Skip to content
Part 16 of 17 in the Series Jawaheer by Fatima Dan Borno

A can gidan su Jabir kuwa, Jawaheer ta haɗu da Zara, sai ya zamana tunaninta kaɗan ne, domin Zara akwai suturu, don hakane zaman ya ɗan yi mata daɗi.

Haka garin Allah ya waye Mujaheed ya kasa sanya komai a cikinsa. Da gaske yake jin wata zazzafar ƙaunar Jawaheer a zuciyarsa. Wannan shi ake kira da lamarin Allah. Baka isa ka gane me zai faru da kai gobe ba.

A cikin kwanaki biyu kacal ya sauya kamanninsa, haka ya rasa ina zai dosa? Har Jabir ya kira ya gaya wa, amma sai ya bi shi da addu’a.

Ita kuwa Jawaheer ganinta agun dangin Mujaheed, ya sanyaya mata rai, ta kwantar da hankalinta, haka tana cin abinci. A gefe guda kuma tana jin halin da Mujaheed yake ciki, ta gode Allah, domin a zahiri ba zata iya rabuwa da Mujaheed ba. Haka tana ji a zuciyarta kamar ta gudu ta je ta gaya masa ga inda ta ɓuya.

Sau tari takan ɓoye kanta ta sha kuka. Tana son Mujaheed, irin soyayyar da bata jin tana yi wa kanta. Tana son ta dauwama tare da shi.

Jin Mujaheed shuru, yasa Umma ta nufi gidan da ninyar ganin ko lafiya? Da isarta ta same shi kwance. Dai-dai da hannunsa baya iya ɗaga wa. Sosai hankalinta ya tashi tasa kuka tana neman taimako. Dole ta kira Abbansa suka ƙaraso a gaggauce aka ɗauke shi sai asibiti.

Bayan bincike da akayi mai tarin yawa, an gano jininsa ne ya yi mugun hawa. Umma ta shiga girgiza kai, tana duban Abba, “Kayi haƙuri Abban Naylaa, ba zan iya barin Mujaheed a cikin wani hali ba. Zan gaya masa gaskiyar inda matarsa take. Haba! Yaro duk ya lalace? Da wanne zai ji? Tunda yanzu kowa ya gane yana son matarsa a dawo masa da ita mana.”

Abba ya harareta, “Ɗanki shi ne ɗa, amma ɗan wasu ba ‘ya’ya bane ko? Har yanzu hankalina bai kwanta da nadamar Mujaheed ba, sai ya sake yin hankali. Nasan kafiya da taurin kai irin na Mujaheed. Don haka ban shirya dawo masa da Jawaheer ba.”

A fusace ta dubi mijinta, “Kana nufin har sai ya mutu sannan zaka gane nadamarsa?”

“Eh haka nake nufi. Kuma bana son Jawaheer tasan halin da Mujaheed yake ciki.”

Kawai ya juya ya fice abinsa.

Umma ta ci gaba da safa da marwa a tsakanin ɗakin Mujaheed da kuma harabar asibitin, ta rasa me ke mata daɗi. Mujaheed ta kafe da ido, a dawowarta na kusan biyar. Yana nan da haskensa, hancin nan ya ƙara fitowa.

Tsakanin uwa da ɗa sai Allah. Umma tasa hannu a goshinsa, da ya yi zafi sosai tana tofa masa addu’a. Hannunta ta kai ta kamo nasa tana magana cikin damuwa,

“Allah ya baka lafiya Mujaheed. Kayi haƙuri ka rage damuwa.”

Ware idanunsa ya yi, da suka yi masa nauyi yana duban mahaifiyarsa, “Umma ina Jawaheer? Ina jin damuwar rashinta. Ina jin ban yi wa iyayenta adalci ba. Ɓacewa tayi Umma.”

