Skip to content
Part 7 of 10 in the Series Jini Ba Ya Maganin Kishirwa by qurratulayn

Karima ta yi ‘yar gajeriyar dariya tana mai gyara zamanta sosai, kafin ta janye mayafinta ta ajiye kan gadon tare da duban Sakinah ta fara magana da faɗin.

“Ka da ki yi min mummunar fahimta, ba fa tashi tsaye na zuwa wajen malamai na ke nufi ba.”

“To ina jinki,” cewar Sakinah da ta kafe Karima da ma daidaitan idanuwanta.

“Gaskiya ki dage da addu’a sosai Sakinah, duk da na sanki ba baya ba, amma ki ƙara dagewa fiye da yanda na sanki a da, ki kuma dinga janyo Kamal a jiki tare da tausarsa a hankali har ya amince da batun aikin, ko ya ki ka gani?”

“Haka ne Karima zan yi ƙoƙarin ganin na jarraba shawararki, Kamal ne akwai shi da wuyar sha’ani sosai wallahi.”

“Nasan da hakan Sakinah amma ki sanya Allah cikin lamuranki da sannu komai zai zamto mai sauƙi cikin sauƙi.”

“Allah ya sa.”

“Amin ya Allah.”

Nan dai suka ajiye zance gefe, tare suka dawo cikin falon suna masu cigaba da aikin kasancewar lokaci na shirin tafiya.

Suna tsaka da aikin Zainu ya iso tare da motar kayan furniture da ma’aikatan da zasu jera, kai tsaye shashin Sakinah suka dinga shigewa da kayan kafin da ga baya suka fara kiciniyar jera su yanda ya kamata.

Sai daf da maghriba suka samu kammalawa gidan ya yi kyau gwanin ban sha’awa sai tashin ƙamshin fenti tsakar gidan ke yi da na turaren wutar da suka kukkunna.

Sai da masu aikin suka ci suka koshi sannan suka yi haramar tafiya, Sakinah ta damƙawa Zainu list na kayan kitchen din kamar yanda Yayan nasu ya buƙata, ya bata tabbacin zuwa safiya insha Allah zai aiko mata da komai, suka yi musu sallama suka tafi.

Dukkan su haramar wanka suka yi, kasancewar gidan madaidaicin gida ne, amma ya na dauke da wada tattun ɗakuna kuma ko wanne yana ɗauke da banɗaki shi yasa ma babu wanda ya tsaya jiran fitowar wani.

Sakinah sashinta ta nufa tun daga falo ta fara zubawa Yayanta godiya akan irin dukiyar da ya kashe ba tare da zatonta ba bare yin tsammani.

Ana kiraye-kirayen sallar maghriba Sakinah ta fito daga wankan da ya ke ta ɗauro alwalarta sai da ta gabatar da sallar sannan ta koma gaban mudubi tana shafe-shafenta.

Sun shirya tsaf kai tsaye falon Hajiya suka sake hallara dukkansu har Karimah da ke har lokacin Jabeer bai zo ɗaukanta ba, haka ma Kamal tun safe da ya fice har lokacin bai dawo ba.

Sakinah ta gabatar musu da abinci, da ya ke sunyi dabara suna aikin gidan suna girki shiyasa suka samu sauƙi yanzu, haka suka zauna suka cin abincin cikin nishadi da walwala tare da hira jefi-jefi, Hajiyama da ke gefe guda tana ɗan sanyo musu baki a hirarsu idan ta kama.

*****

Kamal bayan fitarsa kai tsaye gidansu Zayyad ya nufa ya same shi kwance a cikin ɗakinsa yana aikin karatu, neman guri ya yi ya zauna yana mai ajiye ledar katinan ɗaurin auren a gefe tare da faɗin.

“Ka yi hakuri mutumina, ta so dan Allah muje rabon katin nan.”

Zayyad banza ya yi da shi tun ba yan da ya shigo ya amsa masa sallama bai kuma tanka masa ba, sallamar ma dan ta zama dole ne da ba zai amsa ba.

“Haba mutumina dan Allah fa na ce, magana fa na ke yi maka, kasan dai ba ni da wani amini da ya kai ka ko?”

Kamal ya sake magana a karo na biyu tare da riƙo hannun Zayyad cike da magiya, Zayyad ya janye hannunsa kafin ya rufe littafin da ya ke dubawa ya tashi zaune yana mai duban Kamal sosai kafin ya fara magana da faɗin.

“Kasan ba ka da amini da ya wuce ni amma baka jin shawararta Kamal, mene yasa? Mene matsalarka? Me ka nema ka rasa a rayuwarka?”

“Ban rasa komai ba Zayyad, amma dan Allah kabar tuna baya da abin da ya riga ya wuce, yanzu lokaci ne ƙurarre ke garemu ya kamata mu tunkari abin da yake gabanmu kafin lokacin ya yi gaggawar kufce mana.”

