biron ya yi rawa don haka basu iya karantawa. Har izuwa gurin budurwar da Mai nasara ya yi. Cikin sauri duk suka kawar da kai.  

Jawaheer ta kasa jurewa, don haka taje har gaban mahaifinta ta zube tana kuka, “Dad ku taimakeni ina sonsa. Zuciyata tana min zafi, idan ban same shi ba zan iya mutuwa.”  

A gigice mainasara ya riƙota yana tambayarta, “Wa kike so? Gaya min ko waye zaki same shi da ƙarfin dukiyata.” 

Girgiza kai tayi tana cigaba da kuka, “Dad wannan ba irin samarin da ka sani bane, duk dukiyarka da mulkinka ba zai taɓa burge shi ba. Nidai Dad ka taimakeni insame shi koda kuwa idan na shiga gidan ba zai taɓa kula ni bane.” 

Rungumeta ya yi, yana gaya mata kalamai, dole ta daina kukan tana ajiyar zuciya. Daga Mum ɗinta har Dad babu wanda ya iya rintsawa. Suna mamakin wannan wacce iriyar makauniyar soyayya ce? Ko dai asiri ya yi mata ne? 

Babu asiri wannan zallar so ne, wanda aka halicceta da shi.  

Cikin kwanaki biyu Alhaji Mainasara ya gano ƙanin mahaifin Mujaheed  Alhaji Ma’aruf don haka ya taka yaje ya same shi. Sun daɗe suna tattaunawa, daga bisani ya aika a kira masa Mujaheed.  

Tunda Mujaheed yake sunan Mainasara kawai yake ji bai taɓa ganinsa ba, haka duk zaman da yake yi a matsayin mahaukaci bai taɓa ganinsa ba, idan ma ya gansa daga nesa ne, haka zalika video ɗin da ya gani fuskarsa tayi dishi-dishi. Kafe juna suka yi da ido kowanne yana tunanin inda ya taɓa sanin ɗan uwansa. 

Mujaheed ya nemi wuri ya zauna yana duban kowannen su. Alhaji Ma’aruf ya zayyane masa komai, ya sake ɗagowa suna duban juna. Bai san meyasa ya tsane shi ba. Girgiza kansa ya yi, “Kayi haƙuri ban shirya aure yanzu ba. Kuma ko zan yi aure ba zan auri yarinyar da ta rasa tarbiyya ba.  

“Kai baka isa da arziƙina ka wulakantani ba.” 

 Mujaheed ya dawo da baya, ya zare glas ɗin idanunsa, “Arziƙi? Me arziƙi baya faɗin shine sai dai duniya su faɗa. Arziƙinka amfanin me zai yi min? To bari kaji, ko ‘yarka zata mutu ne ba zan taɓa auren ta ba, domin kuwa babu wurin ajiyeta. Ina fatan zaka dage ka nemo mata wanda zai so arziƙinka?” 

Ya sa kai ya fice abinsa. Jikin Mai nasara yayi sanyi, bai taɓa tunanin abin zai lalace hakan ba.  

Yau Mujaheed ya kammala aiki akan Mainasara, yau kuma yake tattara kayansa domin komawa ga ofishinsa. Haka zai sami sauƙin damuwar da ke tattare da shi. Ya gaji sosai da aikin C.I.D ana yawan sa rayuwarsa a cikin hatsari. Haka ba zai yuwu da mutuncinsa ya ɗinga ɓadda kama ba. Idan ba zai mance ba har mai gyaran takalmi ya zama, saboda kawai aikin bincike. Tuntuni yaso ya bar aikin ya komawa Kwangila irin sana’ar mahaifinsa, amma Nayla ta hana shi. Shafo kansa ya yi, yana duba agogo. Yamma ta riga tayi, dole zai bari sai gobe ya kama hanya.  