Mujaheed kenan, shi har yanzu bai amince yana son Jawaheer ba, haka bakinsa ya gaza furta abinda ke cikin zuciyarsa. Ita kanta uwar ta jinjinawa ƙarfin kafiya irin na Mujaheed, don haka ta gyara zama tana dubansa.

“Mujaheed. Meyasa ba zaka saki kafiyan nan ka fito ka ce ciwon son Jawaheer ne yake ɗawainiya da kai ba? Kasan halin mahaifinka, idan ya kula har yanzu baka son Jawaheer zai iya sawa a nemota, daga ƙarshe ya raba ku. Menene abin girman kai idan ka ce kana son Jawaheer? Bata kai matsayin a sota bane?”

Rufe ido ya yi, kalaman mahaifiyarsa babu wanda ba gaskiya ba ce, sai dai shi kansa ya rasa gane irin halinsa. Girgiza kai ya yi,

“Umma zuciyata Naylaa kaɗai take so. Jawaheer kuwa tausayinta nake ji. Ko tausayi yana daga alamomin so ne?”

Umma ta ce, “Ƙwarai kuwa, tausayi da so suna tafiya kafaɗa da kafaɗa ne, ta yadda ɗaya baya yuwuwa idan babu ɗaya.”

Shuru ya yi ba tare da ya sake furta komai ba. Har barci ya yi awon gaba da shi.

Wasa-wasa jikin Mujaheed sai ƙara rikicewa yake. Tun Abba yana ɗaukar abin kamar wasa har shima ya fara tsorata. Likitoci sun sami Abba sun bashi shawarar ya baiwa Mujaheed abinda yake so, idan ba haka ba abin zai ƙara nisa.

Dole Abba ya kira Baba Ma’aruf ya ce a taho da Jawaheer.

Jawaheer tana kwance a ɗaki, jikinta yana bata akwai matsala, don haka kwanaki biyun nan duk ta yi su ne a cikin kuka. Idan taga Zara sai ta share hawayenta.

Ta na ganin Umma ta shigo ta miƙe kawai tana dubanta. Tuni ta karaya sai ta hau kuka. “Umma wani abu yana faruwa ko? Gaya min mene ne?”

“Ki kwantar da hankalinki Jawaheer, Mujaheed ne baya ɗan jin daɗi zaki shirya ke da Jabir ku je gaishe shi.”

Kukan ya ƙwace mata da ƙarfin gaske, “Umma ko dai mutuwa ya yi ne ake ɓoye min?”

Umma ta jawota ta kwantar da ita a ƙirjinta tana bubbuga bayanta.

“Babu abinda ya same shi, bayan abinda na gaya maki. Maza jeki ki shirya kafin Jabir ya ƙaraso.”

Jiki asanyaye take shiri, ita da Zara babu abinda take son gani kamar mijinta. Ita kaɗai tasan wahalar da take sha.

*****

Da isowar su, suka haɗu da Umma ta fito daga ɗakinsa tana kuka, irin kukan da dole ya kashe wa mutum jiki. Jawaheer ta saki jakarta a ƙasa ta ci gaba da duban Umma, ba tare da ta sake ko da taku ɗaya ba.

“Ummana aboki ya rasu ko?”

Umma ta ɗago ta zuba mata ido, daga bisani ta ƙaraso gaban Jawaheer jikinta yana rawa, “Yauwa Jawaheer kin ƙaraso? Don Allah ki je ɗakin Mujaheed gayi can likitoci sun yi caaa akansa. Zamu iya rasa Mujaheed a ko wani irin lokaci.”

Jawaheer dai tsintar kanta tayi a ƙofar ɗakin da aka kwantar da Mujaheed. Haka bata san lokacin da ta ɗinga ture likitocin ba. Gaba ɗaya suka koma gefe suna dubanta.

Hannunta ta tura a cikin sumar kansa, tana shafawa har zuwa wuyansa. A saitin kunnenta tasa bakinta tana magana cikin sanyi da kuka.

