Skip to content

Jawaheer | Babi Na Shida

5
(2)

<< Previous

Suna hanya tana jin Mujaheed yana cewa babu shi babu Rukayya, ta dube shi, “Aboki meyasa? Naga tana sonka, nima ina sonta. Zan iya yin komai dan ka sameta kaji aboki?”

Hannunta ta miƙa masa, shima ya miƙa mata nasa sai duk suka yi murmushi. Kai tsaye Ice Cream ya siya mata, tana sha tana juya kai alamun daɗi.

Tana isowa gida ta nufi Umma ta sa mata cokali ɗaya a baki, sannan ta nufi Abba ta sa masa cokali biyu ta ce, “Tunda kai ne babba Abbana kai kasha biyu.”

Nayla bata da abokai da ya wuce mutane uku, Abba, Umma, da kuma Aboki Mujaheed. Idan tana jin nishaɗinta dole sai sun biye mata. Haka zata zauna tana buga Game da Mujaheed da gangar sai ya barta tayi ta cinyewa, Umma ita ce me rubuta maki ɗinta, Abba kuma me rubuta na Mujaheed. Idan kuwa tsautsayi yasa Mujaheed ya cinye, ta dosa ihu kenan tana faɗin wani abu ne ya faɗa mata a ido bata kula ba, har ya ci. Nayla ta taso cikin farin jinin mata da maza, duk wanda ya ganta sai ya ji soyayyar yarinyar a cikin zuciyarsa.

Ranar wata asabar ne ni da Mujaheed mun dawo daga training Nayla ta taremu a bakin ƙofa ta ɓare dabino ta sakawa Mujaheed a baki, sannan ta dubeni ido cikin ido ta ce, “Yaya Jabir ba zan baka ba, kai ma kaje Zarah ɗinku ta baka, ko Aboki?”

Murmushi kawai ya yi, mata sannan ya ce, “Ki shirya zaki rakani wajen biki.” Da zumuɗinta ta je tana shiryawa, kasancewar ita ce ƙawarsa duk inda zai je da ita yake zuwa.

A bakin falon Jabir ya ji munanan kalaman mahaifina akan Nayla, abinda bai taɓa ji ba, nima kuma bana wurin tuni na wuce inwatsa ruwa.

“Yaya a lokacin da zaka yanke shawarar aurar da Nayla ga Mujaheed sai da nayi ta roƙonka kada hakan ta faru, amma ka share ni. Tun yarinyar nan tana da shekaru goma sha uku ka aurar da ita ga ɗanka Mujaheed. Yarinyar da baku san asalinta ba. Abin nan da shi nake kwana da shi nake tashi.”

Mujaheed kawai ya buɗe labule, ya ƙaraso har gaban mahaifina ya shaƙe shi shaƙa ba na wasa ba, jikinsa yana kyarma, “Idan ka sake furta wannan kalaman Nayla ta ji, sai na zama ajalinka. Muddin Nayla tasan ba a cikin zuri’armu take ba, sai na kawo ƙarshen numfashinka a duniya.”

Abba da Umma suka yo kansa suna duka suna faɗin bashi da hankali ne? Nayla ce ta shigo falon ta kafe Mujaheed da ido, hakan yasa ya sassauta daga irin fushin da ya yi. Murmushi tayi, ta miƙa masa hannu ya miƙo mata. Kawai suka fice.

Basu sake waiwayar gida ba, suna can ana biki. Idan Mujaheed ya tashi yana jawabi, Nayla tana bayansa. Komai ita ke riƙe masa, haka idan zai zauna iya ke goge masa wurin zama. Kai duk wanda yasan Mujaheed to tare da Nayla yasan su.

Kwance take a cikin Garden ɗin tayi rigingine Mujaheed ya shigo ya zauna kusa da ita. “Sannu da zuwa aboki.” Ta furta haɗi da juyowa. Mamaki yasa shi buɗe baki da ninyar tambayarta yadda akayi tasan shi ne, tana ‘yar dariya ta ce, “Na haddace komai naka Aboki. Ni damuwata yanzu bani da lafiya kawo hannunka kaji wani abu.” Dai-dai saitin zuciyarta ta manna hannunsa, suka ɗan yi shuru. Yana jin yadda take bugawa da ƙarfi, amma sai ya girgiza kai, “Nidai ban ji komai ba. “Dariya kawai tayi, ta mayar da kanta jikinsa ta kwanta shuru.

“Friend wai ke baki da kishi ne?”

“Mene ne kuma kishi aboki? Kishin me zan yi?”

Shafa gashin kansa ya yi ya ce, “Share kawai. Wani fili nake son Abba ya bani akwai abinda nake son inyi, ya hana ni bansan ko zaki iya roƙo mana shi ba.”

