Skip to content
Part 1 of 10 in the Series Jini Ba Ya Maganin Kishirwa by qurratulayn

Bismillahir Rahmanir Rahim

Falo ne ɗan madaidaici mai ɗauke da kayan alatu dai-dai karfi, dai-dai misalin rufin asirin mazauna gidan.

Ƙarar fanka ce ke ta shi a cikin falon kaɗan-kaɗan, hakan kuma bai hana tsinkayo maganar wata Dattijuwar mata ba, da ke zaune kan ɗaya daga cikin jerin kujerun da suke kewaye a falon, daga wajen ƙafafunta a ƙasan carpet wani matashin saurayi ne zaune a, duka-duka shekarunsa ba za su haura ashirin da takwas ba, a ido kuwa zaka yi tunanin bai kai hakan ba,  sabida zubi da tsarin tsamurmurin jikinsa dai-dai misali wanda ya da ce da doguwar fuskarsa, ba fari ba ne haka kuma ba zaka kira shi baƙi ba, kallo ɗaya za ka yi musu zuwa biyu kamanceceniyar kamar da suke zata wanzu a idanuwan masu kallonsu, hakan zai ƙara tabbatar maka da cewa Uwa ce da yaronta ke zaune.

Matar tayi gyaran murya irin nasu na manya tana mai cigaba da faɗin.

“Yanzu Kamal kai gani kake auren Hajiya Shema’u alkhairi ne a gareka? Matar da sai dai ka yi mata kallon Yayarka idan ma bata haifi kamarka ba, ba da ban haihuwa da bata yi ba ai yanzu da tana da sa’aninka…!”

Dattijuwar matar da ba zata wuce shekaru arba’in da biyar ba ta katse maganar da take yi cikin takaicin ɗan nata, da ke zaune kai ka ce abin da take faɗa yana shiga kunnensa.

Jin tayi shiru yasa shi ɗago da Kansa yaɗan dubi mahaifiyartasa kafin ya mai da kallonsa ƙasan carpet yana faɗin.

“Hajiya bawai inason yin auren nan da wata manufa ba ne, sai dan koyi da abin da manzon Allah (S.A.W.) ya yi ne, shima fa idan bamu mance ba Nanah Khadijah ta girmeshi nesa ba kusa ba, amma hakan bai hana shi aurenta ba, Hajiya ! Ni dai fatana a cikin wannan lamari addu’arki na ke da buƙata domin raya sunnar ma’aiki zan yi.”

“Hmmm Kamal kenan..! Ba zaka taɓa gane abin da a ke son ganar da kai ba, duka-duka yau fa shekara guda da aurenka da Sakinah ko ka manta ne?”

“A’a amma Hajiya na ke ganin hakan ba wani abu ba ne..!”

“Sabida ka kwallafawa kanka ɗaukan dala ba gammo ko?”

“Kamal tun da ka dage akan auren nan bazan yi jayayya ba domin bansan a bin da Ubangiji ya ɓoye a cikin auren ba, sai dai ina fargabar halin da zaka shiga kai da matarka ne kawai?”

“Hajiya kiyi min addu’a insha Allahu babu komai sai alkhairi.”

“To Kamal Allah ya tabbatar da alkhairin amma…! Shikenan dai ta shi ka je Allah ya taimaka.”

“Amin Hajiyata addu’a kawai dama ya kamata ki dinga yi min.”

Ya kai maganar bakinsa a washe kamar gonar auduga, kai ka ce kyautar aljannah aka ce an bashi.

Kamal ya ta shi ya fita daga falon fuskarsa wasai yana faman doka uban  murmushi, Hajiya Marka mahaifiyar Kamal tabi bayan ɗan nata da kallo tana girgiza kai a fili ta furta.

“Wanda ya yi nisa baya jin kira dai, inban da namiji namiji ne me zaka yi da matar da ta haifeka ko kuma ince yarinta dai, idan auren ya ke so ya duba yarinya dai-dai da shi mana, yanzu maganar mutanen unguwa ma ta ishemu banda ta ‘yan uwa.”

“Hajiya ya dai, ke da Ya Kamal ne ko?”

Cewar wata siririyar budurwa da ta fito daga ɗaki, kallo ɗaya zaka yi mata kaga yana yi da kama sosai da take da Kamal, hakan ne zai tabbatar maka da cewar ƙanwarsa ce.

Ta zauna gefan Hajiyar tana dubanta.