“Aboki, kada kayi min haka, kada ka tafi ka barni. Idan ka mutu nima zan iya rasa zuciyata. Ka taimakeni ka tashi Umma da Abba suna da buƙatarka. Ka buɗe idanunka don Allah.”

Hawayenta suka cigaba da sauka a jikinsa. Shuru kowa ya yi, hatta su Abba da Umma da Jabir suna tsaye suna kallon ikon Allah. A hankali ya buɗe idanunsa ya zuba su akan na Jawaheer da ke dubansa.

“Jawaheer… Ina kika je kika bar iyayenki a cikin damuwa?”

Kama hannunsa tayi, tana murza su cike da farin ciki. “Aboki gani nan na dawo. Ka warke mu koma gida. Ba zan sake gudu ba nayi maka alƙawari.”

“Bani ruwa insha.”

A gaggauce ta miƙe, ko kafin ta ɗauko ruwan, ɗaya daga cikin nasis ɗin ta haɗa ruwan zafi ta miƙa mata. Ya yunƙura zai tashi, likitocin suka taimaka masa, tare da ɗora  masa filo a baya. Ita da kanta ta dinga ba shi a baki tana yi masa sannu.

Gaba ɗaya basu kula da wadanda suke tsaye a wurin ba. Zata sake bashi ya riƙe hannunta yana girgiza kai. “Ki barshi ya isheni. Ki daina kukan haka.”

Ajiyewa tayi  ta ci gaba da share hawayenta. Gaba ɗaya ɗakin akayi ajiyar zuciya. Likitan ya shiga tafa hannu, “Ashe mutumin soyayya ce take ɗawainiya da kai ka barmu muna ta ɓarnar magungunan mu?”

Gaba ɗaya ɗakin akayi dariya, Jawaheer ta duƙar da kai. Shi kuwa Mujaheed sai ya kirne fuska ba tare da ya ce uffan ba. Ya riga ya tabbata yana son Jawaheer, amma har yanzu kafaffiyar zuciyarsa tana gaya masa tausayinta kawai yake ji.

Umma ta dubi Abba, suka yi murmushi. Wanda sai yau suka shirya. Jabir ya ƙaraso kusa da shi yana kallonsa. Yadda Jabir ya kafe shi da ido yasa ya haɗa rai. Haushin kowa yake ji, don haka ya kwanta kawai yana kallon bango. Tunani kala kala ne birjik a cikin ƙwaƙwalwarsa. Ya rasa a wurin da ya kamata ya ajiye Jawaheer.

Kwanansa biyu aka sallame shi, don haka duk suka wuce gidansa. Kai tsaye Jawaheer ta haɗa masa ruwan wanka, mai zafi domin ya samu ya gasa jikinsa. Su Umma suka wuce gida, Zara kuma da Jabir suka koma Kaduna.

Bayan ya fito wankan ne, ya sa jallabiya suka fito falo ta koma kitchen. Cikin sauri ta haɗa masa kunun gyaɗa ya yi matuƙar jin daɗin kunun. Yana sha yana lumshe idanu.  Ita kuma tana zaune a ƙasa tana matsa masa ƙafafunsa da suka yi nauyi. Tsakaninta da shi babu wata hira, haka babu sakewa. Duk sai ta ji ta tsargu.

Ganin yadda ta koma kalar tausayi ne ya ajiye kofin ya kamota zuwa jikinsa. Gaba ɗaya suka saki ajiyar zuciya mai ƙarfi. Kowa da abinda yake saƙawa a ransa.

Sakinta ya yi yana jin kamar yana son aikata kuskure.

Da daddare bayan yasha magungunansa ya kwanta shuru. Yana jin motsinta, amma sai ya share kamar bai ji ba. Tana nan kwance a ƙasa, ta kasa barcin shima kuma ya kasa. A hankali ya kirawo sunanta, “Jawaheer zo ki ɗan matsa min ƙafafu.”