Fita ya yi, kawai yana zagaye titunan babu gaira babu dalili. Gani ya yi wani yana wasan taya, a titin kuma yana keta tsakiyar motoci. Mujaheed ya ƙurawa mutumin ido, sai yanzu ya fahimci mace ce ba namiji ba. Bai ankara ba yaga ta dafe motarsa. Sarkin zuciya tuni zuciyar ta fara tafarfasa. Buɗe glas ɗin ya yi, wai don ta saki amma abin ya gagara. Kawai ya gangara ya sauka. Fizgota ya yi, da iya ƙarfinsa zai mareta, sai ya ji wata murya, “Aboki me nayi maka zaka dake ni don Allah.”  

Cak ya tsayar da hannun yana dubanta. A hankali ɓacin ran ya sauya zuwa sanyin jiki. Dubanta kawai yake yi, ya kasa cewa komai har ya koma cikin motarsa. A guje ya fizgeta yana jin kamar ya yi tafiyarsa Abuja, zai fi samun natsuwa idan yana gaban Abbansa. 

Jawaheer ta dawo gida tana hawaye, a karo na biyu ta sake zubewa tana hawaye. “Dad ka taimakeni ka sake zuwa gidansu ka bashi haƙuri.” Hankalin Mai nasara a tashe yake ya kasa zaune ya kasa tsaye. Ya sami labarin Mujaheed shegen mutum ne, yana da tsattsauran ra’ayi. Dole ya yanke shawarar sake komawa. 

Sai dai cikin rashin sa’a suna shigowa Mujaheed yana ficewa a motarsa. Gaba ɗaya baya cikin natsuwarsa, a karo na farko yana shakkar miƙa bayanan da ya samu akan Mai nasara. A karo na farko yana tausayin rayuwar Jawaheer. Ya tabbata sai ankama mahaifinta, sai kuma ya shiga gidan yari. Cikin ƙarfin hali ya ƙwaci kansa daga cikin dogon tunanin da ya afka. 

Duban gefen titi ya yi, yaga wata zata tsallaka titi, babu inda ta bar Nayla ɗinsa, cikin ƙaraji ya ƙwala mata kira, *Naylaaa* da sauri ya yi parking, tana gab da shiga titin ya fizgota. Ta dawo ta zube a jikinsa. Sai yanzu idanunsa suka buɗe babu ko alamar kama da suka yi da juna. Kansa ya ɗan shafa ya sake ta, sannan ya yi magana cikin natsuwa, “Ki ɗinga kula da titi.” Daga haka ya sake ta, yarinyar ta ɗinga binsa da kallo har ya wuce abinsa.  

Jawaheer suna shigowa suka gaisa da Baba Ma’aruf anan yake tabbatar masu da Mujaheed ya wuce gidan iyayensa a Abuja. Jawaheer ta miƙe ta ce, “Nasan gidan don Allah ku barni inje. Zan bi shi.” 

Baba Ma’aruf ya tausayawa Jawaheer, haka kuma bai taɓa tunanin akwai macen da zata nunawa Mujaheed so kamar yadda Nayla ta nuna masa ba. Ya ga zallar ƙaunar Mujaheed a ƙwayar idanun Jawaheer.  

Dafa kafaɗarta ya yi, “Kiyi haƙuri ‘yata ki dage da addu’a sai ki ga cikin ikon Allah, Allah ya yi masa sauyi da Nayla ke kuma ki sami shiga zuciyarsa, wannan duk ikonsa ne.” 

“Nayla??”

Gaba ɗaya suka maimaita sunan suna duban juna. “Wacece kuma Nayla?” 

Baba Ma’aruf ya miƙe yana fitar da zazzafar huci, “Nayla ita ce rayuwar Mujaheed. Nayla ƙanwar Mujaheed ce da yake matuƙar so. Akan Nayla Mujaheed ya taɓa shaƙe ni, duk kuwa irin biyayyar da yake min kamar ya kwanta intaka shi. Mujaheed ya taɓa biyo ni da Adda cikin dare, ya yi rantsuwa zai iya kashe ni idan har nace zan takurawa Nayla. Tun daga nan na gane Nayla ita ce rayuwar Mujaheed. Idan kana son ka burge Mujaheed ka nunawa Nayla ƙauna. Idan kana son karɓar kuɗi a hannun Mujaheed ya sameka kana sa Nayla Dariya.”  