“Wato kai dai na gama fahimtar ka a halin yanzu ko kaɗan baka son gaskiya Kamal”.

“Dan Allah tashi muje, wannan maganar ma yi ta daga baya Please.”

Zayyad ya jingina kai kawai cike da mamaki da al’ajabi kafin ya ce.

“Amma dai ka bari na shirya ko?”

“To na ji shirya ina jiranka.”

Nan dai ya azalzali Zayyad akan dole suka tafi rabon katunan bikin duk da cewar ba so yake ba, amma babu yanda ya iya Kamal abokinsa ne kuma amini babu yanda za’ayi hannunka ya ruɓe ka yanke ka yar, dole sai dai ka yi jinyarsa tare da nema masa magani wata rana Allah zai sa a dace, kamar haka ne Zayyad ya dauki Kamal a gurinsa.

Basu jima da kamamala cin abincin ba Jabeer ya bugowa Karima waya cewar ya zo yana kofar gidan, nan ta yi masa izinin ya shigo ya gaishe da Hajiya mana.

Mintuna kaɗan da kammala wayar suka tsinkayo sallamarsa kofar falon.

Kusan dukansu suka amsa, yana mai sanyo kansa falon har zuwa inda Hajiya ke zaune ya ƙarasa tare da russunawa ya gaisheta ta amsa fuskarta fal fara’a, kafin suka duk su gaishe shi, ya amsa yana zolayar Farida da ke sun saba daman.

Duban Karima ya yi a karo na biyu yana faɗin.

“Fatan dai kin shirya ba sai kin jamin jira ba?”

“Tun yanzu ka bari ka ɗan huta ai.”

Cewar Sakinah kenan ta faɗa tana mai wanzar da murmushi bisa fuskarta.

“Bar batun hutun nan Matar Aboki, na yi shi baki ɗaya a gidana.”

Da ya ke haka ya ke kiran sunanta tun bayan aurenta da Kamal.

“To shikenan sai ki tashi yallaɓiya.”

“Kin ji ki kema da alamu dai korata kike, da kin barni ai sai gobe ko zubi.”

Karima takai ƙarshen maganar tana mai duban Jabeer da ya yi kamar ma bai ji mai take fadi ba, duk kuwa da cewar ya jinta.

“Ki ce masa kin zo kenan mana, kin ga tashi ko kya samu gobe ya kawo mana ke da wuri”.

Karima ta miƙe tana dariya tare da gyara mayafinta ta rufa shi bisa kanta sosai, ta dubi Hajiya ta ɗan risina da faɗin.

“Sai da safe Hajiya?”

“To Allah tashemu lafiya, ya kuma kiyaye hanya ya kaiku gida lafiya.”

“Amin Hajiya.”

Suka amsa dukansu yayin da Sajidah da Farida suka rufo mata baya hannunsu ɗauke da leda viva ta kayan da Hajiya ta haɗa mata dana Sakinah, har tsakar gida Sakinah ta raka su suka yi sallama tana mai jajjada mata goben ta fito da wuri dan Allah, ta amsa da.

“Insha Allah babu matsala zaki ganni kuwa.”

Suka fice daga gidan, Sakinah ta nufi shashinta bata koma wajen Hajiyar ba, su Faridah kuwa har bakin mota suka raka su, suka sanya kayan a mota tare da kara yi musu sallama suka koma cikin gida.

10:30

Kamal ba shi ya dawo gidan ba sai  wajen ƙarfe goma da rabi, ya yi sallama cikin falon ɗakin Sakinah, falon shiru ba ka jin komai sai ƙarar fanka da yake akwai nepa lokacin falon gwanin kyau.

Kai tsaye ɗakin baccinsu ya nufa a gajiye, Sakinah na zaune gefan gado bata kwanta ba har lokacin ta yi tagumi tana mai zaman jiran shigowarsa, da fara’a ta tarbe shi tare da yi masa sannu da zuwa.

Ciki-ciki ya amsa kai tsaye ya shige banɗaki ya watso ruwa har lokacin tana nan zaune, kallo ɗaya ya jefeta da shi ya ɗauke kai zuwa wajen wardrobe ɗinsu, Kayan baccinsa ya ɗauko ya sanya ya nufo bakin gadon ya haye da nufin kwanciya.

Sakinah ta dube shi tana faɗin.

“Me za’a kawo maka?”

“Bana buƙatar komai.”

Ya bata amsa a taƙaice, ɗauke kai ta yi gefe tare da yin ajiyar zuciya kafin ta sake dawo da kallonta kansa karo na biyu tana mai cigaba da faɗin.