Mamaki ya kamata, don bata zaci idonsa biyu ba. Tashi tayi, ta ƙaraso tana matsa masa yana lumshe idanu. Hannunsa yasa ya jawota ta kwanta a gefen ƙirjinsa, “Jawaheer gaya min ina kika je?”

“Gidan Baba Ma’aruf naje. Duk su Abba sun san inda nake.”

Ajiyar zuciya ta sake ƙwace masa. “Kada ki sake fita babu izinin mijinki, duk da gidan dangina kika je. Babu kyau.”

Yadda yake mata salo ne yasa ta kasa bashi amsa. Jikinta ya ɗauki rawa ganin wasan ya sake sauya salo. Gaba ɗaya Mujaheed ya fita hayyacinsa, ya koma kamar ba Mujaheed ɗin da ta sani ba. Duk da shima ya kasa sakar mata dukkan soyayyarsa, haka jikinsa babu wani ƙarfi, amma sai da ya kauda budurcin Jawaheer a wannan daren, mai ɗauke da dumbin tarihi.

Kuka take yi, amma ya kasa sarara mata har sai da ya tabbatar da ya huce dukkan abubuwan da ya kwaso tun rasuwar Naylaa. A lokacin da ya dawo hayyacinsa ne kuma, ɓacin rai ya rufe shi ruf! Tsanar Jawaheer yana neman ya rufe tausayin da yake yawan furtawa. Sai dai kuma a yadda take da wayewa ya sha mamakin jinta a cikakkiyar budurwa. Tana ɗauke da wani sirrin tsafta wanda a wannan zamanin ba kowacce mace ce, zata da ce da hakan ba. Babu warin baki, babu datti a kunnenta, haka tana gyara hammatanta zuwa gabanta. A wannan zamanin yadda mata suka yi ƙaurin suna wajen barin wani abu mai ɗauke da wari a jikinsu, ita dai tayi matuƙar ƙoƙari wajen nunawa mijinta cikakkiyar mai tsafta ce ita. Hakan yasa ya tuna Naylaa ɗinsa. A tunaninsa ba zai ƙara samun mace mai ɗauke da wadannan abubuwan a jikinta ba, irin Naylaa ashe abin ba haka bane. Yana yawan jin mutane suna kushe wasu matan, akan irin warin da ke saurin gundurar ma’aurata ga junan su.

Yana son ya jawo ta ya lallasheta, amma kuma baya son ta ci gaba da shige masa. Baya son tayi tunanin matsayinta ya kai na Naylaa.

A wannan lokacin ya sami kiran waya ana nemansa a Office. Har zai ce gayi nan zuwa. Ya tuna da a irin lokacin nan ne ya fice daga gidansa aka kashe masa Naylaa. Kai tsaye ya basu amsa da ba zai iya ba, har yanzu jikinsa. Ƙunci da mutuwar jiki haɗi da mutuwar Naylaa suka haɗu suka yi masa katutu a zuciyarsa.

Ya kasa ko taɓa Jawaheer, ya kasa furta mata komai. Ita kuwa tana tunawa kamar ta taɓa sanin wannan ranar, kamar ta taɓa tsintar kanta a cikin wannan halin. Tana buƙatar kulawar mijinta a irin wannan dare mai matuƙar mahimmanci.

Kamar ya shiga zuciyarta ya ɗauke ta zuwa banɗaki ya dinga kai zuciyarsa nesa yana lallaɓata. A can ya barota ya ce tayi wankan tsarki. Kai tsaye falo ya wuce bayan ya sunkuci filonsa. Kwanciya ya yi shuru, yana tunanin abubuwan da za su faru anan gaba.