Jawaheer da muryarta ke rawa saboda kukan da take fitarwa, tun daga zuciyarta har izuwa kan fuskarta ta ce, “Ba..Ba.. Yanzu ina Nayla take? Ka gaya min inda take zanje inyi mata biyayya inroƙeta saboda in aure shi.” 

Baba Ma’aruf ya yi murmushi me ciwo, “Ban san inda Nayla take ba, amma ina tabbatar maki da Nayla tana nan, taga kina son Mujaheed ita da kanta zata rako shi wurin hira, ta kuma shawo kan Mujaheed ya so ki. Nayla wata irin mace ce, me tsananin son duk wanda ya ce yana son Mujaheed. Jawaheer duk yadda zan kwatanta maki halin yarinyar nan ba lalle bane ki fahimta, amma idan kika zauna da ita zaki fahimci bata da matsala.”  

Kalaman Baba Ma’aruf babu abinda yake sake sa su sai cikin ruɗani, sun rasa ina kalamansa suka dosa? Idan har Nayla zata iya raka Mujaheed taɗi gun budurwa hakan yana nufin ƙanwarsa ce uwa ɗaya uba ɗaya? Idan ta kasance ƙanwarsa ce ta jini me zai sa har Baba ya ambaci ita ce rayuwarsa?   

Ba Jawaheer ba hatta Mai nasara ya shiga cikin tashin hankali, haka a cikin abinda bai fice minti goma ba, wani abu ya shiga tsakiyar ƙwaƙwalwarsa yana bada wani irin haske, wanda tamkar a yanzu abin ke faruwa. Indai hasashensa gaskiya ne akan Mujaheed zai iya cewa ya shiga uku ya lalace. Haka lokacin rasa rayuwar ‘yarsa yazo. Idan kuwa ya rasa Jawaheer babu ko shakka, shima zai iya binta. Dole zai yi duk yadda ya kamata Jawaheer ta shiga gidan Mujaheed tun kafin lokaci ya ƙure masa. 

 “Alhaji ka bani address ɗin gidan zanje ingana da mahaifinsa.” 

 A zabure ta miƙe ta ce, “Dad nasan g…” 

 “Shut up!”  

 Dad ɗinta ya daka mata gigitacciyar tsawa, da ta sanya ta zaman ‘yan bori. Ji take kamar a tsinke mata zuciyar ta samu ta huta. Ji take kamar shikenan ta rasa Mujaheed ɗinta. Bata damu da tsawan da mahaifinta ya yi mata ba, damuwarta taga Mujaheed a gabanta yana gaya mata kalamai. 

Haka suka fice bayan Alhaji Mu’aruf ya basu lambar Alhaji Muh’d. Mum tana ganin su ta tare su cike da damuwa. Ta mance shaf Jawaheer tana ɗakin ta dubi Mai nasara ta ce, “Allah ka raba mu da aikin son zuciya. Allah ka raba mu da shirka. Ina fatan ka fara fahimtar lokacin girbin abinda ka shuka ne ya zo? Lalle lokacin da ka ɗaɗe da sanin zai zo shi ne yake tunkaroka a yanzu. Ni kuma Walh idan na rasa ‘yata har abada na gama zama da kai. Haka kake idan idanunka suka rufe baka jin shawara.” 

Ta rushe da kuka, wanda ya sake gigita shi. Shi kuwa a duniyarsa ya bai haɗa son matarsa da ‘yarsa da na kowa ba. Don haka ya riƙe kansa yana mamakin yadda akayi matarsa ta fahimci lokacin girbin abinda ya shuka ne yazo.  

Jawaheer ta dubi iyayenta cike da zargi tana girgiza kai, “Ku fito ku gaya min meke faruwa? Don Allah me yake faruwa? Kun taɓa sanin Mujaheed ne dama?” 

Da sauri suka girgiza kai, “Jawaheer ban taɓa ganin Mujaheed ba, bansan shi ba. Sai a dalilinki.” 

Ƙarar wayarsa ce tasa ya ɗauka a zabure kamar me jiran kiran wayar. Haka ya buɗe ƙarar wayar gaba ɗaya. 

