Skip to content
Part 8 of 17 in the Series Jawaheer by Fatima Dan Borno

 Jawaheer ta ɗago a razane cikin kuka, harda shessheƙa ta dubi yadda Jabir idonsa suka sauya saboda kuka, ta ce”Sun kashe Nayla? Nayla ta mutu?”

Gyaɗa kansa kawai ya yi, ya cigaba, “A lokacin ne muka ƙaraso, kowa ya kalli gawan Nayla baya iya sake kallo. ‘Yan sanda suka ɗauki Mujaheed da Umma aka nufi asibiti da su, itama Nayla aka ɗauki gawanta da nufin aje asibiti ayi bincike. Abba ya girgiza kai, “Ku ajiye min gawanta zan suturta ta inkaita makwancinta. Tunda baku iya ganota tun a jiya ba, haka baku ganta a lokacin da aka sakota a mota aka kawo ta nan ba, bana jin ko wata zan bar maku gawanta zaku iya gano wanda ya yi aikin nan. Ko zan yi yawo babu kaya ne, sai na gano wanda ya yi min yankan ƙaunar nan.”

Abba yana gama bayaninsa, ya ɗauki Nayla ya rungumeta a ƙirjinsa ya kama hanyar shigowa gida da ita. Almajirai suka cika gidan suna kuka, haka yara ƙanana suma kukan suke yi. Abba ya dubi ɗan sanda ɗaya ya ce “maza kuje ku duba idan sun farka a dawo min da su. Mujaheed yazo ya yi wa matarsa addu’a.”

Haka ya miƙa ta, gun Hajiyarmu ta jagoranci yi wa Nayla wanka. Kisan da akayiwa Nayla kisa ne na wulakanci. Ana nan zaune sai ga Mujaheed da ya zabge a lokaci guda. Tabbas Nayla ta mutu, ga mutane yana gani ko ta ina, shi kaɗai ake kallo ana girgiza kai. Umma ta ƙarasa gaban Abba tana zare idanu, “Nayla ta mutu? Da gaske Nayla ta mutu?”

Abba ya kamo hannunta ya ce, “Nayla ta mutu. Addu’arki take buƙata. Mujaheed jeka kayi wa Nayla addu’a. Kayi tawakkali. Allah shi ya bamu ita a lokacin da bamu zata ba, ya kuma karɓe kayansa. Mujaheed kada kayi fushi da yin Allah. Nayla ta ƙosa mu kaita gidanta, angama shiryata kayi maza kayi mata addu’a. Hajiya ku shiga.”

Mujaheed ya kama hanya ya buɗe labulen ɗakin da aka shimfiɗeta cikin likafani.

“Ba zaka mutu ba sai mun haifi Muhibbat, ita kuma Muhibbat ta haihu sai ka aurar da ‘yarta ko Aboki?”

“Allah ka raya min Muhibbat ɗina, mu haifeta a Aljannah. Aboki muje inzagaya gidana. Ummana zan yi tafiya me nisaaaaa…”

Tabbas Nayla tayi tafiya me nisa, tafiyar da har abada ba zata dawo ba.

A gaban gawan ya durƙusa ya buɗe fuskarta. Fuskar nan ta ƙara haske da annuri. Kamar a kirata ta amsa.

“Kin ce zamu rayu tare Nayla, meyasa kika tafi kika barni? Kin ce sai na jiraki a duniya, ashe ba da gaske kike ba? Nace ki biyo ni mu tafi Nayla, ashe shirin barina kike? Ki taimakeni ki dawo mu shirya sabuwar rayuwa. Nayla ke kaɗai ce macen da na so, daga kanki babu wata.”

Ɗuƙowa ya yi sosai saitin fuskarta, yana addu’a. Tun yana iya gane me yake karantawa har ya koma karanto shirme. Wasu hawaye masu zafi suka zubo masa, sai a lokacin ya samu ya ɗan ji sauƙi.

“Nayla idan mafarki nake yi don Allah ki tashe ni, kada ki bari su sa min ke a rami don Allah Nayla.”

“Kada ka tafi ka barni Aboki, dawo kaji wata magana.”

