Skip to content
Part 17 of 17 in the Series Jawaheer by Fatima Dan Borno

Jawaheer ta sami lamarin cikin sauƙi, haka taga abinda ake kira gigicewa da lallaɓata. Ko a daren su na farko bai yi mata hakan ba. Haka bayan sun kammala tsam ya rungumeta a ƙirjinsa yana sa mata albarka.

Mujaheed bai barta ta matsa ko nan da can ba, yana maƙale da ita kamar wani zai ƙwace masa ita.

Wajajen ƙarfe goma ya fito cikin shirinsa, haka fuskar nan babu yabo babu fallasa. Yana da ji da kansa da yawa. Bayan mutuwar Naylaa da ya taɓa shi, da alamun girman kai agurinsa. Wannan tunanin Jawaheer ne, domin kuwa da ta zo zamanin soyayyarsa da Naylaa da ta fasalta Mujaheed a cikin maza masu sauƙin kai, da son nunawa iyalansu soyayya.

Har mota ta raka shi. Bayan ta sumbace shi ta ce,

“Ka kular min da kanka. Kada ka yarda wata da kalleka.”

Murmushi ya aika mata ba tare da ya furta komai ba. Haka ya fice, ko ba komai ya daina jin haushinta. Haka yau ya fito cikin wani irin annashuwa, wanda rabon da ya ji hakan, tun a ranar farkonsa da Naylaa.

Har ya iso Office mutane suna mamakin irin wannan walwala da ke shimfiɗe a fuskar Mujaheed. Laluban wayarsa ya yi da nufin kiranta, sai dai bai taɓa saving number ɗinta ba, dole ya mayar da hankali akan aikinsa.

Kamar zai jure sai kuma ya miƙe yana faɗin baya jin daɗi. Kai tsaye ya koma gun matarsa yana son sake ɗanɗanan ni’imarta. Amai ya sameta tana kwarawa, hakan yasa ya ɗauketa kawai ya yi asibiti da ita. Gwajin farko aka gano ta ɗauke da ciki. A gaban likitocin ya ɗaga ta sama yana juyi da ita. Kowa dariya yake masa, haka Jawaheer tasha mamakin a saduwarsu na farko ta sami ciki.

Wuraren shaƙatawa ya nufa da ita, yana jin kamar shi ɗaya Allah ya yi wa baiwa. Kai tsaye ya wuce da ita gidan Umma yana aikin murmushi.

“Umma kin kusa yin jika.”

Ba Umma ba, hatta Abba sai da ya ɗago yana duban Jawaheer. A guje ta ruga ɗakin Umma saboda wani irin kunya da ya kama ta. A gigice yake ƙwala mata kira tare da rufa mata baya. A bayan kofar Umma ya ci karo da ita, don haka ya riƙe kafaɗunta, “Idan wani abu ya sami cikin nan kiyi kuka da kanki.”

Kunnensa ta riƙe, “To ka daina kunyata ni.”

“A’a akan ɗana ba zan daina faɗin gaskiya ba.”

“To zo mu zagaya baya ka ji wata magana.”

Kai tsaye duka shige cikin Garden ɗin ta nuna masa wata gwaiba ta ce ya tsinko mata. abu musu ya tsinko ya nufi famfo ya wanke mata. Ta gutsuri kaɗan ta bashi a baki. Sannan ta ci gaba da ci tana lumshe idanu. Murmushi kawai ya yi mata ya kwanta kawai a ƙasan wurin yana duban sararin samaniya. Itama ta kwanta kamar yadda ya yi, ta fara aika masa da kalamai.

“Idan na dubi kaina, sai ingode wa Allah. Ya yi min baiwa da miji na gari kamarka. Ba kowacce ‘ya mace ce take da wannan baiwar ba. Da ace zan iya ƙididdiga iya adadin ƙaunar da nake yi maka, babu shakka da saukar ruwan sama ne abu na farko da zan iya ƙirgawa. Haka ƙirga ‘ya’yan da ke cikin buhun gero ba zai wahalar da ni ba.

Mirginowa ta yi, ta yi matashin kai da ƙirjinsa.