“To shi kenan, daman zaman jiran dawowarka nake, idan babu damuwa akwai maganar da na ke so muyi da kai a yanzu”.

“Zaki iya yin maganarki ina ji.”

Yana maganar yana janyo filo ya kwanta, amma ta san yana jinta tun da yace ta faɗa ɗin.

“Alfarma nake nema dan Allah, tun da kaga auren nan da zaka yi gidan ta daban nawa daban shi ne na ce mai zai hana anemo min aiki abin nufi ina so na fara aiki ni ma kasancewar zan dinga zama ni ka dai a gidan ka ga Farida na makaranta kuma aikin zai taimaka min sosai wajen rage wasu  nauyukan ko kaima zaka samu sauƙin wasu abubuwan musam…!”

“Kin ga dakata Malama..!”

Kamal ya katseta cikin tsawa yana mai tashi zaune ya zauna tare da ƙare mata kallo tsayin wasu daƙiƙu kafin ya cigaba da magana cikin ɓacin rai da ƙunar zuci.

“Har tsawon wanne lokaci zamu ɗauka kina wannan maganar? Wato kin samu an jiga ki ko? To ki sani ki ji kuma ki gani, ki kuma rubuta ki ajiye ni Kamal har gaba da abadan babu matar da zan aura ta dinga fita tana bin titi kullum tare da hulɗa a cikin ƙartin banza da sukan aiki kin ji ko?”

“Dan Allah ka fahimce ni mana aikin nan ba iya ni kaɗai zai taimaka ba har da kai ma, dan Allah?”

“Sabida ke za ki dinga ciyar da ni da shayar da ni ko me?”

“A’a bawai nufina kenan ba”

“Sakinah ina fatan baki manta yarjejeniyarmu ba ko?”

“E ban mance.”

“To akan me kike neman kawo min ruɗani a cikin al’amurana, nasan kin sanni kin fi kowa sanin waye ni Kamal, bani da irin wannan burin a tsarin rayuwata fatan kin fahimce ni.”

“Haba Kamal, Haba Dan Allah wannan wacce irin rayuwa ce? Sabida ka riga ka sai da soyayyarmu shi yasa ka zaɓi ka dinga ƙuntatawa rayuwata Kamal? Me na yi maka? Me na rageka da shi? Mene ba na yi maka? Wacce irin biyayya ce banyi a gareka ba? Me yasa ka zabi ka tauye haƙƙina da ya rataya a wuyanka a kulkum Kamal? Kai kullum ba’a iya maka? duk ta inda na ɓullo maka sai ka zame, me yasa Kamal? Me yasa dan Allah?”

Sakinah ta kifa kai bisa gado tana mai rera kuka, Kamal ya yi kwafa cike da ɗumbin tarin takaici ya miƙa tsaye yana faɗin.

“Me kike cewa? Me kike faɗi? Maimaita min mana?”

Yana magana haɗe da karkaɗa yatsun hannunsa, Sakinah ta yi banza da shi ta cigaba da kukanta, sanya hannunsa ya yi ya ɗago kanta da hawaye ya jiƙe fuskarta sharkaf kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa tare da faɗin.

“Har Allah ya kawo mu lokacin da zaki iya faɗar sunana gadan-gatsai babu sakaye babu komai, e lallai da kyau soyayyarki da son yin aiki ta yi tsamari, amma kinsan wani abu guda ɗaya, ba dai sai na amince za ki yi aikin ba? Kuma sai da yawuna zaki fita ko?”.

“To ki sani indai har kika kuskura kika sanya ƙafa a ko bakin falon nan ne da sunan zuwa aiki, ki sani tamkar kin sanya takalma ne masu ɗauke da igiyoyi uku ne kin fice da su, ko da wasa ka da ki sake kallon gidan nan matsayin gidan mijinki ina fatan kin fahimci zancena”.

Yana kai wa nan ya zari filon daya tashi daga kai ya nufi ƙofa da nufin ficewa har ya kusa isa bakin ƙofar ya dawo yana faɗin.

“Kuma kinsan gobe ne idan Allah ya tashemu da rai da lafiya na ke angwancewa, wato abin nufi za’a ɗauramin aure kin fi kowa sanin hakan, dan haka bani da asara kota misƙala-zarratan akan yankewar igiyoyin aurena da ke, domin gaba ta fi yawa…”

Yana kai wa nan ya juya ya fice abinsa ba tare da ya damu da shashsheƙar kukan Sakinah da ta ke ta faman rerawa ba, komawa ta yi takara kifa kai akan gadon ya yin da ƙarar sautin kukanta ya ƙara yawaita sosai, nan take wasu kaɗan daga cikin maganganun Yayanta kafin aurenta da Kamal suka fara wanzuwa game da kuwwa cikin dodon kunnuwanta tamkar ana buga ganguna.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 6Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×