Kalamanta suke yi masa wani irin kuuuwaa. Da ƙarfi ya riƙe kunnensa yana salati. Kasa miƙewa ya yi, sai ji yayi Baba Ma’aruf ya ɗago shi. Har sun kai bakin ƙofa ya waiwayo, “Allah ya jiƙanki Nayla. Sai nazo. Sai nazo Nayla. Allah ya jiƙanki.”

Da ƙyar yake jawo numfashinsa. Ummansa ya gani a gabansa ta ci kwalarsa da ƙarfi, “Mujaheedu da gaske ne Nayla ta rasu? Innalillahi wa inna ilaihirraji un. Kai jama’a ku ƙaryata wannan labarin, ku ce min ƙarya ne, Nayla da muke tare da ita jiya ba ita ba ce ta rasu. Ashe shiyasa kika rungume ni kika ƙi sakina? Allah ya jiƙanki Nayla.”

Anan gida ya sake rikicewa da kuka. Yana kallo aka janye Ummansa. Duban almajiran ya yi, siririyar muryata ta daki dodon kunnensa,

“Kai ku tsaya zan ba kowa, idan kuna faɗa zan fasa baku inyi shigewata.”

Shafa kan wani almajiri ya yi da yafi kowa kuka a wurinYa girgiza kansa. Buta ya karɓa ya ajiye a gabansa. Shi bai yi alwalan ba, shi bai tashi ba. Yana jin yadda ake ta koke-koke. Kawai ya kama yin alwalan. Yana zaune ya ji ana faɗin, “Allahu akbar!”

Hakan yasa kowa ya miƙe ana binta da addu’a. Yana nan zaune yaga anfito da makara. Shuru ya yi ya tsurawa makaran idanu. Jiya iyawar haka idonta biyu, a irin wannan lokacinne ta tashe shi tayi mafarki.

Miƙewa ya yi, da ƙwarin guiwa suka sallaci gawan. Gani ya yi anɗauki makaran za a fice da ita. Sai a lokacin ya ji duk wani ƙarfin guiwa ya ƙare masa. Hannu yasa ya riƙe makaran. Abba yasa kuka yana girgiza kai, “Mujaheedu kayi haƙuri ka bari akai Nayla gidanta na gaskiya. Wannan ne kaɗai ƙaunar da zaka nuna mata. Yi haƙuri ka bari a tafi da ita.”

Mujaheed ya girgiza kai, “Abba matata bata mutu ba, babu me tafiyar min da matata. Abba idan suka tafi da ita nima mutuwa zanyi. Nayla tayi min alƙawarin zamu zauna tare. Don Allah Abba kada ku raba ni da matata.”

Wuri ya sake gocewa da sabon kuka. Mutuwa kenan sam sam bata da sabo. Mujaheed yana nan riƙe da makaran ya ƙi saki, haka aka haɗu ana bashi baki, kawai ya saki. Yana tsaye yana kallo aka fice da ita. Hannunsa ya miƙa yana son yin magana, amma ta gagara fitowa. Kawai ya zube ƙasa a sume. Umma ta fito da gudu tayi kansa tana kuka tana jijjiga shi. Da ƙyar aka ƙwace Umma daga jikinsa. Mu muka ɗauki Jabir muka maida shi asibiti.

Har akayi ukun Nayla Mujaheed bai farfaɗo ba. A lokacin duk sun koma yiwa Nayla addu’a. Mujaheed yana farfaɗowa da sunan Nayla a bakinsa ya farfaɗo. Ya sake komawa. Tun daga nan sai dai aga yana numfashi, amma babu magana. A haka ya shafe fiye da sati biyu a cikin wannan halin. Hakan yasa iyayen suka yanke shawarar dawo da shi gida.

A hankali ya koma yana buɗe idanun, amma kuma baya magana. Sai dai a ganshi ya ƙurawa wuri ɗaya idanu. Duk wani masoyin Mujaheed idan ya ganshi a cikin irin halin nan sai ya yi masa kuka.

Ya yi baƙi ya rame, idan muka zo duba shi da kuka muke fita. Kullum addu’a ake yi masa da sauƙar Ƙur’ani. Gidansu ya koma gidan kurame. Kusan kullum sai almajiran nan sun taru sun zo gidan sun gaida Abba. Gaba ɗaya aka cire hotunan Nayla a ɗakin da Mujaheed yake zama, saboda sau tari sai dai aga ya kafe Nayla da idanu, sai kuma ya rufe idanun.