“Zan ci gaba da alfahari da kai, zan cigaba da nunawa duniya gwarzona. Zan cigaba da bayyana wa kowa farin cikin da nake tsintar kaina a duk lokacin da nake kusa da kai. Idan kaf duniya suna yi maka kallon wani mutum mai mugun hali, idan ni kaɗai ce na rage a matsayin wacce zata yabeka, zan fito da ƙarfina inyabi mijina.”

Duban fuskarsa tayi, tabbas kalamanta suna sanyaya masa rai fiye da tunaninta. Hakan yasa ta haɗe fuskarsu wuri guda. “Ka bani aron zuciyarka ko da ta minti biyar ce, ni kuma a cikin minti biyar ɗin zan tabbatar maka da ƙaunar da nake maka, ba tare da na bari mintunan sun kubce min ba.”

Mirginota ya yi, kalamanta sun cika zaƙi da yawa, suna son su mantar da shi matsayin Naylaa, dole ya rikirkita ta, da salon soyayyarsa, sannan ya samu ya kashe bakin kalaman.

Abinda Jawaheer ta koma kula agun mijinta, yafi baiwa cikinta kulawa fiye da ita kanta. Amma duk da hakan Allah baya taɓa baka komai ɗari bisa ɗari, dole sai ya barka da jarabawarsa. Ta ɗauki hakan a matsayin matsalar gidan aure, da duk yawancin kowacce mace take ƙunshe da shi a zuciyarta. Wata ma da zata buɗe maka zuciyarta da sai ka kusan suma, saboda tausayawa.

Zai fita tasa masa rigima, ita dai sai dai su fita tare. Babu musu ya ce su tafin. Har Office ya taho da ita, hakan ya jawo gulma akan ga macen da ta sauya Mujaheed. Haka kowa ya kalleta sai ya sake kallo. Wani ya ce ko a ina yake samo irin matan nan oho? Shi dai ko kallonsu bai yi ba. Tana nan zaune tana karatu yana karɓar cases. Dubansa tayi duk ya yi zufa, ta sa hannu ta goge masa zufan, sannan ta kunna AC. Kai tsaye ta nufi frij ta ɗauko lemu mai sanyi ta dawo kusa da shi, tare da kafa masa kofin a baki. Sosai yasha sannan ya dubeta, “Na gode da kulawa.”

Mutanan wurin suka cika da mamakin irin wannan salon. Bai tashi aikin ba, ya dubeta, “Baby muje gida mu kwanta ko? Barci nake ji.”

Da gir ta amsa masa. Suka fito suna ‘yar hirar su.

“Idan kika haihu, yaron nan zai sha gata.”

“A’a kada kuma ka sangarta min yaro.”

“Ta ina ya zama yaronki?”

“Ta yadda na jure dukkan gwagwarmaya a Lokacin samunsa, har azo kan haihuwarsa.”

“Zo nan. Kina son gasa min magana ko?”

Zata gudu ya sha gabanta tare da riƙe hannunta tsam,

“Wayyo kada ka karya min hannu.”

“Gara inkarya maki hannun da ki karya min cikina.”

Dariya sosai tayi, “Dama ana karya ciki ne?”

“Kin ci sa’a muna kan hanya ce, da na kwatanta maki yadda ake karya ciki.”

Da hannu take masa alamu, “A’a na yafe wallahi. Ni dai ka kaini insha Ice Cream ɗina.”

Matse hannun ya yi, har sai da tayi ƙara, “Daga yau na kashe shan Ice Cream likita ya ce ki daina sha kada sanyi ya taɓa min lafiyar babyna.”

“Wai! Amma dai wanda bai taɓa haihuwa ba, ba zai taɓa iya zama kusa da kai ba.”

Banza ya yi mata suka shiga mota. Fuskokin su kaɗai zaka duba ka gane suna cikin farin ciki.

Mujaheed kenan, har yanzu bai taɓa furta mata yana sonta ba, ko da kuwa a cikin gigicewar soyayya. Wannan abu kullum yana damun Jawaheer sai dai babu yadda ta iya.

Yau tana goge-goge tana turara ɗakin da turaren kasko, ya dawo ya ce, “Menene wannan kike sawa?”

Gabansa ta ƙaraso da turaren wutan ta ɗan hura masa hayaƙin,

“Malamina ne ya bani magani ya ce indai ka shaƙi hayaƙin, sunanka bawan mata.”