“Mai nasara ashe kai wayon banza gareka? Mujaheed Muh’d, shi ne MD ɗinnan. MD ya yi wasa da hankalinka, ya zo garin nan saboda kai ne, haka ya sami abinda yake nema. Cocaine ɗin da kake safara duk ya samo bayanai akansu, bai yi hakan ba sai da ya samo taswirar gidanka. Yazo a matsayin mahaukaci, haka ya yi amfani da biro wajen samun duk abubuwan da yake nema. Ina gaya maka hatsarin yaron nan kana ganin kamar wasa nake yi. Ka mance na gaya maka wulakanta ni da ya yi, akan ‘yar iskar yarinyar nan? Ka manta shi ne silar datse ɗan yatsana? Lalle dole ka zauna cikin shiri domin akwai gagarumar matsala. MD dai shi ne C.I.D ɗin da ake ji da shi. Ya ƙware wajen gano masu laifi. Ka gode Allah idan Cocaine kawai ya gano, zamu iya shige da fice mu kashe maganar. Idan kuwa ya gano ɗayar fuskarmu komai zai iya faruwa.” 

Mai nasara ya shiga girgiza kansa da ƙarfi yana jin tashin hankali yans tsattsafo masa,  

“Alhaji Musa, babu amfanin rama mugunta da mugunta. ‘Yata Jawaheer ta faɗa cikin son MD, irin soyayyar da idan bata same shi tana iya rasa rayuwarta.” 

Alhaji Musa ya rikice iya rikicewa. Rasa abin cewa da suka yi ne yasa duk suka ajiye wayoyin su. Tambaya ce cike da zuciyar Jawaheer, matsalar kama mahaifinta ba shi bane damuwarta, damuwarta a ina mahaifinta yasan Mujaheed? Daman Mujaheed shi ke shigar mahaukata ya zauna a unguwar su?” 

Riƙe ƙirjinta tayi da ƙarfi tana jin wani sabon sonsa yana ratsa ko ina na jikinta. “Dad yaushe zamu je gidan su Mujaheed?” 

Girgiza kansa ya yi, “Tashi kije ki kwanta, zuwa anjima zamu tsara komai insha Allahu.” 

Tana tafe jiri na ɗibarta, kafin ta kai bakin ƙofa ta zube a sume. 

Mujaheed ne zaune a Ofishin su, bayan duk ya kammala basu komai ya miƙe yana ƙoƙarin barin wurin. Sai kuma ya dawo da baya, ya nuna wani da yake ta zazzare idanu, ya yi magana cikin takaici, “Idan da irin ku goma a ƙasa ina ƙasarmu zata iya zama lafiya? Muna aiki kuna ɓata mana. Duk wahalar da nasha, yau kai ne ka zama me lalata min aiki, kai kake kwasar sirrin aikin mu kake miƙawa mutanen da muke ƙoƙarin ganin mun kama su.”  

Kawai ya girgiza kai ya fice. Yana jin Ogansa yana ƙwala masa kira, amma ko waiwayowa bai yi ba. 

Yana isowa gida, ya sami Ummansa tana zaune a falo tana duba jarida. Idanunsa ya zura akan Jaridar, har yanzu dai hoton Nayla ne manne a jikin Jaridar. Idanun Umma cike da hawaye, haka bata san da shigowar Mujaheed ɗin ba. Hannu yasa ya ɗauke Jaridar, yasa ɗan yatsa ya ɗauke hawayen fuskar Ummansa, suna haɗa idanu ya girgiza mata kai.  

“Umma Nayla ba zata dawo ba…” Maganar ta tsaya masa a maƙoshi, ita bata wuce ba, ita bata barshi ya ƙarasa fitarwa ba. Duk dauriya irin na Umma sai da ta rushe da kuka. Miƙewa ya yi, ya shige ɗakinsa ya kwanta rigingine. Hotonta ya jawo daga ƙasan filonsa, ya rungume tsam a ƙirjinsa. “Ina sonki Nayla.Na shirya tunkarar kowacce irin matsala akan ki.” 

