Skip to content
Part 14 of 17 in the Series Jawaheer by Fatima Dan Borno

Mujaheed ya kasa magana, haka ya kasa daina dubansu.

“Jabir meyasa baka gaya min kana son Jawaheer ba? Meyasa ka zaɓi kayi mata ciki tana gidan ɗan uwanka? Jabir kai ɗan uwana ne, duk abinda kake so a duniyar nan dole zan tayaka sonsa ko menene. Na gode Allah da nake renon ɗan ɗan’uwana. Haka zan shige maka gaba akan komai insha Allahu.”

Jabir yana girgiza kai, Jawaheer tana girgiza kai, amma tuni Mujaheed ya fice daga gidan gaba ɗaya. Daga dukkan alamu Masallaci ya wuce.

Jabir ya nemi wuri ya zauna saboda yadda ƙafafunsa suka gagara ɗaukarsa. Ya tabbata ya faɗa tarko mai wahalar fita. Gaba ɗaya ya mance da Sallah, kawai Kaduna yake hange. Haka yana da tabbacin idan Allah ya bashi Sa’a ya fice ba zai sake waiwayo Abuja ba.

Jawaheer da ta rasa wani irin duba zata yi wa Jabir, ta cigaba da rera kukanta mai ban tausayi.

Jabir ya miƙe kawai da nufin ya fice kafin Mujaheed ya dawo, sai dai tuni ya makaro Mujaheed tsaye a bakin ƙofar ya kafe shi da rinannun idanunsa.

“Jabir ka ɗauki Jawaheer ku bar min gidana.”

Miƙewa Jabir ya yi cike da ƙarfin guiwar da bai yi tsammanin samunsa ba.

“Mujaheed alamu sun nuna a gidanka na kwana, a ɗakin matarka. Allah kaɗai zai fitar da ni. Bansan lokacin da na shigo ba, amma tabbas nasan lokacin da na farka nake laluban hanyar guduwa har muka ci karo da juna. Idan da gangar na shigo, babu abinda zai sa har inkai matakin da zan bari a kama ni. Nasan ba lallai ne ka yarda da ni ba. Daga yau na bar sake zuwa gidan nan, bare mai sharri ya sami hanyar da zai sake sharranta min.”

Mujaheed ya ɗinga binsa da wani irin kallo yana yamutsa fuska, “Ba zarginka nake yi ba Jabir. Kai ɗan uwana ne kuma dolena. Kawai ina son ka ɗauki Jawaheer ku fice min daga gidana.”

“Ba zan ɗauketa ba, ba zan je ko ina da ita ba. Na gode da uzurin da kayi min. A duk lokacin da gaskiya tayi halinta zaka nemeni, a lokacin ne zan sake dawowa.”

Jabir ya kama hanyar ficewa daga gidan, ga mamakinsa sai ya ga Mujaheed ya bashi hanya. Sai da suka dubi juna na wasu lokuta, sannan kowannen su ya kauda kansa.

Ƙarasowa ya yi gabanta yana dubanta, “Jawaheer kin shigo rayuwata kin tarwatsa min komai. Ɗan ragowar farin cikina duk kinyi gaba da shi. Ta yaya zaki yi tunanin insoki?”

“Nima bana tunanin ka so ni Mujaheed. Tuni na haƙura da kai, a yanzu na dawo cikin hayyacina bana sonka, bana sonka Mujaheed. Zai fi kyau kayi haƙuri ka tsananta bincike. Allah shi ne shaidata Jabir ko kallon banza bai taɓa yi min ba. Ka yanke min ko wane irin hukunci ne na amince da shi.”

Jawaheer ta jero masa kalaman nan cikin kuka mai cin rai.

Mujaheed bai ce mata komai ba ya juya abinsa ya ɗauki aniyar sai ya gano waye yake yi masa hakan? Tabbas ya shaidi ɗan uwansa, haka zalika da Jabir ne da gaske babu dalilin da zai sa ya bar wata shaida ma bare har ya bari a kama shi. Dole akwai abinda ke shirin faruwa.