“Ke ma kinsan dai abin da ya ke sani faɗa a cikin kwanakin nan, Kamal ya kafe baya ji baya gani kan batun auren nan ya da ge dole sai ya yi.”

“To Hajiya banda abinki ki rabu da shi mana shifa ya ji ya gani zai iya sai ki zuba masa ido.”

“Amma Farida kina ganin hakan dai-dai ne? A ce Kamal duk cikar garin nan ya rasa matar aure sai Hajiya Shema’u !”.

“Hmm Hajiya ni dai da za ki bi shawarata ki sauwaƙewa kanki tunanin auren Kamal a ranki, kada ki jawo wa kanki hawan jinin da ba ki da shi, ba muji ba ba mu gani ba.”

“Shi kenan Farida amma abin ne dole ya dame ni.”

“A dai bar maganar Hajiya.”

Farida ta yi maganar tana mai miƙewa zuwa gaban TV ta kunnawa Hajiyar domin ta ɗebe mata kewa ita kuma ta faɗa kitchen domin yi musu sanwar rana.

Kamal na fita bakin titin layinsu ya ci karo da abokinsa kuma amini Zayyad suka gaisa ci ke da kewar juna.

“Ya dai mutumin naga yau cikin  farin ciki ka ke, ko batun aikin ne ya samu?”

“Kai dai bari Zayyad, Wanne batun aiki kuma, ga babban albishir ɗin da yafi min komai daɗi, Hajiya yau ta amince da batun aurena.”

Lokaci guda annurin kan fuskar Zayyad ya ɗauke, domin jin maganar ya yi tamkar saukar aradu cikin kunnuwansa, baki galala ya ke bin Kamal da kallon mamaki.

“Hajiya ta amince fa ka ce?”

“Yes, kana mamaki ko? Ni ma wallahi ko a mafarki ban yi tunanin amincewarta da wuri haka ba.”

“Waima na tambayeka, dama maganar auren har yanzu tana nan baka barta ba?”

“Ya kuwa za’a yi na barta Zayyad? Arziki ya tako ya kwankwasa min ƙofa har cikin gidanmu har makwancina ya zo ya sameni, ni kuma sai in sa ƙafa inture shi? Ina…! Ba zai yi yu ba Zayyad, ina haskoni cikin arziƙi madawwami arziƙin da babu yankewa million ashirin da wani abu ba wasa ba.”

Zayyad ya ja dogon tsaki ci ke da takaicin maganar abokin nasa ya dube shi da kyau.

“Kamal duk wani arziki idan ba alkhairi ba ne kayi addu’a Allah ya yi maka tsari da shi, domin idan har zaka samu arziki mai dorewa ta dalilin auren Hajiya Shema’u to aurenka da ita babu alkhairi a ganina, ka buɗe idonka ka farka daga mummunan mafarkin da ka ke me zaka yi da million ashirin? Ba yan ka ɓata sunanka, ka ɓata sunan danginku, me million ashirin zata yi maka akan auren wata can tsohuwar kilaki…?”

“Dakata Zayyad…! Ka iya bakinka, ka san hakan na ɗaya daga cikin abinda ya ke haɗamu ko? Idan ka san ba za ka dinga faɗin alkhairi ba to ka yi shiru, Annabi ma ya faɗa”.

“Kamal kenan! Shikenan Allah ya taimaka ya ba da sa’a, wanda yaƙi ji, baya ƙi gani ba.”

“Amin”

Kamal ya amsawa Zayyad cikin fushi kowannansu ya wuce ba tare da yiwa ɗan uwansa sallama ba duk da ce war basu ji daɗin rabuwar tasu a haka ba.

BAYAN SATI DAYA

Da sallamarsa ya sanya kai cikin gidan, bayansa yara ne biye da shi ɗauke da akwatuna biyu suka ajiye a filin tsakar gidan Kamal ya zaro naira ɗari ya basu ladansu suka fi ce.

Faridah da ke shirin fita daga gidan cikin shigar uniform hijab har ƙasa da alamu islamiyya ta nufa, ta dube shi tare da ɗauke kai ta gaida shi ta yi wucewarta ba tare da ta damu da amsawarsa ba, domin ita yanzu baki ɗaya haushi ya ke bata, mussamman ganin a kwatunan da ta yi a yanzu ya ƙara tabbatar mata har yanzu yana kan bakansa kenan.