Cikin kayansa ya buɗe jikinsa na rawa, ya ɗauki kwalban giya ya kai bakinsa da ninyar shanyeta ko zai ji daɗi. Kalamanta suna nan raɗau a zuciyarsa, yadda ta rubuta su, har gobe sun kasa gogewa,  

 Kayi alƙawarin ba zaka sake shan giya ba? Kasan meyasa bana son kasha? Saboda abinda likita ya ce, idan ba haka ba, ni zan ɗinga siyo maka a ɓoye kayi ta shan abinka. 

Nayi maki alƙawarin ba zan sake shan ta ba, duk abinda baki so Nayla nima bana son abin. 

Sauke kwalban ya yi, tare da shigewa banɗaki ya juyeta. A banɗakin ya zauna ya takure yana jin zuciyarsa tana yi masa zafi. A hankali ya furta kalmomi bakwai, “Allah ka gajarta min zaman duniyar nan.” 

Wa’innan kalmomi sun zame masa hadda, wanda idan bai furta su ba, baya samun natsuwa.  

Jawaheer ta dubi Zara ido jajir, ta ce “Zara ki taimakeni ina son yayanki, ki gaya min yadda zan yi insamo kansa. Ban taɓa tunanin akwai wani halitta da zan so haka ba. Rayuwata tana cikin wani hali, ƙirjina zafi yake min. Ada ina kallon masu soyayya a matsayin mahaukata, wa’inda basu san ciwon kansu ba, a yanzu na fahimci so wani dafi ne, me wahalar warkewa. Don Allah ki taimakeni ki gaya min wacece Nayla? A ina kuma zan iya samunta? Zan roƙeta ne ta bar min Mujaheed.” 

Zara sarkin kuka da tausayi, ta sharce hawayenta, tana jin tausayin Jawaheer har cikin zuciyarta, “Anti labarin Nayla akwai tsawo, idan zan gaya maki labarin Nayla a gutsure labarin zai zo, Yaya Jabir shike ɗauke da komai akan Nayla, shi zaki nema na tabbata zai taimaka maki. Nayla bata da aboki sai Yayanmu, babu wanda ya isa yasan sirrinta sai Yayanmu.” 

Zara ta ƙarashe cikin kuka, tana jin ɗacin rabuwa da Nayla. Jawaheer ta rufe idanunta, tana ji a ranta lokacin mutuwarta ce ta zo. 

Fitowa falon tayi tana layi, tana kallo hukuma suka zo tafiya da mahaifinta. Cikin kuka take ce masu, “Don Allah kada ku tafi da shi, Dad idan suka tafi da kai waye zai je nemo min Mujaheed? Idan ban ganshi ba, zan iya mutuwa Dad.” 

Ɗaya daga cikin ‘yan sandan ya yi ta dubanta cike da mamaki, hakan yasa ya zagaya ya kirawo Mujaheed a waya, ya gaya masa komai. Mujaheed ya cika ƙwarai da mamaki, musamman da Jabir yake bashi labarin zuwansu gida.  

Duk iya tunanin Mujaheed ya kasa gane komai akan Jawaheer, haka bai damu da lamarin yarinyar ba. Haka yana ji a ransa ko mutuwa zata yi babu abinda zai sa ya kalleta a matsayin mace, bare har ya aureta. Soyayyar mace ɗaya ne tak! A zuciyarsa daga kanta kuma angama. Alƙawari ya yi wa kansa babu macen da ta isa ta matso kusa da zuciyarsa. 

Riƙe hotonta ya yi, yana buga kansa da ƙarfi, iya ƙarfinsa yake haɗa kansa da bango, Nayla kawai take yi masa gizo. Da sauri mutanen gidan suka yo kansa. Umma ta riƙe shi kawai ta fashe da kuka, hakan yasa ya dakata yana dubanta. Abba ya girgiza kai, yana faɗin ba zai taɓa bari ba. Tunda yaga iyayensa suna kuka ya nemowa kansa jarumta, ya nuna masu shi ya haƙura, haka ya ci burin rage damuwa ko don iyayensa su sami natsuwa. Yana jin damuwarsa tana ƙaruwa ne da zarar ya ci karo da hawayen iyayensa. 