Murmushi mai ƙayatarwa ya sakar mata, “Ki gaya masa zan ƙara masa kuɗi, domin tun daga gurin motata na gamsu da maganin ya kama ni, ina shigowa kuma sai na ji tabbas na tabbata bawan mata biyu. Naylaa da Jawaheer.”

Dubansa take yi cike da mamakin kalamansa. Yau ne rana ta farko da ya taɓa mayar mata da martani da zuciyarsa guda.

Ajiye turaren tayi tana murmushi, “Na gode Allah da ya nuna min dawowarka lafiya. Saura kuma ka watsa ruwa ka huta.”

“Wai kullum ne ake wanka sau uku sau biyu a rana? Nikam yau na gaji, tunda ba wari nake yi ba a barni tukun.”

“Haba dai. Idan na barka baka yi wanka ba, da wa zaka kwanta a gado ɗaya?”

Taɓe baki ya yi, yana me gyara zama. “Sai inkwanta a ƙasa. Da dai inyi ta wanka kamar agwagwan ruwa gara inyi kwanciyata a ƙasa.”

Bata ce komai ba ta wuce banɗaki ta haɗa masa ruwan wanka. Tana fitowa ta ce, “Tashi muje ka gani, ina da ayyuka da yawa a gabana.”

Murmushi ya yi, ya miƙe yana cewa, “Lallai magani har ya fara aiki.”

Ita ta taimaka masa ya watsa ruwan sannan suka yi zaman cin abinci.

“Ki shirya gobe zamu je gidanku ki gaida iyayenki.”

Bata san lokacin da ta ƙanƙame shi ba,tana gode masa. Ɗaure fuskar ya yi, “Daman kin ƙosa ne? To anfasa tafiyar.”

Jikinsa ta haye ta ce, “Kayi haƙuri mana. Ayya ni ko? To yau sai na sha ƙanƙara sosai.”

Idanu ya zaro, “Da kuwa kinsha bulala.”

A daren tana barci ta laluba bata ji shi ba, don haka ta buɗe idanunta. Cikin ɗan hasken ta hange shi yana duban hoton Naylaa. Duk abinda zata yi domin ta kwantar masa da hankali Allah ya gani tayi, kuma ta kai matsayin da komai nata yake shirin gazawa. Sakkowa tayi ta dafa bayansa.

“Kayi haƙuri, ka ɗauki ƙaddarar nan, Naylaa ba zata ji daɗi ba, ace kullum kana cikin ƙunci saboda ita. Aboki. Ina sonka ina jin damuwa a raina idan na ganka a cikin damuwa.”

Miƙewa ya yi, ba tare da ya ce komai ba, ya koma gadon. Hakan yasa ta biyo bayansa suka rungume juna. Jikinsa ya ɗauki ɗumi. A hankali take bubbuga bayansa kamar yaro ƙarami. Tasa bakinta tana ɗan hure masa kunne. Kafin wani lokaci barci ya yi awon gaba da shi. Ajiyar zuciya ya ƙwace mata, a lokaci guda ta tofe shi da addu’a.

*****

Yau dai bakin Jawaheer har kunne gata ga iyayenta. Shi dama Mujaheed wani aiki ya kawo shi Kadunan, don haka ya barta a gidan iyayenta shi kuma ya wuce gidan Baba Ma’aruf.

Jawaheer ta samu zantawa da mahaifiyarta, na tsawon kwanaki uku, sannan suka koma.

Cikin Jawaheer yana ƙara girma, cike da kulawan Umma. Haka babu laifi Mujaheed ma yana bata irin tasa kulawar. Yau sun jima suna mahawara akan idan ta haifi mace a sanya Naylaa, shi kuma yana cewa Muhibbat. Ta ce “Naylaa ba suna bane, menene asalin sunan Naylaa?”

Kai tsaye ya bata amsa da “Sunanta Khadija.”

Ta gyaɗa kanta tana shafar wuyansa, “Insha Allahu Khadija zamu haifa.”

Sannu a hankali cikin Jawaheer ya girma sosai, ta yadda take tafiya da ƙyar. Mujaheed yake kama hannunta su yi tafiya mai nisa suna hirar su gwanin sha’awa. Kowa ya gansu sai ya sake duban su.