Kamal yabi bayanta da tsaki, cike da tsantsar tsana da takaici, sabida shi duk wanda ba zai goyi bayan aurensa ba a yanzu to sun raba hanya kenan, baki ɗaya yakan ji ya tsani mutum domin gani yake babu wani babban maƙiyinsa a duniya sama da kai.

Ɗa kansa ya ja akwatunan har cikin falon Hajiyartasu yana mai kwalawa Sakinah matarsa kira ta fito da sauri zuwa falon Hajiya ta zube kan carpet tana jiransa domin tuni ya wuce cikin ɗakin Hajiyar zai kirawota.

Baifi mintuna biyar da shiga ba suka fito tare tana faɗin.

“Wai wane kaya ne haka ka kawo? Da za ka sako ni a gaba dole in zo in gani?”

Ganin akwatuna yasa ta yi turus tana bin Kamal ɗin da kallo, shi kuwa gogan neman guri ya yi ya zauna yana sosa ƙeyarsa.

Hajiya ta zauna tana duban Kamal domin jin mai zai ce.

“Hajiya kayan faɗar kishiya ne na Sakinah na kawo mata domin Hajiya Shema’u ta ce bata buƙatar komai illa sadaki, hakan yasa na fita haƙƙin Sakinan na siyo mata nata kayan.”

Ya mai da dubansa gun Sakinah.

“Ga kayan nan ki duba duk abinda babu kiyimin magana, sannan Hajiya gobe masu fenti za su zo suyiwa gidan fenti za’a gyara duk inda ya kamata.”

Kamal ya sunkuyar da kai yana sosa ƙeya sabida irin kallon da Hajiyar ke binsa da shi, amma hakan bai hana shi dakatawa daga maganar da ya faro ba.

“Hajiya nan da kwana uku fa za’a ɗaura auren ranar juma’a ken…!”

“Allah ya kaimu ya nuna mana.”

Hajiyar ta faɗa kafin ya kai ƙarshen maganar ta miƙe tana mai shigewa ɗakinta tabarsu nan zaune, tana shiga ɗakin Sakinah ta miƙe itama zata fi ce.

“Uban waye zai ɗauke miki kayan?”

Kamal ya dako mata tsawa, Sakinah ta juyo ta dube shi kawai ba tare data ce komai ba taja akwatunan zuwa ɗakinta.

Tana shiga yana sanyo kai shima cikin fushi ya fizgo gashin kanta yana faɗin.

“Duk baƙin cikin da zaki yi da wani munafukin kishi sai dai ki yi ki gama, aure babu fa shi, domin nan da kwanaki Kamal zai koma Alhaji Kamal.”

Ya kai maganar yana mai sanya dariya, Sakinah ta fizge kanta ta yi wucewarta ɗaki ba tare da ta tanka mai ba, Kamal ya ƙara zuciya yabi bayanta.

“Wato kin mai dani ɗan iska ko dan tsabar rashin mutunci da rainin wayo antaimaka miki ansiyo miki kayan amma babu ko godiya bare addu’a.”

“An gode Allah saka da alkhairi.”

Ta bashi amsa a taƙaice, ba tare da ta yi yunƙurin duban inda ya ke tsaye ba.

Kamal ya yi kwafa ya cije leɓe yana mai ƙarewa ɗakin nata kallo.

“Nan da kwanaki wadannan ko ɗaɗɗun kayan naki sai dai mukai bola ba zai yi yu Alhaji Kamal yana kwanciya akan ruɓaɓɓen gadonnan ba, ko da ya ke gida zan siya mai part uku kawai ke ɗaya amarya ɗaya Hajiya ɗaya komai sabo za’a zuba.”

Ya kai maganar yana mai sauke kallonsa akan kayansu da ta fara ninkewa kafin ya shigo kallo.

“Hatta kayanku sai dai Ku bayar ko Ku ƙona komai sabo zan siya domin ba za’a zo gidan Alhaji guda aga tsumma ba.”

Sakinah tayi murmushi kawai tana mai ci gaba da ninkin kayan.

“Au dariya na ke baki ma?”

“A’a Yallaɓai wace ni da yi maka dariya? wani abu na tuna kawai.”

Kamal zuciya ta zo masa wuya, ya yi kwafa tare da cijen leɓansa na ƙasa da ƙarfi, kafin ya fice fuuu daga cikin ɗakin yana mai jin haushin Sakinah akan a abin da take masa cikin kwanakin nan. Tama mai da shi wani hotiho ko hamago, kome zai yi mata domin ta ji haushi ba ta ji, ƙarshe ma shike dakon kayan takaicin ba ita ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×