Tun daga wannan rana bai sake ganin Jabir ba, har aka yankewa Alhaji Musa hukuncin kisa, babu Jabir babu dalilinsa. Haka Mujaheed bai yi gigin kiransa ba, domin ya rasa a irin yanayin da yake ciki. Yasan dai ko alama zuciyarsa bata taɓa jin haushin Jabir ba, amma kuma yadda zuciyarsa take gaya masa Jabir yana son Jawaheer zuciyarsa ta kasa ƙaryata hakan.

Tsugunne yake a gaban mahaifinsa kamar yasa kuka haka yake ji, yana jin zuciyarsa tana ɗaci, sannu a hankali faɗan da mahaifinsa yake masa yana cigaba da tasiri a zuciyarsa.

“Ya zama dole kayi wa kanka faɗa Mujaheed. Wannan kamar kana son ka nunawa Allah ne bai isa ya jarabceka ba. Naylaa ta rasu, ta gama rayuwarta a duniya. Haka kaima ba kowa bane, baka fi ƙarfin Allah ya jarabceka ta hanyar ɗauke taka rayuwar ba. Mutuwar nan jiranta muke yi, daga ni har kai. Masu hankali suna rayuwa ne ba tare da sun saki jikin su a gidan duniya ba. Idan kana ji da girman kai, ka sauke, idan kana jin kai wani ne akwai wa’inda suka fika zama wanin, haka da zaka duba zuciyoyinsu gaba ɗaya cike suke da tsoron Allah. Ina sake baka shawara a matsayina na mahaifinka ka ɗauki duniyar da sauƙi ka rungumi ƙadddararka.”

Jinjina kai kawai ya yi, ba tare da bakinsa ya iya furta komai ba. Haka ya koma gidansa ransa babu daɗi. Ya rasa dalilin da yasa yake son ganin Jawaheer, ya rasa dalilin da Jawaheer take yi masa yawo akai, bayan manyan laifukan da ta aikata masa. Wani sa’in yana jin haushin zuciyarsa, da zarar ta tuno masa da Jawaheer.

Duk lokacin da zai dawo gida da ninyar ya ganta, sai ya ga babu ko alamunta a falon. Shi kuma yadda yake ji da kansa, ba zai iya zuwa ya dubata ba. Yana da lokacin zama ya yi tunaninta, amma kuma bashi da lokacin duba lafiyarta.

*****

Mai Gadinsa shi ne mutum na ƙarshe da zai hukunta, idan har za a iya shigo da Jabir har cikin gidansa, babu shakka ta ƙofar Gate ya kamata hakan ya faru. Ya zama dole da sanin mai gadi ake aikata hakan.

Yana zaune da zungureriyar Radio ɗinsa, ya ji andamƙo shi. A gigice ya ɗago da ninyar antaya ashar! Suna haɗa ido da Mujaheed ya haɗiye zagin, yana cigaba da zazzare idanu. Mujaheed ya yamutsa fuska,

“Bamagujen banza! Da zagina zaka yi? Da tsautsayi yasa ka zageni da sai na cire bakin nan. Muje Police station ka amsa min wasu tambayoyi.”

Sale Mai Gadi ya riƙe kansa da ƙarfi yana roƙon Mujaheed, amma ko kallonsa bai yi ba, ya cilla shi cikin mota.

Da girma da arziƙi yake yi masa tambayoyi, amma fir Sale ya nuna bai san komai ba. Hakan yasa ya bada umarnin a fara azabtar da shi.

Da wahala tayi wahala, ya soma cewa zai faɗa. Mujaheed ya yi murmushi yana cigaba da kallonsa,

“Na roƙeka da Allah ka gaya min gaskiya hakan ya gagara, amma cikin ikon Allah tsoron azabar duniya tasa zaka yi bayani. Masha Allah ina saurarenka.”

“Yallaɓai ka rufa min asiri. Wani mutum ne yake zuwa ya bani kuɗi, sai ya shigo gidan. Watarana ta sama yake haurowa.”