Yau cikin dare ta farka da ciwon naƙuda. Hankalin Mujaheed ya tashi don haka ya kira Umma suka dugunzuma zuwa asibiti. Mujaheed ya kasa zaune ya kasa tsaye.

Kiransa akayi aka ce tana kuka tana kiran sunansa. Ƙarasowa ya yi har gaban gadon, yana shafa kanta. “Sorry zaki haihu cikin ƙoshin lafiya insha Allahu.”

A hankali take magana, “Mutuwa zan yi ka yafe min don Allah.”

Ya gigita da kalamanta, magana yake yi mata a lokacin da shi da kansa bai san yana furta su ba, “Ina sonki Jawaheer. Ina sonki, ina sonki. Kiyi haƙuri mu ƙarasa rayuwarmu a tare. A wannan karon idan na rasa ki babu shakka zuciyata zata iya tarwatsewa.”

Jawaheer da ta ji saukar maganarsa kamar albishir da gidan Aljannah, tayi wani irin nishi mai ƙarfi. A lokacin ne kuma aka buƙaci da ya fita. Tun kafin ya gama buɗe ƙofar ya ji kukan jariri. Da murmushi a fuskarsa ya fito yana duban Umma.

“Ga dukkan alamu Jawaheer ta sauka lafiya.”

Umma ta ce “Kai masha Allah. Allah ya basu lafiya.”

Mujaheed ya kasa haƙurin jiran a fito da jaririn, har zai koma ɗakin, Umma ta riƙe shi. Dole ya ɗan sosa kan ya koma ya zauna.

Cikin fararen kayan sanyi aka fito da babyn, shi ya karɓeta yana kallonta. Yarinyar mai kyau da ita, haka ya kasa tantance da wa take kama, a tsakaninsa da uwarta.

“Ansami ‘ya mace.”

“Allah ya raya Nana Khadija.”

Gaba ɗaya suka amsa da Ameen. Sai yanzu hankalinsa kuma ya karkata kan uwar. Ya juyo yana tambayar Nas ɗin lafiyar matarsa. Murmushi tayi ta ce, “Matarka tana cikin ƙoshin lafiya, tana da buƙatar hutu ne.”

A ranar Mujaheed ya kasa rabuwa da ‘yar dai-dai da minti ɗaya. Haka ya kasa yin kawaici akan yarinyar. Sai misalin ƙarfe tara na safiya ya sami ganin Jawaheer.

Manna mata sumba ya yi, ya ce “Kin gama biyana da kika haifa min ‘ya mai kyau, mai kama da marigayiya uwarta.”

Jawaheer tayi murmushi, ta duƙar da kanta. Har yanzu kalmomin da Mujaheed ya gaya mata suna dawowa cikin kunnenta. Tana son a yanzu ma ta sake jin ko da kalma ɗaya daga cikin kalmomin.

Ya gama kula da yadda take asanyaye. Shi kuma ba zai sake furta mata komai ba.

Haka aka sallame su, suka koma gida. Tuni aka shiga tururuwan ganin Naylaa, hatta Suhaima babu kunya sai gata tazo.

Haka akayi suna suka sha shagali. A cikin taron sunan Mujaheed ya lallaɓo matarsa ta shigo ɗakinsa yasa key ya rufe ƙofar. A jikin bango ya matseta yana aikin zuba mata kiss jikinsa har rawa yake yi. Mamaki yasa kawai ta kauce tana dubansa.

“Meke damunka ne Abban Naylaa? Ka mance ina cikin jini ne? Ko wani abun kasha ne?”

Bai sami daman bata amsa ba, sai da ya kaita har gado ya yamutsa ta son ransa,sannan ya matseta yana sakin ajiyar zuciya. Ita kanta jikinta duk ya gama yin la’asar.

“Walh bansan meke damuna ba baby, na dai san kewarki kawai nake ji. Yanzu na sami gamsuwa ki tashi ki koma cikin jama’arki.”

Turo baki tayi cike da shagwaɓa, “Ni yanzu ya zanyi da kunyar jama’a? Kuma ka sani sarai idan ka taɓa ni, sai inyi ta jin jiri, har mutane ma su gane mu.”

“Ai ba kwartanci kika je ba. Idan baki tafi ba, zan sake yamutsa ki.”