Sannu a hankali Mujaheed yake samun sauƙi, sai dai magana bata dame shi ba, ya koma asalin miskili. Har ya fara tashi yana yin abubuwa da kansa. Sauƙi ya cigaba da samuwa. Ya tsani komai, baya son ganin kowa a kusa da shi. Ya fi son zaman kaɗaici fiye da a matso kusa da shi.

Da nasiha da rarrashi ya koma bakin aikinsa, amma kuma babu me iya tunkararsa. Kullum burinsa ya gano waye ya yi masa wannan yankan ƙaunar? Mahaifinsa yasa kuɗaɗe masu tsoka ga duk wanda ya gano wa’inda suka kashe masa ‘ya. Shiyasa a lokacin hotunanta suka yi ta yawo a jaridu, amma har yanzu shiru. Da nace maki zan kai ki wajen Nayla kuwa, Ƙabarinta zan kai ki, kamar yadda Mujaheed yake yawan kai kansa wurin yana mata addu’a, haka kema zan kai ki can idan kina da buƙata. Haka kuma sai naga halayyarki da na Nayla suna matukar kama, har shi kansa Mujaheed ya ga hakan.”

Miƙewa tayi tana kuka tana ja da baya. “Nayla bata mutu ba, Nayla tana nan da rai. Innalillahi wa inna ilaihirraji’un. Mujaheed ka yafe min. Ka kaini wajen Mujaheed innemi gafararsa. Nayla ɗinsa sunan ta mutu ne amma Walh tana raye.”

Jabir ya dubeta, ya je frij ya ɗibo mat ruwa, ta karɓe ta shanye tass. “Ki natsu kiyi min magana ta yadda zan gane. Da hannayen mahaifina ya saka Nayla a ƙabari. Meyasa zaki ce bata mutu ba? Kin santa ne?”

Girgiza kai tayi jikinta yana rawa, “Ban taɓa ganinta ba. Shekaru huɗu da suka wuce nayi fama da ciwon zuciya, da aka tabbatar da zan iya mutuwa idan ba ayi min dashen zuci ba. A wancan lokacin iyayena basu da burin da ya wuce su ganni ina rayuwa. Duk inda za a sami zuciyar da za a dasa min anyi amma babu. Anan ne abokinsa Alhaji Musa ya buƙaci kuɗaɗe masu yawa agun Abbana ya ce zai kawo masa zuciya, zai nemo wacce bata jima da mutuwa ba, kuma me ƙananun shekaru irin nawa. Dad bai da burin da ya wuce ganina a raye. Ya amince ya haɗa shi da Doctor ɗina.

Ba asan yadda akayi ba ya samo gawan Nayla, aka cire zuciyarta aka sa min. Nayla ta mutu ne kawai, amma a zahiri tana raye, tunda zuciyarta ita ce ita. Sai daga baya ne da naga abubuwan nan sun yi yawa na zagaya na tambayi Alhaji Musa shi yake gaya min zuciyar wata budurwa ce. Amma bai gaya min shi ya yi kisan ba. Sai yanzu na gane dalilin da yasa ya kashe Nayla. Innalillahi wa inna ilaihirraji un. Na shiga uku ni Jawaheer.”

Jabir ya dubeta cike da mamaki. Tirƙashi! Ta yaya zai iya tunkarar Mujaheed da wannan maganar?

Abinda basu sani ba, Mujaheed ya jima tsaye a bakin ƙofar, a kunnensa yake jin dukkan abinda ke faruwa. Mutuwar Nayla ta dawo masa sabo fil! Bai taɓa jin tsanar wata halitta ba, kamar yadda yake jin na Jawaheer a yanzu. A dalilinta aka raba Nayla da rayuwarta saboda a ceto tata rayuwan. Ɗakin ya shigo sai ganinsa suka yi tsaye. Damƙota ya yi ya shaƙeta, idanunta suka firfito, “Kun raba ni da farin cikina saboda a ceto rayuwarki? Dan ubanki wa ya gaya maki irin ku ake so a duniyar? Yau sai kin mutu. Sai na kasheki kafin inje inkashe Musa, yau ba zaku kwana a duniyar nan ba.”