“Ba wannan na tambayeka ba, ya akayi aka shigo da Jabir cikin gidana?”

Mujaheed ya tambaya a cikin natsuwa, kamar bashi bane yake cikin halin damuwa.

“Yallaɓai, duk mutumin ne ya haɗa hakan. Ranar ni ya ba magani na zuba a cikin lemukan da ke frij, ta hanyar sirinji. Sai kuma suka sanya ni inyi ta zagaye ina gaya masu abubuwan da ake ciki. Daga bisani ya zo da yallaɓai Jabir suka kama shi su biyu suka shigar da shi har ciki. Iya abinda na sani kenan. Yauwa sai kuma daga baya wata mace ta zo, itama ta shiga. Sun ɗan jima sannan suka fito.”

Mujaheed ya jinjina kai. Yana dubansa.

“Kana son inyi maka haƙuri?”

“Ina so. Don Allah ka rufa min asiri kayi haƙuri.”

“Ok. Ka sake shirya yadda mutanen nan za su shigo gidana. Wannan ruwanka ne. Haka idan aka baka magani ruwanka ne ka ɓoye maganin ka ce ai ka sa. Idan na kama su su dukka, zan ƙyaleka.”

Mujaheed da kansa ya dawo da Sale gidansa, haka yasa C.I.D da su kula da shige da ficen kowa. Sale da ya yi yunƙurin guduwa, idan ya haɗa idanu da mahaukatan wanda yana sane da C.I.D ne sai ya saki yaƙe.

Cikin hukuncin Allah mutumin yazo ya kawo masa takarda ya ce ya miƙawa Mujaheed. Sale ya karkace kai ya ce, “Yau Jabir a gidan zai kwana, saboda ya ji labarin Mai gidan zai yi tafiya. Da alama dama can Jabir ɗin yana son Jawaheer ne.”

A take mutumin ya koma gefe ya yi waya zuwa can, ya dawo kusa da Sale ya ce, “Duk ranar da Mai gidan yake gida ka gaya mana akwai aikin da zamu baka.”

Baƙin ciki yasa Sale binsa da idanu kawai har ya wuce abinsa.

Duk wainar da ake toyawa Jawaheer tana ciki bata sani ba. Addu’a kawai ta duƙufa yi Allah ya gaggauta fitar da gaskiya kowa ya huta.

A ƙalla sai da aka kwashe kwana biyu, sannan mutumin ya sake dawowa. Wannan karon ma sirinji ya bashi akan ya tabbatar da ya zubawa mutanen gidan maganin barci. Hajiyar da kanta take son duk yadda za ayi, ta sami biyan buƙatunta agun mutumin da ya daɗe yana wahalar da ita.

Angama shirya komai, haka Mai gadi ya tabbatar masu da ya yi dukkan aikinsa sannan suka shigo gidan su biyu. Macen ita ce a gaba, sai namijin a baya. Sai da suka shiga tsakiyar falon, sannan suka ga haske ya gauraya falon. Gaba ɗaya suna neman gurin guduwa, hakan bai samu ba, domin ‘yan sanda ne suke kai masu duka ko ta ina. Mujaheed yasa ɗan makulli ya kulle ƙofar sannan ya zura idanunsa akan macen. Da mamaki yake dubanta, bakinsa gaza rufewa.

Ko alama bai taɓa kawowa aransa ita ce zata iya aikata hakan ba.

“Safina! Dama ke ce?”

A hankali ya ƙaraso wanda ya yi dai-dai da fitowar Jawaheer tana duban kowa cike da mamakin, dalilin kawo mutane haka a irin wannan lokacin? Zuba masu ido tayi tana neman ƙarin bayani.

“Eh nice. Ka yafe min Mujaheed, na soka so irin wanda ban taɓa jin ina yiwa wani mahaluƙi ba. Amma sai ka watsa min ƙasa a ido. Haka akan na iso wurinka a gaban Naylaa kayi min wulaƙancin da har in mutu ba zan manta ba. Kwatsam! Na ji labarin mutuwar Naylaa, a lokacin ne kuma nayi zaton zan cusa kaina gurinka, ƙila insamu shiga. Anan ma sai kayi ta wulaƙanta ni a gaban duk wanda kaso.”