Tana fitowa ta ga wayam, hakan yasa ta fahimci abinda yake nufi. Ta kwantar da kanta akan gado tana rizgar kuka. Haƙiƙa ta kawo kanta wuri mai wahala. Kowacce ‘ya mace tana da irin tata ƙaddarar, daga cikin su akwai ƙaddara irin ta uwar miji, idan wasu ba su yi Sa’a ba, sai ka ga mace tana shan wahala. A cikin su akwai ƙaddara irin na halayyar namiji. Ga dai shi nan ke ɗaya ce agunsa, amma baki da ƙarfi ko ‘yanci a idanunsa. Wannan shi ne irin ƙaddarar Jawaheer. Babu kishiya, babu matsalar uwar miji. Amma kuma suna yin wani irin zama mai wahalar fahimta.

Kukanta ta sha sosai, kafin ta yi alwala ta shinfiɗa dadduma. A cikin sujjadarta tayi kuka, ta yi addu’a ta dinga yi wa Allah kirari tana roƙonsa samun mafita.

Shi kuwa Mujaheed yana nan kwance a falon, shi bai samu ya yi barcin ba, haka bai tashi ya kai kukansa gun sarki Allah ba. Wanda baya gori.

Haka suka kwana har taso ta makara. Tana tashi ta ga wayam! Har ya fice daga gidan. Miƙewa tayi da ƙyar ta shiga wanka ta gasa jikinta. Farfesu ta dafa da kanta, ta dawo falo tana ci tana jin kamar tana cin magani.

Sallama ta jiyo hakan yasa ta ɗago tana duban mai sallama. Sai da gabanta ya faɗi da ƙarfi, a take ta fara neman tsari da ita. Babu yabo babu fallasa ta karɓeta, ta tura mata farfesun suna ɗan taɓa hira. Ita kanta Suhaiman tana kallon yadda yanayin Jawaheer ɗin ya sauya. Duk suka yi shuru aka rasa wanda ke da ƙarfin halin furta wata magana.

Ana hakane Mujaheed ya dawo. Ganin Suhaima yasa shima ya ɗan sha jinin jikinsa. Kai tsaye ya tunkari Jawaheer ya kai hannu bisa wuyanta, “Sorry anyi min kiran gaggawa ne, hankalina yana kanki. Ya jikin?”

Zuciyar Jawaheer tayi sanyi, haka ta gode Allah. Ko a hakan ya barta ya gama mata komai. Langwaɓe wa tayi ta ce, “Da sauƙi.”

Sai a lokacin ya dubi Suhaima suka gaisa, sannan ya zauna yana ɓare magungunan da ya siya mata. Ya bata tasha. Yadda Suhaima taga yana rawar jiki da Jawaheer sai duk ta sake raina kanta. Kunya ta ci-gaba da kamata. Miƙewa ya yi ya ce, “Ki kula da kanki zan sake komawa.”

“A’a gaskiya kada ka sake fita.”

A gabanta ya haɗe hannayensa, “Ayi haƙuri, kin ga Suhaima ta zo zaki sami ‘yar hira kafin indawo. Allah nayi maki alƙawarin ba zan daɗe ba. Kin yarda?”

Suhaima ta yi dariya wanda iyakarta fuska. Jawaheer ta ce, “To idan zaka dawo ka siyo min Ice cream.”

Naylaa ta faɗo masa a rai, sai kawai ya danne yana murmushi ya fice yana ɗan waigenta.

Suhaima ta dawo da kallonta agun Jawaheer tana mamakin yaushe suka ƙulle haka? Tambaya ce cike da cikinta amma kuma babu damar yinta. Jawaheer ta kore shurun da cewa,

“Suhaima me nayi maki? Jarabawa tana kan kowa, Allah yana iya jarabtarki da abinda ya fi nawa. Idan ɗan’uwanka yana cikin wani hali, idan ba zaka iya yi masa addu’a ba, kada ka zamo na ɗaya ayi masa dariya. Ina amfanin zamowarki mai yaɗa sharri? Wace riba zaki ci? Wanda kika gaya wa suna dariya, kina juya baya ke ce ta biyu a cikin wacce zasu zaga. Idan kika kasance a rayuwarki babu mutumin da kike yabo, sai kanki watarana zaki wayi gari babu kowa a kusa da ke. Haka kina yi min dariya ina cikin matsala da mijina, yau gashi na fi kowacce mace sa’a agun mijin aure. Na ji ciwon abinda kika yi min, haka ba zan sake yarda da ke ba, ko damuwa zata kashe ni insha Allahu baki isa ki san komai nawa ba. Idan abun alkhairi ya sameni ƙila in iya gaya maki. Amma damuwata da ga yau damuwata ce.”