Tashi tayi zaune ta ce, “Zo mu je ka gani.”

Babu musu ya bi bayanta suka fice sai falon Abba. Ta kamo hannun Abba ta marerece ta ce, “Abba me kake so inbaka yanzu?” Abba ya girgiza kai alamun babu komai. Ta dubi Mujaheed, “Aboki baka buƙatan wani abu da nafi so?”

Ya nuna mata sarƙar da shi da kansa ya siya mata, tana son sarƙar kamar ranta. Babu yadda Umma batayi ba ta cire sarƙar nan asiya mata wani amma fir ta ƙi. Abin mamaki sai suka ga ta cire ta miƙa masa. Ta sake cewa “Me kake so agun Abbana?”

Mujaheed ya ce, “Filin nan nake so ka bani Abba.”

Nayla ta dubi Abban ta ce, “To Abba ka taimaka ka bashi.”

Abba ya ce, “Zuwa kuka yi ku tsara ni? To bazan bayar ba.”

Nayla ta miƙe fuska a turɓune, Abba yasan hali tana iya yin zuciya, don haka ya ce “To shikenan na bashi filin.” Suka dubi juna tare da tafawa.

Idan na tsaya ina bada labarin Nayla da Mujaheed zamu iya kwana ba tare da mun gama ba. Ni kaina na taɓa shiga matsala, a ranar da nazo fitowa ban sani ba, muka ci karo har ta buge goshinta, tana taɓawa taga jini, kawai ta gigice da ihu tana faɗin jini jini. Ban ankare ba naji duka ko ta ina, Mujaheed bai barni ba, sai da ya ji ihun Nayla ya sake yawaita, sannan ya dawo gare ta. Tunda ya kama hannunta ya fice da ita babu wanda ya sake ganin su, sai bayan magriba.

Abba ya yi masa faɗa akan abinda ya yi min, daga baya ya sameni yana bani haƙuri. Muna dai-daitawa ya dubeni ya ce amma kada insake irin gangancin nan.

Abba da kansa ya buƙaci Mujaheed ya fara shirin ɗaukar matarsa. Sai a lokacin mu ma muka san Nayla matar Mujaheed ce, shiyasa ashe su Abba basu taɓa taka masu burki ba.

Tana zaune yazo ya sameta yasa hannunsa a bisa guiwowinta, “Nayla su Abba sun yi min kyauta me girma. Sun bani ke gaba ɗaya.”

Idanu ta zaro, “Daman ana kyautar mutum?”

“Eh kin zama matata. Kin ga yanzu zaki ɗinga kishina, zaki daina jin zafin da ƙirjinki yake maki. Zamu dauwama a cikin farin ciki, zan zauna mu haifi Muhibbat, in aurar da ita sannan ta haihu insake…”

Ganin ta rufe ido yayi murmushi ya miƙe yana jin kamar duk duniya babu me sa’a kamarsa. Mujaheed yana son Nayla, irin soyayyar da zai iya mutuwa idan bai sameta ba.

Cikin lokaci ƙanƙani muka fara shirin bikin tarewan Nayla, ita ko a jikinta tunda Mujaheed ɗinta yana tare da ita. Ana gobe za ayi dinner ya sameta a ɗaki ita kaɗai kamar mayya. Shigewa cikin bargonta ya yi, ya juyo da ita tana fuskantarsa. Duk abinda yake mata sam ta kasa yi masa musu. Kwantar da kanta tayi a ƙirjinsa tana magana a hankali,

“Aboki su Ummana sai nasiha suke yi min. Zamu rabu ne da su? Ni ba zan rabu da su ba.”

“Wa ya faɗa maki rabuwa zaku yi? Ɗayan gidan Abba zamu koma ni da ke, babu me damun mu. Kwana biyu zaki ɗinga leƙo Umma kuna hira. Ai nasan tunda ina kusa da ke baki da damuwa ko?”

Ɗaga kanta tayi, a lokaci guda ya haɗe bakin su wuri guda. Wani irin sanyi ya ratsa ta. Bata taɓa jin abinda take ji a wannan lokaci ba. Tana fatan su dawwama a wannan yanayi. Tana jin ƙirjinta yana sauya sauti.

A hankali take sake maƙale masa, hakan ya bashi daman sauya salon wasan, wanda yasa ta fara dawowa hayyacinta tana zare idanu. Ƙyaleta ya yi, ko a haka ta barshi ta faranta masa, zai kwana da farin cikin hakan a zuciyarsa.