Safina ta ɗago tana duban Mujaheed don son fahimtar a irin yanayin da yake ciki. Ta kuwa ci sa’an ita yake kallo. Sai dai mamaki ne shimfiɗe a fuskarsa.

Ta cigaba, “Daga nan kuma sai naji labarin ka auri Jawaheer. Duk da ansanar da ni baka sonta, haka nasha zuwa Office ɗinka sai inji hirarku da Jabir akan yadda ka tsaneta. A lokacinne idanuna suka rufe ina son ka rabu da Jawaheer ko ta halin ƙaƙa. Tashin farko Ummanka ta kawo Jawaheer asibitin mu, bata da lafiya. Bayan gwaje-gwaje da muka yi mata anan muka gane damuwa ce tayi mata yawa. A take na sauya takardar nace su koma gefe za ayi gwajin jini. Bayan anɗebi jininta ne, nasa aka buga result ɗin ƙarya akan tana ɗauke da ciki.”

Mujaheed da ya ji wani irin jiri yana ɗibansa, ya dafa bango yana salati. Jawaheer kuwa kukan farin ciki tasa, duk da ita kanta a lokacin da Doctor ɗinsa yazo ya ce zai dubata ta bashi haƙuri ta ce yaje ya yi masa bayani da baki. Ashe da tun a lokacin aka dubata da kowa ya gane bata ɗauke da komai cikin bogi ne. Safina ta cigaba da magana cikin kuka,

“Ka yafe min, dukkan makircin nan ni nake haɗa su da gudumawar mai gadinka. Haka duk lokacin da na turo wani a matsayin kwarto babu abinda suke aikatawa da matarka. Kawai ina yin hakanne saboda ka rabu da ita. Hatta Jabir a hotel ɗin da ya kama yana barci muka sato shi. Don Allah ka yafe min sonka ne ya jawo min aikata hakan.”

“Kai ku kwashe su ku fitar min da su daga gidana. Safina wannan ba so bane, ƙiyayya ce ƙarara. Ban taɓa jin inda soyayya tasa a azabtar da masoyi ba. Ku tafi kawai. Hatta mai gadina kada ku sarara masa.”

Haka aka kwashe su, suna kuka suna roƙo, amma ko dubansu bai yi ba. Shuru falon ya rage daga Jawaheer sai Mujaheed. Ya rasa da idanun da zai iya dubanta. Shessheƙan kukanta kawai ake ji a ɗakin. Ɗagowa ya yi da nufin ya rarrasheta, yana ɗagowa tasa kai aguje ta shige ɗakinta tana kuka.

Gabansa ne ya faɗi da ƙarfin gaske! Maganganun Jabir suka dawo masa kai. Ya zama dole gobe ya sanarwa iyayensa komai. Haka gobe zai kira Jabir ya zayyane masa dukkan abubuwan da suke faruwa.

Kusan a tsaye ya kwana. Haka Jawaheer kwana tayi tana godiya ga sarki Allah. Ta tabbata babu wanda ya isa ya warware mata dukkan matsalolinta inba shi ba.

Da sassafe ya nufi gidansu. Hakan yasa duk iyayen suka bi shi da kallo. A natse ya zayyane masu komai. Dukkan su suka yi shiru, aka rasa mai ƙarfin guiwar yin wani abu. Abba ya yi masa ‘yar nasiha ya ce ya koma ya ba matarsa haƙuri.

Da isarsa gida ya kira lambar Jabir amma baya samu, hakan yasa ya kira Umma yake tambayarta inda Jabir ɗin yake. Umma ta tabbatar masa da ya tafi wurin aiki.

A sanyaye ya ajiye wayar da nufin zai sake nemansa.