Satinsa biyu kenan baya fita ko nan da can, wajen aikin ma ya ɗauki hutu. Fuskar nan ta fara tara gashi, gaba ɗaya yana son komawa gidan jiya. Abbansa ya shigo yana masa faɗan ya daina gyara kansa. Dole yau ya shirya da nufin ya je gun aski. 

Bayan ya je angyara masa fuskar, ya dawo fuskar nan babu annuri. Shi kansa ba zai iya tuna rabonsa da murmushi ba. A falo ya tsinkayi muryarta tana kuka kamar wacce akayiwa mutuwa.  

Jawaheer tana shigowa falon ta ci karo da manyan hotunan Nayla masu kyau, dukka hotunan tana maƙale a jikin Mujaheed tana dariya. Kai tsaye Jawaheer ta bi hoton tana shafawa. Umma da Abba sun tarbe su cikin mutuntawa, ita da mahaifiyarta. Daga ƙarshe mahaifiyar ta zayyane masu komai a game da irin halin da Jawaheer take ciki. Abba suka dubi juna suna jinjina zamani.  

Kukan da Jawaheer take yi, yasa dukkansu jikin su yin sanyi. A fusace ya shigo falon da ninyar yi mata rashin mutunci. Amma suna haɗa idanu ya nemi duk wani fushi ya rasa. Idanu kawai ya zuba mata, shi kaɗai yasan me yake hangowa akanta.  

A hankali yake magana cikin dakewa, “Jawaheer kinsan inda kika kawo kanki kuwa? Zama da ni babu abin sha’awa, mace ɗaya ce a duniya zata iya zama da ni, duk mugun halina zata zauna da ni babu ƙyama. Mace ɗaya ce zata zaɓi rayuwa da ni fiye da rayuwa a cikin ƙabarinta. Idan kika ce zaki shiga hurumin da ba naki ba, zaki gwammace ki zauna cikin ƙabari da zama a cikin gidana. Jawaheer idan na aureki zan cutar da ke ne, zan wahalar da ke, zaki zama da zamanki a gidana da babu duk ɗaya ne. Ba zan iya yin aure a duniyar nan ba. Kiyi haƙuri ki fita a rayuwata.”  

Juyawa ya yi yana jin kamar ya shaƙeta ta mutu, ƙila zai fi samun natsuwa. Yana jiyo kukan Jawaheer tana faɗin ta amince zata jure. Har ya kai bakin ƙofa ya juya yana dubanta, zuciyarsa tana gaya masa yaje ya lallasheta, ya je ya gaya mata kalamai masu daɗi. Girgiza kansa ya yi. Kalamansa ya tanadarwa mace ɗaya ne tak!  

Abba ya dubi Jawaheer da tausayawa ya ce ta je waje zai yi magana da Ummanta. Babu musu ta fice. 

Abin mamaki ta haddace ɗakunan cikin gidan, duban ɗakinsa tayi tana jin gabanta yana faɗiwa da ƙarfi. Zuciyarta tana ingizata cikin ɗakin. Sannu a hankali ta sada kanta da ɗakin. Yana kwance rigingine hannunsa sigari ne yana ta juyata. Ya rasa ta yadda zuciyarsa zata amince masa ya sha sigarin. 

Kafeta ya yi da ido, sai ta juye masa Nayla. Tana zuwa kai tsaye ta kwanta a dai-dai inda Nayla take yiwa kanta makwanci. Tana kwanciya a ƙirjinsa tasa hannu ta cire sigarin, tayi magana cikin shagwaɓarta da shessheƙan kuka, “Aboki kayi min alƙawari ba zaka sake shan sigari ba.”  

Wani irin sanyi ya ratsa Mujaheed, wanda rabon da ya ji hakan tun ranar da Nayla ta bar ƙwayar idanunsa. Mirginota ya yi, yana magana a bisa fuskarta, “Kinyi min alƙawarin ba zaki yi nesa da ni ba, meyasa kika tafi kika barni?” Ƙoƙarin kissing ɗinta yake, suka ji motsi. A lokacin ne kuma idanunsa suka buɗe tarr ya gane ba Nayla ce a gabansa ba, Jawaheer ce. A gigice yaga ta ɗauke sigarin hannunsa ta ɓoye a irin wurin da Nayla take ɓoye masa duk wani abu da tasan iyayensu basu so. 