Suhaima ta ɗago asanyaye, “Kiyi haƙuri Jawaheer nayi kuskure. Kin riga kin yanke min hukunci ne, da sai in ce ki sake bani wata dama.”

Jawaheer ta amsa da cewa, “Ni na yafe maki duniya da lahira. Amma maganar sake baki dama, ya wuce kuma. Idan na sake baki dama nayi ganganci Suhaima. Mu ci gaba da zumuncin mu a matsayin ‘yan uwa. Ya Aliyu yana lafiya?”

Jawaheer ta rufe maganar da tambayar lafiyar Aliyu. Haka dai suka ɗan yi hira, Jawaheer ta ɗaga waya tana wayar ƙarya. Sai shagwaɓa take zuba wa, wanda a zahiri da iska take waya, ba Mujaheed ba.

Suhaima tayi mata sallama ta fice. Gulmar ta riga ta kama jikinta, ta zame mata ciwo wanda idan bata yi ba, bata taɓa samun sukuni. Bakinta ƙaiƙayi yake yi, tana da ciwon matsalar rashin barin gulma a cikinta. A take ta kira Rahma ta ce, “Ke Rahama cikina cike da gulma. Mutumiyarki fa anfaso gari. Miji sai nan nan yake da ita kamar ya goyata. Macen da ko kallo bata ishe shi ba, kina ganin haka kawai ne? Ko dai bariki kawai take son gwada min?”

Jawaheer tayi murmushi tana goge hawayen da suka sakko mata. “Ba Rahama kika kira ba, Jawaheer ce. Idan kika kashe ki duba lambar da kyau.” Sauke wayar tayi, tana lumshe idanu. Wato da ace ta yarda da zigansu akan zuwa gidan malamai, da tuni sun bada tabbacin gidan ‘yan tsubbu ta je kenan? Da rantsuwa za su dage suna yi, su ce ai su suka yi mata hanyar gidan malaman. Jawaheer ta dafe kanta kawai.

Ita kuwa Suhaima jikinta babu inda baya rawa. Tsoro sosai ya shige ta.
Mujaheed bai dawo gidan ba, sai can yamma. Yana shigowa ya sameta tayi tagumi. Ya sa hannu ya cire mata tagumin. “Me ya faru?”

A natse ta gaya masa komai. Har da lokacin da taje gidan malami, kuma ta kasa aiwatar da abinda suka zugata.  Shima shurun ya yi, sannan ya koma ya zauna. “Kada wannan ya dameki. Hassada taki ce. Haka babu wanda ba a zagi a duniya. Babu wanda ba a gulmarsa a duniya. Sai mun yi da gaske sannan zamu iya shiga Aljanna, domin da gulma kaɗai idan aka barka, ta isa ta hana bawa kwanciyar ƙabari, ta isa tasa kana ganin Aljanna amma tayi maka wahalar shiga. Maganar gidan malamai duk na san hakan, har gidan malamin na tura Jabir. Ki kwantar da hankalinki, ki taya ni addu’a. Malami bai isa ya yi maki abinda Allah bai rubuto maki ba. Haka asiri baya daɗewa yake warwarewa, a lokacin ne kuma zaki yi ta shan wahala, har ma ki ɗinga tunanin ko an sanya maki hannu ne a cikin lamuranki. Wanda a gaskiyar magana abinda kika shuka ne kike girbe kayanki.”