Jawaheer kuwa ji tayi gaba ɗaya Mujaheed ya fice mata a rai, don hakane ta kwatanta miƙewa da nufin barin masa gidan, kusan sau biyar, hakan yana gagara. Zama tayi ta rushe da kuka. Wanda ya yi dai-dai da shigowarsa. Da idanu ya raka ƙaton akwatin da ke yashe a ƙasan ɗakinta, har izuwa kan Hijabin da ke maƙale da jikinta. Wani abu ke fizgan sa, sai dai ko giyan wake yasha ba zai fara zubar da ƙimarsa agaban Jawaheer ba. Tsaf ya gama karantar ƙwayar idanunta abinda take nufi ya zo lallashinta ita kuma ta wulaƙanta shi. Yamutsa fuska ya yi, ya ce “Me ya hanaki tafiya? Naylaa ta rabu da ni a dai-dai lokacin da nake da buƙatarta, kuma na haƙura bare kuma ke? Tunda ban rasa rayuwata a lokacin da na rasata ba, bana jin don kema kin tafi zan sami damuwa. Kina iya tafiya.”

Ficewa ya yi da sauri, baya son ta gano rauninsa. Jawaheer ta durƙushe a wurin tana cigaba da kuka, ta tabbata ba zata taɓa samun soyayyar Mujaheed ba. Ya riga ya makance ason gawa. Shawarar Mahaifiyarta, ta ɗauka ta haɗa da na Jabir, taga duk tafiyarsu guda. Don haka zata gwada ta gani ko zata yi zarra a zuciyar mijinta.

Wanka ta faɗa a gaggauce, ta fito ta gyara zama a gaban madubi, ta fara ɗorawa kanta kwalliya, wanda rabon da tayi har ta soma mancewa. Gyara gashinta tayi, ta tubke shi a tsakiyar kai, sannan ta zari wata riga mara hannu da dogon wando ta zura. Ita kanta sai da tayi ta kallon kanta a madubi tana sake duba. Saisaita fuskarta tayi, a sakamakon rauni da ke kwance a fuskar. ‘Yar humra ta gogawa jikinta, sannan ta fito ta nufi kitchen ta ɗora ruwan zafi. Tana nan zaune tana kallon film, wanda bata sani ba ya daɗe tsaye a falon yana dubanta. Ƙirjinta ya fi komai ɗaukar hankalinsa. Tana juyo wa ya kauda kansa kamar bai taɓa ganinta ba. A gurguje ta miƙe tana faɗin, “Na shiga uku kada abinda nasa ya ƙone.”

Bin bayanta ya yi da kallo, ya zuba wa ƙugunta idanu, yana jin kamar da gayya take juya su. Rintse idonsa kawai ya yi yana nazarin yarinyar. Ganinta babu damuwa yasa ya cika da mamaki.

Yana nan tsaye yana kallon ikon Allah ta zo ta gabansa ta wuce tare da harɗewa abisa kujera tana kallo tana dariya. Fice wa kawai ya yi yana huci.

A office, a masallaci, a cikin mota, hoton Jawaheer ne manne da wuraren, tana tafiya cikin shigarta ta riga da wando. Ya kasa goge duk wani motsi nata da ya gani a yau. Haka ya ci burin ba zai taɓa kusanto inda take ba.

Yanzu ya yanke wa kansa shawarar ya daina zaman gida, kullum yana office cikin ayyuka. Haka ya karɓi duk wani case da ada ya kaucewa karɓarsa. Hakan ba ƙaramin faranta ran ogansa ya yi ba.

Mujaheed ya takura wa kansa babu ji babu gani, haka ya shirya ya taho Kaduna wurin Jabir, sun jima suna tattaunawa. Jabir ya nuna masa babu komai, dama shi damuwarsa ya dage da bincike kafin yanke hukunci.

Sannu a hankali damuwa suka fara samun matsugunni a zuciyarsa. Ya kullum yana jin idan bai haɗa ido da Jawaheer ba wani abin yana iya samunsa. Sai dai girman kansa ya wuce duk yadda yake tunani.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jawaheer 13Jawaheer 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×