Da ƙyar Jabir ya ƙwaceta daga hannunsa, don har ta fara jin ƙamshin ƙabari, “Mujaheed ka dawo hankalinka! Ita ina ruwanta? Meyasa kake da zafin zuciya ne haka? A lokacin da aka dasa mata zuciya bata sani ba, ba ita ce tace a sa mata zuciyar matarka ba.”

Wani mahaukacin mari Mujaheed ya ɗauke Jabir da shi, kafin ya dawo hayyacinsa, ya sake fizgo Jawaheer ya ɗinga dukanta kamar an aiko masa da jaka. Nan da nan bakinta ya fashe, hannunta ya yi targaɗe, tana nan zaune ta ƙi neman hanyar guduwa, shi kuma ya ƙi ya sarara mata. Mujaheed da yaga hakan ba zai samar masa da natsuwa ba ya ce, “Ki tattara kayanki ki bar min gidana na…” Jabir ya ci kwalar rigarsa ya ɗaga hannu da nufin marinsa, Mujaheed ya riƙe hannun, suna yi wa juna wani irin kallo. “Idan ka sake ka saki Jawaheer sai kayi danasani. Jawaheer dole ta amsa sunan Nayla tunda daman zuciyar Nayla kake so kuma gashi Allah ya bar maka. Jawaheer bata aikata laifin komai ba, kada ka ɗauki haƙƙinta.”

Mujaheed ya fizge kansa yana duban Jabir, “Ka bani mamaki, a zatona kai ne zaka fara ɗaukar mataki akan duk wanda yake da hannu a kashe min Nayla. Sai gashi yau kai kake roƙona inƙyale mutanen da suka raba ni da Nayla. Don son zuciya ma suka ƙi ƙyaleta ta ji da zafin ɗaukar rai, suka cire zuciyar da ke jikinta aka baiwa wannan shashashan, ‘yar gidan marasa tarbiyya. Wacce addinin ma ba wai ya isheta bane. Suka sa min ciwo, irin wanda har abada ba zai taɓa barina ba. Har gobe ji nake kamar yau aka raba ni da Nayla. Sai na koyawa Musa hankali. Wallahi sai Musa ya baƙunci lahira. Sai ya ji irin azaban da Nayla ta ji. Daga ƙarshe na tsaneki bari ingama da shi, kema sai nasan yadda zan yi da ke. Dole a cire zuciyar nan koda kuwa hakan yana nufin rasa ranki ne.”

Cikin matsananciyar kuka take magana, “Nima na tsani kaina, ashirye nake da na amince a cire zuciyar nan, babu abinda sa zuciyar nan ta haifar min sai ciwon rai. Kullum cikin wahala nake yi. Ada zuciyata babu soyayya, amma a yanzu son mutum ɗaya ne a cikinsa. Ka bani tausayi Mujaheed, na cancanci ko wani irin cin mutuncinka. Don Allah ka fara kashe ni kafin ka kashe Alhaji Musa.”

Harara ya sakar mata yana jin ɓacin rai na ƙara kama shi, “Kafin indawo ki sagale kanki ki mutu ne, anan zan gane da gaske kin tsani kanki. Ki wuce gidanku kafin indawo bana son inbuɗe idanuna insake ganinki.

Bindigarsa ya koma ya ɗauko yana shafata. Ya yi rantsuwa da yau sai ya ɗauke ran Alhaji Musa da bindigar nan. Jikinsa na rawa ya fice, hakan yasa Jabir mara masa baya. Kafin ya fita sai da ya gargaɗi Jawaheer da kada ta tafi ko ina. Suna ficewa ta ɗora hannu akai tana cigaba da kuka. Tausayin Nayla kaɗai ke sake hargitsa ta. Tana jin ba ayiwa Mujaheed adalci ba. Tana ji da tana da dama da taje ƙabarin  Nayla ta fiddota ta maida mata da zuciyarta. Can ƙarshen gado ta je ta manne da lungun gado tana jin wani sanyi na shigarta alamun zazzaɓi. Haƙoranta sai karo suke ci da juna. Tana danasanin matsawa dole sai ta ji wacece Nayla, sai gashi babu abinda hakan ya haifar mata sai tsantsar nadama. Ita ta sani, har abada Mujaheed ba zai taɓa kallonta da haske ba. Indai irin soyayyar da ake faɗi da gaske ne yake mata. Ta jinjina ƙarfin shaƙuwa irin nasu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jawaheer 7Jawaheer 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×