Babu shiri ta miƙe tana ƙoƙarin daidaita natsuwarta. Duk da hakan sai da ƙawayenta suka gane, suka yi shewa suna zolayarta. Ita dai tayi banza da su kawai.

Anyi taro lafiya anwatse an bar Mujaheed da ‘yarsu Naylaa.

Haka suka ci gaba da renon ‘yar su cikin so da ƙauna.

Bayan shekaru uku

Naylaa ce a guje tana ƙyalƙyaltan dariya, hannunta ɗauke da zinaren Jawaheer, bayan ta tsinka shi. Ran Jawaheer ya yi mugun ɓaci, don haka tana kama ta ta shiga duka. Yarinyar ta sa ihu, hakan ya yi dai-dai da shigowar Mujaheed, ya ɗauketa cak ya rungume yana lallashi. Fuskar nan babu alamun fara’a yake dubanta.

“Dan baki da hankali zaki dukar min ‘ya? Na jima ina kallon take-taken ki so kike ki dinga gallazawa ‘yar nan, kuma ba zamu taɓa shiryawa ba.”

Jawaheer ta dube shi, “Yanzu Abban Naylaa babu dama tayi laifi sai a zuba mata idanu? Sarƙar zinarena fa ta tsinka.”

“Sai me? Kin gaya min kika ga ban biyaki ba? Walh akan ki ɗinga taɓa yarinyar nan zan iya ɗaukar mummunar mataki akanki.”

“Mummunar mataki na nawa kuma? Indai ‘yarka ce ga ka ga tanan, a lokacin da zata sangarce ƙila ma bana duniyar. Dama ba sona kake yi ba, don ka wulaƙanta ni ba komai bane, don na saba.”

Ta wuce da sauri tana kuka. Naylaa ta dubi uban ta ce, “Aboki momi tana kuka.”

Shafa kan ‘yar ya yi, ya ciro mata kayayyakin tsarabarta yana biyewa shirmanta. “kada ki damu Friend kin ji? Momi tayi fushi kinyi mata ɓarna.” Bata bashi amsa ba, domin hankalinta yana kan kayan wasanninta.

Da kansa ya yi mata wanka ya ɗauketa ya kaita gidan Umma, sannan ya dawo.

Ɗakin Jawaheer ɗin ya wuce tana ta haɗa kayanta. Jikinsa ya yi sanyi, ya ce “Ina zaki je kike haɗa kaya?”

“Zan tafi gidanmu ne inbarka da taka ‘yar.”

Dole ya kwantar da murya, domin da ‘yar buƙatarsa ya dawo. Jawota ya yi jikinsa ya ce, “Haba Jawaheer daga gaya maki gaskiya? Ban san Jawaheer ɗina da irin wannan halin ba. Yarinyar nan ita kaɗai garemu, idan ta isa hukuncin sai kiyi mata, amma yanzu tayi ƙanƙanta da yawa.”

Mace kenan sarkin rauni. Da ace ita tayi masa laifin ba lallai ya dubeta ba. Nan da nan ta bayar da kai bori ya hau. Sai da suka kintsa ta ware idanu, “Ina ‘yata?”

“Na kaita gurin kishiyarki ta fara koyon reno kafin ta iso.”

Filo ta dinga buga masa tana faɗin, “Ni dai bana so, bana so.”

Ya ya riƙe hannunta, “Ni dai ina so.”

“Allah da gaske nake yi.”

“Nima da gaske nake yi.”

“To Allah ya kawo ta lafiya.”

Tana ƙoƙarin miƙewa ya dawo da ita jikinsa yana murmushi.

“Wasa nake maki. Sai kin haifa min ‘ya’ya uku zan ƙaro maki wata.”

Haka rayuwar tasu take tafiya, duk yadda suke soyayya hakan baya hana ɗaya ya ɓatawa ɗaya. Musamman ma shi Alhaji Mujaheed, sarkin fushi da zuciya. Haka take lallaɓa ‘yan kayanta suna zama lafiya.

Dawowarsa daga gun aiki kenan, yaga yaran almajirai sun yi layi. Hakan yasa ya fito daga motar ya ƙaraso har gabanta shima ya miƙa mata hannu. Almajiran sai cewa suke Allah karɓa.