Yana maganar yana rage kayan jikinsa, ba tare da ya dubeta ba. Sai yanzu kuma ya tuna da Ice cream ɗinta, don haka ya miƙe ya ɗauko mata. Tana sha tana lumshe idanu. Ce mata ya yi ta miƙe ta zo gurinsa. Abinda bata sani ba tafiyarta yake son gani. Sosai ya ji mata ciwo, don haka ya ɗan rintse idanu, “Kiyi haƙuri na ji maki ciwo ko?” Shuru tayi tana rufe fuska.

*****

Mujaheed dai kamar mai ciwon aljanu. Kwata-kwata baya sakar mata fuska, ya daina kula ta. Idan suka gaisa shikenan kuma angama. Tun da suka yi kwanciyar aure har yanzu babu abinda ya sake shiga tsakanin su. Duk wani salo da ‘ya mace zata yi wa miji, Jawaheer ta aikata amma hankalinsa baya kanta. Tana yi wa sauran mata fatan kada Allah ya haɗa su da namiji mai kafiya irin Mujaheed.

Yau a gaban hoton Naylaa ya sameta tana gogewa tana magana, “Allah ya jiƙanki, yasa kin huta. Halayyarki na gari su biki. Mijinki yana wahalar da ni Naylaa. Ina shan wahala akansa. Ina gab da zuwa a cire min zuciyar nan ko zan sami sauƙi. Duk da ban taɓa ganinki ba, ina sonki Naylaa.”

Ta sumbaci hoton idanunta suna zubda ruwan hawaye, wanda ita kanta bata san da sakkowarsu ba. Da baya ya koma ya zauna kawai a kujera yana tuhumar kansa, da me Jawaheer ta kasa? Duk inda ake neman cikakkiyar mace Jawaheer ta kai. Ya rasa meke damunsa. Haka ko da wasa bai taɓa furta mata kalmar so ba. Kullum cewa yake yana tausayinta. Sau tari tausayin baya wani tasiri. Acan ƙasan zuciyarsa kuwa yasan yana jin wani abu mai kama da so, sai dai rashin kulawa yasa ya kasa baiwa abun mahimmanci.

Fitowa tayi tana ganinsa, ta ɗan durƙusa tayi masa sannu da zuwa. Babu yabo babu fallasa ya amsa mata. Abincinsa ta gabatar masa, ya ɗan ci kaɗan sannan ya miƙe ya shige ɗakinsa. Ta gyara ko ina, babu inda baya tashin ƙamshi. Tsaftar yarinyar kaɗai ya isa yasa a sota, bare akai ga ƙwarewa akan girki. Tana yi masa biyayya kamar ta kwanta a ƙasa ya taka ta, amma kuma ta gaza samo zuciyar mijinta.

Dole ta dage da tashin dare. Haka mahaifiyarta ta aiko mata da wata addu’a wacce ake yinta a ranar juma’a. Ƙarya ne ‘ya mace tayi wannan Sallar bata sami sauyi da girma a zuciyar mijinta ba. Kullum idan ta ce zata gwada yin addu’ar sai ta mance.

Yau ta tashi da zazzaɓi, tana kwance ya shigo. Yatsa yasa ya sa a goshinta ya ji zafi zau! Sosai ya gigice yana tambayarta ko lafiya? Ta bashi amsa da zazzaɓi take yi, amma kuma ta ji sauƙi.

“Me kika ci?”

“Ruwan tea.” Girgiza kansa ya yi,

“A’a Jawaheer ruwan tea ba abinci bane, ki daina hora kanki da yunwa.”

Da kansa ya sama mata abinda zata ci. Yana nan zaune akanta har barci ya kwashe ta. Duk ta rame.

Sallamar Umma ya ji hakan yasa ya fito yana gaidata. Wanda ya yi dai-dai da farkawan Jawaheer ta fito kawai ta rungume Umman. Sosai Umma ke dubanta, ta dawo da kallonta ga Mujaheed tana Salati.