Yana ficewa ta zauna tayi tagumi, idan ta tuna sai ta shafa laɓɓanta ta saki murmushi. Haka da ta kwanta ta kasa barcin tunanin Mujaheed ne fall a cikin zuciyarta. A hankali ta sakko daga kan gadon ta tsaya a windo tana jin nishaɗi yana shigarta. Komai Mujaheed ke koya mata.

Haka a nasa ɓangaren ya tsinci kansa a cikin wani yanayi me wahalar fassara. Ya yarda ya amince rayuwarsa ba zata taɓa cika ba idan babu Nayla. Komai yarinyar tayi yana burge shi.

Haka aka yi dinner Nayla ko a jikinta, ita dai Mujaheed shi ta riƙe, kuma yana kusa da ita dan haka bata damu ba. Idan taga abinda bata gane ba, shi take tambaya.

Sai da za a kaita ɗakin Mujaheed ne ta soma kuka tana faɗin babu me rabata da Ummanta da Abbanta. Duk yadda akayi dan a rarrasheta abin ya faskara. Umma ta ɗinga share hawaye kasancewar ba ƙaramar shaƙuwa suka yi ba. Dole aka kira Mujaheed ya ratsa mutanen ya sameta kuɗunɗune a jikin Umma ta riƙe ta ƙam tana kuka. Mujaheed ya kamo hannunta, ta ɗago cikin kuka, tana ganin Mujaheed ne ta miƙe. Da idanu kawai ya kalleta ta kama bin shi, tana yi tana waigen Umma. Ya damƙata a hannun Hajiyarmu ya fice abinsa.

Haka aka kai Nayla ɗakin Mujaheed, yadda tasha kuka yasa zazzaɓi me zafi ya kama ta, dole Mujaheed ya ɓuge da zaman jinya. A karo na farko ya fara tunanin ya maidowa Umma da Nayla, sai a gyara mata ɓangare ɗaya, ya zamana dai suna tare. Sai dai shawararsa bata karɓu ba, domin iyayen suna son Nayla ta koyi zama babu su ko da ta Allah ta kasance akan su.

Shaƙuwa me ƙarfi ta ƙara shiga tsakanin Nayla da Mujaheed, ta zama jakarsa, duk inda zai je da ita yake tafiya. Abu ɗaya ke damun Mujaheed da Nayla, shi ne yadda bata kishinsa, haka ya sha gwada karɓar hakkinsa, sai Nayla tasa masa kuka, hakan yasa ya ƙyaleta.

Ranar da Nayla ta fara ganin Mujaheed da giya da sigari, bata wani damu ba, amma ta tuna masa da maganar Abba, ya nuna mata Abba ba zai sani ba.

Watarana da sha’awa ta dame shi, kawai ya yi ta shanta, hakan yasa duk ya sauya. A wannan rana Nayla tana windo tsaye ta hango shigowar Umma, a firgice ta nufi ɗakinsa ta tallabo shi, “Aboki ga Ummana. Yau mun shiga uku ya zamu yi?”

Da sauri ta ɗauke kwalaban ta ɓoye, shi kansa sai ji ya yi ya wartsake. Jikinta babu inda baya rawa, kawai ta ɗauko turare ta fesa a ɗakin, ta ce ya kwanta ya rufe ido. Jin ɗakinsa yana warin abin, yasa ta taimaka masa ya koma ɗakinta ta rufe shi da bargo ta jawo ƙofarsa ta rufe.

Sai a lokacin ta buɗe ƙofar da Umma take ta faman bugu. Umma ta dubeta bata ce komai ba ta shige suka zauna suna ta hira. Ta tambayeta ina Mujaheed sai ta hau kame-kame.

Umma ta kafeta da ido kawai ta miƙe ta kama hanyar ɗakinsa, Nayla tayi maza ta ce, “Ummana barci yake yi yana ɗakina.”

Umma ta kafeta da idanu kafin ta wuce ɗakin Nayla. Ta kai hannu zata tashe shi, Nayla ta riƙe hannun tana girgiza kai cike da damuwa, “Ummana baya jin daɗi ne shiyasa ya samu ya kwanta. Kuma bai jima da yin barcin ba. Don Allah kada ki tashe shi.”

Umma ta juya kawai, hakannan bata yarda da Nayla ba, saboda tasan wacece Nayla farin sani, idan har tana irin kame-kamen nan to babu gaskiya a tare da ita.

Mujaheed yana zaune yana tunanin zuci, ya ji ankwara masa ruwa, hakan yasa ya juyo kawai yana dubanta. Ya kasa ƙwaƙƙwarar motsi, haka yadda take kwasar dariya yasa kawai ya zuba mata idanu.

“Nayla ruwa kika jiƙani da shi.”

Cikin dariya ta ce, “To naga ka tsaya ne shiyasa na zuba maka.”