Yarinyar tana son ɗaukar halayyar Naylaa. Ji ya yi kamar yau ya rasa Naylaa. Yana jin mutuwa tayi masa yankar ƙauna. Cike da fara’a ta dubi mahaifinta. “Aboki sannu da zuwa.”

Yana murmushi ya ce, “Friend sadaka kike yi?”

Cikin surutunta ta ce, “Eh Momi ce ta ce min inɗinga yin hakan, irin halin Mommana da ta rasu kenan. Ita ta bani sweet ta ce inbasu. Aboki wai haka yana da kyau?”

Shafa kanta ya yi, “Yana da kyau sosai da sosai. Mommanki tana cikin Aljanna tana ganin aikin ladan da ‘yarta take yi. Sai almajirai suyi mata addu’a ko?”

Ta ɗaga kanta tana faman washe baki.

Tsayawa ya yi ya taya ta raba masu sannan ya kamo hannunta suna tafe suna hirar su.

Cikin ikon Allah suka halarci bikin Jabir wanda aka haɗa har da na Zara. A lokacin ne kuma Jawaheer take samun labarin mutuwar auren Suhaima, har ma mijin zai ƙara aure.

Mujaheed ya yi masa faɗa, anan yake gaya wa Mujaheed irin halayyar Suhaima na shige-shige da yawon roron gulma. Ba zai iya ba, kada ta haihu da shi ta shafawa zuri’arsa.

Sun sha biki lafiya, sun dawo ɗauke da tsarabar baby.

Yau dai ta gaji yana kwance a cinyarta ta ce, “Aboki, wai kana sona kuwa?”

“Me kika gani?”

“Babu komai tambaya ce kawai.”

“Kina son ingaya maki da baki ne, ko kuwa in nuna maki a aikace?”

“A’a da baki ya gamsar.”

“To ina sonki Jawaheer. Mutuwar Naylaa ya tsaya min a rai, har gobe mutuwarta sabuwa take dawo min. Ina iya bakin ƙoƙarina wajen nuna maki kulawa, kiyi haƙuri nasan ba zamu taɓa dauwama a hakan ba.”

“Babu komai aboki zan ci-gaba da yi maka addu’a. Babban fatana Allah ya bamu zaman lafiya. Ita kuma Allah yasa ta huta.”

Shuru ya yi ya kasa magana, sai ma rufe idanunsa da ya yi kawai yana hasaso Naylaa.

Naylaa ƙarama itama ta ƙaraso hakan yasa Jawaheer janye kan Mujaheed cikin dabara. Tana zuwa ta haye jikin Babanta. Jawaheer ta ce, “Kin ga Naylaa Aboki barci yake yi, ki barshi ya huta.”

Maƙale kafada tayi alamun a’a. Shima kuma yasa hannu ya ƙara kwantar da ita idonsa a rintse. Ita dai tana ganin abin ya motsa ta tattara ‘yan kayanta ta shige cikin ɗakinta. Anan ta barshi da ‘yarsa.

Sai can dare ta ji shi a bayanta yana magana ƙasa-ƙasa, “Na zaɓi wannan rana domin ta zama ranar da zan yaba maki. Kin zama jajirtacciyar mace, wacce samun kamarta a wannan zamanin zai zama aiki ne mai matuƙar wahala. Kin jure dukkan gwagwarmayata. Don Allah Jawaheer ki yafe min. Ban yi maki alƙawarin na sauya halayyata ba, amma zan yi ƙoƙarin ganin na rage su.”

“Babu komai Abban Naylaa. Tun ranar da kace kana sona, na ji kamar ansauke min wasu kaya ne akaina. Baka yi min komai ba, idan ma kayi min na yafe maka.”

A haka suka nausa wata duniyar, wannan karon tafiyar tayi nisa, haka ya dage ya saki jikinsa sosai. Don haka ne nima na tattaro alƙalamina na kamo hannun Aisha da ke ƙoƙarin ganin ƙwaƙwam na raɗa mata a kunne, “Ke sirrin ma’aurata ne bai kamata mu ci gaba da ɗaukan rahoton ba.”

Aisha ta fizge hannunta tana zabga min harara. Ganin tana ƙoƙarin komawa na fincikota muka bar wurin.

Alhamdulillahi

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jawaheer 16

2 thoughts on “Jawaheer 17”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×