“Mujahee ka ji tsoron Allah. Me kake yi wa Jawaheer ne haka duk ta lalace ta ƙare? Kana tuna mutuwarka kuwa? Kana sane da irin hakkin yarinyar nan da kake ɗauka? Zan ko haɗa ka da mahaifinka don babu ruwana.”

Mujaheed ya yi shuru kamar ruwa ya ci shi. Jawaheer ta ɗago tana duban Umman, ta ce “Lahh Umma baya yi min komai, bani da lafiya ne ma, yanzu ya kawo min abinci na ci.”

Umma ta ce, “Dalla matsa can, sokuwa. Kin zauna namiji yana ta wahalar da ke, har kina iya kare shi. Ni gafara ku bani waje.”

Umma ta nemi wuri ta zauna. Wannan karon lamarin Mujaheed ya koma bata tsoro. Kafiyansa ya wuce duk in da take tunani.

Ficewa ya yi daga gidan gaba ɗaya, hakan yasa Umma ta zauna tana bata shawarwari. Abinda Umma bata sani ba, duk Jawaheer tana kwatanta irin abubuwan da take gaya mata, sai dai kafaffen ɗanta ko a jikinsa.\

Daga ƙarshe Umma ta ce zata aiko mata da wasu magunguna, ta kuma gargaɗeta da ta dinga jan ajinta. Haka ta ƙara bata addu’ar wanda iri ɗaya da wanda mahaifiyarta ta bata. Jawaheer ta dinga jinjina yadda iyayensu suka san kan riƙe miji. Har ma sun fi ‘yan matan na yanzu. Tunda ‘yan matan yanzu ƙarya ce kawai tayi masu yawa. Amma babu abinda suka sani, sai iya shafa jan baki.

A daren juma’a ta gabatar da addu’ar nan, akan dadduma ta kwanta. Shi daman bai nemeta ba, har garin Allah ya waye ya sake ficewa. Umma da kanta ta kawo mata magunguna, ta rubuta mata yadda zata yi amfani da su, don ta kula kunyarta take ji.

Jawaheer bata yi sanya ba, tayi amfani da su, har da ƙarawa. Ta shiga ta tsalo wankanta ta turara kanta, ta zira ‘yar ƙaramar riga.

Sai da akayi Isha’i ya shigo da wani irin kewarta. Yana shigowa ta miƙe da kanta ta tarbe shi tare da mayar da kanta a ƙirjinsa. Sassanyar ƙamshi take fitarwa, hakan yasa ya jawota har ɗakinsa.

“Bani labari yau bayan bana nan me ya faru?”

Mamakin sauyawarsa kawai take yi. Farin ciki zata yi ko me? Sai dai kuma mijin nata baya dauwama a hakan. Yau farin ciki ne gobe baƙin rai. Amma kuma sauyin yau ya fita daban da sauran.

“Um, ka gani ko? Bayan baka nan sai na ji kamar inbiyoka.”

Shafar kumatunta ya yi, ya matso da fuskarsa, ya kama laɓɓanta yana bata zazzafar sumba. Yana buɗe idanun ya yi arba da hoton Naylaa kamar shi take kallo. Hakan yasa ya ɗan kauce yana ci gaba da cire kayansa.

“Kada ki damu, gani na dawo sai yadda kika yi da ni.”

Bai jira amsawarta ba, ya shige banɗaki ya yi wanka tare da alwala. Wannan ƙa’idarsa ce, kwanciya da alwala. Kashe wutan ɗakin ya yi, ya jawota jikinsa ya yi shuru, kamar mai nazarin wani abu. Jawaheer tayi amfani da irin tata basirar, ta maƙale ƙafafunsu wuri guda, ta dinga juya ƙafafun a cikin na juna, hakan ya taimaka wajen tado masa da tsohon tsuminsa. A wannan lokacin ne suka sake komawa wata duniyar a karo na biyu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jawaheer 15Jawaheer 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×