Miƙewa ya yi kamar zai biyota, aikuwa ta ruga da gudun gaske. Mujaheed ya ɗinga nazarinta, zuciyarsa tana gaya masa bata sonsa so irin na soyayya, saboda bata kishinsa. A lokaci guda ya fara tunanin ya gwada ta.

Ƙarfe biyar na yammacin tana zaune tana rubutu, daga ita sai wata ‘yar riga mara nauyi, kanta babu ɗankwali, ya shigo tare da wata budurwa. Kallo ɗaya tayi masu ta ɗauke kai tana duban Mujaheed.

“Aboki kayi baƙuwa ce?”

Gira ya ɗaga mata, hakan yasa ta miƙe ta je ta kawo mata ruwa. Dubanta ya yi, ya ce, “Budurwa ta ce anan zata kwana.”

Nayla ta ƙarasa gabanta ta gama dubanta, sannan ta ɗago ta ɗaga masa gira alamun tayi. Mujaheed ya kafeta da ido ko zai ga wani sauyi, sai gani ya yi tana ta ji da budurwar. Daga ƙarshe ta ce,

“Idan kina son Aboki, zan so ki fiye da komai. Ina son me son aboki, bana son duk wanda zai ɓata masa.”

Ita kanta budurwar kallon mamaki kawai take yi mata. Haka yarinyar ta kwana a gidan, cikin dare ya miƙe yana sane da idonta biyu ya kama hanya da jinyar zuwa gun yarinyar, sai ji ya yi Nayla ta kamo hannunsa, “Aboki kaje wurinta, bana son tayi zuciya ta tafi, ta ɓata maka rai.”

Mujaheed ya dawo falo kawai ya zauna yana dogon tunani. Ya rasa ta yadda zai ɓullowa Nayla, ya rasa sai yaushe zai fara yin kuskure ta yarda wannan kuskure ne.

Da safe ta fito tsakar gida ta hango Umma tana ƙoƙarin shigowa, hakan yasa ta ruga da gudun gaske, tana tsoron dalilin da zai sa Umma tayi wa Mujaheed faɗa, don haka ta jawo hannun yarinyar ta ɓoyeta, sannan ta fito. Umma ta dubeta bayan sun gaisa, sannan ta dubi gyalen da ta gani a falon. Tun kafin Umman tayi magana Nayla ta hango gyalen, suka dubi juna da Mujaheed gaba ɗaya suka yi tsuru-tsuru. Kafin Mujaheed yasan abin yi, Nayla tayi carab ta ce, “Ummana kada ki tambayi gyalen nan, ƙawata Shema’u ce ta zo jiya ta ɗauki Hijabina ta bar min gyalen.”

Umma ta ɗinga yi mata faɗa akan bata son ƙawaye, ta rabu da harkar ƙawa. Nayla dai tana zaune gaban Umma har ta gama faɗan sannan ta haɗa da yi mata nasiha. Mujaheed ya kafeta da ido, yana tunanin wannan so ne ko kuwa yarinta?

Umma tana tafiya ya ce wa yarinyar ta zo ta tafi. Nayla har da su rakiya.

Yana kwance a ƙafafunta yana latsa waya, aka kira shi, taga lambar ansa Babyna. Bata ce komai ba, ya ɗauka tare da buɗe Muryar wayar.

“Jiya baka zo ba nayi fushi da kai.”

Nayla ta ware ido tana jin takaicin meyasa za ayi fushi da Mujaheed? Kawai ta karɓe wayar, “Kiyi haƙuri budurwar Aboki yau zai zo kada kiyi min fushi da shi don Allah.”

Mujaheed ya karɓe wayar ya kashe, kamar zai sake tambayarta ko bata da kishi ne? Sai kuma kawai ya share. Aikuwa ta dame shi da mitan sai ya kirata ta bata haƙuri, ya yi mata banza.

Ranar da Mujaheed ya yi wani ciwo ne, Dakta ya yi ta masa magana akan abinda yake sha, yana da illa, yasa bayan ficewar Daktan ta kasa jurewa kawai tasa kuka. Ta rungume shi tsam a jikinta, “Kayi haƙuri ka daina sha, tunda zai yi maka illa. Bana son wani abu ya taɓa min kai kaji aboki? Kayi min alƙawarin ka daina sha.”

Baya jin akwai wani abu da Nayla zata nema agunsa ya kasa yi mata, don haka ya ce, “Nayi maki alƙawari daga yau na bar komai.”

Hankalinta ya kwanta sosai, tun a ranar tasawa ranta Mujaheed ya daina shan duk abubuwan da yake sha. Wanda a zuciyarsa haka abin yake.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×