Mamaki yasa kawai ya cigaba da kallonta. Turare ta buɗe ta fesa masa. Sannan ta buɗe ƙofar ta fice. Iya ruɗu Mujaheed ya shiga. Sai kuma daga baya ya gane Jawaheer tana son koyon halin Nayla ne, domin ta samu fada agunsa. A hankali ya mayar da kansa yana faɗin har abada. 

Duk yadda Mujaheed yake tunanin iyayensa zasu kawo masa maganar Jawaheer shuru basu ce masa komai ba. Hakan yasa ya sami natsuwa. A bakin abokinsa yake jin ansaki mahaifin Jawaheer, girgiza kansa kawai yayi yana jinjina halin ‘yan Najeriya. Sam me kuɗi baya aikata laifi. 

Dawowarsa kenan daga Office ya ga babban falon baƙi a buɗe hakan yasa ya cika da mamaki. Har zai wuce ya dawo da baya. A bakin ƙofar ya tsaya yana sauraren su. 

Shi kansa bai san lokacin da ya shigo falon ba, yana ƙarewa iyayensa kallo, “Abba, aure zaku yi min? Abba har yaushe kuka mance  Nayla? Abba bazan iya rayuwa da wata ‘ya mace ba. Idan kuka yi min hakan zaku sa ni a cikin wani hali ne, zaku sake rasa ɗanku a karo na biyu. Meyasa Abba?” 

“Mujaheed ka shiga gida zan shigo.”  

Abinda Abban ya iya furtawa kenan. Girgiza kai kawai yake yi, ya shiga gida. A gaban Ummansa ya zube. “Umma meyasa zaku yi min haka? Ni nace maku ina son aure? Me kuma zan sake ci da aure? Umma kun zaɓi ku ƙuntatawa naku don kawai kuna son ku farantawa wasu? Yaushe kuka gama kukan Nayla? Kuna nufin har kun shafe Nayla daga babin wannan gidan?” 

Umma ta girgiza kai, “Kayi haƙuri Mujaheed ka karɓi zaɓin mahaifinka, ta hakane zaka iya gode masa da irin tarbiyyar da ya baka. Ka zama mai yarda da ƙaddara me kyau ko akasinsa. Kayi haƙuri Allah yana tare da kai. Idan kayi masa biyayya zaka ga amfaninsa anan gaba.” 

Miƙewa ya yi, yana girgiza kai, yana jin iyayensa basu yi masa adalci ba. Ficewa ya yi da sauri ya ɗauki motarsa. Gudu kawai yake shararawa a titin, yana jin kamar motar bata sauri. Ba zai iya auren Jawaheer ba, bai taɓa jin sonta ba, mace ɗaya yaso a duniya daga kanta angama. Ya gwammace ya bar masu garin har komai ya lafa, da a kawo masa Jawaheer a matsayin mata. Ba zai iya duban Nayla ya ce mata ya yi aure ba. Ba zai taɓa iya saka mata da wannan cin amanar ba. Tafiya yake yana ganin kamar za a sake dawo da shi cikin garin Abuja.  

A karo na barkatai yake jin tsanar Jawaheer a ransa, Jawaheer ta zame masa masifa. Jawaheer zata sake wargaza masa dukkan wani shirinsa. Kiran wayar mahaifinsa ya dawo da shi hayyacinsa, cijewa ya yi ya ɗauka,   

“Mujaheed idan har ni na haifeka, ina baka umarnin duk inda kake ka dawo. Ka dawo ka karɓi matarka Jawaheer. Idan kuwa ka wuce baka dawo ba, ba zan taɓa yafe maka ba Mujaheed.”  

Wani irin burki ya taka da ƙarfi, wanda ya yi dai-dai da bugawa wata mota, a take motar da Mujaheed ɗin suka yi ratsa-ratsa. Wannan lamari ya faru ne akan kunnen Abbansa. Hakan yasa ya ɗinga salati a cikin tsananin gigicewa. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jawaheer 1Jawaheer 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×